Showing 12001 words to 15000 words out of 37653 words

Chapter 5 - MIJI GOMA. Hausa novel

23 Oct 2025

86

farko ita ce ta ce ta yarda za su zauna da Gwaggo amma kowa ya yi harkarsa, kowa ya yi girkinsa, to da farko ban amince ba, shi ne abin da ya tada tarzomar, duba da ganin mahaifiyata ce, tana da cikakken iko a gidana, kuma ta cancanci mutuntawa daga matata, amma da na ga hakan ya ƙi kawo maslaha sai na ce na amince da sharaɗin nata, ita ma kuma Gwaggon ta amince, amma dai har yanzu Maryam ɗin ta ƙi ta nuna saki kawai take nema".

Baba ya ce"Saki!? Kai ɗan yau ka haife shi ba ka haifi halinsa ba, ka ga ni fa shiyasa ba na saka baƙincikin ɗan yau a kaina, sai su kashe ka a banza, kuma dama Maryam ta fita da ban da ƴaƴan gidan nan, za ta aikata, auren ma da ya ta yi?"

Nazifi ya ce"Sai haƙuri Baba".

Baba ya tashi ya ce"Jira ni kaɗan".

Ya shiga cikin gidan ya ƙwalawa Maryam kira, har ta tashi Uwani ta mayar da ita ta zaunar tana tsuke fuska ta ce"Malam lafiya?"

Ya shigo ɗakin yana cewa"Uwani wannan wane irin shirme ne haka? Ya za ki ɗaurewa yarinya ta samu saken cewa ba za ta koma ɗakin mijinta ba?"

Maryam kamar za ta yi kuka ta ce"Baba ni fa wannan zaman ba zai yiwu ba".

Ya ce"A kan me? Ba matsalar babar shi ba ce? Ai ya karanta mini komai, ya ce zai bi sharaɗin da kika kafa da farko, ku zauna da uwar tashi ba ruwan kowa da kowa, sai kace wasu facaloli, kai Allah Ya shirya yaran zamani, maza saka hijjabinki ki wuce ku tafi".

Uwani ta ce"Haba Malam don ka ga ba ni na haifi yarinyar nan ba, shiyasa ba za ka ƙyale ni na ƙwatar mata ƴancinta ba?"

Ya ce"Ko wacce kika haifa ce haka zan yi mata, ni ba na ma taɓa sakawa a raina ba ke kika haifi Maryam ba, tun da ba kya wani abu na nuna bambanci, amma kin san wannan zaman nata ba shi da wata fa'ida".

Ya kalli Maryam ya ce"Ba ki tashi kin saka hijjabin ba?"

Ta tashi a zabure kamar wacce za ta kai wa wani duka, tana turo baki da haɗe gira ta saka hijjabin ya fita ta bi bayansa, ya ce"Ina akwatin?"

Ta ce"Gobe a kawo mini".

Uwani takaici ya rufe ta, sai take jin kamar da zuciyarta za ta tafi, sam ba ta so hakan ba, so ta yi a yita ta ƙare, auren nan ya mutu a cikin satin nan, duniya ta shaida.

"Maryam!" Ta ƙwala mata kira murya a shaƙe.

Ta koma ɗakin tana share hawayen da ya zubo mata, idan ta tuna haka za ta tsufa cikin bauta da rayuwar ƙunci sai ta ji har gara mutuwa a kan gidan Nazifin.

Uwani ta ja hannunta har ƙuryar ɗaki ta ce"Ba kuka za ki yi ba, ki koma ɗin amma ki ɗaura ɗamarar yi musu gashin ƙuma shi da uwar tashi, kada ki sake ki saurara musu, musamman ita uwar, saboda idan ta ga abun ba na ƙare ba ne, ita ce za ta saka dole ya sake ki, sannan kada ki sake yarda ku haɗa shimfiɗa, idan kuma kin je kin sakar masa jiki kin samu ciki kin ga kanki kika cuta, ki yi zaman zawarci da ciki".

"Ke Maryam!" Muryar Baba ta katse musu tattaunawar.

Wannan karon tare suka fito Uwani tana cewa"Allah Ya ba da sa'a Maryam".

Suka tarar da Nazifi a zaure, Baba ya ce"Tashi ku tafi Nazifi, Allah Ya rufa asiri".

