Showing 123001 words to 126000 words out of 155081 words
na kirki yasa akoda yaushe suke zaman tattaunawa akan abinda ya shafi yankinsu dama ƙasar baki ɗaya. Wanda suna iya bakin ƙoƙarinsu sai dai sukan rasa a ina matsalar take akoda yaushe suna tufƙawa ana warwarewa?.
Akoda yaushe sai dai suyi zaman kawai su tashi, dan duk da kasancewarsu manya masu faɗa aji a hukumomin tsaro basu iya yin komai dake dai-dai da burikansu. Aikin da I.G ya fara ɗaura master a sirance yayi nasarane yaja ra'ayinsu gareshi har sukai kwaɗayin dinga sakashi ayyuka na musamman, duk da kuwa shi baida alaƙar aiki da su ta wani fanin. Ba yau kawai bane Master ya fara musu aiki. Yasha zaƙulo musu bara gurbi a cikin jami'ansu da manyan mutanen dake akan karagun mulki, kuma idan sukabi diddiginsu sukan samu abinda suke buƙatar.
Bai wani jimaba tare da su saboda halin da yake ciki, sun tabbatar ƙarfin haline kawai yakeyi badan lafiya ta ishesa ba. Sallama yay musu akan zai ƙarasa sauran ayyukan da suka rage masa na tattare dukkanin bayanai na kowanne fanni nan da kwanaki biyu insha ALLAH da zasu kasa komai a fai-fai dangane dasu A.G da ire-irensa. Daga haka yay musu sallama ya fito cike da dakewa kamar yanda ya shigo. dan baya buƙatar wani ya fahimci halin da yake ciki musamman akan ciwukan harbin dake tare da shi.
★★★★
Gudu yayi sosai akan titin, hakan yasashi isowa gidan cikin ƙanƙanin lokaci duk da kuwa ya ɗan tsaya a wani waje. Ledojin dake bayan motarsa na tsarabar su Habib ya ɗiba zuwa sashensu. Koda ya shigo suna baje a falo suna aikin da ya sasu, sai dai hakan bai hanasu shan shaftarsu ta hira ba kamar ko yaushe. Ko sallamarsa basuji ba sai da Sharifat ta nufosa da gudu tana kiran “Uncle oyoyo”.
Tattausan murmushi ya saki a karon farko yana ajiye ledojin hanun nasa ya kai duƙe dai-dai da tsahonta yana buɗe mata hannayensa. Jikinsa ta haye tana dariya, ya lakaci hancinta shima yana murmushi da faɗin, “Beauty ɗin gidanmu batai barci ba”.
Sharifat data makale masa kafaɗa tai yar dariyarta da kwantar da kanta kan kafaɗarsa. “Uncle ina game ne a wayan Yaya Idris”.
“Lallai ƴar gatan Yaya Idris”.
Ya faɗa yana kaiwa zaune batare da ya kula su Habib da sukai tsitt ba tun kiran da Sharifat tai masa. Ledojin daya ajiye ma Adam ne ya miƙe ya kwasosu. Leda ɗaya ya amsa a ciki ya bama Sharifat. “Tom ga wannan maza ki cinyesa duka ki kara ƙatuwa. Kina gamawa kuma ayi brush da alwalan barci ai addu'a. Ki gaidamin baba sai da safe”.
Cike da ɗoki ta amsa sheƙa da gudu tana faɗin, “Yeee thanks you Uncle ”.
Hannayensa ya harɗe akan ƙirjinsa yana binta da kallo da murmushi harta shige. Yana son yara matuƙa tun shima yana yaron, shiyyasa a yanzu bashi da babban burin daya wuce yaga jininsa a rayuwa. Numfashi ya ɗan ja da gyara fuskarsa ya gimtse yana maido dubansa gasu Habib. A kusan tare suka haɗa baki wajen gaishesa da tambayarsa jikinsa. Cike da nazartar yanayinsu ya amsa musu dai-dai idonsa na sauka kan Habib da yaƙi yarda ya kallesa.
