Showing 111001 words to 114000 words out of 155081 words
yanason zuwa kodan wani bincike.
★★★★★
Kusan awa ɗaya kenan da barin su Habib gidan amma babu su babu labarinsu. Gaba ɗaya su Idris sun kasa zaune sun kasa tsaye. Sai kaiwa da kawowa suke a falon hankalinsu nakan wayoyinsu suna ganin abinda ke faruwa ta yanar gizo. Basu kunna tv bane saboda fahimtar gaba ɗaya Master baya buƙatar wata hayaniya. Dan tun korar Hibbah da yay a wajen ya maida idanunsa ya lumshe kai kace barci yakeyi. Koda Khalid ma ya tambayesa ko zaisha tea bai tanka ba dan yayi zurfi matuƙa a tunani.
“What!!?”
Khalid dake rike da waya a hannu ya ambata yana mikewa tsaye a zabure cikin alamun gigita. Idris dake zaune gefensa yay saurin dubansa da faɗin. “Lafiya?”.
“Inafa lafiya!, wai kaji mi matsiyacin A.G ɗin nan ke faɗama ƴan jarida kuwa akan alaƙar Master da aunty queen?!”.
Hannunsa ya janye a kansa da ke masa tsananin ciyo, tare da buɗe lumsassun idanun ya sauke akan Khalid da yay maganar. Kafin Idris dake ƙoƙarin buɗe baki yay magana yayi ɗin ya katsesu.
Cikin muryarsa da ke a shaƙe na mura da tsananin ɓacin rai ya ce, “Television”.
Kai Khalid ya jinjina masa da ajiye wayar hannunsa ya ɗauka remote ɗin tv ya kuna. Hakan kuwa yayi dai-dai da hasko A.G da ke bayani ga ƴan jarida, da alama yabar wajen su alhajin Mande ya koma office.
“Tabbas har yanzu babu wanda yasan fuskarsa. Saboda yana amfani da facemasks iri daban-daban idan zai aikata laifinsa. Misali kamar yau an samu fuska biyu da yaje banki da ita, inda mutane da yawa suka tabbatar da sun gansa a matsayin alhajin ƙauye daya shigo bankin tankar baisan komai ba. Sai a yanzu ne kowa ya fahimci shine yay shigar ɓurtu tamkar yanda ya saba. Tabbas mun bibiyesa adalilin yarinyarsa kuma har mun sami nasarar harbinsa. Sai dai yanzu-yanzun nan muke samun labari a majiya mai ƙarfi dangane da ita yarinyar da tai kiran ta sanar da inda yake. matarsa ce, soyayya sukai kuma kafin aure. Hakan na nufin ahalinta sun san wanene shi suka ɗauketa suka bashi. Dan a yanzu haka zancen da nake muku harda ƙanin mahaifin ita yarinyar dake dauke da ɗawainiyarsu tun suna kanana saboda mahaifinsu ya rasu suka yashema asusu. Kenan hakan na nufin harda ita a cikin tawagar tasa.......”
“Amma yallaɓai idan harda ita mi zaisa ta tona masa asiri?”.
Wani yayma A.G tambayar cikin katsalandan na ƴan jarida.
A.G yaja numfashi, “Muma wannan itace tambayar da muke nemawa amsa. Sai dai a ganina kawai sun shirya mana wasa da hankaline kawai sai suka rufta..”
“Kenan dama kuna bibiyar al'amuransa a koda yaushe?”.
“Sosai ma kuwa. Dan bamu da burin daya wuce mu kamashi. Shiyyasa dare da rana muke tsaye tuƙuru akan dukkan motsinsa...”
“Amma yaya akai duk da jajircewar nan taku harya samu nasarar yashe asusan bankunanku kuma a yau?”.
A.G ya kafe ɗan jaridan da yay tambayar da ido har saurayin ya tsargu. Ganin sauran ƴan jaridar na juyawa suna kallon saurayin saboda kallon da yake masa ya sashi basarwa yana sakin murmushi. “Tambaya mai ƙyau. Sai dai zan bada amsartane anan gaba bawai yanzu ba...”
