Showing 3001 words to 6000 words out of 37653 words
ce"Ai kin san dama gidan haya ne, ina da burin gina mata gida, to da na ci rabin ginin nan na ce mata nata ne, sai ta ce sam ita dai na yi aurena na tare idan ya so sai na ba ta ɗaki ɗaya ta zauna, gobe za ta dawo in sha Allah".
Kamar wacce aka fizgi zancen daga bakinta ta ce"Kuma tun gobe?"
Ya ji tambayar ba ta yi masa daɗi ba, da alama dai Maryam ba ta maraba da mahaifiyarsa, ya ce"To ai dayake ita kaɗai ce dama a gidan, sai wata jikarta ƴar yayana ita kuma yarinya ce, kin ga tare muke kwana a gidan, yanzu kuma ba na nan, akwai dai ƙanwata wacce take makarantar kwana, kin ga yanzu sai ita kaɗai, ba na son barinta ita kaɗai a gidan, shiyasa na ce gobe sai ta taho".
Maryam ta jinjina kai ta ce"To Allah Ya kaimu".
Ya amsa da"Amin my Love, ki yi alwala, ni ma bari na yi".
Ta ce"A'a ni na yi sallar isha'i yanzun nan".
Ya ce"To ai ta godiya ga Allah za mu yi".
Ta ce"Ka bari dai gobe ma yi".
Ya ce"Da dai kin daure mun yi yau ɗin, don ina cike da ɗokin kasancewa da amaryata, kin ga ya kamata mu fara gabatar da sallar tun da sunna ce".
Maryam ta kyaɓe fuska kamar mai ƙyamar wani abu ta ce"Wallahi kar ma ka saka rai, don yau a gajiye nake, sai dai mu bar wa gobe".
Ransa bai so ba, amma ba ya son takura mata, don haka ya ce"Yau da gobe ai duk ɗaya, ni bari na yi nafila".
Ya ɗauki buta ya shiga banɗaki, ita kuma ta koma ɗaki da sauri, ta ɗauki wayarta ta kira babarsu, ta ɗaga tana cewa"Maryam lafiya kuwa da daren nan?"
Maryam ta ce"Babarmu kin ji wata sabuwa? Wai ashe wannan ɗaki da ya kulle na babar shi ne a nan gidan za ta dawo ta zauna".
Uwani ta dafe ƙirji ta ce"Na shiga uku! Me kika ce Maryam? Hauka ake yi? To wallahi ba ki samu gidan zama ba, kada ma ki miƙe ƙafa!".
Ƴarta Mardiyya da take kwance tana shirin yin bacci ta ce"Haba babarmu! Yanzu Maryam ɗin da aka kai yau kowa yana murnar ta yi aure kike cewa ba ta samu gidan zama ba? Me ta ce miki?"
Uwani ta ce"Maryam ki kwanta kin ji, gobe za mu yi waya, akwai ƴan sa ido a ɗakin" Ta kashe wayar tana tsuke fuska.
Mardiyya ta tashi zaune tana cewa"Wai me ta kira ta ce miki?"
Uwani ta ce"Mardiyya ba na son shiga shara ba shanu, ina ruwanki ne?"
Mardiyya ta ce"Gaskiya da ruwana! Ya za a yi a ce awanni da kai ta ɗaki har ta fara kiranki tana kawo miki ƙorafi? Ke kuma ai bai kamata tun yanzu ki ce mata ba ta samu gidan zama ba, ki duba ki ga fa duk mun yi aure sai ita kaɗai a gidan nan, ana ta murna ita ma ta yi kuma sai ki ƙi ƙarfafarta ta zauna? Me yafu ma wai?"
Uwani ta ce"Mardiyya me kike nufi ne? Na fa fi ku damuwar ganin Maryam ta yi aure ta zauna, gani na yi kamar ba ta yi dace na, wai ashe wannan ɗakin da kuka ce ya ce ban da shi a jere babar shi ce za ta dawo ta zauna".
Mardiyya ta ce"To sai me? Ita Naziyya da take zaune da uwar mijinta a gida ɗaya mene ne ya same ta?"
