Showing 48001 words to 51000 words out of 155081 words
ta haifeni a wani dare na juma'a. Ina canyara kuka kakana na yanke jiki ya faɗi, faɗuwar da daga ita ko shurawa baiyi ba dan ya mutu. Hakama mahaifiyata tunda ALLAH yasa na fito da ga jikinta ta tada kanta da ƙyar ta kalleni hawaye na kwaranya a idanunta, tai murmushi mai ciwo da faɗin, “ALLAH ya albarkaci rayuwarki, ya ɗaga darajarki, ya kareki da dukkan sharri. ya saka haƙuri da juriyar duk abinda zaki gani a rayuwarki cikin zuciyarki” sai ta shafa kaina ta maida kanta ta kwantar shikenan anyita an gama.”
“A rana ɗaya aka binne gawar kakana da mahaifiyata kusa da juna, yayinda aka barni hannun kakata da itama ta koma tamkar zautacciya. Bazance ban samu gata ba a hannun kakata, domin kuwa itace ta shayar dani har na tsahon shekara biyu. Sai dai sam bata son ganina, tunda ta yayeni bata sake yarda na raɓu jikinta ba. Kullum cikin tsangwamata take da nuna ƙyamata tamkar yanda jama'ar gari kemun. Babu maison ganina, babu maison na raɓu ɗansa nai wasa. Nasha cin duka wajen iyayen yara da yaran kansu batare da nasan laifin dana aikata garesu ba. Shekarata biyar a duniya mahaifina ya dawo kauyenmu. ko hutawa baiyiba kakata najin labari ta ɗaukeni ni da kayana taje ta damƙa masa batare da tace uffan ba ta juya ta tafi. A kuma wannan daren ta gudu a garin ta bar ƙannen mahaifiyata su Kawu Hannafi. Har yau ɗin nan da nake baku labari babu wanda ya sake jin labarinta.”
“A yanda mahaifina ya amsheni babu musu ya tabbatarma jama'ar gari ya san ni ɗiyarsa ce, dan kakata na tafiya ya ɗaukeni ya damƙa hanun mahaifiyarsa, ya kuma tabbatar mata dole ta riƙeni dan shima ya dawo gida da zama, dama wani aikine ya sashi tafiya bawai dan yayima mahaifiyata fyaɗe ba. Babu wanda ya iya cewa ƙala saboda tsoron da suke masa. Sai dai dukannin haushinsa da takaicinsa akan saukeshi kainane a gidan. Shima ba sauki nake samu a garesa ba, dan babu irin kalar azabar da bayamin, sai dai kuma wani yana taɓani inhar ya gani sai ya rama mani.”
“Haka na cigaba da rayuwa cikin azaba da ƙasƙanci, a wajen baban mahaifinku malam Hamza ne kawai nake samun sauƙi. Dan shi mutum ne mai ilimin addini. harma almajirai ke garesa. Sai dai sam bai dace da mace ba (Hajiya mama). Hajiya mama asalinta ba ƴar garin bace, acan indai yay almajiranci aka aura masa ita, hakan yasa ɗanta na fari da suka haifa mai suna Aliyu tun daga yaye da aka kaisa garinsu ba'a dawo da shi ƙauyenmu ba. Sai dai lokaci-lokaci yakanzo ya gaishesu.”
“Mahaifinku Aliyu shine mutum na biyu da yake nunamin tausayi bayan kakanku kuma kawu na, dan duk sanda yazo kauyenmu nakan shiga cikin farin ciki matuƙa. Shine mutum na farko da ya fara koyamin karatun boko, yayinda kakanku kuma kawu na malam hamza yake koyan na addini duk da matarsa bataso. Saboda tsabar ƙiyayyar da Hajiya mama kemin a duk sanda naje gidan sai ta saka Halilu ƙanin Aliyu yamin dukan tsiya. Dan haka tun fil azal bama shiri da Halilu sam. Shakuwarmu da Aliyu ta cigaba da faɗaɗa a duk sanda yazo hutu ƙauyen. Tun mutane basu fahimta ba har kowa ya fahimta, dan yazamto duk sanda Aliyu yazo bashi da abokin yawo sai ni, akoda yaushe muna tare can bakin fadama. Dare ne kawai ke sakamu rabuwa. A randa labari yazo kunnen Hajiya Mama kowa yaga tsantsar masifa a ƙauyen nan. Dan haukacewa tai matuƙa taita bala'in da har sai da Babana ya kama Halilu yay masa dukan mutuwa saboda dukana da yayi. In takaice muku ranar ɗan ƙaramin yaƙine ya kusa tashi a ƙauyen mu. Karku manta na faɗa muku babana mutum ne da lamarinsa sai addu'a. Duk da kuma yana nunamin halin ko in kula kowa yasan yana sona. Dan soyayyar mahaifiyatace gaba ɗaya ta dawo kaina. Sam yaki aure, hasalima yayi alwashin tunda Mahaifiyata ta bar duniya babu aure a sanadinsa shima har abada bazai auri wata mace ba, zai karasa rayuwarsa a hakan dan itace ta farko da yataɓa so kuma itace ta ƙarshe.”