“Tabbas zaka amsata kuwa! Koda su sun manta ni Isma'il Aliyu Hikima zan sakaka ka amsata!!”.
Master ya faɗa cikin wani irin kaushin murya da ɗaci yana sake maida idanunsa ya rufe. A haka ya cigaba da sauraren A.G daya ke tabbatarma da duniya a yanzu haka sun sami nasarar tattaro ahalin Hibbah, dan sune kaɗai zasu iya faɗama duniya a inda master yake a yanzu.
Cikin tashin hankali su Khalid ke duban Master daya maida idanunsa ya rufe. Sun san sarai yana jin A.G ɗin shima. “Innalillahi.... Boss akwai matsala kenan”.
Bai motsaba, bai kuma tanka ba duk da yaji abinda Idris ɗin yace. sai dai faman taunar lip ɗinsa yake na kasa alamar zuciyarsa na masa zafi da ciwo. Dan tsabar yanda yake taunar lip ɗin har ya koma jaa sosai.
Shigowar baba saude da ke faɗa musu Hibbah fa babu lafiya jikinta sai rawa yake ga kuma zazzaɓi ya sakashi buɗe idanu a hankali. Kallon baba Sauden kawai yakeyi yana cizar lip. Su Idris kam duk sun zabura kan baba saude suna tambayarta miya sameta? ba yanzu ta shigaba lafiya lau.
“Gaskiya inaga firgici ne. Da alama bata taɓa gamo da makamancin wannan tashin hankalin ba. Tunda ta shiga fa sai surutai takeyi. Maida idanun yay ya lumshe, gaba ɗaya kansa ciwo yake masa tamkar zai buga.
Jin yaƙi cewa komai yasa sukai tsuru-tsuru suna kallonsa. Musamman ma su Khalid. Ganin haka yada Baba Saude takowa ta ƙaraso inda yake. Cikin taushin murya tace, “Babana ko jikin ne?”.
Idanunsa ya sake buɗewa, yanda suka sake kaɗawa sukai ja har kamar suna ƙyallin ruwa sai ka ɗauka kuka yake. Yay ɗan murmushi mai ciwo yana girgizama baba sauden kansa.
“Naji sauƙi baba, kice mata tazo nan”. Yay maganar acan ƙasan maƙoshi cikin rauni da ɗacin dake addabar zuciyarsa da maƙoshinsa.
Baba saude da gaba ɗaya itama zuciyarta ta ƙara raunana. Ta kaɗa masa kai da juyawa ta koma. Babu jimawa kuwa sai gata ta fito riƙe da hannun Hibbah da kallo ɗaya zakai mata ta baka matuƙar tausayi. Duk ta susuce ta firgice. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunta sun kumburo matuƙa, jijiyoyin kanta duk sun miƙe ruɗu-ruɗu. Duk da haushinta da su Khalid ke ji sai wani irin tausayinta ya kamasu. Suka shiga jera mata sannu cike da damuwa. Bata iya ta amsa musu ba, dan gaba ɗaya a yanda Hibbahn take ta fita hayyacinta ba lallaine ma tana fahimtarsu ba.
Shi kansa master tunda baba Saude ta zaunar da ita gefensa ya buɗe idanu ya kalleta sai da tsigar jikinsa ya tashi. Yaja numfashi batare da ya ce komai ba ya maida dubansa ga baba Saude. “Baba kije abinki kawai”.
“To babana, amma babu wani abinda kuke buƙata?”.
Kansa ya jinjina mata kawai. Sai kuma ya maida dubansa ga su Khalid. “Tea da bargo”. Ya faɗa a taƙaice dan baya son yawan maganar.