Ta ce"Babu komai, amma ita ai kin ga kowa da ɓangaren shi, ita kuwa Maryam ga ɗaki ga ɗaki fa suke, suna shaƙar numfashin juna, a kan idonta fa za su shiga wanka su fito, ko leda ya shigo da ita idonta a kai, to kuwa ina za su more amarci?"
Mardiyya ta yi ƴar dariya ta ce"Ta ina za su shaƙi numfashin juna kamar a ɗaki ɗaya za su kwana?"
Uwani ta ce"Ke dalla can rufe min baki, ku da ba ku san komai ba".
Mardiyya ta koma ta kwanta tana cewa"Allah Ya kyauta".
A ɓangaren Maryam amarya haka suka kwana tana tunanin irin zaman da za su yi da mahaifiyarsa, da yake babu nisa tsakanin gidansu da gidan su Nazifi ta san mahaifiyar tashi, sai dai taƙaimaimai ba za ta ce ga halinta ba, tun da su kaɗai ne a gidansu ballantana wani ya ga wani halin nata mara kyau, ita dai ta saka a ranta babu ruwanta da babar shi tun da ba a kanta za ta zauna ba, kowa ya yi ta kansa, sai dai fa ba za ta ɗauki raini ba, duk abin da ta ga an yi mata ba daidai ba ba za ta yi shiru ba, don gidan aurenta ne tana da cikakken ƴancinta, Gwaggo ta ja girmanta ita ma ta ja ƙanƙantarta. Haka shi ma Nazifi ya kwana da tunanin Allah Ya ba su zaman lafiya da mafimtar juna a zaman su da Gwaggo, yana son Gawaggo yana son Maryam don haka dole zai yi wa kowa adalci don ganin sun zauna lafiya.
Washegari da safe suna cikin karyawa sai ga kiran Gwaggo, ya ɗaga suka gaisa ta ce"Nazifi ka manta da mu ka tafi aiki ne?"
Ya ce"A'a ina gida yanzu dai zan fito".
Ta ce"Ikon Allah! Yanzu ƙarfe tara kana gida Nazifi? Daga yin auren jiya za ka watsar da aikinka kenan? To ni dai na shirya ina jiranka".
Ya ce"To ga ni nan zuwa".
Maryam tana jiyo sautin muryar gwaggo da tattaunawarsu, ta jinjina kai kawai tana ayyana lallai wannan tsohuwar a tsaye take, to ai kuwa muddin tare za su zauna dole sai ta zaunar da ita, zaman dirshan ma kuwa.
Bayan ya fita ta wanke kofunan da suka ɓata, ta share gidan ta koma ɗaki ta kwanta, sai ga sallamar Nazifi tare da Gwaggo tana cewa"Gafaranku dai!".
Maryam ta tashi zaune tana taɓe baki, tana ji suna ta shiga da kaya ɗakin nata, ba ta fito ba sai da ta ji an buɗe mata kitchen, ta fito tana ɗaura ɗankwali da rarraba ido, Gwaggon ce ta buɗe har ma ta shige, kamar ta bi ta sai dai ta daure ta koma falo ta zauna, Nazifi ya shigo yana cewa"Maryam ki fito ku gaisa mana".
Ta ce"Ai za mu gaisa ita da ba yau za ta tafi ba, ba gobe ba, gaggawar ta mene ne?"
Ya ce"Hakane".
Ta ce"Na ga an buɗe min kitchen? Me ake nema?"
Ya ce"Tukwanenta da kwanuka ta ajiye".
Ta ce"Ok".
Ya daɗe da fita sannan ta fito ta shiga ɗakin Gwaggon, ta yi sallama Gwaggo ta amsa tana yi mata kallon tsaf, Gwaggon irin uwayen nan ce masu kishin ɗansu haka siddan, kuma haka kawai ta ji Maryam ba ta yi mata ba, saboda rawar jikin da Nazifi yake yi a kanta, Maryam ta gaisheta, ta amsa babu yabo babu fallasa, ga jikar tata a kusa da ita, wacce take ta kallon Maryam ɗin ba tare da ta gaishe ta ba, yarinyar za ta kai shekata tara, a ganinta ai ta san gaida manya, ta tashi za ta bar ɗakin Gawaggo ta ce"To mu fa ba mu karya ba muka taho".
