Showing 150001 words to 153000 words out of 155081 words
yake sanar musu suyi sauri harsu Master sun iso za'a wuce. Babu ɓata lokaci mai kwalliyar ta kammala mata komai ta fito tsaf tamkar wata ƴar daren sha biyar. Ga ƙibar da tayi ta ƙara ƙawata tsarin shigar tata masha ALLAH.
Ummi kanta da su Zahidah kasa haƙuri sukayi sai da suka tanka wannan ƙyawu da Hibbah tai. Su Yaya Muhammad dake jin wani ɗunbin farin ciki suka zagayeta suna zuba mata ruwan hotuna.
A haka suka fito da Hibbah harabar gidan inda su Master ya ke tsumayen fitowar ta su. Akan su Habib da ke zagaye da shi cikin shiga iri ɗaya tamkar wasu bodyguard ta fara sauke ido. Taja gajeren numfashi da satar kallon mai gayya mai aiki dake sanye cikin wasu Haɗaɗɗun suit sky blue kalar kayan jikinta. Shi kansa tun fitowar tasu yay mutuwar tsaye yana jan wani hargitsatstsen numfashi da ajiyar zuciya har su Habib na iya jinsa.
Kunyar Ummi data Yaya Muhammad ta hanashi xuwa ya tareta ya rungume ko zaiji nutsuwar abinda yakeji na ratsa ɓargonsa zuwa cikin jini. Maimakon ya nufi Hibbah sai ya matso kusa da Ummi cikin girmamawa ya gaisheta. Ummi ta amsa cike da fara'a tana sanya masa albarka shi da su Habib da suka ƙaraso suma suna gaida Ummin.
Ya gaisa dasu Yaya Muhammad ma sama-sama kowa ya shiga mota dan jiransu akeyi. Duk da tsokanar da su Habib kema Hibbah bata iya cewa komai ba dan gaba ɗaya idanun Master sun hanata sukuni. Duk yanda yaso daurewa ya kasa. Suna shiga motar da Habib ya kawosa a ciki ya jawota jikinsa ya rungume. A tare suka saki ajiyar zuciya suna sake ƙanƙame juna har yana mamakinta. Habib dai yi yai tamkar bai gansuba yaja motar suka fice a jere da sauran nasu Yaya Muhammad.
A cikin kunnenta ya raɗa mata “I miss you so much Baby luv”.
Hibbah da ɗunbin kewarsa da kunya ke zagaye da ita ta sake cusa kanta jikinsa tana mai shaƙar ƙamshin turarensa da yay mata matuƙar daɗi. Itama a hankali tace, “Ni dai bana kewarka”.
Sassanyan murmushi ya saku da ɗago fuskarta ya sumbaci goshinta. Kasancewar Habib a wajen ya sashi daurewa bai tsotse janbakin ba. Bai kuma sake magana ba har suka isa wajen taron daya gama cika fam da nutane.
Tarba ta musamman ta mutunci suka samu. tare da wajen zama da aka tanada dominsu. Ba'a wani ɓata lokaciba wajen fara gudanar da taron daya tara manya-manyan mutane. Inda aka gabatar da abubuwa masu yawa tare da kyaututtuka ga su Master. Aka kuma tayasa murnar aure da kowa ke ɗauka yanzune yayisa. Daga haka akaci akasha taro ya tashi lafiya.
A yanzu kam dole Hibbah tabi su Ummi suka koma gida tare dan ƙarasa shirin miƙata gidanta nan da anjima. Dan acan ɗinma sun baro baƙi sosai dan ma su Mama Jiddah nan dasu Ummansu Zahidah.
