Showing 18001 words to 21000 words out of 37653 words

Chapter 7 - MIJI GOMA. Hausa novel

23 Oct 2025

83

kake yi mini kwana biyun nan!". Ta ƙarasa maganar a hasale.

Ya ce"Kin ga ni ban ce ki ɗaga mini murya ba, masalaha ce na zo da ita".

Ta yi shiru tana sauraron shi . Ya ce"Maryam kin ga fa har yanzu ba a yi wata biyu da aurenmu ba, ɗan amarcin nan ba mu ci ba, ni da na so a ce matata sai ta yi shekara ɗaya ko wata shida haka kafin ta samu ciki, kin ga lokacin an ci amarci an fara marmarin samun ɗa ko ƴa, amma yanzu kalle ki fa don Allah, ni yanzu a shawarata kawai a cire cikin nan, tun da ba ƙwari ya yi ba, sai na siyo miki ƙwaya ki dinga amfani da ita, idan aka kwana biyu kika huta kamar nan da wata shida haka sai ki ɗauki wani cikin, don ni gaskiya yanzu duk na takura gidan ma ba daɗi yake yi mini ba".

Haushi ya kamata ta ce"Ka gama?"

Ya ce"Na gama".

Ta ce"Hamza ashe haka kake ba ka da kirki ba ka san ya kamata ba? Yanzu idan da tausayi ina ta wahala da cikinka za ka kalle ni ka ce na cire shi? To bari ka ji na faɗa maka, ko cikin shege na yi ba zan cire shi ba sai na haife shi, ballantana na halak, idan ka ga ba za ka iya zama da ni a haka ba ka sallame ni, ba a kanka na fara rabuwa da miji ba, miji goma ba uba goma ba ne!".

Tun da ta furta masa ba shi da kirki ya kafe ta da ido cike da mamaki, duk da ya san Maryam ko a wajen siyar da abinci ba kanwar lasa ba ce amma bai yi zaton za ta iya kallon mijinta ta ce masa ba shi da kirki ba, ya ce"Kina cikin hayyacinki kuwa? Ni ne ba ni da kirki?"

Tana yi masa wani mugun kallo ta ce"Akwai ƙarshen rashin kirkin da ya fi wannan? Ina fama da cikinka a maimakon ka tausaya mini sai ka ce a cire?"

Ya ce"Kin ga, ni fa ba tausayinki ne ba na yi ba, kawai dai dama can na tsara idan na yi aure matata ba za ta haihu da wuri ba".

Ta ce"To da ka san haka me ya hana ka zuge tazugen wandonka? Ai ka ga da ba zan ma samu cikin ba ballantana ka ce a zubar na ƙi".

Ya yi shiru ya rasa abun cewa, ta ce"Hamza! Na aureka ne saboda ina sonka, wallahi son da nake yi maka ba zai saka na ɗauki wulaƙanci daga gareka ba, idan ka san ba za ka iya ba tun wuri ka sallame ni, na je na raini cikina a gaban iyayena".

Tsaki kawai ya yi ya tashi ya fita.

Yana fita kuwa ta ɗakko waya, ta kira babarta ta juye mata komai, Uwani a zaune take amma sai da ta miƙe tsaye, a ranta tana faɗin 'lokaci ya yi'

Ta ce"Innalillahi! Ke dai Maryam ba kya dacen mazan aure, shi kuma ba ya son haihuwa? To ai har gara ma Nazifin shi matsalar babar shi ne, shi fa miji da ba ya son haihuwa ya fi uban kowa matsala a rayuwar aure, kin ga wannan maganar ma ai ba ta waya ba ce, gobe zan zo mu baje ta a faifai, ina! Ai ba ki ga wajen zama ba".

Maryam ta ce"To Allah Ya kaimu".

Haka kuwa aka yi, washegari da yamma ta je gidan nata, tana ganinta ta fara salati tana tafe hannu ta ce"Maryam kin ga yadda kika zama kuwa? Kamar wata horuwa! Mun shiga uku, nan duk cikin ne babu yunwa?"