“Bayan lafawar komai Hajiya mama ta haramtama Aliyu zuwa ƙauyenmu saboda ni, hakan ya ɗagamin hankali matuƙar gaya. Nayi kuka harda kwanciya ciwo, amma babu abinda ya canja. Haka na haƙura na cigaba da rayuwa a ƙauyenmu cikin halin tsangwama da ƙyara da ƙyama. Kawu Hamza ne kawai nake jin sanyi da sauƙi a garesa. Sai ko babana idan yaso haka. Na kasa samun miji a ƙauyenmu. Dukan sa'annina sunyi aure wasuma sun hayayyafa, kusan dai aure irin nada kuma na mutanen karkara. Duk wanda zaizo da nufin sona sai dai yay yunƙurin lalatamin rayuwa, dan a cewarsu ni ɗin ƴar shege ce. Hakan na matuƙar bani tsoro. yana kuma sakani kukan da babu mai lallashina. Ban kuma shiga tashin hankalin rayuwa da garari ba sai a shekarar da mahaifina ya rasu. Lokacin inada shekaru goma sha tara cif a duniya tamkar yanda Tanee take a yanzun. Duk da ba kulawa yake bani yanda ya kamata ba shi ɗin garkuwa nane. Dan ko a cikin gidanmu shakkarsa nasa a ragamin wani abu. Dama dangin mahaifiyata ba nuna sunada alaƙa dani sukeba. Sun matukar tsanata saboda mahaifiyarsu acewarsu ta gudu ne dan ni, sun kuma rasa ƴar uwarsu dalilin mahaifina. Rayuwa ta ta sake shiga matuƙar garari dan waɗanda suke ɓoye maitarsu akan mutuncina sun fiddosa. Ciki kuwa harda.....”(kuka ya ci ƙarfinta)
Da ƙyar ta iya haɗiyesa saboda ganin yanda su Hibbah ke kuka. Hatta da Yaya Umar duk jarumtarsa kuka yake rurus. Ummi ta cigaba da faɗin, “Harda Halilu. Dan shine ya kaimin hari na ƙarshe har gida a wani dare. Sai dai ALLAH ya kuɓutar dani saboda ihun da nayi har kakana ya fito shi da kawu Hamza (kakanku). Duk da naga wanda ya shogomin ɗin sai ban faɗa ba, nace kawai ban sanshi ba. Bawai dan ina tsoron faɗar bane, kawai dai ba yaune ranar da Halilun ya fara min irin wannan titsiyen ALLAH na kuɓutar dani ba. Na yau ɗinne dai yaso fin na ko yaushe muni. Washe gari malam da kansa yace na dawo kwana ɗakin kusa da shi, hakan ya baƙanta ran hajiya mama taita masifa a ɓoye, dan tana tsananin tsoron malam. Anyi haka da kwana biyu sai ga Aliyu. Bansan yanda zan musalta muku halin dana shiga ba. Sai dai tabbas naci kukan farin cikin ganinsa matuƙa gaya, shi kansa har ƙwalla yayi, sai dai yayi ƙoƙarin ɓoyemin.”