Ya tashi ya naɗe tabarmar yana cewa"To Baba na gode, Allah Ya saka".

Ya yi gaba, Maryam ta bi bayansa, sai da suka ɗan yi nisa da gidan suka kusa kai wa titi sannan ya tsaya har ta ƙaraso, saboda su samu damar jerawa.


08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_



*SADIYA ABDULRAZAƘ*


*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?*

Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu

*FIRST CLASS WRITERS*

PAGE 6

Yana ɗan murmushi ya ce"Ki yi haƙuri Maryam komai zai wuce in sha Allah!".

Ta yi banza da shi. Ya ce"Ni fa ba nufina kawowa Baba ƙararki ba, da na san ma zai tilasta miki ki koma da ban zo ba, na fi so ki dawo mini ta daɗin rai ba dole ba".

Nan ma dai ba ta kula shi ba, sai ma ƙara sauri da ta yi, yana biye da ita har suka ƙarasa titi, a ranta tana ayyana zai gane kuskurensa na kafewa sai ya zauna da ita, a cikin adaidaita sahu ma da ya kamo hannunta fizgewa ta yi tana aika masa mugun kallo, ya ce"Kin ce abinci kuwa? Ko na tsaya mu siya?"

Ta yi kamar ba ta ji shi ba, sai ya kama kanshi ya ƙyale ta, ya ciro waya ya kira Gwaggo, ya ce"Gwaggo na siyo miki tuwon ko sai na zo na dafa mana wani abun?"

Ta ce"La ai ni yau na yi tuwona, ina ka tsaya ne?"

Ya ce"Ga ni nan a hanya".

Ya ajiye wayar yana kallon Maryam wacce ta haɗe fuska tamkar ba ta taɓa dariya ba, shi mamaki ya ƙi barinsa yadda soyayya take neman rikaɗa ta zama ƙiyayya, sun sauka a bakin titi, sai ya tsaya don ya siya mata wani abun, ita kuwa ba ta jira shi ba ta wuce gidan, a buɗe ƙofar take ta tura ta shiga ko sallama babu, har tana cin karo da kofin sulba da Yasmin ta bari a tsakar gidan, tana jin Yasmin ta ce"Gwaggo kamar wani ya shigo".

Gwaggo ta ɗan ɗaga murya ta ce"Wane ne a nan?"

Ta ce"Ƙila tumakai ne, je ki kora su".

Haushi ya kama Maryam, wacce ta ja ta tsaya a ƙofar ɗakinta, saboda mukullin yana wajen Nazifin, Yasmin ta fito ta haskata da fitila ta ce"Au!" Sai ta koma ta ce da Gwaggo"Maryam ce fa ta dawo".

Gwaggo ta ce"Au kuma shi ne babu sallama?"

Daga nan Nazifi ya shigo da sallama, Gwaggo ta amsa daga ɗaki, ya ƙarasa wajenta ya miƙa mata ledar hannunsa guda ɗaya, ta kau da kai gefe ba ta karɓa ba, sai ya ajiye su a ƙasa ya ciro mukulli ya buɗe mata ɗakin, ta shiga, ya ɗakko ledar ya ajiye mata ɗaya, ya ɗauki ɗayar ya shiga ɗakin Gwaggo, ya zauna yana cewa"Sannu da gida".

Ta ce"Yawwa, ashe ɗakkota ka yi".

Ya ce"E wallahi, kun gaisa?"

Gwaggo ta ce"Ba ta shigo ba".

Ya ce"Bari na kira ta".

Ta ce"Nazifi ba na son tada zaune tsaye, me gausuwarta za ta yi mini? Tun kafin a haife ta ake ta gaishe ni, kuma har yau ban rasa masu gaishe ni ba".

Ya ce"Ki yi haƙuri Gwaggo".

Ta ce"A'a haƙuri ita ya kama ai, ga tuwonka nan" Ta ƙarasa tana miƙa masa kulolin da suke ajiye a gefe.

Ya ce"Bari na yi sallah tukunna, kin ga har an shiga". Ya fito ya yi alwala ya tafi masallaci.

Kafin ya dawo Maryam ta fito ta yi alwala ta yi sallah, ta rufe ƙofarta, ta saka sakata, ta ɗauki ledar, tsire ne a ciki da lemon jarka, ta cinye tass ta sha lemon ta kwanta, tana ta tsara nau'in wulaƙancin da za ta fara aiwatarwa a gidan har bacci ya ɗauke ta.

