Showing 27001 words to 30000 words out of 37653 words

Chapter 10 - MIJI GOMA. Hausa novel

23 Oct 2025

84

mata ma shi ne tana da farinjinin masoyan, wannan karon ma tun kafin ta yaye Abba maza suka fara sallama da ita, sai dai ta ce musu sai ta yaye ɗanta. Akwai wani Alhaji Haruna da suka haɗu da shi a kasuwa, ya fi kowa naci cikin masu sonta, don har cewa ya yi zai aure ta a hakan, amma ta ce a'a sai ta yaye, ita bai ma wani kwanta mata sosai ba, saboda yana da matarsa da ƴaƴa huɗu, ita kuma tana da kishi, sam ba ta son zama da kishiya, amma ta sani tun da ita ma yanzu ba buduruwa ba ce dole ta jingine burinta a gefe, aurenta uku da ƴaƴa biyi ba zai yiwu ta ce sai saurayi ba, don haka take ɗan kula shi.

Sanda ta yaye Abba ta fara zancen aure sai Nasiru ya ce to zai ɗauki ɗansa, don har ma ya yi wani auren, nan Uwani ta fara subaɗaɗi tana cewa a bar mata shi, a cewarta yaron ya shiga ranta, ba za ta iya rabuwa da shi ba, ita kuma Maryam ta fi zargin wannan dubu ashirin ɗin da yake kawowa duk wata ce ta ruɗe ta, don haka ta ce a'a gara ya ɗauke shi ɗin, ba ta so a ɗora mata wahala, haka dai Nasiru ya ɗauki ɗansa, gidan iyayensa ya kai shi, tun da ba a daɗe da yin auren na shi ba, kar ya hana su cin amarci, duk sati ake kawo mata yaran nata su wuni wataran ma su kwana ɗaya sai a mayar da su, tana jin babu daɗi a ranta, saboda fargabar yadda tarbiyyar yaran za ta kasance, idan ba ƙaddara ba me zai saka uwa tana raye a raba ta da ɗanta? Haka dai take danne damuwarta tana bin su da addu'a, kwanciyar hankalinta ɗaya ce duk mariƙan yaran suna son su, ba ta ga alamar wahala a tare da su ba.

Wata ɗaya da mayar da Abba, Alhaji Haruna ya zo da zancen aure faka-faka, ya ce sati biyu za a saka, Maryam da yake har lokacin ba sosai take son shi ba sai ta fara yi masa kwana-kwana, a wannan karon aure take son yi na har abada, saboda haka yana da kyau ta samu wanda zuciyarta ta amince da shi ɗari bisa ɗari, shi auren wanda kake yi wa so sahihi fa yana da alfanu, saboda idan zama ya yi zama saɓani ya fara shiga tsakaninku wannan son da kake yiwa mutum yana taka muhimmiyar rawa wajen haƙurtar da zuciyarka ka ci gaba da zama da shi, kana jure wasu abubuwa, saɓanin wacce ta yi auren manufa babu son miji a zuciyarta, daga wannan abin da ta aure shi don shi ya gushe, shikenan sai ta tsane shi, tun da dama babu so tun farko, idan kuwa ka tsani mutum ba za ka taɓa yi masa uzuri ba, komai ya yi na laifi sai ka yi masa hukunci.

Ƙiri-ƙiri Uwani ta nuna ba ta son wannan auren, saboda ganin yadda Alhaji Haruna yake son Maryam kamar bai taɓa aure ba, sai bushasha yake yi mata da kuɗi kamar ba ya so, da alama duk ya fi mazajen ƴaƴanta rufin asiri, dama mijin Mardiyya shi ne abun tutiyarta da nunawa a gari ƴarta ta yi goshi tana auren mai kuɗi, sai ga shi Maryam za ta dusashe tauraruwar Mardiyyar, don haka ta ɗauki hassadar duniya ta saka a ranta, ta yi ta zuga Maryam a kan kar ta aure shi, ta ce"Ke yanzu Maryam da ajinki da kyaunki da komai za ki auri babban mutum mai mata da ƴaƴa huɗu? Ni sai nake ganin kamar kin faɗo"

Maryam ta yi murmushi ta ce"Ba faɗuwa ba ne babarmu, kin ga zaman gidan ba shi da wani amfani, kuma idan kika duba kika gani ni ma fa kullum ƙara girma nake, ban yi ƙanƙantar da za a ce Alhaji ya yi mini girma ba, saboda haka wannan ba komai ba ne, Allah dai ya ba mu zaman lafiya".