Maryam a zuciyarta ta ce'To zumuɗin uban me kuke yi?' A fili kuma ta ce"To" A daƙile ta tashi ta fita tana tura baki gaba, saboda ita fa gani take takura ne zaman uwar shi a gidanta, shayi ta dafa dama biredi biyu ya shigo da shi jiya, ta kai mata ta ajiye ta fice, ta same shi yana shirin fita, ya ce"Zan fita, zan aiko da cefane, sai ki dafa da ɗan dama tun da ga Gwaggo kuma na san za a yi baƙi ma ko?"
Ba ta ce komai ba, har ya gama shirinsa ta ce"A dawo lafiya".
Yana fita ta ɗauki waya ta kira babarsu, sun gisa ta ce"Ya kuka kwana?"
Maryam ta ce"Lafiya ƙalau, amma fa kin ga tsohuwar nan har ta dawo, ta jera kayanta, wai abun takaici har kitchen ma haɗawa za mu yi, haka ta kwaso jiki don sauri ko karyawa ba ta tsaya ta yi ba".
Uwani ta rafka salati da sallallami kamar wacce ta ji mutuwa ko tashin hankali ta ce"Har ta dawo gidan, kenan amarcin ma a gabanta za ku ci!? Maryam wannan wane irin gidan aure kika faɗa, anya ba za ki yi bore ba kuwa?"
Maryam ta ce"Bari dai na ga yadda zaman zai kasance, idan na ga ba zan iya ba wallahi sai dai na bar mata gidan, yanzu ma har yana cewa ba yi girki da yawa, ga baiwa an kawo musu".
Uwani ta ce"To ai shikenan, idan dai kin ga da matsala kar ki yi shuru ki cuci kanki, aure irin wannan da aka fara shi da matsala babu inda yake zuwa, idan kuwa kin ga ya yi nisan zango to tabbas durƙushe matar aka yi, irin matan da suke ɗaukar miji kamar rayuwarsu, ke kuwa daraja da ƙimarki ta fi gaban nan wallahi, ƴata wanke hannu ka taɓa ce ta wuce zaman haƙuri a gidan miji wallahi".
Maryam ta ji daɗin maganganun babarta mai sonta, tana murmushi ta ce"Zan dai ga take-takensu tukunna".
Uwani ta ce"Yawwa, kuma kin san su iyayen miji idan kika nuna musu ke mai haƙuri ce da biyayya to fa tamkar kin ce musu ke bola ce a zuba miki kowace ƙazanta, wallahi ke ce ƴar iska a idonsu, don haka idan ta yi miki kallon yamma ki yi mata na arewa, wannan cewata ce".
Maryam ta naɗe huɗuba tass a kanta, suka yi sallama, ta ɗakko kazarta ta jiya da ba ta ci ba ta fara ci. Wajen sha ɗaya babarsu ta aiko mata da sauran kayanta, da kuma kula fal da jar miya wacce ta ji nama, shi ma Nazifi ya aiko cefane, sai ta soya naman da ya kawo ta ajiye ta dafa taliya ta ɗauki wata kula cikin tarkacen kayan Gwaggon da ta ajiye a kitchen ɗin ta zuba mata, ta yi sallama ta kai mata, tana ajiyewa Gwaggo ta buɗe ta ce"Kuma kya zuba miyar a kai?"
Maryam ba ta ce komai ba ta fice daga ɗakin, har zuciyarta take jin haushin matar kuma daidai take da zamaninta, dayake tana ta yin baƙi taliya leda uku da ta dafa ta ƙare, dab da magriba ta dafa macaroni leda ɗaya, ta raba gida biyu ta zuba mata rabi ta bar wa Nazifi rabi, don ita ba ta jin yunwar ma, da ta kaiwa Gwaggo ta buɗe ta gani, sai ta tura kular gefe.
Ana idar da sallar isha'i Nazifi ya dawo gidan, da ledojinsa biyu, ya siyo musu balangu da biredi ne, ya fara shiga ɗakin mahaifiyarsa da sallama, ta amsa tana yi masa sannu, ya ce"Yawwa sannu Gwaggo, ga wannan".
Ya miƙa mata biredin da balangu, ta buɗe ta ce"Allah Ya amfana, dama ban ci komai ba".
Da mamaki ya ce"Ba ki ci abinci ba Gwaggo?"
