Showing 24001 words to 27000 words out of 37653 words
yake yi alaye yake yi mata, kurman baƙi ne kawai suke yi saboda a gabanta ne, kuma da fari ba haka take yi ba, ta yarda da shi sosai, nan ma Uwani ce ta zuga ta ta ɗora ta a keken ɓera ta ce duk ƙarya ce, dama ƴan kasuwa ba a isa a raba su da mata ba, ga su da watsewa da masu abinci, har da cewa Allah Ya sa ma bai ɗebo mata alaƙaƙai ba.
Tun daga ranar da Maryam ta ji haka shikenan ta kasa zaune ta kasa tsaye a gidan aure, ta matsewa Nasuru lamba take tuhumarsa babu dare babu rana, dayake yana sonta haka yake ba ta hujjojin kare kansa, daga ƙarshe ma ta ce munafurci ne yasa yake saka password a waya dole sai ya cire, kuma ta cire ɗin saboda a zauna lafiya, don haka ta samu damar bincikar wayarsa kullum, tsakar dare za ta tashi ta ɗauki wayar ta fice falo ta yi ta bincikenta, yana kallonta amma bai damu ba tun da ya san babu komai ba rashin gaskiya da za ta gani.
Ana haka ne ya sayi wata waya sakan a wajen abokinsa, ya ɗora wani daga cikin layinsa a kai, da yamma ya karɓi wayar bai ma duba ya ga mene ne a ciki ba, ashe da fina-finan batsa kala-kala, ta ɗauki wayar ta duba ta gani, shi ne ta tashe shi tsakar dare suka yi tijara har ya sake ta, tana ganin ba komai ba ne don aurenta ya mutu, sai kuma ta dawo a ranar ta san matsayinta da gadar kwalin da Uwani ta sakawa rayuwarta ta hau kai ta kwanta a rashin sani.
Wannan shi ne abin da ya faru a baya, yanzu za a ci gaba da labari.
08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?*
Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu
*FIRST CLASS WRITERS*
https://chat.whatsapp.com/G08KLEmlF3gJ3X4npkfIee
PAGE 11
Wunin ranar Maryam ba ta bar zuciyarta ta huta ba, tunani kawai take yi na irin zuciyar wasu mutanen, ta ɗauki Uwani tamkar mahaifiyarta, tana yi mata kallon gatanta, kusan ma za ta iya cewa ta fi sonta fiye da mahaifinta, saboda yadda take riƙe ta da amana, tun tana yarinya take kula da ita bayan rasuwar mahaifiyarta, ba ta taɓa ganin wani abu na nuna bambanci a tsakaninta da ƴaƴan da ta haifa ba, kuma da yake ita ma Maryam tana da sakin jiki da mutane da surutu sai ya zamana ba ta rakuɓewa kamar na ƴaƴan da babu uwarsu a gida, sabgarta kawai take kamar Uwani ce ta haife ta.
Ita Hansatu mahaifiyar Maryam ƙawar Uwani ce tun ta ƙuruciya, kowa ya san amincinsu komai tare suke yi, ƙawance irin na da mai cike da tsafta da yarda da juna, musamman da suka kasance maƙota, ga gida ga gida, Uwani ta samu miji da wuri ta yi aure, saɓanin Hansatu da ta samu jinkirin aure, har ana cewa aljani ne ya aure ta sai da ta girma Uwani ta yi haihuwa uku sannan ta samu miji, shi ma abokin mijin Uwanin ne, wanda bai yi auren wuri ba shi ma abun ya damu iyayensa, kawai sai mijin Uwani ya yi wani tunani, ya ce tun da ƙaddararsu ta zo ɗaya da Hansatu kawai a haɗa su a gani ko za a dace, kamar wasa aka haɗa su suka fara soyayya, kuma sai abun ya ɗore har aka yi aure, wata biyu da auren Hansatu da Malam Habu Allah Ya yi masa rasuwa, sanadin hatsarin mota, da yake direba ne shi, yana kai kaya Legas.