Uwani ta ce"Amma Maryam za ki iya zaman kishi kuwa? Ba mu san halin matarsa ba".

Ta ce"Babu ruwana da ita, ba zamanta nake yi ba, idan kin ji kanmu to ita ce ta so hakan".

Duk inda ta yi sai Maryam ta tare, haka dai ta rabu da ita ta zubawa sarautar Allah ido, tana jira a yi auren ta ji ta ina matsala za ta fara, ita dai ta san a yadda ta tafi haka za ta dawo, ko ta dawo da ciki ta ƙara haihuwa a gida, haka za ta yi ta rabon yara gida-gida.


Sai da Alhaji Haruna ya je wajen Baba da ƙoƙon bara kan a yi wa Maryam magana ta amince da auren da wuri, saboda babu amfanin jinkirtawar, Baba ya zaunar da Maryam ya yi mata nasiha sosai, saboda ya yaba da hankalin mutumin, kuma shi ma a yanzu ya fi so ta auri babba, kamar zai fi haƙuri da halinta, saɓanin yara da ƙuruciya kawai ake zabgawa a zaman auren, ya faɗawa Maryam shi Alhajin ya ce zai yi mata komai na kayan ɗaki, don haka ba ta da wani uzuri na cewa ba ta shirya ba, ta ce shikenan ta amince, Baba sai ya bi ta da kallon tausayi, ba ya jin daɗin wannan mace-macen auren nata, ga shi kwana biyun nan ya ganta duk a sanyaye kamar tana da wata damuwa, duka ta rage tsiwa har ma yawon bin ƙawaye.

Yayin da Maryam ta amince da auren Alhaji Haruna, shi kuma yana can ana gumurzu a gidan shi, matar shi Rabi masifaffiyar mace ce, tun da ya yi zancen ƙara auren shikenan ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai tijara take yi, amma shi ya ce mata aure babu gudu ba ja da baya, sai ya yi, wannan ne karo na uku da yake niyyar yin aure, amma sai ta je gidan su yarinyar ta tada tarzoma har a fasa, don haka wannan karon sai ya zaɓi sanarwa Maryam halinta.

Ranar ya zo zance yake cewa"Maryam a gaskiya ba zan ɓoye miki ba, matata ba tana da kishi sosai, tun tuni nake son ƙara aure ta hana ni, dama kuma dai lokaci bai yi ba, amma a yanzu ina ji a jikina ke ɗin ce ta aure in sha Allah! Saboda na shirya fito na fito da ita a wannan karon".

Maryam ta ce"A'a don Allah ka lallaɓata, kar ka rabu da matarka saboda ni".

Ya ce"Ba zan rabu da ita, amma aure dai babu fashi, ke kuma sai ki shirya zama da ita, kar ki ce za ki rabu da ita ta ci tuwo a kanki, ku zauna lafiya dai kawai saboda ni ma hankalina ya kwanta, tun da kin ga gida ɗaya za ku zauna".

Maryam ta ce"Ni idan da hali ka raba mana gida mana".

Ya ce"Wallahi haka na tsara tun farko, ginina na mata biyu ne ita ma ta sani kuma tun da na gama ginawa na sanar mata zan ƙara aure".

Ta ce"To shi kenan, Allah Ya sassauta zuciyarta".