Kamar da wasa sai gashi anyi wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan biki a gidan su Hibbahn, anci ansha an rakwashe an ƙwalle musamman su Habib da suka jone da Ammar sukasha shaftarsu. Zuwa takwas na dare kuma aka haɗu a babban hall ɗin da aka tanada domin gudanar da liyafar cin abinci. Anan ɗin ma ba ƙaramin zauta Master gayun na Hibbah yayi ba. Dan gaba ɗaya ta wani canja masa tamkar ba ita ba. Itama kanta gayun nasa ya matuƙar ɗaukar hankalinta danko sanye yake da shadda ƴar ubansu dataji ɗinkin zamani mai ɗaukar hankali. Anci ansha su Habib sun cashe a filin rawa sai kace wasu ƴan daudu😂. Tun Master na hararsu harya shiga sahun masu dariya duk da ƙoƙarin dannewa da yay tayi. Ƙarfe goma dai-dai taro ya tashi, daga nan kuma aka ɗunguma rakkiyar amarya sabon gidansu inda Master ya ɓoye su Ummi. Zuwa yanzu an gama komai gida ya haɗu matuƙa kai kace wani ƙaramin estate ne. Dansu Musbahu kowa da sashensa matan aure kawai suke jira. Mutane basu wani zauna ba kowa ya kama gabansa akabar amarya da angonta dasu Khalid da suma gajiya ta sakasu kwanciyar wuri a sashin baƙi da suke zaune yanzu kafin matayen nasu su shigo kowa ya koma nasa sashen.
Master da dama yana gidan abinsa dan tare suka taho da ƴan rakkiyar amarya suna tafiya ya nufi ɗakin Hibbah da kayan tsarabar da aka tanadar mata dan yaga bataci komai ba a wajen liyafar.
Tana zaune a tsakkiyar gadon tana kwasar kuka kai kace yau ɗin aka fara kawota gareshi. Kayan hannunsa ya ajiye ya nufi gadon yana murmushi, cikin neman tsokana ya ɗaga mayafin yana faɗin, “Haba Hajjaju keda kika dawo wajen mijinki minene na kukan?”.
Hannu tasa ta ture nasa tana ƙoƙarin juya masa baya ya riƙota yana sakin wata siririyar dariya data nema narkar da Hibbah, dan a cikin kunnenta yakeyi. Ƙoƙarin haɗe bakinsu yakeyi tana ture masa kai cikin bore hardai ya samu nasara. Salon da yake mata da kuma halin da take a ciki yasata miƙa wuya har tana maida murtani. Sai da ya tabbatar ya sakata yin laushi sannan ya barta yana sauke ajiyar zuciya. Kunya ta sata saurin sauka a gadon ta nufi toilet dan fitsari takeji.
Ta kammala tana ƙoƙarin fitowa sukaci karo da shi zai shiga shi kuma. Hanunta ya kama yana binta da wani kallo ƙasa-ƙasa daya sata kauda kanta daga kallon nasa. “Muje muyi alwala”. Ya faɗa acan ƙasan maƙoshi tamkar mai gudin ajisu. Ba yanda ta iya dole ta bisa suka koma. koda suka yo alwalar suka fito tare suka gabatar da salla. Yaja musu addu'oi masu tsayi na zaman lafiya da haƙuri da juna Hibbah na amsa masa da amin. Bayan sun kammala duk yanda taso zillewa bai bartaba sai da ya sakata cin abinda ya shigo dashi. Gasasun ƴan shila ne da yogurt dayay mata matuƙar daɗi har tana masa cin zalama da ya bama Master mamaki. Sai dai baice komaiba ya sata yo brush da barin mata ɗakin dan tai shirin barci.
Har taji daɗi ya fita sai gashi ya dawo tana ƙoƙarin kwanciya. Badan taso hakanba ta kwanta kamar yanda shima kai tsaye gadon ya hawo yay kwanciyarsa hankali kwance.
Wata irin soyayya ce mai tsayawa a rai da zuciya da Hibbah bazata taɓa mantawa da ita a rayuwartaba Master ya nuna mata a wannan dare. Sai dai ta jigatu matuƙa dan har saida taita masa kuka da magiya amma bai sauraraba sai da ya more kwanakin kewarta tsaf. Tun a daren suka gyara jikinsu suka koma barci, da Asuba suna idar da salla bai sarara ba sai da ya ƙara dan gaba ɗaya ta dagula masa lissafin kansa, saboda gyaran da tasha bana wasa bane ba. Ga ƙaramin ciki a jikinta wanda shi baisan dashi ba yaketa faman bidiri da bireɗensa.