“Babu zato babu tsammani bayan sakkowa massallacin juma'a sai jin an ɗauramin aure da shi kawai nayi. Firgici ya sakani yanke jiki na faɗi a sume sai da aka yayyafamin ruwa. Cikin ƙanƙanin lokaci labari ya karaɗe gari, yayinda Hajiya mama ta rikice da ihu da kururuwar sam bata yarda ba da wannan haɗin. Babu yanda ta iya dan malam yafi ƙarfinta. Hasalima ana kammala sallar la'asar ya saka Aliyu tattarani da gani sai kayan jikina muka baro ƙauyenmu. Barowar da ban sake komawa ba sai rasuwar malam da kakana data faru kusan lokaci guda. Bazance muku banyi murna da baro ƙauyenmu ba a lokacin, domin kullum hakan shine mafarkina. Nasha aunawa a raina dama na gudu idan har irinsu Halilu sun cigaba da bibiyar mutuncina, sai gashi ALLAH yaymin sutura na barosa tare da igiyar aure da miji ɗan gaske irin mahaifinku.”
“Nayi matuƙar mamaki lokacin da muka shigo garin nan naga Aliyu ya kawoni wani madaidaicin gida mai ɗakuna biyu da kitchen ƙarami sai toilet da rijiya a tsakar gida. Babu komai a gidan sai katifa a ɗaki ɗaya da ƙaramar Wadrobe ɗin kayansa. Ɗayan ɗakin kuma kafet ne malale kawai sai tv babu kujeru. Sai ƴan kayan girki a kitchen ɗin da alamar shike abinci da kansa. Bai barni na huta ba sai da ya zagaya dani lungu da saƙo na gidan, tare da min bayanin komai na amfani. Da kansa yay mana girkin abu mai sauƙi mukaci a ranar, bayan ya yambayeni girki nace ban iya ba. Dan tunda nake ko zuba manja a wuta babu wanda ya taɓa sakani a ƙauyenmu. Aliyu shine ya koyamin girki, shine ya koyan aikin gida, ya sakani islamiyya. Ya kuma cigaba da koyar dani karatun boko. Kamar yanda bai taɓa zama yamin tambaya akan bayan rabuwarmu ba, nima ban taɓa masa tambaya akan ƙin sake dawowarsa ƙauyenmu ba har ALLAH ya albarkacemu da samun ciki. Ya nuna tsantsar murnarsa da farin ciki akan wannan ciki. wadda har ta ban mamaki sosai, amma sai na shanye mamakina nima ina maijin daɗin zanga jinina bayan mahaifina dana rasa.”
“Na cigaba da rainon cikin Muhammad a ƙarƙashin kulawar Aliyu har ya cika watan haihuwa, sai a lokacinne kuma wani baƙo ya taɓa zuwa wajenmu da ga ƙauyenmu. Dan kuwa babu zato babu tsammani sai ga Hajiya mama da Halilu. Cikin farin cikina na nuna murnar ganinsu, sai dai tun a tsakar gida Hajiya mama ta katse murnar tawa ta hanyar daka tsalle ta dire tana kallon cikin jikina. Aliyu da abin nata ya bashi mamaki ya tambayeta ko lafiya. Kai tsaye ta nuna masa ciki da tambayar ina aka samosa?. “Mama ƙyautace da ga ALLAH ya bamu mana tunda jinin ɗanki ne”. Aliyu ya bata amsa kai tsaye dan shi ba mutum bane mai ɓoye-ɓoye ko kwana-kwana a magana.”
“Cikin daka tsawa tace “A gidan ubanwa ya zama jinina? To idanma zaka dawo hankalinka ka dawo. duka-duka ƙaddararren auren naku watansa takwas kenan ace da wannan tulelen cikin mai kama da shekarre. Sai dai idan ɗan shege ne aka zomaka da shi da ga waje kamar yanda aka samota itama za'a nana maka”. Wannan magana ta tashi hankalin Aliyu dani kaina, ya shiga rantsuwa akan sam ba haka bane ba, amma sam hajiya mama taƙi saurarensa. Hasalima washe gari suka juya ƙauye ita da Halilu. Babu shiri shima Aliyu ya bisu batarema dana sani ba. Dan nima tunda hajiya mama ta ɓunta maganar jingina cikina da bana Aliyu ba sai ciwo yaymin rijif. Ba ƙaramar ƙurace ta tashi akan cikin jikina ba. Har takai da malam yace a jira na haihu sai a san mai gaskiya. Cikin amincin ALLAH kwana goma sha ɗaya dayin wannan al'amari sai ga naƙuda. Batare da ALLAH ya ƙaddaramin shan wahala ba na haifo Muhammad Aminullahi. Wanda tunma yana cikin jininsa daka kallesa kaga Aliyu tamkar yayi kaki ya ajiye. Bakin kowa ya mutu tun daga haihuwar Aliyu, har takai dangin hajiya mama sunzo taron suna, kafinma taron wata tsohuwa tazo ta zauna dani dan malam yace koda wasa kar Aliyu ya kaini ƙauyenmu. Babu kowa a dangin mahaifina da mahaifiyata bayan malam da Halilu. Duk da hajiya mama bataso ba Aliyu yayi bajinta dai-dai karfinsa.”