Ya amsa da amin, sannan ya nuna mata vedion gidan a waya, gida ne babba mai kyau, daga farfajiyar tsakar gida babba sai a shiga babban falo, mai ɗauke da manyan kujeru, kayan kallo da firji komai dai an saka falo ya haɗu, akwai dining a ciki, sai kitchen da banɗaki, sannan a shiga cikin gidan, ɗakin da zai saka Maryam ɗin ne a farko, ciki da falo da banɗaki a ciki, ita ma na uwar gidan haka yake, sai ɗakin shi da kuma ɗakunan yara guda biyu, sannan wani banɗakin a tsakar gida, ga bantileson mai ɗauke da shuke-shuke da famfuna, gidan ya burge ta, ta miƙa masa wayar tana cewa"Ma sha Allah ya yi kyau".

Ya ce"Zuwa gobe jibi za a gama kayan ɗakinki, sai a saka, zan ba ki kuɗi sai ki sayi kayan kitchen ko? Gobe muka yi da ƴan gidan namu za su kawo kayan lefe".

Ta ce"Allah Ya kaimu".

Ya ɗan yi jim kafin ya ce"Don Allah ku yi haƙuri da abin da ƙila ƴan'uwana za su iya yi a yayin kawo lefen, kin san da yake Sauda ƴar'uwata ce, auren gida aka yi mana, kuma ita Innar tawa ita ta riƙe ta tun tana ƙarama, da ta isa aure ta aura min, to yanzu haka tana nan tana taya ta kishi, don ban faɗa miki ba ne ba ma, amma Sauda ta yi yaji tana can gidanmu, kuma Innar ta goya mata baya ta ƙyale ta, sannan akwai wasu ƙananun maganganu da suke yi, wai ai ba zaman aure kike yi ba, ko na aure ki za ki fita, sai dai kin toshe kunnuwanki gaskiya".

Jikin Maryam ya ɗan yi sanyi ta kasa cewa komai ta tafi duniyar tunanin kalar zaman da za su yi.

Alhaji ya ce"Maryam kin yi shiru, ina son ki, kuma sannan zan kwatanta adalci daidai gwargwadon iyawata a tsakaninku, ba zan ga wata ɓaraka na ƙyale ba, amma kin san komai sai kin yi haƙuri kafin ki ci riba".

Ta ce"To Allah Ya ba mu zaman lafiya bakiɗaya".

Suka yi sallama Maryam ta shiga gida a sanyaye, da a da ne da tuni ta juyewa Uwani komai, amma a yanzu sai ta yi shiru ta bar abun a cikinta tana fatan Allah Ya ba su zaman lafiya.

Washegari ƴan kawo lefe suka zo, mata ne su biyar, suka kawo akwati guda huɗu, kuma babu laifi ya saka mata kaya sosai, duk da sun rage a cewarsu ai wannan kayan bai cancanci bazawara ba, ƴan'uwa da aka gayyato karɓar lefe da ƙawayen Uwani suna ta ɗaga kaya suna cewa"Ma sha Allah! Kaya sun ce".

Wata cikin masu kawo kayan ta taɓe baki ta ce"Iyyi kaya sun yi fa! Sai fatan Allah Ya sa kunun banza ya ƙare a farau-faru ɗin banza".

Wata ta ce"A to, tun da dai amaryar an ce ba mazauniya ba ce a gidan aure".

Wata cikin dangin babar Maryam ta ce"Daɗin abun dai shi ya gani ya yaba, sai a bar shi da zaɓin shi".

Wata ta ce"Kuma mutuwar aure ai ƙaddara ce, ƙaddara kuwa tana kan uban kowa, ko a yau idan uban mutum ya kwanta ya mutu uwarsa ta zama bazawara".

Wata cikin masu kawo kayan ta hasala ta ce"Kin ga kar ki zage ni, wallahi kar ki sake, dama an faɗa mana ba gidan arziƙi ba ne, ƙaddara ce da biyewa zuciya ya kawo shi".

Nan aka fara maganganu, hayaniya ta kaure a gidan, aka rabu baran-baran dutse a hannun riga, ko tukuici ba a samu damar ba su ba, suka tafi.