Dukansu tarbiyarsa ce, dan haka ko laifi sukai masa a ƙanƙanin lokaci yake gano wanda ya aikata ɗin. Komai baice ba game da abinda ke a bakinsa ya miƙe, kai tsaye ƙofar fita ya nufa, sai da yaje gab fitar batare da ya juyo ba yace, “Habib ka sameni”. Daga haka yay ficewarsa.
Dama tun kallon da yake binsu da shi suka sha jinin jikinsu akan an masa laifi, kowa fatansa kar yazam shine ya aikata. Jin ya ambaci Habib ya sasu maida kallonsu kansa. “Yaron nan wane ruwa ka ɓallo mana ne?”.
Cewar Musbahu cikin ɗan tsoro. Harararsa Habib ɗin yayi yana miƙewa yabi bayan Master ɗin dan gudun sake wani laifin. Yana fita Adam yace, “Ni wlhy tun shigi da ficin danaga yanayi jiya akan waya nai tunanin hegen mai jajayen kunne wata tsiyar yake shiryawa. Sai dai banyi tunanin bahagon zaki zai ɓallo ba”.
Salis yace, “Ni nasan laifin daya aikata, amma ku jira dai ya dawo muji a bakinsa”.
Kansu duk suka jinjina alamar gamsuwa. Kafin su ajiye aikin gaban nasu a koma buɗe ledojin tsaraba cike da jin daɗi da farin ciki.
Habib kam koda ya fito can ya hango master ya ɗebo sauran ledan daya bari a motan. Nufarsa yay ya amsa suka sufi sashen nasa tare. Kamar yanda yabar falon a haka ya samesa. Ya kai zaune bisa kujerar 1seater yana ɗan dafe kansa da ke masa ciwo har yanzun. Yasan akwai issue ɗin jini tattare da shi, shiyyasa ciwon kan yaƙi barinsa sam. Bayansa ya kwantar jikin kujerar da zare mask ɗin fuskarsa ya ajiye, yana daura ƙafarsa ɗaya kan ɗaya, razanannun idanunsa ya zuba akan Habib dake tsaye kai a ƙasa.
“Miyasa ka aikata?”.
Yay maganar yana dauke idonsa a kansa ya maida ga takardun dake a saman centre table ya ɗebo su yana dubawa.
Habib da kansa ke ƙasa saboda girman laifin da ya aikata. Sanin halin yayan nasa akan buƙatar yin magana kai tsaye koda ta laifi ce, yace, “Itama taji irin raɗaɗin da kaji”.
Master da bai ɗago ba ya sake tamke fuska da cizar lip yana cigaba da aykin gabansa
“Yaushe na fara wasan banzan nan da kai?”.
Shiru Habib yay yana faman haɗiyar zuciya.
Master da yaji shiru ya ɗago ido ya dubesa fuska a tamke. “Ince da kai nake magana ko?”.
Yanda yay maganar aɗan zafafe yasa Habib ɗin girgiza masa kai. “Yaya hakan dazan mata ne kawai zaisa na huce da ga abinda ya faru, itama kuma zata kiyaye sake yin wani yunƙuri makamancin hakan.”
Idanu kawai Master ya zuba masa saboda mamakin Habib ɗin matuƙa. Shiko yaki yarda ya kallesa dan yasan yayi ba dai-dai ba.
Kansa ya sake maidawa ga takardun, “Hum aure kake buƙata kenan? Ko ka fara neman mata ne?”.
Da sauri Habib ɗin ya ɗago ya dubesa yana girgiza masa kai. “Wlhy Yaya ni ko ɗaya babu a raina. Kawai dai.....” sai kuma yay shiru bai ƙarasa ba
Takardun hannunsa ya ajiye ya maida hankalinsa gaba ɗaya garesa yana sake tsuke fuska irin yanda bai taɓa gani ba. “Ƙawai dai me?. ƙarya kakeyi, idan har baka neman mata taya kasan ka sakamin pills nasha dan naje ga mace koda babu niyyar haka a gareni.”