Nan fa marasa ilimi suka ƙara gasgata lallai aljani ne ya auri Hansatu, bayan ta fita daga takaba babu zato babu tsammani mijin Uwani ya ce zai aure ta, Uwani irin matan nan ne ma su tsananin kishi don haka ta girgiza matuƙa da jin zancen, ta tada hankali ta ce ba ta san zance ba, a cewarta Hansatu fa aljani ne ya aure ta, idan ya aure ta shi ma mutuwa zai yi, shi kenan ya bar ta da marayun ƴaƴa, ta ci kuka ta yi magiya, shi kuwa namiji idan ya so ƙara aure babu mai hana shi sai Allah, don haka ya ɗaura ɗamara, musamman da ya kasance ita Hansatu tana son shi ta karɓe shi hannu biyu-biyu, duk kuwa da caccakar da ake ta yi masu a gari ita da iyayenta na cewar za su yi auren cin amana, a haka dai aka yi auren nan tun da Allah Ya ƙaddara, kuma ana yi aka samu rabon cikin Maryam.
Sam ba a ga miciji a zaman nasu, duk yadda Hansatu ta so su sasanta Uwani ta ƙi ba ta dama, masifar yau da ban ta gobe da ban, a haka har aka haifi Maryam, sai kuma Allah Ya jarabci Uwani da son Maryam, idan ta rarrafo ta fito waje haka za ta ɗauke ta, sai ta ga fitowar Hansatu sannan ta ajiye ta ta shige ɗaki, to da Maryam ta girma take shiga ɗakin Uwani sai suka ja ta a jiki sosai, yaran suka haɗe kansu kamar ba ƴaƴan kishiyoyi ba, shekarar Maryam bakwai a duniya mahaifiyarta ta rasu, wajen haihuwa ta biyu, dama tun farkon cikin ya zo da matsala, kuma Allah Ya yi cikin ma abokin tafiya ne, ba ta haihu ba ta rasu, kuma dama tun da ta fara naƙuda aka tabbatar ɗan ya mutu a cikinta.
Kowa ya ji tausayin ƴar marainiyar nan Maryam, mutane sun yi mamakin yadda Uwani ta saka ta a jikinta ta rungume tsam, ta hana dangin babarta tafiya da ita, dama shi ma Baba ya hana, saboda ya san kishin Uwani da uwar kawai take yi tana son ƴar, haka aka bar mata Maryam, ana ta yabonta a gari, ita kuwa ta haɗe ta da ƴaƴanta aka ci gaba da yaruwa.
Sai dai me? Mayam ita ce ƙarama a kan ƴaƴan Uwani Mardiyya da Murja, amma samari ita suke hari tun tana ƙwailarta, ita a tunaninta Maryam za ta yo ƙashin baƙin jini irin na babarta, sai ga shi ta ga saɓanin hakan, nan hassada ta fara shiga zuciyarta sannu-sannu, ta fara jin haushin Maryam ɗin, su kuwa su Mardiyya ba su damu ba, don sun ɗauki Maryam ƙanwarsu kamar uwa ɗaya suke, sai Uwani ta dinga nuna musu suna cikin matsala sanadin haka, a cewarta babarta ce kafin ta rasu take yi mata maganin farinjini, su dai ba su saka a ka ba.
Da farko sai ta samu Baba kamar abun arziƙi take nuna masa illar wannan farin jinin na Maryam, ta ce tana da ƙuruciya mazan za su iya amfani da wannan damar su hillace ta, saboda haka a samu wani Malamin wanda zai iya dakatar da maza daga kanta zuwa sanda za ta yi hankali ta isa aure, Baba ya nuna sam bai yarda ba, duk da shi ma abun yana ba shi tsoro, musamman da ya kasance ita ta fi ta zakka da sauran yaran gidan, ita ba ta jin magana sosau, ga yawon bin gidajen ƙawaye, wani feleƙe da rawar kai da son girma ga kwalliya kamar babbar budurwa, Baba ya ce ko maza dubu ne za su zo babu wani dakatarwar Malami da ake buƙata, tun da dai ba zance ta fara yi a ɓoye ba, to a barwa Allah komai, kuma ba yanzu zai yi mata aure ba ai, sai ta gama sakandari, haka Uwani ta haƙura ta bar zancen.