Wannan abu da ya faru ya ƙarawa Maryam baƙinjini a wajen dangin Alhaji Haruna, musamman mahaifiyarsa da ta cika ta yi fam kamar za ta yi bindiga, musamman idan ta kalli Sauda da yaran a gida, a cewarta ya zaɓi wata mara tarbiyya ya watsar da matarsa ta ƙuruciya da ƴaƴansa, don haka fushi take yi da shi sosai.

A haka dai Alhaji ya toshe kunnensa, suka yi ta hidimar gabansu shi da Maryam, har ranar auren ta zo, aka ɗaura aurensu, an yi yini a gidan su Maryam saɓanin shi da babu abin da aka yi, ko abincin ƴan ɗaurin aure a can gidan matar baban shi aka yi, shi dai yana ta zumuɗin zuwan amarya babu abin da ya dame shi.

Bayan sallar isha'i aka ɗauki Maryam aka kai ta gidan miji a karo na huɗu, wanda take fatan ya zama na ƙarshe da za a sake ɗaura aurenta, ma'ana wannan aure ne ta yi na mutu-ka-raba.



(To fa! Ya kuka hango zaman Maryam a irin wannan gidan?)


Littafin nan na kuɗi ne a kan naira 500 kacal!
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay


08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_



*SADIYA ABDULRAZAƘ*


*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?*

Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu

*FIRST CLASS WRITERS*

https://chat.whatsapp.com/BuEB69AOiqBKg0PMiBzdG3

PAGE 14


Suna ƙule a ɗakinsu baban nasu ya dawo, Maryam ta tare shi ranta fess, ta haɗa masa ruwan wanka ta kai banɗaki, abin da ba ta taɓa yi wa sauran mazan da ta aura ba, ko ruwa a buta ba ta taɓa zuba musu ba, amma shi wannan da yake zaman gaskiya ta zo ta ɗaura ɗamarar yi masa hidima iyakar iyawarta, tsaf ta taya shi shiryawa bayan ya fito, sannan ta ja hannunsa kamar wani ɗanta zuwa falo, ta kawo masa tuwon, tana ba shi a baki suna ta firarsu cike da nishaɗi, har ya yi mamakinta saboda shi kansa ya san kafin auren ba wani son shi take sosai ba, kiran sallar magriba ne ya tashe shi, ya yi alwala ya tafi masallaci yana jin shi fess da shi, ya manta rabon da ya samu kulawa da soyayya irin wannan, sautari sai bayan magriba yake yin wanka saboda sai ya ce Sauda ta dafa ruwan take dafawa, wataran ma a haka yake kwanciya ko ya yi da na sanyi, sannan Momy ce mai kai masa abinci dining, idan ma ya shiga ɗakinsa yana wani aikin ko kuma ya shigo da wata damuwar, babu ruwan Sauda da zuwa ta ji dalilin ƙin fitowarsa, sai dai ta aiko masa da abincin ɗakin nasa, sannan babu ruwanta da tambayar shi fita unguwa, indai ka ga ta tambaye shi sai dai idan nesa sosai za ta je, gidan Inna kuwa idan za ta je tun rana idan ta tafi sai dare idan ya je yi mata sai da safe su taho tare, babu ruwanta da me zai ci ranar, babu dai wata kulawa akwai matsaloli birjik, wanda shi ne dalilinsa na son ƙara auren, kuma tun yau ya fara tunanin za a samu canji in sha Allah!

Ya dawo daga masallaci Maryam ta ga bai yi maganar yaran ba, ta dai leƙa bayan fitarsa ta ce duk su yi alwala su yi sallah.

Ta ce"Alhaji dama ina so mu yi magan a kan yaran nan".

Ya ce"To, wasu yara?"

Ta ce"Yaranka".

Ya ce"Me ya faru? Ba za ki samu matsala da su ba in sha Allah! Kin ga ma yara ne, uwar ma don Allah ki kau da kai ga matsalolinta".

