Showing 1 words to 3000 words out of 37653 words

Chapter 1 - MIJI GOMA. Hausa novel

23 Oct 2025

88

[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_



SADIYA ABDULRAZAƘ


*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?*

Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu

*FIRST CLASS WRITERS*

PAGE 1


Dare mahutar bawa, ta wata fuskar kuma rigar mugu, lokacin da dubban mutane suke samun damar ajiye haƙarƙarinsu bayan shafe tsayin awanni cikin yini suna gwagwarmayar rayuwa, walau ta waje ko ta cikin, a daren yau ba haka kalmar take ba a wajen Maryam domin kuwa ba ta damu da agogo ba a lokacin da ta tashi mijinta suke ta zabga tijara cikin talatainin daren, sakamakon binciken da ta yi a wayarsa ta ga bidiyoyin banza, inda a ce kishi cuta ne to za ta iya cewa ita shi ne kaɗai cutarta, wacce take wujijjiga ta, ta zabtare jarumtarta, ta kuma rufe ido wajen yankawa namiji kazar rashin daraja, su haɗu su figeta tare.

"Maryam idan kika sake danganta ni da kalmar mazinaci a bakin aurenki! Na faɗa miki yau na siyo wayar, ban zauna na bincike ta...".

A matuƙar harzuƙe ta katse mijin nata da faɗin"An faɗa ɗin mazinaci! Sai me idan ka sake ni? Ai ba a bakinka na fara jin kalmar saki ba, kuma ba ta damuna, don miji goma ba uba goma ba ne!".

Ya ce"Tabbas wanda bai ji bari ba zai ji woho! Babu abin da ba a faɗa mini ba kafin na aure ki na cewar ba kya zaman aure kuma ba za ki iya ba har abada, amma tsautsayi da ƙaddarar wannan cikin jikin naki ya sa na ƙi saurara".

Ta ce"Ka ma daina ƙalawa ƙaddara sharri, ka ce dai saboda son zuciyarka ka aure ni, duk kuwa da tsanar da tsohuwarka ta yi mini".

Ya ce"Maryam! Ki je na sake ki saki ɗaya".

Ta ce"Tabbatar mini kake yi ko kuwa saki ka ƙara a kan saki? Ka san dai tun da ka lanƙaya kalmar kiranka mazinaci da mutuwar auren ban fasa ba na sake furta maka, saki na farko ya tabbata, yanzu kuma ka sake yin ɗaya, biyu kenan, saura igiya ɗaya, duk da ko ka mayar da ni ba komawa zan yi ba, domin jaki shi yake maimaita aji!".

A fusace ya ce"Dama wane tsautsayin ne zai saka na mayar da ke? Ki fice mini daga gida kafin na shayar da ke mamaki!".

Ta yi wata dariyar rainin hankali na ce"Hehehe! Amma ai ba ƙarfe uku na dare ka auro ni ba, sannan a wajen ɗaurin auren ba a ce mini za ka sake ni na koma gidanmu uku na dare ba".

Ya ce"Ki fice mini daga gida tun kafin zuciya ta ɗebe ni a yi ɓatacciya!"

Ta ce"Don Allah idan ta ɗebe ka kar ta sauke ka sai ka kashe ni, wallahi idan ba uwata Hansatu ce ta taso daga ƙabari ba babu wanda ya isa ya saka ni barin gidan nan a yau!".

Nasiru ya yi ƙwafa ya bar mata ɗakin, ya shige falo ya kwanta a doguwar kujera, yana ji a ransa ta ci darajar tsohon cikin da yake jikinta, da sai ya lakaɗa mata mugun duka samfurin tashi ki sha kunu, ya yi nadamar auren Maryam, duk da dama abu ne da ya tsammata, amma bai san girman rashin kirkinta ya kai haka ba sai da ya aure ta zama ya yi zama, yau dai duk haƙurinsa ta ƙure shi mai afkuwa ta afku.