Yasha taɓara da shagwaɓa dan daƙyar ya lallaɓata suka dawo falo kusan sha ɗaya na safe dan ta samu ta karya. Sun sami ƙayataccen breakfast daga baba saude dasu Habib, tsananin yunwar da Hibbah keji yasata zaman dirshan ta dira kan abincin nan babu sauƙi. Tana gab da gamawa ta buɗe kular ƙarshe da nufin duba abinda ke ciki dan Master yace natane shi bayacin sa. Wani irin dukan kanta ƙamshin farfesun kifin yayi. Cikin zabura ta saki murfin kular tai baya har abin na bama Master tsoro.
Kanta ta dafe dake juya mata tana masa nuni da hannu akan ya rufe amma bai ganeba. Babu shiri ta saki aman dake taso mata dan ƙamshin kifin sake hauro mata kai yakeyi.
Da hanzari Master ya miƙe kanta ya riƙota. Ganin aman daya tsaya yake sake taso mata dole ya kwasheta da sauri suka nufi hanyar bedroom. A toilet ya direta yana riƙe da ita harya lafa. Ya gyara mata jikin yana jera mata sannu cikin damuwa da tambayarta dama bata da lafiya ne.?
Kanta ta girgiza masa a galabaice ga hawaye shaɓe-shaɓe ta sanar masa batason ƙamshin kifi ne. Mamaki ya kamashi dan yasan dai tana cin kifi ai, akwai lokacin da ya taɓa jin su Habib na sanar mata shi baya cin kifi tace saiko ta sakashi yaci wataran saboda ita kifi tamafi sonsa akan nama.
Saboda laushin da jikinta yayine ya sashi neman number Abdull domin zuwa ya dubata. Babu bata lokaci kuwa Abdull ya iso, sai lokacinne ma su Habib kejin Aunty Queen babu lafiya. Gaba daya suka ɗunguma sashen domin dubata.
Tun a kallo guda da Abdull yay mata ya fahimci cikine da ita. Amma sai ya bata tsinken gwajin ciki yace su gwada ya gani yanzun. Ana kuwa gwadawa da tsinken ciki ya nuna kansa. Wayyo farin ciki ga waɗan nan ahali ai bama acewa komai. Master kam jin abun yayi tamkar wata almara ko tatsuniya. Ya tsare Hibbah da idanunsa dake canja launi suna tara hawaye. Abdull dake kallonsa ya rungumesa yana mai tayasa murna. Hakama su Habib gaba ɗayansu suka ruƙunkumesa suna ihun murnar zasuyi ɗa.
Hibbah dai baka gane farin ciki ko akasin hakan tattare da ita. Dan tunda taji ihunsu Salis na hawa mata kai ta rarrafa ta koma ɗaki ta kwanta. Acan Master ya sameta. Ya ƙanƙameta hawayen da yake riƙewa na ziraro masa. Yana hawaye yana murmushi da kissing Hibbah tako ina. Yama rasa ta ina zai bayyana farin cikinsa a rayuwa. Godiya yaketa faman jerama UBANGIJI da kirari a zuciyarsa.
A gaba ɗaya yinin yau waɗan nan ahali sun yisane cikin wani irin farin ciki mara misali da kwatance. Duk da zuwa azhar Hibbahn ma ta martaye garau tamkar ba itaba. Sai dai ta samu tumatur ɗinta mai yawa tasha dan yanzu bata da abu mafi soyuwa sama da shi.
Duk da garau ɗin data koma dukan motsinta a idanun Master ne. Kaɗan-kaɗan saiya tambayeta mike mata ciwo? Mitake son ci?. Tun tana cemasa babu komai harta koma tura masa baki irin ya dameta ɗin nan. Ko kaɗan baijin haushi, sai ma murmushi da yakeyi kawai.
_________________________
Sam Hibbah bata wani laulayi, kifi kuwa tun daga ranar ko su Habib daina cinsa sukai a gidan. Sai wata tsadaddiyar soyayya Master ke nuna mata suna gurzar amarcinsu yanda ya kamata dan cikin nan ba ƙaramin saka masa kwaɗayinta yake ba. Gashi abin ya haɗa da zaman hutu da yakeyi a gidan harna tsahon watanni uku da aka bashi. Tun kwananta uku da dawowa gidan ita ke girkinta da Master, wani lokacin kuma taje sashen su Baba Saude suyi gaba ɗaya, musamman idan Abdull na gidan. Shafta tsakaninta dasu Habib sai abinda yay gaba. Dan ma an sama musu aiki zuwa yanzu ba zaman gidan sukeba sosai sai idan Master na bukatarsu akan wani aikin.