Ba ta ce komai ba, ta gaishe ta ta kawo mata ruwa da abinci, ta ce"Ai Maryam ba zan iya cin komai ba, wai me ma kika ce mini? Har ya ce a cire cikin?"

Ta ce"Haka ya ce, ni kuwa babu mai saka ni na cire cikin nan wallahi!".

Uwani gabanta ya faɗi jin ba za ta yarda a cire cikin ba, ta san halin Maryam sarai idan ba ta son abu babu wanda zai mata dole, sai dai da siyasa da dabara.

Ta ce"Maryam kin san matsalar wanda ba ya son haihuwa kuwa? Kin ga na farko dai idan kika samu ciki a wulaƙance zai dinga kallonki, ga wahalar laulayi ga wulaƙanci da rashin kulawa, irin su gani suke ma asara ce su kashewa cikin kuɗi, sai ki ga mace idan ba sana'a take yi ba zuwa awo ma ya gagare ta, wani kuma hanawa zai yi ko da kuɗin nata, ke akwai wacce tana naƙuda mijin ya kulleta a ɗaki tana ihu tana magiya har sai da ta haifo ɗan ya mutu sannan ya buɗe..."

Dariyar da Maryam ta yi ce ta katse ta daga shararo ƙaryarta, ta ce"Maryam! Dariya ma kike yi?"

Maryam ta ce"To ai abun dariya ma ya bani, ya rufe ta a ɗaki fa?"

Ta ƙara sautin dariyar ta ce"Lallai wannan ba shi da kirki, ai kuwa da ni ce idan na fito kai ma sai na shaƙe ka ka mutu".

Uwani ta ce"Kina wasa da iskancin maza, to ai ni ba ma wannan gaɓar ce ta fi damuna ba, kin san kuwa idan aka haifi ɗan shi da babu duk ɗaya a wajensa? Wallahi ko sutura ba yi masa zai yi ba, wani ma sai ki ga yana tsangwamar yaron kamar ba jininsa ba, wani agolan ma ya fi shi gata, sannan kina nan zaune sake da baki zai auro yarinya ta yi planing su yi ta soyayyarsu suna ƙunsa miki takaici".

Maryam ta ce"Kamar dole? Wallahi babu namijin da zai yi mini haka".

Uwani ta ce"To kuwa maganin kar a yi kar a fara, muddin ba za ki iya ɗaukar wannan ba gara ma ki cire cikin nan, kuma ki nemi saki, don haihuwa da irin wannan mijin ba ƙaramar matsala ba ce".

Maryam ta ce"Ni fa ba zan cire cikin nan ba, haka kawai nake jin ina son abin da zan haifa, idan na haihu komai sai ya biyo baya".

Uwani ta ce"Kina nufin za ki jure cin mutuncin shi kafin haihuwar?"

Ta ce"Ba zai ma fara ba".

Duk ta inda Uwani ya ɓullo sai Maryam ta kauce, saboda ita ba za ta zubar da ciki ba, don haka Uwani ta tattara ta tafi, lokacin dab da sallar magriba.

A ƙofar gida suka yi kiciɓus da Hamza zai shiga, ya rage tsayi ya gaishe ta, ta amsa tana cewa"Ya mai jikin?"

Ya ce"Da sauƙi".

Ta ce"Ai yau dai na ce bari na zo na duba ta, ashe haka ta zama ta yi yarab kamar haihuwa ta goma? Na ci to Hamza dai sai haƙuri ba a samu damar angwancewa ba, to wannan yaushe mutum ta tada komaɗarsa? Ana ta jigilar amai da yawu".

Hamza ya ce"Wallahi kuwa, sai haƙuri".

Ta ce"Haƙuri ya zama dole ai, tun da abun nata na gado ne, uwarta ma fa haka ta yi, idan ta samu ciki duk haƙurin Malam sai ya ƙosa, ƙarshe daina rabon kwana yake da ita, kuma ba ma wannan ba, haka take haifo ɗan a yaƙune da cutar tamowa, duk mutuwa suka yi sai Maryam ɗin ce ta rayu, amma fa ta ci wuya, an kashe kuɗi maƙudai, idan aka kwantar da ita kamar gawa, a yaƙune, uwar ta sha mantawa ta fizgota ta yi zaton zani ne babu mutum a ciki".