Habib da idanunsa suka kaɗa sukai jajur ya kai tsugunne gabansa. “Wlhy yaya ban taɓa aikata zina ba ka yarda dani, kamar yanda na faɗa maka kawai nayine dan karta sake tunanin kwatanta abinda ta aikata, sannan inason ku rayu har abada”.
“Kai da wa kukai shawarar aikata hakan a cikinsu?”.
“Ni kaɗai ne, dukansu babu wanda yasan abinda ya faru sai Yaya Abdull da ya bani”.
Idanu kawai master ya zubama Habib ɗin batare da ya sake cewa komai ba. Dama ya zargi babu wanda zaiyi wannan aikin garesa sai Abdull ɗin. Tunda aka ɗaura aurensa da Hibbah kullum cikin masa tsegumi yake su baby suke so da wuri. Habib da yaji yay shiru ya ɗago ya dubesa, shi kaɗai ne ya san ainahin fuskarnan a cikinsu, dan haka bai wani damu da ganinta a yanzu ba. “Yaya dan ALLAH kayi haƙuri. Nasan nayi kuskure tunma kan na aikata hakan. Inason naga kunyi zama irin na kowaɗanne ma'aurata da ita. Bana son ka rabu da ita saboda ƙyawawan halayyarta. Duk da ƙarancin shekarunta tasan kanta matuƙa kuma tanada tarbiyyar da kowanne irin nagartaccen namiji zaiso ta kasance uwar ƴaƴansa. Mu ɗin nan marayune, daga mace tagari kawai muke saran samun zuri'a mai albarka da zamu sake ginawa. Wadda zaka fara ginawa kuma itace ginshiƙin da zata riƙe tamu mu duka bakwai ɗin”.
Harararsa Master yay, da alamar dai ya huce ya ɗauke kansa. Matsowa Habib yay jikinsa ya ɗaura kansa bisa ƙafafunsa. “Please yaya karka rabu da ita dan ALLAH, inaji a raina idan tasan kai ɗin ko wanene zata sakko ta fahimceka ku rayu tare”.
Lumshe idanu yay bai tankaba nan ma. Shima kuma Habib bai janye kansa ba. Kusan mintuna biyu yaja ajiyar zuciya da furzar da numfashi, a hankali ya kai hannunsa bisa kan Habib ɗin ya shafa. Habib da wani farin ciki ya mamayesa ya miƙe da sauri ya rungumesa yana dariya. “Thanks you Mastern mu. I love you so much”.
Karan farko Master ya rankwashi kan Habib ɗin yana murmushi. “Mara kunya tashi mun a jiki tunda ka sadaukar dani ai.”
Cikin shagwaɓa Habib yace, “A'a Yaya ba duka na bataba fa. Ita rabi mu rabi.”
Nan ma murmushi kawai yayi baice komai ba. Sai da ya miƙe batare da ya dubesa ba ya nufi hanyar bedroom ɗin da Hibbah ke ciki yana faɗin, “Kaje ka sanar musu kowa ya nemo matar aure nan da wata biyu”.
Idanu Habib ya zaro, kafin yace wani abu Master ya shige. Wata shaƙiyyar dariya ya saki yana haɗiye sauran maganar a ransa ya juya ya fita da gudu dan kai rahoto.