Ita kuwa Maryam baccinta ta kwanta hankali kwance, don wannan shi ne karo na uku da ta ji kalmar saki daga bakin miji, ko na farko bai ɗaɗata da ƙasa ba ballantana wannan da za a ce abun ya zama jiki. Har makara ta yi sallar asuba saboda dama shi ne take tashinta, ƙarfe shida ta yi sallah, ta shiga kitchen ta dafa indomi da shayi, ta cika cikinta sannan ta koma ɗaki ta hau haɗa kayanta, ta kusa gamawa ta kira wayar babarta, tana ɗagawa ta ce"Babarmu za a samu mai mota kuwa?"

Daga can ɓangaren Uwani ta tashi zaune tana cewa"Maryam! Me kike nufi?"

Maryam ta ce"Ya sake ni, jiya tsakar dare".

Uwani ta ji farinciki ya yi dirar mikiya a zuciyarta, ta ce"Maza hanzarta ki haɗa kayanki, yanzu zan fita na samo mai mota, duk wanda ya rasa ki shi ya yi asara!".

Maryam ta yi murmushi tana ƙara jin ƙaunar babar tasu, ta ƙarasa haɗa kayan, tana wanka ta ji tsayuwar mota tare da bugun gida, sai kuma sallamar Lami da Dije ƙawayen babarmu na kurkusa, ta fito tana yi musu sannu da zuwa, suka shiga kwashe kaya mai motan ya shigo yana taya su fita da kayan gadon, sai a lokacin Nasiru dake falo ya fito, ya same ta ranta fess tana saka kaya, ga kayansa da ta juye su cikin babbar rigarsa wacce ya yi fitar ɗaurin aurensu da ita, ta ajiye masa su a gefe, ransa a ɓace ya ce"Ina takarduna?"

Ta ce"Suna ciki har takalma".

Ƙwafa kawai ya yi ya fice daga gidan, zuciyarsa a dagule, a ƙofar gida ya zauna har suka gama kwashe kayan tsaf, Maryam ta fito ta yi tsaye a kansa da ƙaton cikinta ta ce"Nasiru ya za a yi da batun cikin nan? Jaririn zan kawo maka bayan na haihu ko kuwa ciniki za mu yi ka dinga biyana ina shayar maka da shi?"

Ya ce"Allah Ya sauke ki lafiya sai a san abun yi".

Bai jira cewarta ba ya shiga gidan ya saka sakata, ɗakunan wayam babu komai sai ƙunshin kayansa, ya fara tunanin yanzu yau a ina zai kwana? Katifa zai fito ya shimfiɗa ko tabarma? Gabaɗaya ya ji tsanar gidan ta kama shi tun kafin a je ko'ina tabbas mutum rahama ne ko da ba zaman lafiya kuke yi ba, ya kullo gidan ya tafi gidansu don sanarwa iyayensa, wanda ya san ba za su tausaya masa ba, sai dai su bi shi da Allah Ya ƙara, tun da tun farko sun nuna masa Maryam ba matar aure ba ce ya ce ya ji ya gani.

A ɓangare Maryam, da gudu Uwani ta tare ta ta rungume tana cewa"Ƴata ta dawo kusa da ni, wallahi Maryam ko ƴaƴan da na haifa a cikina ba na yi musu son da nake yi miki, saboda kin fi su bin umarnina sau da ƙafa, zo ki huta ki sanar da ni abin da ya faru".

Cike da ƙaunar babar tasu ta bi ta ɗaki, Uwani ta ce "Kwanta ki huta, bari na taya su shigar da kayan, ai kina kirana na ce to ban ga ta zama ba, na tashi na share ɗakinki tass, bari na sako miki ɗumamen tuwo".

Maryam ta ce"A ƙoshe nake babarmu, sai da na yi girki na ci, cikin kayan ma akwai kayan abinci da yawa, don shekaran jiya ya yo mana siyayyar wata, na kwaso su duka ko ashana ban bari ba".

Uwani ta ce"Allah Ya yi miki albarka ƴata, duk wanda ya rasa ki shi ya yi asara, wallahi har mamakin yadda kullum kike ƙara kyau da zama matar manya nake yi? Ban da kin ce kina so kuma ni ina son farincikinki dama ina ke ina Nasiru? Waye ubansa ma?"

