Showing 6001 words to 9000 words out of 37653 words

Chapter 3 - MIJI GOMA. Hausa novel

23 Oct 2025

85

mu gaisa, ta yi girkinta na yi nawa, zan iya zubawa a roba na bata don zaman tare da fita haƙƙin maƙobtaka, sannan zancen haɗa kitchen ba zai yiwu ba, tun da ga abin da hakan ya fara haifarwa, gaskiya ta haƙura ta mayar da kayanta ɗaki, ko ka ɗan buga mata rumfa a tsakar gidan, sannan wannan yarinyar kar ta ce za ta dinga shigo mini ɗaki, don na lura ba ta da kunya, kowa ya yi harkarsa, ka yiwa Gwaggo cefanenta da ban nawa da ban, ta yi girkinta na yi nawa, idan ka yi haka za mu zauna lafiya".

Nazifi ya ce"A gaskiya Maryam wannan ba tsari ba ne, kuma ni zan ji nauyin faɗawa nahaifiyata haka".

Ta ce"To salun-alun ka sallame ni tun tafiya ba ta fara miƙawa ba, sai na tafi gidanmu, don mutuwar aure ba komai ba ce".

Ya ce"Ni ba haka nake nufi ba, zan ji ta bakinta dai, yanzu ki dafa shayin".

Ta tashi tana taɓe baki ta shiga kitchen ta ɗora shayin, a nan ta zauna ta kira lambar babarta, tana ɗagawa ta ce"Babarmu ni fa zan taho gida".

Uwani da take zaune tana shan kunu ta ce"To abun ya ƙi ko?"

Maryam ta kwashe komai ta faɗa mata, Uwani ta ce"Tabɗijan! To shikuwa Nazifi kwana-kwanar me yake yi? Ai gara ma ya fito fili ya sanar da duniya ƴar aiki ya ɗakkowa uwarsa! Maryam da ƙuruciyarki da kyaunki za ki ƙare a gidan da za ki dinga yin bauta? Ga ɗakinki ga na suruka, to wannan uban gwanjon da kike ta siya na ƙananun kaya duk ita za ki yi wa kwalliya ashe? Yanzu ya amince da sharaɗinki ko kuwa?"

Ta ce"Ya dai ce za su tattauna".

Uwani ta ce"To su tauna sa kyau ta yadda za su ji daɗin haɗiyewa, Maryam idan fa kin ga da takura ki kamo hanya ki taho gida, don ba gajiya muka yi da ke ba, muka ba shi".

Ta ce"Bari dai na ga yadda za su tsara, wallahi ba sai kin ce na taho ba, don indai haka zaman aure yake to gara ma na dawwama a gabanki".

Suka yi sallama, ta juye shayin a flas, ta zuba na Gwaggo a ƙaramin flas ta a ajiye, ta ɗauki nasu ta tafi da shi ɗaki, ba ta same shi a ɗakin ba, sai ta fito ta ga takalmansa a ƙofar ɗakin Gwaggon, hakan ya tabbatar mata yana ciki, ta yi saɗaf-saɗaf ta je ta laɓe a jikin labulen ta kasa kunne, daidai sanda Gwaggo take cewa"Yanzu dai Nazifi kenan ka zo ka faɗa mini na takura muku kai da matarka na bar maka gidanka ne ko?"

Muryarsa cike da damuwa ya ce"Subhanallah! Kar Allah Ya kawo ranar da zan yi wannan tunanin, kin san Maryam yarinya ce..."

Ta ce"Kai dakata, Allah Ya sa a nonon uwarta ka tsigota ka kawi gidan nan, mu sanda muka zauna da surukanmu wace bauta ce ba mu yi ba? Tuwon dawa kwano biyar nake tuƙawa, bayan na yi daka na yi surfe na niƙa, idan ban da lalacewar zamani har yarinyar da aka auro shekaran jiya ce za ta kafawa miji wani sharaɗi kuma akan mahaifiyarsa? Nazifi ka fice min daga nan zan haɗa kayana na tafi kawai".

Maryam ta ja wata ajiyar zuciya a hankali jin Gwaggo za ta tafi, Nazifi ya ce"A'a babu inda za ki je, ni fa ba haka nake nufi ba, shikenan zan fahimtar da ita za ta dinga yi miki komai, ki yi haƙuri, bari na karɓo miki shayin".