Master da ke jiyo dariyar Habib ɗin baima san murmushi ya kufce masa ba shima. Ya ɗan girgiza kai yana ƙarasawa cikin ɗakin da sallama a bakinsa. Shiru babu motsin komai alamar barci Hibbah keyi har yanzun. Ya zare jacket ɗin jikinsa yana ƙarasawa gaban gadon ya zauna ta gefenta. Babu abinda yafi buƙata a yanzu kamar kwanciya. Sam bayajin ƙarfi da daɗin jikinsa dauriyace kawai. Dan bashi da burin daya wuce ya tattare aikin nan ya ɗauki matarsa suje su huta. Bargon da take ciki ya ɗan janye da kai hannunsa saman goshinta. Zazzaɓin ya sauka, a yanda numfashinta ma ke fita kawai ya isa tabbatar da hakan. Yaji daɗi har cikin ransa, fasa tashinta yayi dan karya takaloma kansa wata rigimar, ya ɗauka ledar daya shigo da ita ya sake fita. Babu jimawa ya dawo ɗauke tea. Zama yay yasha tare da maganinsa. Shima yay shirin barci ya haye gadon yana sauke ajiyar zuciya............✍🏻
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI......_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*
*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽
#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Chapter Forty one_*
.............*_WASHE GARI_*
Da asuba Hibbah ta rigashi tashi, dan cikin barci ya dinga jiyo motsinta a bayi. Tashi yay da ƙyar yana ambaton sunan ALLAH. Alhmdllhi jikin ya masa daɗi, dan magungunan da yake sha sun matuƙar taimaka masa. Koda ta fito kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta. Shima baice komai ba ya mike zuwa bayin yayo alwala. Koda ya fito shine yaja musu sallar, yana lure da yanda Hibbah taƙi yarda ta kallesa bai nuna ya damu ba. Bayan sun idar tana ƙoƙarin miƙewa ya riƙota ya zaunar a jikinsa. Kanta ta kauda gefe tana ƙoƙarin haɗiye ƙwallar da suka ciko mata idanu.
Hijjab ɗin jikinta ya cire, tare da riƙo fuskar tata cikin tafin hannunsa ya juyota garesa. “Nikam wai har yanzu ba'a huceba”. Yay maganar yana ɗaura kansa bisa goshinta”.
Duk yanda taso ƙwace fuskar tata hakan ya gagara. Dole ta nutsu waje guda, gashi tanason yin magana amma babu dama. Ta tabbatar datayita kusancin laɓɓansu zai iya sawa ya haɗu da nasa.
Fahimtar hakan da yayine ya sashi ɗaura laɓɓan nasa saman nata ya ɗan sumbata. Sai kuma ya janye goshinsa yana kallonta da ƙyau. Duk yanda yaso su haɗa ido ko tayi magana taƙi. Sarai ya fahimci borin kunyane kawai. Dan haka ya saketa yana murmushi.
Zumbur kuwa ta miƙe tabar wajen, har tana cin tuntuɓe da ƙafarsa.
“Ni dai kar amin asarar ɗan tayi na”.
Ya faɗa cike da shaƙiyanci yana binta da kallo. Cikin tunzura baki gaba ta haye gadon taja bargo ta rufe har kanta tana ƙunƙunj. Duk da dariyar dake son kufce masa dai ya danne abinsa baiyi ba. Sai ma ya miƙe shima ya hau gadon dan barci yake son ƙarayi. Hibbah data ƙudundune waje guda tai saurin buɗe idanunta a tsorace. Zata miƙe ya riƙota yana daidaita fuskarsu waje guda. Yatsansa ya ɗaura saman laɓɓanta ya shiga zagayawa dashi a hankali. Tsigar jikintane ya fara tashi amma sai ta danne taƙi nunawa.
Cikin ƙasa da murya sosai tamkar mai raɗa yace, “Mikike faɗa da banaji?”.
Hannunsa ta ɗan ture daga bakinta tana kumbura bakin kamar zatai kuka, “Ai dai ALLAH ya sani bance komai ba”.
Ganin zata juya masa baya tana maganar yay azamar tareta, laɓɓansa ya matsar gab da nata yana wani narke idanu, “Ni nasan kince ai”.
Kafin ta samu damar cewa wani abu ya rufe bakin nata, cikin shauƙin dake ɗibarsa ya shiga aika mata da sumbata a nutse data saka zuciyarta shiga tsoro harta fara tsuma. Duk da yaji a yanda jikin nata ke ɓari bai saketa ba ya cigaba da abinda yake har sai da ya tabbatar tayi laushi. Hagitsatstsun idanunsa da suka kaɗai sukai jajur ya ɗago yana kallon fuskarta, idanunta dake hawayen tsoron ya sumbata da jan nannauyar ajiyar zuciya.
“Nasan ni mai laifine a gareki ta kowacce fuska Muhibbat, sai dai inason kisani kece kika faramin laifi.”