Daga haka ta fita ta shiga ɗakin Maryam ɗin, don taya aminanta aiki.

Maryam ta ajiye hijjabinta, ta miƙe ƙafa wannan ne karo na biyu da aurenta ya mutu da ciki, sam ba ta jin nadamar ɗaukar mutuwar aure ba a bakin komai ba, tun da ba ta fuskantar tsangwama a gida ko ta nemi wani abu ta rasa kamar yadda ta ji an ce zawarawa suna fuskantar wannan ƙalubalen, ta yunƙura ta tashi don zuwa ta taya su aikin don ta ga har yanzu babarsu ba ta shigo ba shaidar ba su gama ba, ta fito ta ga labulen ɗakin a sake, saura taku biyu ta shiga ɗakin ta ji suna magana ƙasa-ƙasa, Maryam tana da wata al'ada ta laɓe, wannan duk wanda ya zauna da ita tabbas zai santa a kan haka, yanzu ma laɓewar ta yi daidai sanda babarsu take cewa"Lami wallahi Maryam ta yi ta aure-aure kenan, alƙawari na ɗauka ba za ta taɓa zaman aure ba, wannan ba na uku ba ne? Ku ci gaba da taya ni lissafi sai ta yi aure goma muddin ina raye! Wannan ce kaɗai fansar da zan ɗauka na cin amanar da uwarta ta yi mini, ina ma Hansatu tana raye ta ga yadda ƴarta za ta zamewa maza tamkar banɗakin kasuwa?"

Sai suka saki shewa Lami tana cewa"Wallahi Uwani ba ki da dama!".

Wani irin tashin hankali ne ya ruftowa Maryam, da ƙyar ta ja ƙafa ta koma ɗaki ta zauna jagwab, wani irin sanyi jikinta ya yi har ma zuciyarta, ta shiga tariyo maganganun masoyiyar babarsu tana yi musu sukola mai inganci, babar nan tasu mai kirki da ƙaunarta wacce ta sha cewa ta fiye mata mahaifiyarta tun da ba ta girma tare da ita ba, ashe wannan ƙaunar tata a gare ta duka ta bogi ce? Ta shiga tunanin me yasa za ta yanke mata wannan hukuncin? Ashe burin kashe mata rayuwa take yi take yaudararta da sunan inganta mata rayuwa? Ba kasafai Maryam ta fiya yin nadama a kurakuranta ba, amma yau ta ji nadamar biyewa babarsu, a hankali ta furta"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Ta shiga tunanin mafita, yanzu ya za ta yi da wannan bita da ƙullin da ake binta da shi? Tabbas da a ce ba babarsu ce ta yi mata wannan abun ba da tuni yanzu wata maganar ake yi ba wannan ba, sanin hali ya fi sanin kama, babarsu ita ce malamarta a duk wani halinta na rashin mutunci, don haka ba za ta iya karawa da ita ba, to ta ina ma za ta fara?

Tana cikin wannan tunanin ta ji tana yi wa ƙawayenta sallama da godiya, ta shigo ɗakin ta kalli Maryam sheƙeƙe ta ce"Maryama! Ba dai damuwa kike saboda mutuwar aure ba?"

Hawayen da ba ta tsammata ba ne suka sakko mata, Uwani ta dafe ƙirji tana cewa"Yau ga muguwar shekara, inji kwaɗo da ya faɗa ruwan zafi, ke Maryam da gaske mutuwar aure kike yi wa kuka tun daga yanzu?"

Ta ƙarasa maganar tana zama a kusa da ita, ta kamo hannunta ta ce"Maryam, wai ina huɗubata a gare ki? Ko yanzu kin ajiye maganata ta miji goma ba uba goma ba ne? Uwar me Nasiru yake ba ki da har za ki yi kukan rashin shi a rayuwarki?"

Maryam tana danne zuciyarta don ta yi alƙawarin ba za ta bari babarsu ta san ta san manufarta a gare ta ba, ta ce"Babu komai babarmu, wallahi tausayin ɗan da zan haifa kawai nake yi, Al'amin yana can yana rayuwa ba tare da ni ba, wannan ma haka ce za ta faru, a ce na yi ta haɗawa ƴaƴana ƴan uba?"