Amma ta kasa haƙura, sai da ƙawarta ta zuga ta ta karɓo rubutun farinjini take bawa ƴaƴanta ba tare da sanin Maryam ba, a haka dai har suka samu mijin, a rana ɗaya aka haɗa na Mardiyya da Murja, dama daga su sai Maryam sannan ƙaramar ƴarta Fatima, wanda tsirarsu kaɗan ne da Maryam, don bai kai shekara ba.
To ita ma Maryam ɗin da yake ba ta jin magana, sam babu auren a gabanta, duk wanda zancen aure ne ya kawo shi ba ta fiya sauraron shi ba, tun ba a farga ba har aka gane, Uwani ta fara farinciki tana tunanin ƙila ita ma ƙaddararsu ɗaya da mahaifiyarta.
A hankali shaiɗan ya tunzurata, take tuna auren da ta kira da na cin amanarta da aka yi tsakanin ƙawarta da mijinta, ta ji a ranta lokaci ya zo da ya kamata ta ɗauki fansa a kan Maryam, ta yi ta tunanin abin da za ta yi mata, kafin ta yanke shawarar hana ta zaman aure, ba ta yin shirya kuma ba ta so ta yi a kan Maryam, sannan idan ta yi mata cutarwa ta ƙiri-ƙiri mutane za su gane da wuri, a yi mata terere, ta ruguje yardar da aka yi mata akan Maryam, shiyasa ta ga gara ta yi mata kisan mummuƙe, ta so a ce ta ƙi aure kamar babarta, yadda za ta fake da dama gado ta yi, sai ga shi ta tsayar da Nazifi, don bayan auren ƙanwarta Fatima sai Baba ya matsa da zancen auren nata.
Tabbas Maryam ta shiga ƙunci, ta ji baƙinciki da takaici, ta yi kuka tsakar dare ta share, wanda ta saka a ranta ba za ta sake hawaye saboda butulcin babarsu a gare ta ba, sannan ta saka a ranta ko da wasa ba za ta taɓa nuna mata ta san mummunan ƙudirinta a kanta ba, Uwani ta nuna mata so, ko da a ce ba so ba ne duka taku ne to fa tabbas ta yi ƙoƙari, don wasu ba sa iya sarrafa kansu har su danne ƙiyayyar mutum, sannan ta kasa yarda ma da cewar Uwani ba ta sonta, kawai ta fi yarda da shaiɗan ne da zugar ƙawayen banza ya sa take aikata mata haka, ko kuma ta ce ta aikata haka a baya, saboda komai da Uwani ta yi mata na hana ta zaman aure ya wuce a zuciyar Maryam, ta saka a ranta yanzu sabuwar rayuwa za ta fara yi, sai yanzu ta gane tabbas ta yi kuskure, ta kuma yi nadama.
Baya ta wuce, yanzu ta gaba ake yi, gaba ake iya gyarawa ba baya ba, don haka dole za ta yi gyara a rayuwarta, yanzu ita dai ba za ta fito ƙarara ta nunawa Uwani ta ajiye zancenta na miji goma ba uba goma ba ne, saboda shi maƙiyi ba ka ba shi ƙafar sanin abin da yake ranka, saboda kar ya canza taku ya shigo maka ta bayan gida.