Maryam ta yi wuff ta shige ɗaki, zuciyarta tana zafi, a ranta tana ayyana ta ga wanda zai sauka a kan bakansa tsakaninsu, ya shigo yana cewa"Ina shayin nata?"

Ba tare da ta kalle shi ba ta ce"Yana kitchen".

Ya ce"Ai da sai ki kai mata, don Allah Maryam ki zauna lafiya da babata, wallahi ba ta da wata matsala".

Ba ta ce komai ba, ta fara haɗawa kanta shayin, sai da suka gama karyawa ya shirya fita aiki, amma ya kasa yiwa Maryam bayanin Gwaggo ba ta amince ba, saboda yadda ya ga ta yi kicin-kicin da fuska, sai janta yake da wasa ta ƙi sauraronsa, ganin sai kame-kame yake yi yasa ta cewa"Wai ni kam ba fita za ka yi ba?"

Ya yi murmushi ya ce"Au korata ma kike yi?"

Ba ta ce komai ba. Ya ce"Maryam kin san dai ina sonki, ina son zama da ke, dalilin da yasa na zaɓi aurenki kenan, to kin kafa sharuɗa na samu Gwaggo amma ita ba ta amince ba, ni sai nake ganin ta fi mu gaskiya, don Allah ki yi haƙuri ki yi yadda ta tsara ɗin, wallahi kamar kin yiwa mahaifiyarki ne lada za ki samu, kuma ni ma za ki samu ƙima da mutunci a idona".

Ta ce"Wato da ba ni da mutunci ko?"

Ya ce"A'a ina nufin za ƙaru".

Ta ce"Nazifi ina ga zan tafi gidanmu sai hakan ya fi kawo masalaha, sai ka auro wata ta zo ta yi mata hidima, matsalar da aka samu fa duk kai ka ja, ka ga ba ka faɗa min zaman mutum biyu zan yi ba, dama da ba zan ma fara aurenka ba, don abin da zai yiwu shi ake yi".

Ransa ya ɓaci ya ce"Maryam ina lallaɓa ki ne saboda a zauna lafiya fa, amma na ga abun naki sai gaba yake yi, kin san dai yanzu ni mijinki ne ina da ikon saka ki da hana ki, don haka umarni zan ba ki yanzu, ya zama dole ki kula da mahaifiyata, ki yi mata biyayya, indai kin yarda aljannarki tana ƙarƙashin ƙafata, na ji ita ba ta isa da ke ba, amma ni ai na isa da ke, to ni za ki yiwa ba ita ba".

Maryam kallon shi kawai take yi da maɗaukakin mamaki, don bai taɓa faɗa mata maganganu kai tsaye haka ba, wato yanzu yana ganin tun da ya aure ta zai iya taka ta yadda ya so, bai ma tsaya jiran amsarta ba ya fice, a ransa yana jin babu daɗi, amma dole ya nuna mata muhimmancin mahaifiyarsa.

Ita kuwa yana fita ta kira babarta, ta zayyana mata komai, ta ƙara da faɗin"Ni zan haɗa kayana na taho".

Uwani ta ce"Kul! Kar ki taho yanzu, ƴan gulma sun tashi daga bacci, ki yi haƙuri sai dare, ana sallace sallar magriba ki taho, ba ki ga wajen zama ba Maryam".

Ta tashi ta haɗa kayanta cif a kwati ƴar tsakiya, ta gyara ɗakin ta fito tana wanke-wanke tana jin waƙoƙi a wayarta, tana bin waƙar cikin nuna ko ajikinta, wani jinta take a sama ta yadda take jin tana da gatan da ba za ta ɗauki raini daga wajen kowa ba, ta gama ta shiga kitchen ta tattaro kayan gararta danginsu cincin da dubulan ta kawo su ɗaki, tana ci tana chart har sha ɗaya ta yi, sai ga ɗan aike da ledoji wai ga shi inji Nazifi, ta buɗe ta ga ledar farko kayan miya ne da nama, sai kuma garin masara da na alkama, ta yi wani murmushi na takaici ta ɗauki ta kayan miyan ta kai kitchen ta garin kuma ta je ajiye a ƙofar ɗakin Gwaggo, ta koma ɗaki ta ci gaba da harkokinta, sai sha biyu da rabi da Yasmin ta dawo daga makaranta, ta ci karo da kedar, tana buɗewa take cewa"Gwaggo wannan ledar fa?"