Hamza ya cika da mamakin surutun matar nan, gefen zuciyarsa kuwa cike yake da tsoron kar a haifo masa ɗa irin wannan.

Ta ƙara da faɗin"Kai dai ka fara banki kawai, don da alama ita ma gado ta yo, sai anjima Allah Ya sawaƙe".

Ya ce"Bari na raka ki titi".

Suna tafe tana ƙara zuga shi da ƙarairayi kala-kala, shi kuwa ya hau kai ya zauna daram, ya sake jin haushin Maryam da ƙin zubar da cikin da ta yi, ya samar mata adaidaita sahu ya biya kuɗin sannan ya koma gida.

Ya tarar da ita tana sallah, ya yi alwala shi ma ya fita masallaci, da ya dawo ya zauna ta kawo masa abinci, ya ci kaɗan, saboda yanzu abincin nata ma ƙyanƙyamin shi yake ji saboda amai da tofe-tofen yawun da take yi, shi a yadda yake jin labarin haihuwa wannan jinin biƙin da sauransu bai ma san yadda zai zauna da ita inuwa ɗaya ba idan ta haihu, dole dai ta tafi gida dab da za ta haihu, idan ɗan ya yi wata uku sai ta dawo, saboda shi ko wata mata ce a unguwarsu take siyar da wani abu, daga ranar da aka ce ta haihu to fa ya daina siyan abu a wajenta, ƙyanƙyami yake ji, har sai ya manta ɗan ta ɓa girma sannan ya ci gaba da siya, ballantana kuma a ce matarsa wacce dole ya ci abincinta.

Ya yi nisa a duniyar tunani ya ji muryar Maryam ta ce"Wai me yasa yanzu ka rage cin abinci?"

Ya ce"Babu komai".

Sannan ya tashi ya fice daga gidan.

Tun daga ranar ya yi mugun jan baya da ita, duka ya canza mata, a da yana biyo ta ɗakin da ta koma da kwana su kwana tare ko ba ta so, daga baya ya daina, tsakaninta da shi da safe idan ya fito zau tafi aiki ya zauna ya karya, da yana dawowa ya ci na rana daga baya ya daina, sai na dare shi ma ba kullum yake ci ba, sannan ba ya dawowa gidan da wuri, sai ya kai sha biyu a waje, kuma tun da gara ta ƙare ta lura shi mutum ne mai maƙo da bin diddigin abinci, idan ya auno shinkafa kwana ɗaya sai ya yi ta mitar ta ƙare da wuri, ya ce duk cikin nan ne yake saka ta cin abinci, idan ta yi faɗawa Uwani ba ta ba ta shawarar komai sai ta cire ciki, wanda ita kuma ba ta so, don haka ma ta daina faɗa mata komai, jira take kawai ta haihu ya sake ta ta ƙara gaba.

Cikin yana wata biyar wataran ya shigo mata da balangu da lemo, ta manta rabon da ya siyo mata nama, ko ƴar kankana da lemon nan ba ya siyo mata, cike da marmari kuwa ta cinye tass, ta shanye lemon dama jarka ɗaya ne, babu jimawa kuwa ta fara jin ciwon mara, abu kamar wasa ciwon yana ra ƙaruwa, fitsari ya matseta, tana shiga banɗaki ta ga jini, ga shi ita kaɗai a gidan, ta nemo wayarta don ta sanar masa ta rasa ta, don ya ɗauka ya fita da ita, a tunaninta ba za ta nemi wata mafitar ba sai ta zauna har cikin ya zube.

Da ta ga abun ba na wasa ba ne, sai ta saka hijjabinta ta tafi gidan iyayen shi, da yake ba su da nisa, a jigace ta shiga gidan, tana shiga ta durƙushe a gaban Umman shi dake zaune a tabarma tare da ƙannen shi, da yake da hasken wutar nefa ta gane ta, ta ɗago ta tana faɗin"Maryam lafiya?"

Ta ce"Marara ciwo take kuma na ga jini".