A karon farko Hibbah ta buɗe idanunta ta kallesa, ga hawaye shaɓe-shaɓe. Sai kuma cikin sauri ta sake maidawa ta rufe, dan batason ganin idanun nan nasa da fuskar nan ta yaya Isama'il da ya saka, ga matsananciyar kunyarsa dake matuƙar cizon ranta da ɓargo. Batare da ya damu ba ya tura yatsun hanunsa cikin gashin kanta da sake matsota jikinsa. “Inason ki nutsu a yau kisan kowanene Muhammad Shuraim (Master). Asalin sunan shine Isma'il Aliyu Hikima”.
Cikin sauri Hibbah ta sake buɗe ido har yawu na sarƙe ta. Ganin ta miƙe zaune shima ya miƙe, ruwan dake a bedside ya ɗakko ya ɗora mata a baki. Babu musu tasha tana kallonsa tamkar idanunta zasu zubo a karon farko wajen kallonsa.
“Tabbas Isma'il shine sunan, kuma shine a gabanki yanzu haka da fuskar zahiri bata bogi ba Muhibbat.”
Wani irin bugawa ƙirjin Hibbah ya sakeyi. Cikin rawar jiki da son ƙin gaskatawa takai hannunta saman fuskarsa tana rumtse ido. Sake buɗe idon tai da sauri taja baya jikinta na sake ƙarfin karkarwa. “M....master kana nufin kaine Yaya Isma'il?”.
Kansa ya jinjina mata yana lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta.
“Na shiga uku ni Muhibbat wane irin rikitaccen mafarkine wannan nake a ciki?. Impossible hakan ta kasance”.
Tai maganar tana ƙoƙarin sauka a gadon. Saurin riƙota yay ta dawo jikinsa. “Shiyyasa nace ki nutsu ki saurareni”. Ya faɗa a cikin kunnenta da wata murya mai taushi tamkar bashi ba. Batare da ya bata damar sake cewa komai ba ya cigaba da maganarsa. “Sunan mahaifina Aliyu..........” tiryan-tiryan ya cigaba da bata labarinsa tamkar yanda ya bama su Ummi. Sai kuma ya ɗora da “A farkon shigata tawagar su Master an taɓa kamamu, lokacin ina farkon shiga aji shida na sakandiri. Tunda aka kawomu police station wani babban jami'i keta kallona har kallon ya gundireni naji haushi. Fahimtar hakan da yay yasashi ɗauke kai yana murmushi. Bansan yaya akai ba bayan kamar awa guda aka fiddani ni kaɗai kuma babu wani bayani. Hakan ya tsayamin a rai, daga baya kuma saina watsar na cigaba da harkar gabana.”
“Bayan na kammala jami'a na kaima wanda ya ɗauki nauyin karatuna result ɗina dan ya gani, tare da sake masa godiya, sai naci karo da jami'in nan da yayta kallona a station, abin ya ɗauremin kai, na kuma sha mamaki amma sai na danne. Yaji daɗi ya kumayi farin ciki a take anan kuma yaymin tayin aiki saboda ganin yanda nake da matuƙar ƙwazo da kaifin basira akan harkar kimiya da fasaha. Babu musu na amsa cikin farin ciki da murna dan kuwa aiki ne na jami'an tsaro. Na miƙe cikin farin ciki zan tafi ya dakatar da ni ta hanyar faɗin, (dakata yarona ai bamu gama magana ba). Komawa nai na zauna ina basa dukkan hankalina.”
“Yarona zaka zama jami'in ɗan sanda amma na sirri, dan haka zakai aiki kafaɗa da kafaɗa ne da mu ƴansanda amma a sirrance batare da kowa yasan wannan ba sai ni. Inada abubuwa masu yawa dake cimin rai da zuciya, sai dai ina matuƙar jin tsoro da shakku akan wanda zan ɗora yaymin. Wannan yasa a randa na fara ganinka a station naji a raina zaka iya. Hakan yasani komawa na biya maka kuɗin karatu dan a cikin idanunka na fahimci da gasken zaka iya. A yau zan sanar da kai wani abu, duk