Shi kuwa yana dawowa daga masallaci ɗakin Gwaggo ya shiga, ya zauna suna fira yana cin tuwon, har tara ta gota, sannan ya tashi ya yi mata sai da safe. Ya ga Maryam ta rufe ƙofa bai kawo komai ba, a zatonsa turo ta kawai ta yi ba ta saka sakata ba, amma sai ya tura ya ji ta a rufe, da mamaki ya fara ƙwanƙwasawa ya ji shiru, ya fara kiran sunanta ƙasa-ƙasa don kar Gwaggo ta jiyo shi ta gane halin da ake ciki, ƙarshe ya kira wayarta tana ta ringin ba ta ɗauka ba, ya rubuta mata gajeren saƙo ya ce"Don Allah ki buɗe kar a fahimci wani abun". Shiru babu amsa, da ya sake kira ma sai ya ji wayar a kashe, haka ya shige falo ya rufo ƙofar ya kwanta da kayan jikinsa, a ransa yana ta mamakin kalar zuciyarta, da ƙyar bacci ya ɗauke shi.

Da asuba da ya dawo daga masallaci ya yi zaton zai ga ɗakin a buɗe, amma sai ya gan shi a rufe, har ya yi tunanin ko ta makara ne? Sai kuma ya ga alamar ruwan alwala a takalminta da yake ƙofar ɗakin, ya jinjina kai ya shiga falon ya zauna, yana ta saƙa da warwara har gari ya waye, ya ji motsin Gwaggo ta fito hura wuta, sai ya fito ya gaishe ta, ya kalli ƙofar ɗakin har yanzu ba ta buɗe ba, ita ma Gwaggo ta kalli ƙofar don a zatonta yana ciki bacci suka koma, ta bi shi da kallo ganin ya koma falo.

Har takwas ta gota Maryam ba ta buɗe ƙofa ba, shi kuma wanka yake so ya yi ya canza kaya ya tafi kasuwa, ya kira wayarta, yanzu ta shiga amma ba ta ɗauka ba, ya yi mata text ya ce"Maryam wai mene ne haka? Ki buɗe mini ƙofa mana, wanka zan yi na tafi kasuwa".

Can anjima ya ji ƙarar buɗe ƙofar, yana fitowa yana banko ƙofar ta rufe, ya bi kayan da ta jeho waje da kallo, duka jakar kayan shi ne, dama bai samu nutsuwar jera su a cikin sif ɗin ba, mamaki ya daskarar da shi, sai ya yi saurin ɗaukar jakar ya shige falo don kar Gwaggo ta fahimci wani abu, ya ajiye ya fito ya yi wanka ya canza kaya, ya shiga ɗakin Gwaggon, ta miƙo masa kofin kunu da ɗumamen tuwo a roba, ya ce"Alhamdulillah Gwaggo".

Ta yi masa wani kallo ta ce"Kana nufin haka za ka fita ba ka ci komai ba? Ko teburin mai shayi za ka je?"

Tun da ta ce hakan ya san ta gane wani abu a tsakaninsa da Maryam, don haka ya sha kunun, ya ba ta ɗari biyar ta yi cefane ya yi mata sallama, ya tafi, ta bi shi da kallon tausayi don zuwa yanzu ta gama saddaƙarwa ɗanta bai yi dacen mace ta gari ba, tana fatan idan da alkhairi a zaman nasu Allah Ya daidaita, idan kuma babu alkhairi Allah Ya kawo rabuwar cikin sauƙi, amma ta ji haushin rufe ƙofar da aka yi wa ɗan nata mai haƙuri.

Ransa babu daɗi ya je kasuwa ya kama harkokinsa, komai yake yi yana tunanin me zai yi ya shawo kan Maryam su daidaita? Saboda yana sonta shi bai shirya rabuwa da ita ba, ko sati ba a yi da aure ba a ce a rabu? Sau ɗaya rak suka haɗa shimfiɗa da ita, kenan duk kuɗin da ya kashe daga neman auren zuwa auren ya yi asararsu a banza? Gaskiya ba zai yiwu ba, ko ta kama dole zai rabu da ita sai ya mori kuɗinsa tukunna.