Umma ta hau salati ta ce"Tashi mu tafi asibiti wannan ai ba ƙaramar matsala ba ce".

Suna zuwa aka ba ta maganin da aka yi nasarar tsayar da jinin, suka ba ta gado, sai a lokacin Umman ta kira Hamza a waya, ta faɗa masa asibitin da suke, ya ce ga shi nan zuwa, a ransa yana addu'ar Allah Ya sa cikin ya zube.


08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_



*SADIYA ABDULRAZAƘ*


*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?*

Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu

*FIRST CLASS WRITERS*

PAGE 9


https://chat.whatsapp.com/G08KLEmlF3gJ3X4npkfIee


Lokacin da ya ƙaraso asibitin Maryam tana kwance luf an saka mata ƙarin ruwa, ya shigo yana cewa"Umma wai me yake faruwa?"

Ta sake sanar masa a yadda Maryam ta zo, ta ɗora da faɗin"Kai ina ka shiga?"

Ya ce"Yanzu shikenan cikin ya zube?"

Ta ce"A'a Allah Ya taƙaita, amma ga scanning sun rubuta a yi".

Ta miƙa masa takarda, ya karɓa jiki a suluɓe yana jin babu daɗi na rashin cikar burinsa.

Maryam ta ce"Ina wayata?"

Ya ciro daga aljihu yana miƙa mata ya ce"Dama na ga cajin ya yi ƙasa kuma ba su kawo wuta ba, shi ne na kai miki".

Ta ji sam ba ta yarda ba, ta ce"Amma Hamza wannan lemon da ka ba ni akwai wani abun a ciki ko?"

Ya kalli Umma da ta kafe shi da ido, ya fara muzurai ya ce"Kamar ya? Ban gane ba".

Ta ce"To ya za a yi a ce daga shan lemo sai ciwo?"

Ta kalli Umma ta ce"Dama fa ba son cikin yake ba, ya ce na zubar na ƙi yarda, kuma ma na manta rabon da ya shigo min da ɗan wani abun motsa baki, sai yau ɗin ya kawo min balangu da lemo, kin ga tun da ba son cikin yake ba ai zai iya saka min maganin ma".

Hamza ya fara zabure-zabure ya ce"Wai kamar ya? Me kike nufi ne?"

Umma ta ce"Lallai biri ya yi maka da mutum, za ka aikata Hamza, na sanka dama ba son haihuwa kake yi ba, amma kuwa idan haka ta tabbata sai dai na ce Allah Ya shirye ka, Ya ganar da kai gaskiya! Ke kuma Allah Ya saka miki".

Ya ce"Wallahi Umma ban zuba mata komai ba".

Ta ce"Allah Ya san komai".

Sai ya fice ya bar asibitin.

Umma ta je gida ta kwaso ƴan abubuwan buƙata tun da sun ce sai gobe za a sallame ta, ƙanwar shi ce ta kwana da ita, washegari da safe aka yi scanning aka ce cikinta lafiya ƙalau, ashe ma ƴan biyu ne, kowa ya cika da farinciki ban da Hamza da ya ƙara sarewa da lamarin, mai ɗa ɗaya ma ya aka cika ballantana biyu? Ai kwamacala kawai za a yi masa a gida kafin su girma, ya kasa ɓoye baƙincikinsa har sai da Umma ta gane, ta san halinsa ta san haihuwa ba ta dame shi ba, ta zaunar da shi ta yi masa nasiha sosai, ya ce shi fa bai ce ba ya son haihuwa ba, da aka sallame su ƙanwarsa ce ta zauna a gidan har sati biyu, ba ta faɗawa Uwani wannan abun ya faru ba ma, har ta warware, laulayin ma yanzu ya tafi sai amai da ba ta daina ba har yanzu, da ta yi masa zancen zuwa awo ma cewa ya yi wannan awon kawai yawo ne, sai da ta haɗa shi da Umma sannan ya barta ta fara zuwa.

