Showing 36001 words to 37653 words out of 37653 words

Chapter 13 - MIJI GOMA. Hausa novel

23 Oct 2025

94

dai na faɗa miki, idan kuma kin ƙi ji ba kya ƙi gani ba!". Ya fice ya barta tana ta bambami.

Inna duk a gabanta a ka yi komai, ba ta ce wani abu ba, dama idan da sabo ta saba da faɗan nasu, sai da ya fita ta ce"Sauda a nan fa ba ki da hujjar da za ki saka yara su raina matarsa, idan har ba kya son ta shiga sabgar yaranki to ya zama dole ki koma kansu ki ci gaba da kula da su, kin ga dai yadda ya gigice a kan yarinyar nan yake rawar kai, kina nan a zaune za ta gama mallake shi da kissarsu ta zawarawa, irin wannan gogaggun yaran da suke yin aure-aure wallahi ki kiyaye su,sai kin tashi a tsaye kin ɗaura ɗamara, saboda haka ni yanzu umarni nake ba ki ba shawara ba, ki kama hanya ki koma ɗakinki a yau, ki kula da ƴaƴanki, sannan ki yi iya yinki na ganin ba ta mayar da ke bora ba, kar ki yarda ta ƙwace miki mijinki da gidanki".

Sauda ta ce"Shi kenan Inna an jima zan koma".

Inna ta ce"Ko ke fa, wannan ai kina nuna mata ta fi ƙarfinki ne ba za ki iya da ita ba, saboda haka ki koma ki nuna mata gida naki ne, kuma miji da ƴan'uwan shi ma naki ne!".

Sauda ta jinjina kai cike da gamsuwa, ta tashi ta shige ɗaki.

Zama ta yi ta kira ƙawarta a waya ta sanar da ita za ta koma, ta ɗora da faɗin"Don Allah ya za a yi ki haɗa ni da wannan mai maganin? Na san shegiyar tana nan ta gigita shi, bazawara ana marari za a samu miji".

Aliya ta sheƙe da dariya ta ce"Alhamdulillah! Allah na gode maka da ka nuna mini ranar da Sauda za ta nemi maganin gyara zama".

Sauda ta ce"Au shaƙiyanci za ki yi mini kenan".

Ta ce"To ai ke ce kullum cikin kuri kike kina da ni'imarki ba sai kin sha komai ba, yanzu kika dawo hanya Hajiyata, zan turo miki lambarta".

Sauda ta ce"Malama yanzu fa nake so, zai yiwu ta aiko mini kayan a yau?"

Aliya ta ce"In sha Allah!".

Tana turo mata, ta kira ta a waya, suka yi ciniki gabaɗaya irin wanda ake cewa ban da me kishiya su ta siya na dubu ɗari, kuɗin gudunmawa ne dangi suka haɗa mata don ta yi gyaran dama, da yamma aka aiko mata da kayan, ta gama shirinta tsaf jira kawai take yi ya zo yi wa Inna sai da safe ta bi shi su tafi.

Yau ɗin Maryam shinkafa da miya ta yi, da alama yaran ba ma su taurin kai ba ne, don kuwa yau babu wanda ya yi magana a kan abinci, kowa ya ci, sannan sun tsaya ta yi musu wanka, ban da babbar da ta ce ita ce take yi da kanta dama, sai ta rabu da ita, amma dai sam sun ƙi yin fira da ita, don haka ita ma ta ke ta harkar gabanta.

Da yamma da ya dawo sai da ya tambaye ta yaran, ta ce babu wata matsala, ya yi wanka ya ci abinci, ya fita sallah ya dawo, dama idan zai fita sallar isha'i da mota yake fita saboda daga can yake wucewa gidan Inna ya yi mata sai da safe, don haka yau ma ya wuce, ya ɗan zauna bayan sun gaisa, hat yanzu ta ƙi dawo masa kamar baya, babu wata fira haka dai babu yabo babu fallasa, ya tashi zai tafi ta ce"Ka zauna".

Ya zauna yana sauraronta.