Maryam sai ƙarfe goma ta fito, shi ma yunwa ce ta fito da ita, ta ga Gwaggo a tsakar gida tana wanke wake, don gyara shi take yi ta yi garinsa saboda yin ƙosai da safe, kallo ɗaya ta yi mata ta ɗauke kai, ta shige kitchen, ita ma Gwaggon ba ta kula ta ba, ta tsaya tana ƙarewa kitchen ɗin kallo, babu sauran kayan Gwaggo a ciki, ta ƙarasa ta dafa shayi da indomi, ta gama ta fito ta koma ɗaki, yanzu ta bar ɗakin a buɗe, tana gama karyawa ta fito ta share iya ƙofar ɗakinta, sannan ta shiga wanka da guntun tawul ko kunyar Gwaggo ba ta ji ba a matsayinta na surukarta sai ma ita ce ta kau da kai, tana Allah Ya kyauta a zuciyarta.

Tun da ta shiga ɗaki ba ta fito ba sai azhar ta fito za ta yi girki ta ga babu kayan miya, ta saka hijjabi ta je ta fita, ta yi ta yawo a unguwar har ta samu inda ake siyarwa ta siyo ta koma gida, daidai lokacin Nazifi ya sauka daga adaidaita, hannunsa ɗauke da ledar cefane, da bai yi niyyar kawo mata cefanen ba saboda abin da ta yi masa, sai kuma ya duba ya ga ai haƙƙinsa ne, ya kamata shi ya sauke nashi ko da ita tana tauye masa, kuma maslaha yake nema bai kamata ya yi abin da za a ce ga laifinsa ba, shiyasa ya yo cefanen, sai kuma ya ganta a waje.

Kallo ɗaya ta yi masa ta kau da kai za ta shige gidan, ya tare hanya yana cewa"Maryam daga ina kike?"

Ta harare shi za ta gota ta gefen shi ta wuce, ya ce"Tambayarki fa nake yi, ina kika je babu neman izini?"

A fusace ta ce"Kenan ba ka yarda na gama aurenka ba, shiyasa har kake tunanin idan zan yi wani abu sai da izininka!".

Yana saita ɓacin ransa ya ce"Mu shiga mu yi magana".

Ya matsa ta shige, ɗakin nata ya dosa, yayin da ita kuma ta shiga kitchen ta fara gyara kayan miya, ya na ta zaune yana jiran shigowarta ya ji shiru, sai da ya ji ta fara daka sannan ya fito ya shiga kitchen ɗin ya tsaya yana kallonta, ta gama dakan ta ɗauku ruwan da ta wanke kayan miyan ta watsa masa da gayya, ya matsa gefe yana cewa"Subhaballah! Mene ne haka? Maryam ƙalau kike kuwa?"

Ta ce"Gobe ma Gwaggon zan watsawa shi".

Nan ransa ta ɓaci ya ce"Ke Maryam kar fa ki ga ina lallaɓa ki, ki yi zaton za ki taka mahaifiyata na rabu da ke..."

Ta katse shi da faɗin"Ai ban ga alamar ka san darajarta ba, kuma wallahi ko ita ce ta zo ta yi mini tsaye a kai sai na watsa mata".

Ya ce"Me kike so da ni?"

Ta ce"Ka sake ni!".

Ya ce"Ba zan sake ki ba, ki ma daina wannan tunanin, don ba sadaƙa aka ba ni aurenki ba".

Ta ci gaba da aikin gabanta, ya ce"Wallahi ban yi zaton haka daga gare ki ba, na faɗa miki indai Gwaggo ce ta ce kowa ya yi sabgarsa, ba ki ga ta kwashe kayanta ba ma ta bar miki kitchen ɗi ba?"

Ta yi banza da shi.

Ya ce"Jiya kika kulle ƙofa, idan Gwaggo ta gane hakan kin ga ba za ta ji daɗi ba, sai ta ga kamar har yanzu ba ma zaman lafiya, ko me za mu yi don Allah kar ki sake yi mini haka, mu yi abun mu a ɗakinmu mu biyu".

Nan ma dai ba ta kalle shi ba.

Ya ce"Kenan kayan miya kika siyo? Ki yi haƙuri ai ga shi ma na siyo miki, bai kamata ki fara fita tun yanzu ba, har gara ki aiki Yasmin".