Da daɗi da ba daɗi cikin Maryam ya shiga wata na tara, idan ka ganta kamar ba ita ba, ta kumbura ta cika fam, hanci ya bubbuɗe, duk ta gaji da cikin, ko fita ba ta son yi sai a filin tsakar gida take ɗan zagaye tana tattaka ƙafarta, Hamza idan ya kalle ta wani mugun haushinta yake ji, shi kam inda ya san haka za ta samu ciki da wuri har gara ma bai yi auren ba, babu wani amarci da ya sha sai na laulayi. Wataran tana zaune a falo ya zo ya zauna ya ce"Maryam ya kamata ki tafi gida haihuwa ko? Tun da an shiga watan".

Ta yi wani murmushin takaici ta ce"Hamza ba don cikin jikina ba a cikin maza kai ba kowan kowa ba ne a wajena da har sai ka kore ni zan bar maka gidanka".

Ya ce"Ni kike faɗawa haka?"

Ta ce"Bari dai Allah Ya sauke ni lafiya sai mu tattauna, ni ba wannan ba, ban ga fa wani shiri da kake yi na haihuwar nan ba, ko riga ɗaya b a siya ba, me kake nufi?"

Ya ce"Kin ga kin haihu ban siya ba?"

Ta ce"Sai na haihun? To cikin kayanka sai ka zaɓo wanda ƴaƴan za su saka na tafi da shi a sibiti kafin ka siyo musu".

Ya ce"Kin ga ni na riga ma na faɗawa babarki gobe za ki koma gida, kuma zan bada kuɗin kayan yaran kafin ki haihu".

Bai jira cewarta ba, ya tashi ya fice.

Ta ɗauki waya ta kira Uwani, suka gaisa ta ce"Kin gama shiryawa?"

Maryam ta ce"Shiri na me?"

Uwani ta ce"Ba mijinki ya ce yau za ki dawo gida ba?"

Ta ce"E, yanzu zan tashi na shirya".

Ta ce"To sai kin ƙaraso".

Ta haɗa kayanta a akwati, ta ɗauki waya ta kira Hamza, ya ɗaga ta ce"Na gama shiryawa zan tafi".

Ya ce"To ki gaida gida, ki biya ta gidan Umma ki ajiye mini mukullin".

Ta ce"Kana nufin ba za ka zo mu yi sallama ba? Kuma haka zan tafi ziƙau-ziƙau ko ɗan kayan shayi ba za ka siya mini ba? Sannan ma ni ko kuɗin adaidaita sahu ba ni da shi".

Ya ce"To wane kayan shayi kuma sai ka ce wacce za ki tafi daji ba gida ba? Su a gidan naku ruwa ake sha? Kuma ni ban da ko sisi".

Ta ce"Ka ga Hamza dakata mana! Kar ka sake ka zage ni ballantana iyayena!".

Ya ce"An zage ki ɗin me za ki yi?"

Ta ce"Ramawa zan yi fiye da wanda ka yi mini, don kai mijina ne ba ubana ba!".

Ya yi tsaki ya kashe wayar, ta mayar da akwatinta ɗaki, ta zauna ranta a ɓace tana mamakin wai ita ce namiji yake yi mata haka, kamar wanda ya asirce ta, ji take har yanzu ba ta son rabuwa da shi, kuma babu wata hujja da zuciyarta take ba ta sai na cikin nan na jikinta, don haka ta bari har zuwa ta haihu ɗin ta gani, shin da gaske cikin ne sila ko kuwa Hamza ne ya samu nasarar canza mata tunani?

Azhar ta yi ta tashi ta ɗora girki, saboda ta yi alƙawarin ba za ta tafi ba sai ya yi mata siyayya kuma ya ba ta ɗan kuɗi ta riƙe a hannunta, ta gama cin abinci ta yi wanka ta kwanta baccinta, sai la'asar ta tashi, ta idar da sallah Uwani ta kira ta a waya, ta ce"Ya na ji shiru? Ko sai yamma?"

Ta ce"Ai na fasa tahowa yau".

Ta ce"To! Sai yaushe?"

Ta ce"Sai yadda ta yiwu".

Ta ce"A kan me?"

Ta ce"To ya ce ko kuɗin babur ba shi da shi, ballantana ya yi min ƴar siyayyar tahowa gidan, sannan ko tsumma bai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login