Uwani ta ce"Au ke wannan ne kaɗai tunaninki? To mene ne da ƴan uba? Ke matsala kuke samu da naki ƴan uban? Ke uwa ce, addu'arki kaɗai ƴaƴanki suke buƙata, matuƙar dai su ma kin ɗora su a tarbiyyar da na ɗora ki ta jajircewa da ƙwatarwa kai ƴancin rayuwa, wallahi ba za su yi kukan rashin uwa ba kamar yadda ke ma ba na fatan ki yi shi ko bayan raina".

Maryam ta ce"Hakane babarmu na gode, bari na je na kwanta".

Ta tashi ta fita, Uwani ta bi ta da kallo tana mamaki da fargabar abin da ya sanyaya mata jiki.

Kwanciya ta je ta yi ta shiga tunanin baya, ta tuna ranar aurenta na farko da huɗubar babarsu a gare ta.

Kowace amarya musamman wacce ta kasance buduruwa da aka yi mata auren fari, takan shiga damuwa da jin kewar rabuwa da gidansu da iyayenta a ranar da za a kai ta ɗakin mijinta, takan yi kuka ko da kuwa tana son wanda za ta aura ɗin, jikinta ya yi sanyi har ma wata takan ji dama ba ta yi auren ba, saɓanin Maryam da har yanzu da ta samu labarin motocin ɗaukarta ita da ƴan rakiyarta sun zo garau take jinta, babu wata fargabar shiga sabuwar rayuwa ko wani ƙalaubalen da za ta iya fuskanta a gidan aurenta, babu ruwanta da kewar iyayenta don ita ba mutum ba ce mai saka abu a rai, sabgar gabanta kawai take yi.

"Don Allah Maryam ki saka mayafinki, ki rufe fuskarki, ga shi nan za a kai ki wajen Baba ya yi miki nasiha" Cewar ƙawarta Aisha tana miƙo mata mayafinta.

Ta ce"Wai ni kam Aisha shi rufe fuskar nan dole ne? Baban zan ji kunya ko shi Nazifin da ya aure ni?"

Ta yafa mata mayafin tana dariya, daidai lokacin da ƴan'uwa suka zo suka ɗagata don kai ta gaban babanta, nasiha sosai Baba ya zage yana yi mata, kanta a sunkuye tana sauraron shi, kalamansa suna shiga ta nan suna fita ta can, domin duk wata nasiha da ta gamsu da ita a rayuwar aure masoyiyar babarsu ta gama yi mata ita, _"Maryam ki riƙe wannan kalmar da zan sanar da ke ruƙo ba na wasa ba, miji goma ba uba goma ba ne! Ita rayuwar aure ba a yi ta don ƙunci ko tauye hakki ba, ba a yi ta don haihuwa da rainon ƴaƴa kaɗai ba, sai don samun ƴancin kai da soyayya daga wajen miji, duk macen da mijinta ya yi wani abu dake nuna ba ta isa ba a wajen shi, ko kuma ya kalli wata macen bayan ita to tabbas sunanta bora! Da a kira ki da bora gara a kira ki da bazawara, saboda haka ina ba ki shawarar kar ki sake ki ɗauki raini daga wajen miji ko danginsa, ko da hakan zai yi silar mutuwar auren, ni fa da a ce kin yi wuni ɗaya a gidan aurenki cikin baƙinciki gara a ce kin yi auren wuni ɗaya mijin ya sake ki! Don haka ki ɗaura ɗamarar samarwa kanki aji da ƴanci daga wajen mijinki, zawarci ba komai ba ne"_.

"Maryam! Ba dai kuka kike yi ba?" Muryar yayana Sunusi ta ziyarci kunnenta, yana tambayar da mamaki da kuma izgili.

Ta ɗago ta buɗe fuska da soyayyun idanunta fess ta ce"Kukan me zan yi Sunusi? Kawai dai na rufe fuskar ne". Ta ƙarasa maganar da gadara tana juya masa kai gefe.