Gwaggo ta ce"Leda kuma?"

Yasmin ta ce"Ai garin tuwo ne ma, kuma kika ajiye a waje?"

Gwaggo ta fito tana cewa"Garin tuwo kuma? Sai ta ƙwalawa Maryam kira, ta fito tana ɗaura ɗan kwali, Gwaggo ta ce"Wnnan fa na ga an ajiye a ƙofar ɗaki?"

Maryam ta ce"Ƙila ɗan aike ne ya kawo".

Ba ta jira cewarta ba ta koma ɗaki, tana jin Yasmin tana tambayar me aka dafa?

Gwaggo ta ce"Shiga kitchen ɗin ki duba" Ta koma ɗaki tana mamakin kalal surukar da Allah Ya haɗata da ita.

Maryam tana jin ƙarar buɗe kitchen ta fita, ta samu Yasmin tana buɗe-buɗe, ta haɗe rai sosai ta ce"Ke ƙalau kuwa? Uwar me kika ajiye da za ki ɗauka?"

Yasmin ta ce"Ba dai uwata ba".

Mamaki ya kama Maryam ta ce"Zaginki na yi? To na zage ki ɗin uwarki da ubanki! Na fi ki iya rashin kuya, a fagen nan ke jikata ce ba ƴata ba, fice ko na kikkifa miki mari!".

Yasmin ta fita tana kwarara ihu kamar wacce aka cirewa ido, Maryam ta fara kwashe kayan abinci na gararta tana kaiwa ɗaki, har ta gama Yasmin ba ta fasa ihu ba, Gawaggo kuma ba ta fito ta ce komai ba, tana zaune sai ga kiran Nazifi, tana ɗagawa ya ce"Amma Maryam sai da na faɗa miki babu ruwanki da yarinyar nan, akan me za ki dakar musu ƴa?"

Ta yi tsaki ta kashe wayar, saboda ba ta da lokacin tsayawa faɗa musu ba ta kai ga dukanta ba, abu ɗaya da ta sani dai shi ne auren nan ba mai yiwuwa ba ne, dole a kira ta da ƙaramar bazawara, don ko miji bai isa ya saka ta ciwon kai ba, ballantana kuma uwarsa da wata ƴar tsakuwar jikarta.

Ya yi ta kira ba ta ɗaga ba, hakan ya sa ya taho gidan don kukan da ya ji Yasmin tana kurmawa ta waya da yadda Gwaggo take ta masifa ya tada hankalinsa.



08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_



*SADIYA ABDULRAZAƘ*


*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?*

Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu

*FIRST CLASS WRITERS*

PAGE 4


Yana shigowa gidan ya shiga ɗakin Gwaggo, da yake Maryam ta ji sallamarsa sai ta tashi ta fito, ta je ta laɓe tana sauraron su, Gwaggo tana ta tsara masa son ranta kamar a gabanta aka yi, sai da ta ji ya ce"Ki yi haƙuri don Allah Gwaggo bari na je na same ta". Sannan ta yi wuff ta shige ɗakinta, ta haɗe rai tana jiran ta ga ta inda zai fara, ya shigo da sallama, ransa a ɓace yake da abin da ta yi, amma sai ya kasa karaɓus saboda yana son Maryam, ya zauna a sanyaye ya ce"Maryam don Allah ki rufa mini asiri ki fita daga harkar yarinyar nan".

Ta ce"Na fita daga harkarta fa ka ce, kamar dai wata sa'ata, yarinyar da a haihuwar kaji na haife ta amma ta yi yunƙurin zagina..."

Ya katse ta da faɗin"To kin ji ke ma yunƙuri kika ce, ba ta zage ki ba, a kan me za ki dakar musu ƴa?"

Ta ce"To shi yunƙurin ba raini ba ne? Ai wallahi inda ta zage ni sai bakinta ya yi jini, kuma ni fa ban dake ta ba, sharri ne kawai ta so ƙullawa, kuma sai dai ya ƙare a kanku don yau zan bar muku gidan".

Ya yi murmushi ya ce"A haba, da wasa kike yi, babu inda za ki tafi ki bar ni".