“Bayan haihuwar Muhammad abubuwa da yawa sun buɗe mana musamman ƙofofin arziƙi. Dan abin tamkar roƙo sai ga alkairai nata shigowa, cikin shekara biyun danai ina shayar da shi harmun canja gida, Aliyu ya sai mota. Wannan arziƙi shine ya sake saka damuwa tsakanina da Hajiya mama. Dan gaba ɗaya ta tashi hankalinta akan bazanci ni kaɗai ba sai Aliyu ya ƙara aure. Shi kuma da yake mutum ne mai taurin tsiya yace bashi da ra'ayin zama da mace fiye da ɗaya yayi kenan dan yanaso na. An buga an buga yaƙi. Ganin fitinar ma tayi yawa sai ya daina zuwa ƙauyen bisa shawarar mahaifinsa. Sai dai kuma an gudu ba'a tsira ba, dan kuwa hajiya mama na ganin an kulleta ta ko ina sai ta canja salo, ta kwantar da kai ta nuna nadama a lokacin da akace mata ina da wani cikin. Da farko malam bai yarda da ita ba, sai da akaja lokaci ina gab da haihuwa bansan yaya akaiba sai ga Halilu da jakar kaya wai yadawo zama da mu zai dinga tsare shago da Aliyu ya buɗe a kasuwa tunda shi aiki baya barinsa zama. Hankalina bai tashi ba, dan ni a tunanina ai yanzu na wuce da duk wani shaiɗancin Halilun na kafin aure na. Dan haka na amshesa hannu bibbiyu na kuma saki jiki da shi. Shima kuma sai ya kwantar da kai yay tamkar babu komai a ransa. A wanann karon ma na haihu lafiya namiji, wanda yaci suna Abubakar, shima dai gaba ɗaya ya kwaso kamanin Aliyu. Tun bayan haihuwar Abubakar Halilu ya fara fiddo min wasu sabbin halaye, sai dai sam baya yarda yayi a gaban Aliyu da Malam ko gaban mutane. Iya ni kaɗai yakemawa sai Muhammad da zaita duka babu gaira babu sabar, hatta da Abubakar na goye bai ƙyale ba. Ko kallon inda yake banayi balle na nuna nasan yanayi ɗin. A haka na sake samun ciki na uku, shima na haifi Umar. A wannan haihuwa kam banjita da daɗi wajen Hajiya mama da danginta ba. Dan ƙiri ƙiri suka dinga kwaɓamin magana na mamaye musu ɗan uwa. Babu mai cin arziƙinsa sai ni da ƴaƴana. Duk alkairan da yake musu da yanzu ya bari komai sai ni. Haka suka dinga tsogumi har sai da abin nan ya sani kuka, sai dai ban yarda na sanarma Aliyu ba dan ba'a gabansa sukai ba. Ina da tsohon cikin Usman ne muka dawo wannan gidan, dan haka lokacin dana haifesa sai yazam ƴan uwa sunzo suna haɗe da tayamu murnar sabon gida. A wannan zuwa ma dai ba daɗin naji ba. Dan maimakon tayani murnar haihuwa sai habaicin ina haihuwa bi da bi ba hutu, wai inayine danna mamaye komai na Aliyu shiyyasa duk sai ƴaƴa maza. A wannan karon kam ɓacin ran dana shiga har sai da takai malam yazo da kansa. Dan gaba ɗaya na sauya harshi Aliyun yama kasa gane kaina. Na tubure masa akan ya ƙara aure kozan sami sassaucin cin kashin nan nasu. Musamman ma Halilu da ya zama mai fuska biyu, a gaban malam ya nuna babu wadda yafi ƙauna da so sama da ni da ƴaƴa na. Dan aurensa ma da aka saka da matar daya samo acan cikin dangin hajiya mama yace nice uwar biki. Nasan a zancen nasa akwai manufa, amma sai na watsar da shi kawai. Malam ya lallasheni da kalamai masu daɗi harna huce komai ya wuce muka koma yanda muke da Aliyu.”