Ya ce"Ai na yi zaton kuka kike yi, in ce uban wa za ki yi wa? Hmm wannan aure Allah dai ya ba da zaman lafiya kawai, amma Nazifi ya ɗakko Dala da gammo".

Baba ya ce"Sunusi ka faɗi alkhairi ko ka yi shiru, Maryam tashi ki je, Allah Ya kai ki a sa'a".

Suka tashi aka yi ɗakin babarsu da ita, tana zaune cikin ƙawayenta, ta zauna kusa da ita, ta kama hannunta ta ce"Babarmu zan tafi".

Ta yi murmushi ta ce"Maryam duk wata nasiha da zan yi miki ai na gama ta, kar dai ki zubar da karatuna kawai shi ne fatana". Ta kawo bakinta saitin kunnenta ta ce"Miji goma ba uba goma ba ne!".

Ta gyaɗa mata kai cike da gamsuwa tana murmushi, yayin da matan ɗakin suke binsu da kallon burgewa, na ƙaunar dake tsakaninsu da babarsu wacce ba ta ɓoyewa har kullum ƴaƴanta ƙawayenta ne, ita ta ja mayafinta ta rufe mata fuska aka fitar da ita waje.

Aka saka ta a mota lokacin ana ta kiraye-kirayen sallar magriba aka tafi da ita gidan mijinta wanda ya kasance zaɓinta, domin duk cikin samarin da suka nuna mata so Nazifi ne yake daidai da ra'ayinta, ba don komai ba sai don shi ne mai sauka a kan ra'ayinsa ya bin ra'ayinta ko da ba ya so, shi ne mai yi mata biyayya da kwantar da kai tamkar uwarsa, sakamakon sonta da ya zame masa tamkar wata jarabawar rayuwarsa.



08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_



*SADIYA ABDULRAZAƘ*


*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?*

Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu

*FIRST CLASS WRITERS*

PAGE 2


Ƴan kai amarya da rakiyar ƴan ango kowa ya watse, wannan washe bakin da wasu kalaman soyayya bai damu Maryam ba, burinta kawai ta ji dalilin da ya sa ya rufe wani ɗaki guda ɗaya a cikin gidan, wanda tun da aka je jeri ya ce musu ban da ɗakin nan, ta sakko daga gadon da take a zaune, ta fice, ya bi bayanta yana cewa"Alwala za ki yi?"

Tana ƙarewa gidan kallo ta ce"A'a ina ganin yanayin gidan ne".

Ɗakuna uku ne sai kitchen da banɗaki a tsakar gida, ɗaya aka saka mata gado, ɗaya kujerunta, ta ce"Ni kam Nazifi wannan ɗakin da ka cewa ma su jeri ban da shi mene ne a cikinsa? Ko aure za ka ƙara?"

Ya yi ƴar dariya ya ce"A haba dai aure! Ko auren zan ƙara ai dai kin san ba yanzu ba, kuma idan hakane me zai hana ki saka kayanki sai auren ya kusa sannan ki kwashe?"

Ya yi wata dariya ya ce"To ballantana ma ban da ra'ayin ƙara aure, ai ba irinki ake yi wa kishiya ba my Love".

Maryam ta taɓe baki ta ce"Ni dai ba ka ba ni amsar tambayata ba, me yasa ka kulle? Ko turakarka ce ai dai ka buɗe ko labule na saka maka".

Ya ce"'A'a ma wallahi ba turaka ba ce, ki yi haƙuri ban faɗa miki ba, dama Gwaggo ce za ta dawo nan da zama, don ma ba a gama ginin da wuri ba, da sai ta riga mu tarewa, yanzu kuma da ta ga abun ya zo dab sai ta ce idan an gama bikin kin tare sai ta dawo".

Wani abu ya daki zuciyar Maryam, wai ita yake nufi ta zauna gida ɗaya da uwar miji, tun tana amarya? Ta ce"Wai kana nufin da Gwaggo za mu zauna? To inda take a da me ya same shi?"

Ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login