Ta taɓe baki ta ce"To ka san ni ba cin kayan basir ɗin nan nake yi ba, da rana ta dafa taliya, da daddare ta dafa macaroni, ni gaskiya ba zan iya wannan rayuwar ba, gara ma tun wuri ka auno garin tuwo, idan ba za ta ci ba ni ta dinga dafa mini, na fi gane na ci tuwona idan zan kwanta, da safe na ci ɗumame".
Jikinsa ya ɗan yi sanyi, ya ce"To babu damuwa in sha Allah gobe zan siyo, amma dai yau ɗin ki daure ki ci macaronin".
Ta ce"To bari na gani".
Ya fita ya shiga ɗakin Maryam, tana kwance tana kallon hotunan biki a wayarta, ya sakar mata murmushi ya zauna a kusa da ita cike da shauƙin sonta, yau dai ta karɓe shi sun sha amarcinsu, sanda suka fito suna alwala ma sai da Gawaggo ta leƙo ta ce masa"Alwalar me kuke yi? Me kake yi a waje ba ka yi sallar isha'i ba?"
Cike da kunya ya ce"Na yi sallah Gwaggo kawai dai zan kwanta da alwala ne".
Ta taɓe baki ta koma ɗaki, haka da komai ya wakana ya ji kunyar fita yin wanka, sai ya bari sai tsakar dare sosai sannan ya fita ya yi, kuma ya yi taka-tsan-tsan sosai wajen zubar da ruwa ta yadda ba sosai za a jiyo ƙara ba, bai saka a ransa Gwaggo za ta saka musu ido ba, kawai dai shi ne yake jin kunya.
Ita kuwa Maryam da asuba ta yi nata wankan, lokacin ya tafi masallaci, Gwaggo da ta makara yau ta fito don shiga banɗaki ta ji ƙarar ruwa ana yin wanka, ta ce"Waye a ciki? Waye yake wanka da asubar fari?"
Wani ƙululun baƙinciki ya tsayawa Maryam a wuya, sai da ma ta ɓata lokaci sosai sannan ta fito tana haɗe rai. Gwaggo ta ce"Ashe ke ce".
Ba ta kula ta ba, ta shige ɗaki.
Da sassafe ta ji motsin an buɗe kitchen, don tun asubar ba ta koma bacci ba, tana dai kwance tana jira gari ya waye ta fita, ta fara tunanin me tsohuwar nan za ta yi a kitchen? Jin shiru ba a rufe ƙofar ba ya tabbatar mata har yanzu ana cikin kitchen ɗin, ta tashi ta fito ranta yana ɓaci, daidai sanda Gwaggo ma ta fito daga ɗakinta, tana cewa"Haka kawai kun ƙule a ɗaki kun bar mutane da yunwa? Yasmin!" Ta doshi kitchen ɗin tana ƙwalawa jikarta kira.
Ko kallon arziƙi ba ta yi wa Maryam ɗin ba, ita ma kuwa ta bi su kitchen ɗin, zaune ta samu Yasmin ɗin a kan turmi ta saka kwanon naman da Maryam ta soya jiya da rana a gaba tana ta ci har ta kusa cinyewa, ranta ya ɓaci don dama ita ba ta cikin jerin mutane masu haƙuri, ta ce"Kutt! Ke uban wane ya ce ki shigo mini kitchen har ma ki ɗauki abu ki ci?"
Gwaggo ta ce"Ke dakata! Kar ki zagar mini ita, don ta ci naman da ba da kuɗinki aka siya ba?"
Nazifi da y ƙaraso kitchen ɗin yanzu ya ce"Me yake faruwa ne?"
Takaici ya hana Maryam cewa komai, saboda ba ta son nunawa babar shi halinta tun yanzu, sai kawai ta jinjina kai ta fice daga kitchen ɗin.
08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?*
Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu
*FIRST CLASS WRITERS*
PAGE 3
Ɗakinta ta shiga ta riƙe ƙugu tana huci kamar mai jiran dambe. Nazifi jiki a mace ya ce"Gwaggo ya kamata ki nunawa Yasmin kuskurenta fa, wannan ai ba ɗabi'a ba ce mai kyau ta dinga ɗaukar abin da ba a bata ba".