“Hidimar auren Halilu ce ta sake canja komai. Dan kuwa naci matuƙar wahala a lokacin. Komai aka nema sai suce a zo wajena shi da hajiya mama. Ko ɗan kwali ƙin saya sukai balle ƙwayar abinci. Idan nace ma Aliyu yayi yayta faɗa akan ai ya basu kuɗaɗe masu nauyi na hidimar nabar damunsa. Haka na shiga tsaka mai wuya a tsakanin. Duk ɗan abinda nake samu na haihuwa na ƙwaƙule nai hidimar Halilu dan nasan bazan taɓa fita a garesuba idan ma na nuna Aliyu baiyiba. to ashe yin danayi ma ba mafita bace dan sabon zancene ya tashi akan eh da gaske na mamaye komai ɗin. Bani da abin cewa dan haka nai musu shiru akai biki aka ƙare lafiya amarya ta tare a tsohon gidanmu da muka taso, dan da hajiya mama ta matsa anan zasu zauna tare damu tunda akwai ɗakuna. Aliyu yace sam bai yarda da wannan gwajin gwalar ba. Salon haɗa rikici. indama kowa da part nashine sai ya amince. Amma flat ɗaya ne a gidan iya na iyalinsa sai BQ. ita kuma tace Halilu bazai zauna BQ da matarsa ba ni ina ciki inacin daɗi. Bayan ƙurar data tashi ta lafa dan malam ya tsawatar suka yarda Halilu ya zauna acan. Sai dai kuma duk wani abu da zasuci acan bazai saya ba, sai dai yazo nan gidan direct ya ɗiba koda kuwa gishiri ne. Ban taɓa faɗama Aliyu ba sai da ya gani da idonsa. ranar naga asalin faɗansa. Dan murje ido yay yayma Halilu tas har nima na samu rabona a ciki. Wata sabuwar ƙurar ta sake tashi akan wanann magana, har takai Hajiya Mama ta nema Aliyu ya sallami Halilu da ga kasuwa shima ya rinƙa juya na kansa, kokuma su dinga raba ribar duk abinda aka tara a ƙarshen shekara. Ƙince musu komai yay akan hakan, yaƙi kuma bashi kuɗin ya ƙi sallamarsa. Shine dalilin da yasa Halilu ke ganin nice na hana shi da hajiya mama. Duk da kuwa a shekarar Aliyu ya biya mata hajji ita da malam da shi sukaje. Wannan karon na samu hutu, dan tun Usman babu wani labari. Hakan yamin daɗi, dan na samu sauƙin wasu fituntunin, duk da shi kullum mahaifinku cikin tambayata yake wai yaji shiru, danshi mutum ne mai son yara matuƙa. Shiyyasa kuka kasance ƴan gata a wajensa. Komai na buƙatunku baya sakaci da shi komai ƙanƙantarsa. Wanann yasa ake ganin ya lalace a kanmu. Shekara na zagayowa ya sake biya mana hajji ni da shi mukaje. Muna dawowa ya sayamin mota tare da danƙamin wani ƙaramin gida yace na zuba haya, sai jari na sana'a.”
“Musalta muku halin da na shiga awanan tsakanin bazai musaltu ba. Dan saida na gwammace da bai baninba. Dama akan tafiyarmu hajji ansha dabi hajiya mama tace bata yardaba sai dai ya biya musu shi da Halilu. Bansan miyazo kan Halilu a lokacinba shi ya nuna goyon bayan naje, harda nunama hajiya mama bayajin daɗin abinda takemin, ai koba komai na haihu da Aliyu ya kamata a ɗagamin ƙafa zuwa yanzun. Hakan da yayi ya saka malam jin daɗi. Tun daga sannan ma suka koma ɗasawa dan shi malam ya yarda da tuban Halilu ɗari bisa dari. A cikin wannan tarnaƙin na samu cikin Ammar. Wanda yazomin da matuƙar wahala da jigatuwa. Bani kaɗaiba hatta mahaifinku yaji a jikinsa kafin ALLAH ya sa na haihu ko nace akaimin cs aka cirosa. Babanku na ɗaukarsa ya gansa ƙato da shi ga kamanninsa sak nashi tako ina sai cewa yay “Lallai kaci suna Aliyu gadanga kodan wahalar daka bama matata”. Hakan ya sani murmushi, dan har cikin