Ta ce"Sauda za ta bi ka ta koma kan ƴaƴanta, saboda haka kar na ji kar na gani, ka zama mai adalci a tsakaninsu, kar sabo ya sa a watsar da tsoho, ta farkon dai ita ce dahir ɗinka, ba zan ɗauki wulaƙanta mini ƴa ba wallahi, don haka ka ja kunnen yarinyar nan, ta kula ta kiyaye, tun da zuwa ta yi ta tarar da ita da ƴaƴanta, ba ta san faɗi-tashin da aka yi kafin ka kai matakin da kake a yanzu ba".

Ya ce"To Inna za a kiyaye in sha Allah!".

Ya tashi ya fita yana yi mata sai da safe, ya ɗan jima a motar kafin Saudar ta fito da akwatinta, ta buɗe motar ta shiga ya ja suka tafi, babu wanda ya ce wa wani ƙala har suka ƙarasa gidan, lokacin yaran suna ɗaki, Maryam kuwa tana hakimce a babban falo cikin wata fitinanniyar rigar bacci, suka shigo da sallama, niyyarta idan ya shigo ta je yin oyoyo amma sai ta yi turus ganin shi tare da wata wacce ba sai an faɗa ba ta san matarsa ce, sai da gabanta ya faɗi, ta daure ta ce"Sannunku da zuwa".

Alhaji kuwa ya bi ta da kallon burgewa, wankan ya burge shi, don Sauda babu ruwanta da wani wankan dare ballantana kuma kayan bacci, dogayen riguna ne marasa nauyi kayan baccinta tun da ta fara haihuwa, ya haɗiyi wani yawu muƙut wanda har Sauda ta ji sautin, zuciyarta ta ƙara kumbura, ta kasa shigewa kawai tana tsaye tana ƙarewa Maryam kallo, sai Alhaji ne ya katse shirun nasu da cewar"Na barki ke kaɗai a gida".

Sauda ta yi masa mugun kallo ta ce"E tabbas ita kaɗai, tun da a yanzu ita kaɗai kake kallo a mutum, su ƴaƴan naka ba mutane ba ne, komai ma ya same su ta matarka kake yi! Hmm!" Ta wuce fuuu ta yi cikin gidan.

Ya yi murmushin yaƙe ya ce wa Maryam"Kin ga Sauda ta dawo ko? Don Allah ku zauna lafiya, kin ga ma tun da ta dawo kan yaranta za ki fi kula da ni sosai ko?"

Ta yi farr da ido ta ce"Ƙwarai kuwa, zo ma mu je ka gani".

Ta yi ɗakinta, shi kuwa ya bi bayanta kamar raƙumi da akala, a gaban Sauda suka shige ɗakin nata, wacce ta fito daha ɗakin yaranta za ta shiga nata, ta manta rabon da ya shiga ɗakinta, sai dai ita ta bi shi nashi ɗakin idan ya kira ta, amma shi ne ya zo ya shige ɗakin amarya ko kunya ba ya ji, ta yi ƙwafa tana cewa"Lallai akwai aiki a gabana, tsohuwar kilaki ya kwaso".

Ta gagara zama a ɗaki, ko wanka ta kasa yi, sai leƙe take yi tana jiran fitowarsa amma shiru har ƙarfe sha ɗaya ta yi, ga shi ko sallar isha'i ba ta yi ba, kuma ta kasa yi, saboda tana son tabbatarwa da gaske a nan zai kwana? Shi kuwa Alhaji yana can Maryam ta saka shi a kwana ta kalallame shi, ta kanainaye shi har ya manta ma a ɗakinta yake.

Ƙashe dai sai sha biyu Sauda ta haƙura da leƙen ta yi sallah, ta kwanta, sai ta gagara yin bacci gabaɗaya ya ƙaurace mata, ta fara tunanin yanzu fa yana can tare da ita, lallai namiji ba shi da kunya, can dai ta fara tunanin ya za ta yi ta hana su sukuni, ta tashi ta fito a hankali ta shiga ɗakin yaranta, ta haska su, sai baccinsu suke yi hankali kwance, ta shiga tashinsu bisa shawarar zuciyarta, ta dinga jijjiga su duk suka tashi suna murza ido, ta sakawa fuskarta alamun firgici ta ce"Ku tashi don ubanku, aljanu ne suka shigo gidan! Suna ɗakin nan a ƙarƙashin katifarku!".