Cikin sauri Khalid ya nufi inda yake tunanin kitchen ne. Idris kuma ya nufi bedroom. Sai da duk suka shige ya maido dubansa gareta, batare da yace mata komai ba ya ɗaura hannunsa mara ciwon saman goshinta. Zafin da ya ratsa masa hannu ne ya sashi cije lip yana janyewa ya maida kan wuyanta. Ɗan zabura tai dan abin yazo mata a bazata duk da taji sanda ya taɓa goshin. Baice komai ba ya janye hannun. Hakan yayi dai-dai da fitowar Khalid ɗauke da babban bargo mai laushi. Zai warwaresa Master ɗin ya girgiza masa kai. Dai-dai nan shima Idris ya dawo ɗauke da shayin. Saman table ɗin ya ajiye yana jawosa gaban master ɗin duk da ya fahimci na Hibbah ne.
Zamansa ya ɗan gyara yana riƙo hannunta, a ɗan zabure ta buɗe idanunta, kallon cikin idonsa da tai a mistake ya sakata saurin maida idanun ta rumtse hawaye masu zafi na silalo mata. Ɗan jawo hannunta da yay ne ya sata matsowa jikinsa dan gaba ɗaya a firgice take da shi da komai ma. Fahimtar hakan da yay ne ya sakashi kwantar da kanta a kafaɗarsa. Ta ja wata nannauyar ajiyar zuciya na tabbacin babu abinda tafi buƙata kamar ɗumin jikin uwa. Ganin haka yasa su Khalid barin wajen.
“Bana son kuka”.
Ya faɗa acan ƙasan maƙoshin da yasa ita kaɗai ta jisa. Haɗiye kuka ta shigayi tana jan tagwayen ajiyar zuciya. Dan tunda ya ɗan jinginata da jikinsa tsinkewar da zuciyarta ke mata ya ɗan fara sassautawa. Hannu ya kai bisa fuskarta ya share mata hawayen yana faɗin, “Kinsan zuciyarki bazata iya ɗaukar duk wannan ba miyasa kika ƙirƙira?.”
“Dan ALLAH kayi haƙuri”.
Ta faɗa tana fashewa da sabon kuka. Komai baice mata ba, sai kofi tea ɗin da ya ɗakko ya miƙa mata. Babu musu ta amsa ta hau sha, dan yau babu wata ƙofar samun damar masa gardama. Taso mata yake amma haka ta danne taita sha. Tana ajiye kofin tamkar jira sai ga amai. Ƙoƙarin barin jikimsa tai amma ya riƙeta. Tanata jujjuya masa kai alamar ya barta shi kuma bai fahimta ba. Sai kawai ta saki aman ya wanke musu jiki baki ɗaya.
Da sauri su Khalid suka miƙe zuwa garesu. Hakan kuma yayi dai-dai da fitowar baba saude itama a firgice.
“Dan ALLAH kayi haƙuri”. Tai maganar wani aman na yunƙuro mata, duk ta sake firgicewa, ta cire hijjab ɗin jikinta ta fara goge masa aman daya ɓatasa. Komai baice mata ba, sai riƙeta da yay ganin kamarma jiri na neman ɗibarta ta faɗi. Sai da ya tabbatar ta gama ya maida kanta kan kafaɗarsa ya kwantar.
Duban su Idris da ke ta faman jera mata sannu yayi, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Mikewa yay riƙe da ita suka nufi bedroom duk da bayajin daɗi da ƙarfin nasa jikin shima. Har cikin bathroom ya rakata, bayan ya zaunar da ita ya haɗa mata ruwan ɗumi. Batare da yace mata komai ba ya fito ya barta.
Da kallo tabisa wasu hawaye masu zafi na sake silalo mata. A ranta tana mamaki da tambayar kanta shi ɗin wanene shi?. Rashin mai bata amsa ya sakata fara zame kayan jikinta ta fara wankan batare da tunanin zai iya sake dawowa ba. A kiɗime ta waro idanu da saurin saka hannu ta kare jikinta tare da kaiwa tsugunne ganin ya turo ƙofar ya shigo kansa tsaye, shima da ga shi sai guntun towel.