Komai na Hibbah ya sake canjawa. Ta buɗe ko ina ya cika a jikinta ga ƙiba cikin yana sakata masha ALLAH. Cikinta na watanni huɗu ta fara wani matsanancin laulayi da batayisa a baya ba. Ga shi Master ya koma aiki kuma. Dole Baba Saude ta dawo yini sashen nasu ko yana fita Hibbah ta koma can har sai ya dawo. Dan zuwa yanzu komai bata iyayi sai kwanciya. Ƙarin ruwa kuwa duk bayan kwana biyu sai an mata shi ake samun nutsuwa. Sau biyu Ummi dasu Zahidah na zuwa dubata. Su Yaya Muhammad kam ai basusan adadi ba. Balle Ammar yaji labari wanda kullum babu fashi idan ya dawo school sai ya biyo tanan ya ganta yake iya wucewa gida.
A cikin wannan tsukun da Hibbah ke dirzar nata laulayin aka saka aurarrakin su Habib da ƴammatansu. Zai kama dai-dai da haihuwar Hibbah insha ALLAH. Bayan saka ranar da kusan sati biyu wani aiki ya tasoma Master zuwa kudancin ƙasar. Dole ya tattara matarsa suka wuce tare dan bazai iya barinta a halin da take ciki ba. Ta tafi da kewar su Musbahu, suma ta barsu da kewarta. Dan hatta Ummi taso Master yabar Hibban anan amma dan karta shigar masa rayuwa tai shiru ta bisu da addu'a.
Sai kuma tahowar ta saka Hibbah cikin ɗunbin farin ciki dajin daɗi. Dan kai tsaye wajen shakatawa na musamman a bakin ruwa Master ya samar musu masauki. Kasancewar aikin nasa kuma na sirrine ya sai ya koma a real Isma'ill ɗinsa suka sake baje shafukan soyayya da rainon cikinsu da Master ke matuƙar so da ƙauna da fatan fitowarsa duniya lafiya. Ɗan yawon da yake da ita wajaje daban-daban yasata fara samun ƙarfin jikinta, sai dai randa laulayin ya bugar da ita kuma dole ne su kasance a gida. Akwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI sai gasu da wattani uku da tahowa har sun shiga na Huɗu.
Taso komawa gida a watan daya gabata dan a farkonsa su Zahidah duk suka haihu kusa da kusa. Sai dai aikin Master dake gab da kammaluwa ya sashi hanata zuwan sai a waya akaita tura mata hoton babys masha ALLAH. Ranar sunayen ne dai da aka haɗe ta birkice masa da kuka harda su zazzaɓi. Sai da ya haɗa da Ummi dasu Yaya Muhammad a masu lallashi sannan ta haƙura. Ammar kuwa ya dage yayta ɗauka mata videon komai yana tura mata. Dan mutane ne sosai suka halarci taron musamman dangin Hajiya mama da ƴan ƙauyen su Ummi. Ita Ummi ma har mamaki da al'ajab abin ya bata. Amma saita ɗau hakan matsayin wani hikima da rahama na UBANGIJI.
Washe garin suna akai zama na musamman da su kawu ballo game da gida da kayan gadon su Yaya Muhammad ɗin da Halilu yaso handamewa. Duk da dama an raba musu tun lokacin da babansu ya bar duniya sai yanzu aka sake raba abinda ya rage musamman gidan da suka taso dan ance su Momy su tashi. Kuka momy ta dingayi tana neman alfarmar Ummi akan a barsu su zauna Hajiya mama dake kwance tace bata yarda ba. Su Ameera su fitar da miji su Yaya Muhammad su aurar dasu. Ita kuma Momy ta koma can gidan da Mahaifin su Hibbah ya bama Halilu tunkan ya rasu ta cigaba da jiyyar Junaid.
Dole kuwa haka akayi, dan su Ameera da suka fahimci tsohuwar son tona musu asiri take babu shiri suka kawo ƴan samarinsu da abaya suka raina. Gudun kar wata matsalar ta biyo baya su Yaya Muhammad suka saka bikin a kurkusa. Dan sati uku kacal suka saka. Komai kuma daya shafi kayan ɗaki basuyi ƙyashin yimusu shi ba.