Ya ce"Mun shirya ko? Me kike dafa mana?"

Ganin dai da gaske ba za ta kula shi ba sai ya fice daga kitchen ɗin, ya shiga ɗakin Gwaggo yana cewa"Bari na koma, cefane na kawo mata".

Cike da tausayin shi ta ce"Allah Ya tsare".

Da ta gama girkin ta juye a kula ta kai ɗaki, dama iya cikinta ta dafa wanda zai ishe ta har dare, ta ci ta ƙoshi, ta kira babarsu a waya suna ta fira, tana ba ta labarin abin da ya faru tsakanin jiya zuwa yau, ta ƙara zugata sosai ta ce ita ma Gwaggon ta fara taɓa ta don sai ya fi fusata.

Da magriba da ya dawo ya shigo ɗakin, ya ƙaraci surutunsa ba ta ce masa ƙala ba, sannan ya tambayi abinci ba ta ba shi ba, har aka kira isha'i yana zaune, yana tafiya masallaci, ta fito ta yi alwala ta sakawa ɗakinta sakata, da ya dawo ya ga ta rufe ƙofar sai da gabansa ya faɗi, ga shi ba ya son ya cikata da bugun ƙofa har Gwaggon ta gane, sai ya shiga ɗakin nata, ya zauna shiru, ta ce"Nazifi ka ci abinci kuwa?"

Ba don yunwar yake ji ba da zai yi ƙaryar ya ci, sai ya girgiza kai alamar a'a, ta miƙo masa kula tama cewa"Shiyasa na dafa muku shinkafa kai da Yasmin".

Ya ɗauka ya ci, ya gama ya zauna shiru, yau ya kasa taya ta firar ma, saboda hankalinsa ba ya kanta, yana can wajen tunanin mafita a wannan auren nasu, har tara ta yi, ta ce"Ka je ka kwanta mana Nazifi, na ga kamar ba ka jin daɗi ko?"

Ya ce"To sai da safe".

Ya tashi ya fita, ya je a hankali yana buga ƙofar ɗakin, wanda Gwaggo tana ji, dama ta na son tabbatar da jiya a falo ya kwana, don haka ta leƙo kaɗan, ta kuwa gan shi tsaye, can kuma sai ya juya ya shiga falon ya rufe ƙofa, ita ma ta rufe ƙofarta tana jin tausayin shi, sai ta ji nadamar zuwa gidan tun farko, da ta sani ta yi zamanta a gidanta ƙila da haka ba ta faru ba.

Washegari ma haka ce ta faru, da safe a ɗakin Gwaggo ya karya ya fita, ƙarfe tara Maryam ta fito ta gama karyawa ta shiga kitchen tana wanke-wanke, ta gama ta fito da ruwan, ta samu Gwaggo duƙe tana sharar tsakar gidan, ta ɗaga ruwan ta sheƙo shi duka a kanta, Gwaggo da ta samu saukar ruwan babu zato firgita ta yi, ta ɗago da mamaki take kallon Maryam, Yasmin kuwa salati ta rafka har da ɗora hannu a ka, ta ce"Kai Gwaggon kika watsawa ruwa?"

Ita kuwa Maryam kamar wata makauniya kuma kurma haka ta koma kitchen ɗin ta fara sharewa, ta gama ta zo ta wuce ɗaki, har lokacin Gwaggo tana tsaye mamaki ya daskarar da ita, ta jinjina ki ta shiga ɗaki ta zauna jaɓar, saboda ba za ta iya ƙarasa sharar ba, a ranta tana ta tunanin wace irin mara kirki Nazifi ya kawo cikin rayuwarsa?

Yasmin ta ce"Ruwa fa ta watsa miki Gwaggo".

Gwaggo da zuciyarta take a kumbure ta ce"Babu komai Yasmin".

Ta shiga haɗa kayansu, ta ɗauki waya ta kira lambar babban ɗanta Shazali, suka gaisa ta ce"Don Allah zan iya samun ɗaki a gidanka ko na sati ɗaya ne?"

Ya ce"Gwaggo kamar ya? Mai zai hana? Ai ke kika ƙi tun farko".

Ta ce"To ga ni nan zuwa".

Ta ajiye wayar, tun da Shazali ya gina gidansa ya ware ɗaki ɗaya har banɗaki ya yi a ciki ya ce nata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login