Ɗauke idanunsa yay da ga kallon da yay mata shima, kayan da ya cire na jikinsa data ɓata da amai ya ajiye yana ɗan jan numfashi a sarƙe.............✍
*_Kuyi manage da wannan, da hanau gara mannau😬🚶🏻_*
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI......_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*
*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽
#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Chapter Thirty Six_*
...........(Kura ga tsoro ga ban tsoro) ya faɗa a ransa ganin yanda jikinta keta uban tsuma tama rasa inda zata tsoma ranta taji daɗi. Kansa ya sake ɗaukewa tamkar baiga halin da take a cikin ba ya ƙaraso gareta bayan ya ajiye kayan. Kuka ta fashe masa da shi tana girgiza kai, dan a duniya bata taɓa shiga cikin tsananin kunya da firgici kamar na yau ba. Tayi matuƙar daburcewa, wajen ɓuya kawai take nema amma babu.
Hannusa mai lafiya yasa ya zame hannayenta duka da take faman rufe jiki, duk ƙoƙarinta na son ganin ta faɗa jikinsa ta ɓuya kuma yaƙi bata daman hakan, sai ma sake mannata da yay da bango ya tokare ta da hannunsa mai ciwo duk da zogin da yake masa har zuwa yanzun. Cikin tsareta da idanu babu ko kunya ya fara magana cikin izza da ƙasaitar fushin da yake ciki har zuwa yanzun, “Nuna tsoro anan gazawace ga wadda ta nunama duniya ta girma, tunda har kika iya ɗaukar wancan da kika ƙulla, wannan ma dole ki ɗauka. Lokaci yayi daya kamata nima naga little Master a duniya, kafin ki ɗanamin tarkon da bazan tsallake ba Hibbaty”.
Duk da ba komai ta fahimta a maganganunsa ba saboda ruɗanin da take a ciki, kanta ta shiga girgiza masa. Cikin rawar harshe da son ɓoye kanta tace, “Dan......”
“Shiiii!!.” Ya faɗa yana ɗaura yatsansa bisa leɓenta.
“Karma ki roƙeni dan zugani kike. Barinki a haka gareni haɗarine, saboda wannan kan naki ba kowane yare yake ganewa a cikin baƙi. Kinfi buƙatar dalla-dalla. Gara na tabbatar da kaina a gareki, kafin lokaci ya ƙuremin na ajiye jini na a jikin ki, maybe ki fara nazari kafin kiyi abu” .
Baki ta buɗe zata sake yin magana ya rufe bakin da yatsunsa yanda har sai da azaba ta sakata cire hannuwanta da take kare jikinta da shi ta riƙe nasa hawaye na rige-rigen sakkowa a kumatunta.
A karon farko ya saki wani lalataccen murmushi mai bayyana ƙunar zuciya, “K tsoro ce mai ban tsoro Muhibbat. Da yaren tsoro kawai ake fahimtar da ke karatun duniya. Tunda haka kikafi buƙata kuwa, sai ki shirya zaman jira da rainon ƴata ko ɗana har na fito a gidan yari tunda a can kikafi buƙatar ganina”.
Yana gama faɗa ya ɗan lakaci hancinta da janye jikinsa a nata, tana son yin magana yay mata alamar gargaɗi, idanunsa tamkar zasuyo aman bala'in da ke a zuciyarsa. Bai sake ce mata uffan ba ya juya mata baya ya sakarma kansa ruwa tare da cire towel ɗin jikinsa kansa tsaye tamkar yama manta da ita a wajen. Da sauri ta zame tai ƙasa jikinta na matuƙar rawa ta ɓoye fuskarta. Jin kamar ya kashe ruwan ya sata sake rumtse ido da ƙarfi kamar zatai kuka. Dan ita duk tunaninta tsayawa yay kallonta, duk da tanajin motsin da yakeyi alamar yin wani abu. Kaɗan ta buɗe idanunta sai taga har yanzu yana a yanda ya juya mata bayan. Ta ja ɓoyayyar ajiyar zuciya da fara ɗauraye jikinta da sauri-sauri. Duk da yanajin yanda take facal-facal da ruwa har yana fallatso masa a jiki bai juyoba, sai da ya kammala abinda yake a wajen sannan.