A wannan daren Maryam ta ɗaukarwa kanta wani alwashi, ta ƙudure a ranta tabbas sai ta ba wa Uwani kunya, sai ta rusa mata burikanta, kuma ta hanya ɗaya hakan zai tabbata shi ne ta ɗaura ɗamarar jure zaman aure, ta saka a ranta za ta yi aure na mutu-ka-raba, idan ta gama idda ta yi aure ko wa ta aura, kuma ko wace matsala ta tarar a gidan auren, za ta yi haƙuri da ita, za ta zauna ta jure duk wani ƙalubale, kawai saboda mafarkin Uwani ya zama ƙarya.
Duk da tana kallon abun da kamar wuya gurguwa da auren nesa, saboda ta riga ta ginu a kan kalaman Uwani na ƙanzon kurege, ta san ba abu ba ne mai sauƙi a ce a lokaci a ɗaya ta sauka daga kan wannan hanyar da ta yi nisan tafiya a kanta, wannan ƙudurin da ta ɗauka daidai yake da mayar da kanta ƙasƙantacciya, a yanayin halittarta dama can ba ta da haƙuri, to ta ya za ta koyi wannan haƙurin ta dinga jure halin mijin da za ta aura ko yaya yake? Wannan shi ne babban ƙalubalen da take ganin za ta fuskanta, amma ta saka a ranta za ta jure ta kuma haɗa da addu'ar Allah Ya tallafe ta Ya zama gatanta.
Duk wata jarumta da dauriya Maryam ta yi, wajen nunawa Uwani ba ta gano komai na shirinta a kanta ba, ita kuwa Uwani da ba ta san wainar da Maryam take toyawa a zuciyarta ba sai ta ci gaba da biya mata karatunta, wanda sai yanzu ne Maryam ta ƙara gasgata lallai ita doluwa ce a baya ta yi wasa da damarta.
Ba ta ma gama tsinkewa da lamarin ba sai ranar da Murja ta yo yaji, saboda mijinta zai ƙara aure, ta ce ita wallahi sai dai ya sake ta, tun kafin Uwani ta ce wani abu a kai Maryam ta yi farat ta ce"Lallai wannan miji naki akwai ɗan banza! Duk zamanku nai ƙara aure ba sai yanzu? Wallahi kar ki yarda, da ki zauna da kishiya gara ki yi zaman gida, ai miji goma ba uba goma ba ne".
Uwani ta yi wuƙi-wuƙi ta ce"Amma Murja wa za ki barwa ƴaƴanki?"
Maryam ta ce"Ƴaƴa kuma ai dama tarbiyyarsu a hannun Allah take, ta bar masa su can su ƙarata ya riƙe su, ta nemi wanda ya fishi ta aura, ai wallahi wanda ya rasa Anti Murja shi ya yi asara, kalle ta fa sankaɗaziyya da ita, ƙila ma ta samu wani saurayin ya yi wuf da ita".
Murja ta yi dariya ta ce"Kai Maryam, ni kuwa wani saurayi ne zai kwashe ni? Kina kallon yadda wahala ta fara mokaɗar da ni?"
Maryam ta gyara zama har da kamo hannun Murja ta ce"Wallahi Anti Murja ni nan na yi miki alƙawarin sai na samo miki miji na gagari ko ba saurayi ba, ke dai ki yi ƙoƙari ya sake ki kawai, ina haihuwa na tsige yaron ko yarinyar mu fara falla zawarci, yasin sai na wayar da ke, idan kika fantama a gari sai an taro ki, wai wa ya ga Anti Murja a gaban motar wani Alhajin!".
Ta kwashe da dariya tana kallon yadda fuskar Uwani ta nuna rashin jin daɗi, hakan kuwa ya ƙara raunana zuciyarta tabbas wata kishiyar uwar ba uwa ba ce, kuma ba za ta zama uwar wani ba har abada.
Maryam ta dage ta dinga zayyanowa Murja jawabai, tana kwaɗaita mata yadda rayuwar zawarci take, Uwani ƙarshe tashi ta yi ta fice daga ɗakin, ta fara kiciniyar ɗora girki gabanta yana faɗuwa da fargabar kar fa Maryam ta yiwa Murja huɗuba, ta zo ta kashe aurenta ta rasa miji, tun da dama can sai da ta basu rubutun farinjini suka samu mijin, tana buduruwa ma kenan, ina ga yanzu da ta yi haihuwa huɗu? Lallai dole ta yi wa tufkar hanci, amma ta yadda Maryam ba za ta gano komai ba.