Gwaggo ta ce"Au! Nazifi kenan dai ka goyi bayan matarka ko? Yanzu ƙarfe nawa? Ƙarfe bakwai da rabi kun ƙule a ɗaki kuna ta bacci ba ta fito ta sallame mu ba? Saboda na dawo gidanka da zama sai karatun yarinya ya ɓalɓalce? Ai shikenan". Ta faɗa tana rausayar da kai kamar abar tausayi.
Sannan ta ja hannun Yasmin tana cewa"Mu je ki shirya sai na ba ki kuɗi ki sayi koko a hanya".
Nazifi ya shiga ɗaki ya samu Maryam kamar za ta fashe, ya ce"Maryam yarinyar nan ba ta yi daidai ba, amma ke ma bai kamata ki yi magana ba, da sai ki faɗa min na tsawatar mata, kin san tana zuwa makaranta to don kar ta yi latti ne ya sa ta nemi abin da za ta ci".
Ta ce"Ka ga dakata Nazifi! Ta ya zan san tana zuwa makaranta alhalin a sharuɗan auren ba ka sanar da ni har da kula da wasu ba?"
Ya ce"Gwaggon ce wasu?"
Ta ce"Duk yadda ka ɗauka!".
Ya jinjina kai ya ce"To ki yi haƙuri ki je ko shayi ne ki dafa musu tun da akwai biredi, amma daga yau sai ki dinga tashi da wuri, tun da ita Gwaggo ta fi son karyawa da abinci ko kunu da ƙosai, shi ma sai idan babu ɗumamen tuwo, na manta na faɗa miki anjima zan auno gari, ita ta fi son tuwo".
Maryam ta ƙanƙance ido ta ce"Ni Nazifi na tambaye ka mana".
Ya ce"Ina ji".
Ta ce"Ku nawa aka aurawa ni? Kuma sannan zaman wa nake yi?"
Ya ce"Maryam! Kina nufin mahaifiyata ba ta da matsayin da za ki yi mata hidima?"
Ta ce"Ba zancen matsayi ake yi ba, ka ga ba na son abin da za a zo ana jin kanmu, tun wuri gara mu baje ta a faifai kowa ya ɗauki rabonsa, kai ka auro ni, zamanka nake yi, wallahi babu wacce za ta mayar da ni baiwa, to tsaya na tambayeka ma, da Gwaggo take gidanta kafin ta dawo nan wace take yi mata girki?"
Nazifi ransa ya ɓaci sosai, amma ya san halin matarsa ba a yi mata hayaniya, kuma ba zai so su fara samun matsala tun yanzu ba, ya ce"Kin ga zauna mu yi magana ta fahimta".
Ta zauna tana ɗauke kai.
Ya ce"Gwaggo fa uwata ce, idan kika kyautata mata ni kika yiwa, kuma ladanki yana wajen Allah, sannan ke ma za ki so idan zama ya haɗa babarki da surukarta ta kyautata mata..."
Ta katse shi da faɗin"To yaushe aka fara rayuwar aure a barzahu? Ni uwata ta gama tata rayuwar kuma babu surukar da ta takurawa".
Ya ce"Kenan uwata takura miki ta yi?"
Ta ce"Za dai ta fara".
Nazifi ya ce"Maryam ina sonki, amma gaskiya son bai kai yadda zan bari wani raini ya shiga tsakaninki da mahaifiyata ba".
Maryam ta ce"Sanin kana sona ne yasa na amince na aureka, amma ai kai ma ka san ka so kanka da yawa, a ce daga zuwana gidan na hau hidima da jama'a? Wai har wani tuwo zan dinga yi ina ɗumame?"
Ya ce"To ai ban ce ke za ki ci ba, ita za ki yiwa".
Ta ce"Nazifi idan kana so mu sasanta aurenmu ya yi ƙarko to ka yiwa sharaɗin da zan kafa assam'u wa ɗa'a".
Kallonta kawai yake yi, ta gyara zama ta ce"Ka ga dai a wajen ɗaurin aure ba a ce zan dinga kula da Gwaggo da jikarta ba, cewa ma aka yi za ka kula da ni, ni ban ce ba zan zauna da mahaifiyarka ba, amma sai dai mu rayu kamar ƴan zaman haya, idan gari ya waye ta fito na fito za