________________
A satin dasu Hibbah suka dawo a satin aka ɗaura auren su Ameera. Haka taci biki a wahale ta ƙaton ciki Ammar na mata iya shege. Daya kalleta saiya kwashe da dariya. Video kuwa da hotuna yayisu kala-kala. Tun tana kulashi harta daina dan yay bala'in taso rayuwarta gaba shi dasu Habib da ayanzu suka ɗinke abokai shaƙiƙai.
Bikin dai ba wani armashi yayi ba sosai. Dansu Yaya Muhammad ɗin ma sunfi maida hankali a shirye-shiryen nasu Habib da za'ai satin sama. Wanda Ummi ce matsayin uwar anguma I.G uban anguna. Hatta lefe su Yaya Abubakar haɗa hannu sukai da Master aka haɗa komai na birgewa da nunawa tsara. Ana miƙa amare su Ameera ɗakunansu kowa ya maida hankalinsa akan nasu Habib. Dan Hibbah ma dole ta koma gida dan Master yaƙi yarda akan zata zauna anan har satin bikin. Shi fatansa ma ta haihu lafiya kafin a shiga ruguntsumin taron.............✍
*_Chapter Fifty (End)_*
............ALLAH kuwa ya amsa addu'ar tasa. Dan a daren data koma gida kusan ƙarfe uku ta farka da matsananciyar naƙuda da dama kusan sati kenan tanata cinta a tsaye tadaiyi shiru ne kawai dan karya hanata halartar bikin su Amira. A rikice ya miƙe ya kira baba Saude. Wadda tana zuwa ta fahimci haihuwarma ta taho.
Duk yanda yaso su tafi asibiti hakan bai yuwuba. Dan kuwa dai abin yazo inji mai tsoron wanka. Ansha fama da gwagwagwa kafin ALLAH ya sauki autar Ummi lafiya gab da kiran sallar asubahi. Ta santalo ɗanta namiji mai kama da Ubansa sak. Lokaci da Master ya ɗauki yaron sai ga hawaye na rige-rigen sakkowa kan fuskarsa dan hakan ya tuna masa da randa Mamynsa ta haifi Habib. Ya rungume yaron wata irin ƙaunarsa na rsatsa jini da ɓargonsa. Sai da aka kammala gyara Hibbah tsaf bayan sallar asuba sannan ya shiga ya ganta. Su Habib ma sai lokacin suka sani.
Wayyo zo kaga murna da ihu. Yaro kuwa gaba ɗaya suka hau rububin ɗaukarsa Hibbah na kallonsu tana dariya da hawaye ita da Master, dan Alhmdllhi batajin wani damuwa a jikinta. Amma duk da haka sai da suka fita asibiti taga likita. Kasancewar babu wata damuwa suka dawo gida da wuri. Inda suka iske matan su Yaya Muhammad dasu Ameera amare cike da gidan. Dan tuni su Idris sun baza batun haihuwar. Hotunan yaro kuwa nata yawo a wayoyin ƴan uwa da abokan arziƙi.
Master yama yaro huɗuba da *ALIYU HAYDAR, ZAKI GADANGA ƘUSANR YAƘI*. Sosai Hibbah taji daɗi, duk da dai tasan shima sunan mahaifinsa kenan. Ammar kuwa ai cayay shi akaima takwara babu wasu su daddy.
Tsaye Baba Saude take akan Hibbah hakan yasa Ummi sam bata damu da batun a maidota gida ba tunda biki zasu shiga. Kwana biyu da haihuwa aka dire tarin kayan barka daga su Yaya Abubakar na ban mamaki. Dan har sai da Master yace sunyi yawa ai. Amma suka nuna masa zama su ƙaro kuwa.
Dole ya tsuke bakinsa yay godiya hakama Hibbah.
★★★
Duk da ɗanyen jego dake a jikin Hibbah haka aka tsunduma hidimar biki, sai dai ita kam babu damar yawan shigi da fici. idan kuwa ta kama dole zaka ganta cikin dogon Hijjab kamar yanda Baba Saude ta tilasta mata sakawa.
Randa take cika kwanaki shida da haihuwa aka