Juyowar tasa tayi dai-dai da fisgar towel ɗin daya ajiye ta ɗaura. Duk da bai gama rufe mata jikin ba dai taji ƴar nutsuwa fiye da ɗazun da take a sule. Ya ɗan bita da kallo ganin yanda ta nufi hanyar fita da sauri har tanayi kamar zata faɗi, ga santsin ruwa da tiles ga na rashin ƙarfin jiki.
Ya ɗan girgiza kansa da sakar ma kansa ruwan shower tausayinta na ratsashi. Tabbas yasan abinda ya faru a yau ɗin rubutaccene da ga alƙalamin ƙaddarar Sa. Ko babu ita sai hakan ta faru, tana da laifi yanada laifi. yasanma yafi yawa fiye da natan, sai dai yanda ya santa inhar ya nuna mata sassauci sake birkice masa zatayi, a yanzu kuma rayuwarta tafi ta kowa haɗari dan ita kowa kema kallon lagonsa. Haka dai ya kammala wankan cikin dabara da tunane-tunane. Bathrobe ya saka maimakon towel ɗin da ya shigo da shi tunda ta ɗauke. dan ya fahimci gaba ɗaya tsurewa take idan ta gansa babu rigan. Koda ya fito kwance ya sameta a kan gado ta kudindine da bargo. Komai baice mataba ya ƙarasa ga mirror yana ɗan duban kansa zuwa real face nasa na Isma'il da ya fito da shi. Jakar kaya daya gani ajiye a gefe ya sashi fahimtar su Habib sun dawo kenan. Koda ya buɗe kayansa ne a ciki da dukkan abin buƙatarsa na yau da kullum irinsu mai, turare da makamantansu. Ya ciri abinda zai buƙata ya ajiye gefe da wanda itama zata buƙata ɗin. Harya gama kintsawa Hibbah na cikuykuye abinta a bargo duk da tana jin motsinsa. Amma tsananin kunya da zazzaɓi sun hanata ƙwaƙwaran motsi.
Shima duk da yasan idonta biyu komai baice mata ba, sai ma salla da ya tayar ta azhar. Sai da ya idar ya miƙe ya saka sabon mask sannan ya karasa saitin inda take a gadon. Hanunsa dafe da kansa dake sara masa ya kai zaune. Batare da yace komaiba ya yaye bargon da ɗaura hanunsa saman goshinta. Sosai jikin ya ƙara zafi, dan haka ya ɗan tsura mata jajayen idanunsa da ke sake tabbatarma mai kallonsa baida lafiya. “Ki tashi kiyi salla, sai ki sha magani ki kwanta”. Yay maganar har yanzu muryarsa bata fita da ƙyau.
Sarai Hibbah tajisa. sai dai ta kasa koda motsawa harya tashi. Sai da taji ya fita a ɗakin gaba ɗaya sannan taja numfashi tare da miƙewa zaune tana share hawayen da ke ziraro mata wanda ba komai ya kawosu ba sai tsananin kunya da nadamar abinda ya faru. Ga kewa da ƙulafucin son ganin ƴan uwanta da Umminta da ke cike da zuciyarta.
★★
Sosai su Habib sukaji daɗin ganin yay wanka ya sauya kaya. Sai dai tsananin tausayinsa na nan shimfiɗe akan fuskokinsu. Dan a kallo ɗaya da zaka masa zaka iya fahimtar rashin jin daɗin jiki dana zuciya dake tattare da shi. Kawai dai ƙarfin hali ne da juriya irin tasa.
Sannu da tambayar yaya jikinsa suka shiga jera masa. Batare da ya iya buɗe bakin yayi magana ba ya shiga ɗaga musu kai kawai alamar amsawa. Basu damu ba, dan su kansu idan yana cikin irin wannan yanayin sunajin tsananin shakkarsa. Yanayine da yake a cikin fushi da zafin zuciya. Ƙiris yake jira wani ya shiga gonarsa ya tabbatar da fushin a kansa.
“Ga magani ko a kawo tea sai ka sha?”.
Musbahu ya faɗa cikin girmamawa. Master da ke kallonsu na tabbatar da suna a cikin ƙoshin lafiya ya jinjina kansa kawai yana rufe idanu.