Ta ce"Wallahi Nazifi da gaske nake, ba zan iya ba, bari na faɗa maka gaskiya inda na san haka zan samu gidanka da ban aureka ba, a ce daga aure sai saka ni ɓacin rai ake yi?"

Ya ce"Ki yi haƙuri don Allah! Komai zai daidaita in sha Allah, kuma ke ma fa har da laifinki, kin ƙi kwantar da hankalinki, yau da wuri zan shigo mu sha shagalinmu amaryata".

Ta taɓe baki, don ba ta da lokacin ɓatawa wajen nuna masa dole yau za ta tafi gida.

Ya ce"Kin yi girki? Na aiko cefane za ki iya yi mata tuwon yau ko sai gobe? Kin ga cikinta ita kaɗai ne ko kaɗan ne kin ji Sweety".

Takaici ya kamata, ta kwanta tana cewa"Don Allah ka tafi harkarka".

Shi ma ya kwanta kusa da ita yana cewa"Ba zan tafi ba, kin ga yi haƙuri tashi mu shiga kitchen ɗin tare sai na taya ki".

Ta ce"Wallahi Nazifi ba zan yi tuwon nan ba".

Zai yi magana suka ji Gwaggo tana ƙwala masa kira, ya tashi ya fita jiki a mace.

Gwaggo ta ce"Nazifi tun da ka zaɓi matarka ta huta ni na wahala to mu je ka koya min yadda ake kunna gas ɗin, sai na ɗora".

Ya ce"Haba Gwaggo za ta yi, duk fa ba yadda kike tunani ba ne, kin san Maryam tana da aljanu shiyasa wani abun sai an yi mata uzuri".

Gwaggo ta ce"Allah Ya sa tsamiya ce a kanta, wa za ta faɗawa aljanu? Ni da nake da guda saba'in a kaina na gado, zaman gidan nan fa idan ba zai yiwu ba tun wuri ka faɗa min na koma inda na fito".

Inda za ta koma ɗin tabbas da zai ji daɗin hakan, amma ba zai iya nuna mata yana so ta tafi ba, don haka ya ce"Ki yi haƙuri Gwaggo, bari na samo miki tuwon, gobe sai ta dafa miki".

Bai jira cewarta ba ya fita daga gidan. Ya siyo mata tuwon ya kawo ya koma kasuwarsa, ba tare da ya sake shiga ɗakin Maryam ba.

Can da magriba Maryam tana sallayar da ta idar da sallah ta jiyo hayaniyar Gwaggo tana cewa"Wallahi Yasmin idan fitina za ki yi sai ki bar gidan nan, ga tuwo ki ce sai kin yi girki, alhalin ba iya kunna gas ɗin kika yi ba?"

Yasmin ta ce"Wallahi na ga yadda ake kunnawa, idan na kunna sai ki dafa min indomin don Allah, idan kuma so kike na kwana da yunwa shikenan".

Gwaggo ta ce"Rufa min asiri na mutu babu hakkin kowa a kaina, ungo siyo ashanar, don wannan matar ƙila ɓoyeta ta yi".

Maryam ra ƙufula, sanda ta fito Yasmin har ta fice, tana dosar kitchen ɗin ta fara jiyo ƙarar gas ɗin shuuuu alamar ta kunna shi, kuma wai ta tafi siyo ashana, a ranta ta ayyana lallai dole dai ta bar gidan nan, don ba ta shirya mutuwa ba, ta kashe gas ɗin ta fito ta ja ta tsaya a ƙofar kitchen ɗin.

Sai ga Yasmin ra dawo da saurinta, ta yi turus ganin Maryam a ƙofar kitchen, ta haɗe rai ta shiga ɗaki, sai ga Gwaggo ta fito tana gyara ɗaurin zani, Maryam ta ɗauke kai kamar ba ta ganta ba, Gwaggo ta ce"Baiwar Allah za ki iya ba mu waje ko?"

Ta ce"Gwaggo ba zai yiwu a kunna gas yanzu ba, ya kamata ku fara sanin yadda abun yake kafin ku fara amfani da shi, wallahi yanzu idan aka kunna gas ɗin nan gobara ce za ra tashi gagaruma ku mutu, don haka ko za a kunna shi a yau dole sai warin iskar nan da ya fita ya baje".