Ta ƙwallawa Murjar kira, ta fito, Uwani ta rufe ta da faɗa"Kin shige ɗaki kin bar ni da aiki, ni zan yi muku girkin kenan ko? Sai surutan banza kuke yi kamar yau kuka taɓa sanin juna?"
Maryam ma ta fito, Uwani ta ƙaƙalo murmushi ta ce"La Maryam ba da ke nake ba, ke ai kin yi nauyi, ina ke ina aiki? Ki koma ki yi kwanciyarki".
Maryam ta koma tana tunanin shin ta zuga Murja ta kaso aurenta saboda Uwani ta ɗanɗani baƙinciki, ko kuwa Murjar za ta kalla da matsayin ƴan'uwantaka da ke tsakaninsu ta ƙyale ta?
*Mun kusa gama free page fa, za ku iya biyan kuɗin karatunku 500 kacal ta nan*
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay
Ko ta nan
1869739740
Sadiya Abdulrazak access bank
08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?*
Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu
*FIRST CLASS WRITERS*
https://chat.whatsapp.com/G08KLEmlF3gJ3X4npkfIee
PAGE 12
Jin shiru babu motsinsu a tsakar gidan sai ta leƙo ta kuwa ga wayam, alamun suna cikin ɗaki, ta fito ta nufi ɗakin ta laɓe jikin labule tana sauraron su, daidai sanda Uwani take cewa"Shi ne za ki biyewa shirmenta? Ita ba ki ga kalarta ba? Kin manta da farinjininta? Ko kin manta sai da na karɓo muku taimako kafin ki samu mijin? Kina buduruwa ma kenan, ina ga kin zama bazawara? Maza ki tattara ki koma ɗakinki, kishiya ba kanki farau ba, ni ma na zauna da ita ballantana ke!".
Murja ta ce"Amma babarmu..."
Ta daka mata tsawa ta ce"Rufe mini baki! Wallahi sai kin koma, uzuri ɗaya kawai zan yi miki za ki zauna har sai ya zo biko, amma yana zuwa to wallahi ƙafarki ƙafar shi, ni za ki ja wa abun magana a gari?"
Daga nan Maryam ta ja ƙafa ta koma ɗaki jiki a sanyaye, sannan ta yi kokowa da zuciyarta da take ta faɗa mata ta zuga Murja, ta raya a ranta ƴar'uwarta ce, idan ta cuce ta kanta ta cuta, haka kuma idan an kasa gulmarta a tire ba za ta ji daɗi ba, don haka ta share su, kwananta biyu a gidan mijin ya zo, ai kuwa ko Baba ma bai shiga zancen ba, ita ce ta sasanta su, ta bi shi suka tafi, suka ci gaba da zamansu shiru abunsu.
Nasiru ya zo ya kawowa Maryam kayan abinci, sannan ya ba ta kuɗi don a yi siyayyar jariri, a haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Allah Ya sauke ta lafiya, ta haifi ɗanta namiji, aka yi suna yaro ya ci sunan mahaifin Nasiru Yusufa, suna ce masa Abba, duk wata sai ya zo ya ba ta dubu ashirin, amma sam bai yi zancen kome ba, wanda a lokacin a yadda Maryam take ƙishin yin aure da burin ta yi zaman aure babu abin da zai hana ta yarda ta koma gidan nasa, sau tari takan tuna da Nazifi ta ce dama ya dawo ya ce ta koma da za ta zauna da Gwaggo lafiya, to amma damarta ta wuce sai dai ta gaba, sai ta ci gaba da kula da ɗanta, ta kuma koma kasuwancinta, tana ra adana ribarta.
Taimako ɗaya da Allah Ya yi