Ta ce"Ba wata matsala ba ce, ka ga yau taliya na dafa da safe, na ba su suka ce wai ba sa cin taliya, sai kowaccensu ta shiga zaɓar abin da take so, ni kuma na ga ba zao yiwu na yi girki har kala huɗu ba, ko hakan bai zama almubazzaranci ba ai ka ga ni ma ina buƙatar hutu, tun da ba bautarsu na zo yi ba, sannan ba ma tarbiyya ba ce yara su dinga zaɓin abin da za su ci, na ce su tsayar da guda ɗaya, suka ce tuwo, shi ne na yi, loma ɗaiɗai suka yi suka ce mini ba daɗi, ƙarshe sai suka sha golden morn suka ƙule a ɗaki".

Alhaji ya ce"Ikon Allah! Wai kina nufin su yaran suna gidan nan? Waye ya kawo su?"

Maryam ta ce"Wai dama ba ka sani ba? Daga makaranta mai adaidaita sahu ya kawo su".

Ya ce"Yanzu suna ina?"

Ta ce"Suna ɗaki".

Ya shiga ƙwala musu kira ransa a ɓace, suka fito, Kausar da Momy suka haɗa baki wajen faɗin"Abba yunwa muke ji, ba mu ci komai ba".

Ya daka musu tsawa da faɗin"Ku nemi wajen zama!".

Suka zauna duk suka sha jinin jikinsu, saboda Abban nasu ba mai yawan faɗa ba ne.

Ya ce"A cikinku waye ba ya cin taliya? Yaushe kuka daina cin taliya?"

Duk suka yi shiru suna raba ido.

Ya ce"Wato ku har kun yi girman da za ku yiwa babba rashin kunya? Ku sa ta yi tuwo ku ce babu daɗi?"

Ya kalli Maryam ya ce"Idan akwai ki sako musu".

Ta tashi ta je ta ɗakko shi a yadda suka bar shi, ta ajiye, ya saka su a gaba sai ga shi sun cinye tass, har da ƙari, ya yi mamakin dalilin da ya sa suka yi mata haka, ya zaunar da su ya yi musu nasiha sosai, ya nuna musu ita ma Maryam babarsu ce, duk abin da suka san ba za su yiwa babarsu ba to kar su yi mata, suka ce to, sannan ya saki jiki da su suka yi fira, Maryam ta ce su je ta yi musu wanka, ba su yi musu ba suka wuce, sai a lokacin ma ta sa suka yi home work, ƙarfe takwas Abba ya ce su je su kwanta, ita kuma Maryam ta kwashi unifom ɗinsu ta tafi wankewa, sai ga shi sun yi wankin a tare da Alhaji suna yi suna fira.

Ita kuwa Momy suna shiga ɗaki ta ɗauki wayar ta sanarwa Sauda duk yadda aka yi, Sauda ranta ya ɓaci matuƙa ta ji kamar ta taso ta taho gidan yanzu, ta fara tunanin wato daga zuwanta za ta sa ya tsani ƴaƴansa har yana yi musu faɗa? Nan gaba ai sai duka, kenan ya goyi bayanta nan gaba ko ita ce da laifi tana kallo za a tauyewa ƴaƴanta haƙƙi, ai kuwa ba zai yiwu ba, ta fara tunanin hanyar da za ta bi don ta hana su cin amarci, sai dai yaran sun yi ƙanƙantar da za ta saka su yi wata kissar, don haka kawai ta yanke gara ta dawo su fara gabza yaƙin, ta ce wa yarinyar ta yi haƙuri su kwanta, amma kar su sake bari ta yi musu wanka, ita ta yi da kanta sannan ta yiwa ƙannenta.

Washegari haka Maryam ta yi sammakon tashi saboda yaran, don tun a daren ya faɗa mata girki biyu ake yi da wanda za su ci, da wanda za su tafi da shi, ta dafa shayi ta soya doya da ƙwai ta saka musu a lunch box ɗin, sannan ta tafi ɗakinsu, ta tarar Momy ta yi wanka za ta fara yiwa sauran, Kausar tana cewa ita ba za ta yi mata, ta ce"Ya za a yi ki yi musu? Ke ma ai ba wuce wankan kika yi ba, ku wuce na yi muku".

Momy ta ce"Mu fa Ummanmu ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login