Ta ce"Ke Yasmin daga yau kar ki sake gwada kunna gas ko a wani wajen, ba haka ake yi ba".

Gwaggo ta tafi ɗaki tana cewa"Oh! Ni kam Nazifi wa ya auro ne? Yau ni za a faɗawa zamani? An hana ni abinci kuma an hana ni dafawa? Ba laifinki ba ne".

Maryam ta ce"A'a Gwaggo ku zo ku kunna, sai dai na ce Allah Ya ji ƙanku, don ni yanzu zan bar muku gidanku ma".

Daga haka ta shige ɗaki, ta ɗauki akwatinta ta saka wayarta a jakar hannu ta fice, Gwaggo ta bi ta da kallon mamaki, sai kuma jikinta ya yi sanyi, ita dai ba ta ga abin da aka yi da zai saka ta yi yaji ba, "Daga kunna gas? Allah Ya kyauta" Ta faɗa tana shigewa ɗakinta.

A ɓangaren Maryam ranta fess ta ƙarasa gida, duk da tana ɗan fargabar abin da Baba zai ce, faɗa ne ta saba da shi musamman ta wajen shi, kuma shi Baba yana da wani hali wanda yake burge ta, idan ya yi maka faɗa da nasiha a kan abu, ka ƙi yarda ko ka ƙi dainawa, shikenan sai ya ce ka fi ƙarfinsa ya zare hannu a tafiyarka, sam ba zai takura maka ka yi dole ba, shiyasa take ganin ba zai takura sai ta koma gidan Nazifi ba.

Ai kuwa da Baban ta fara cin karo, a ƙofar gida ta same shi, suna tattaunawa da wani maƙocinsu, dama gaida manyan unguwa ba ɗabi'arta ba ce, don haka kanta tsaye ta wuce su ta shiga gidan, Baba da ya gane ta sai da gabansa ya faɗi, ya bita da kallo.

Tana shiga da sallama Uwani ta tare ta ta rungume tana cewa"Sannu da zuwa, maza shige ɗaki, ai ba neman kai muke yi da ke ba" Ta yi maganar tana jan akwatin zuwa ɗaki.

Maryam ta shiga ta ajiye hijjabinta, ta kwanta a gado, Uwani ta shigo tana cewa"Kuma Nazifin yana kallo kika taho?"

Ta ce"A'a ba ya nan, sai dai ya dawo ya ga wayam".

Uwani za ta yi magana suka ji sallamar Baba, ya ɗaga labulen ɗakin yana cewa"Wace ta shigo yanzu kamar Maryam?"

Uwani ta ce"Ita ce, zama ya ƙi daɗi, tun a daren da aka kaita suke ƙunsa mata baƙinciki ba ta huta ba".

Baba ya ce"Ban gane zama ya ƙi daɗi ba, amma dai kin manta kwana biyu da kaita gidan miji ko? Da har za ta kwaso ƙafa ta dawo ta shimfiɗa miki ƙarairayi ki yarda. Ke ta shi ki fice ki koma gidanki".

Uwani ta rafka salati har da tafa hannu kafin ta ce"Wallahi Malam irinku ne masu siyar da ƴarsu a gidan auren, ta yi ta bauta da sunan zaman aure, ai aƙalla ka tsaya ka ji me ya dawo da ita tukunna kafin ka kore ta".

Ya ce"Wane irin rashin haƙuri ne zai sa ta dawo gida kwana biyu da aure?"

Ta shiga tsara masa ƙarya da kashi-kashi, har da cewa yau ɗin Gwaggon har marinta ta yi a gaban shi bai ce komai ba, ga shi kullum sai ta yi mata tuwo, ga jikarta tana zaginta. Baba ya yi shiru yana nazari kafin ya ce"Uwani duk da hakan wannan bai kai ta taho gida, ko waya ce sai ta yi wani ya je a sasanta yanzu idan aka fahimci har ta zo gida me duniya za ta ce?"

Uwani ta ce"Ita fa rayuwa indai za ka biyewa duniya za ka ƙare a wahala ne, ina ruwanka da duniya ko mutanen cikinta, yadda za su yi suka don ta dawo haka za su yi idan miji da uwarsa sun kassara ta".

Tsaki Baba kawai ya yi, don ba ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login