Ai kuwa a tare suka fara ihu, ta ce"Ku kwanta ba za su yi muku komai ba".

Suka fara kuka suna rirriƙe ta suna cewa a ɗakinta za su kwana.

Ta fizge tana cewa"Suna can a ɗakina sun cika ɗakin kowa ya yi ta kansa".

Ta fice a guje suka mara mata baya, amma kafin su shiga ta banke ƙofarta ta saka sakata, gabaɗaya suka ruɗe suka dinga ihu a mugun firgice kamar za su shiɗe.

A tare Maryam da Alhaji suka fito a ruɗe, suka tarar yaran suna ta buga ƙofar ɗakin babarsu, fitowarsu ya sa suka yi wajensu suna shigewa jikinsu cikin matsanancin kuka, Alhaji ya ruɗe ya fara tambayarsu me ya faru?

Suka ce"Aljanu, Abba aljanu a ɗakinmu".

Gabansa ya faɗi ya ce"Aljanu kuma? Me kuka gani?"

Inaa sun ruɗe, sai a lokacin Sauda ta fito tana cewa"Mene ne?"

Suka yi kanta suna kuka.

Alhaji ya ce"Kin ji wai aljanu".

Ta ce"Aljanu kuma?"

Ya wuce ɗakin a tsorace yana addu'a, ya haska bai ga komai ba, ya dawo a sanyaye ya ce"Abun ya bani mamaki wallahi".

Sauda ta ce"To kar dai fa ture aka fara yi musu".

Ya ce"Wane irin ture? Waye zai yiwa yaran nan ture?"

Ta ce"Wanda suka tsonewa ido mana, an ga yara sun cika gida tubarkalla ana son haukata su don kar ƴaƴana su moru".

Alhaji ya ce"Subhanallah! Kar na sake jin magana irin haka!".

Ya janyo yaran yana cewa"Tsorata kawai kuka yi babu komai a ɗakinku kun ji? Ku je ku kwanta zan yi muku addu'a".

Sauda ta ce"Au da gaske sai ka kora su, saboda kar kwanan ɗakin amarya ya wuce ka? Hmm dama uwa ce ba ta gudun ƴaƴanta duk runtsi, ku shigo nan!".

Ya ce"Ba za su shiga ba! A ɗakin nasu nake so su kwana ina son fahimtar wani abu ba ne kafin Allah Ya kaimu gobe na kira malamai a yi addu'a".

Maryam ta ce"Allah Ya rufa asiri". Ta koma ɗakinta, ita ma duk sai tsoron gidan ya kama ta.

Ya saka su a gaba suna turjewa suka shiga, ya zauna ya kunna karatun qur'ani a wayarsa, yana addu'a yana tofa musu, amma da bacci ya fara ɗaukarsu sai su zabura su farka suna maƙale shi, a haka suka kwana, ita kuwa Sauda ta yi baccinta ranta fess, tun da dai ta haramta musu wannan daren to ita fa buri ya cika, kuma ta saka a ranta yanzu aka fara wasan, ta ɗau alƙawarin sai ta fitini gidan gabaɗaya, sai kwana a ɗakin shi ya gagari Maryam, kafin ta tankaɗa ƙeyarta waje.



LAST FREE PAGES! A NAN ZAN TSAYA DA FREE PAGE, DAGA WANNAN SHAFIN DUK WANDA KUKA GANI A PAID PAGE NE, ƳAN'UWA KU BIYA KU KARANTA CIKIN AMINCI, YANZU ZA A FARA WASAN NAN, TAFIYA TA KISHI MAI CIKE DA ƘULLA-ƘULLA TURA ƊARI BIYAR ƊINKI TA NAN KI SHA KARATU CIKIN AMINCI.

8028966015
Sadiya Abdulrazak opay


08028966015

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login