Showing 1 words to 3000 words out of 36102 words
P*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_
BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_
*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*
Page 1
Ranar bakwai,ga watan d'aya,shekara ta dubu biyu da goma sha shida,ita ce ranar da littafin k'addarata ya fara bud'ewa,ranar da na shiga cikin damuwar da ba na tunanin zan fita har abada!
Zaune na ke a cikin adaidaita sahu,kan hanyata ta komawa briged daga gidan yayata da ke unguwar hotoro,kaf hankali na ya na kan wayar da na ke amsawa ta masoyina,wanda yau watanni biyu ya rage auren mu.
"Y'an mata don Allah zan shiga nan,na kar'bawa maigidana sak'o"
Na ji muryar mai adaidata sahuna
Sai na kai duba na ga laundry (wurin wanki)d'in da ya ke nuna min,na ce"ok"
Tsautsayi ba ya wuce ranar sa,da na san zan ga abin da na gani yanzu me zai fito da ni yau? Wata bak'ar mota ce ta ke k'ok'arin fakin a wurin,duk da ban san tsadar motoci ba na san wannan dai ba k'arama bace,ya yi minti uku da fakin ga shi dai ya bud'e murfin motar amma bai fito ba,haka ne ya sa ni sake tattara duk hankali na wurin ganin wannan mashahurin.
A kan idona ya fito daga cikin motar,gabana ya fad'i daga yi masa kallo d'aya tak!
Fari ne tass,mai manyan idanuwa ,farare tas kamar bai ta'ba yin kuka ba,ba wani dogon hanci ne da shi ba,madaidaicin bakinsa ya hau sosai da zagayayyiyar fuskarsa,
Bak'ar riga ce a jikinsa da bak'in wando iya k'wauri,ga wani bak'in agogo da ya yi wa farin hannunsa kyau sosai
Ba k'aramin tafiya da imanina ya yi ba,nan take na ji wani irin yanayi a zuciya da gangar jikina,na yi wata kasalalliyar ajiyar zuciya,ina kuma k'are masa kalllo
Yamutse fuska na ga ya yi,tare da kai hannunsa kan gashin kansa da ke ta shek'i da alama ya sha gyara har ya gaji,ya wani hautsina sumar wanda na ji kamar da gayya ya yi,don kuwa wani irin kyau na ga ya k'ara,kai ka ce ba d'an Nijeria ba ne,wallahi ban ta'ba zaton a kwai irin kyawawan nan a garin Kano ba
Mota ya koma,ko shiga ciki bai yi ba hannu kawai na ga ya mik'a ya ciro wata jar facing cap ya saka.
Wanda ya yi daidai da dawowar mai adaidata sahu na,hannunsa d'auke da wata jaka
Ina kallo matashin ya shiga wurin,ya na ta b'ata rai.
"Yi hak'uri hajiya,na 'bata miki lokaci" Mai adaidaitar ya fad'a
Na yi guntun murmushi lokacin da mu ke wuce wurin na ce"babu komai"
Sai da mu ka d'an yi tafiya,na ji muryarsa"sunan shi Salim,shi ne mai wurin wankin nan,kuma shi ne me wurin cin abincin nan na sabin sati(seven thirty) ba shi da kirki,kuma ya na shan sigari,an ce ya na da kamfani a sharad'a,wanda da kan shi ya ke kula da shi,kuma gidan su ma a can ya ke"
Ban yi mamakin maganganun sa ba,don na san ba ya rasa nasaba da irin kallon da ya ga ina yi wa wanda ya kira da Salim d'in
"Hmm!" Na sauke ajiyar zuciya kafin na ce
"Ba ka san wani abun ba game da shi bayan wannan?"
"Abin da na sani kenan" Ya fad'a
"Ba ka da number shi?" Na tambaya zuciyata na bugu
Ya yi dariya ya ce"tabb! Wane ni?"
Cikin zak'uwa na ce"to don Allah maida ni wurin, idan ya fito ka bi min bayan sa"
Mai adaidaita ya yi wata irin juyowa ya zaro ido kafin ya ce"ki rufa min asiri,ban shirya mutuwa ba,y'an mata ina da iyali"
Ni ma y'ar dariya na yi na ce"don ka bi bayan shi sai ka mutu?"
Ya ce"to me zai hana? Ko ban mutu ba na san zan sha wuya,ke watak'il ma na k'are rayuwata a gidan yari"
Dariya kawai na yi na ce"hakane".
"Amm...ka ce ya na shan sigari? Ta ya ka san da hakan?"
Na yi tambayar da zumud'in jin amsar da zai bani.
Mai adaidaita ya ce"eh,sau biyu ina ganin shi a wurin nan ya na zuk'a,da alama ta bi jikinsa don ya na sha a gaban kowa"
Na jinjina kai kafin na ce"Allah ya shirye sa".
Har mu ka k'araso unguwar mu ban kuma magana ba,na fad'a duniyar tunanin Salim.
Da sallama na shiga gidan,na tadda Mama Saude ta na tsintar shinkafa,ga wutar murhun da ta kunna sai hayak'i ta ke yi,gidan duk ya kaure da k'auri
.Mama Saude matar mahaifina ce,bai jima da auro ta ba,sakamakon rabuwar su da mahaifiya ta,wanda ni ce silar rabuwar,a duk lokaci da na tuna da haka na kan shiga damuwa,wata rana ma har hawaye na ke yi.
Mama Saude ba ta da kirki,sam ba ta k'auna ta kullum cikin ganin ta had'a ni da mahaifina ta ke,gashi shi kuma duk abin da ta fad'a masa yarda ya ke yi,ya hau kai ya zauna ya yi ta surfa min masifa. Ko da ya ke ban cika ganin laifin sa ba,tun da nawa laifin ya fi yawa,ba na jin magana ko kad'an,shi ya sa ma a k'a k'agauta na yi auren kowa ya huta.
Hmm! Nan gaba dai za ku ji ko wacece ni.
Ban ko kula Mama ba,na shige d'akina da ba wani tarkace ne a ciki ba,wulli na yi da jakata ina fad'awa kan katifa ta.
Kiran sallar la'asar ne ya tashe ni daga guntun baccin da na tafi,kai tsaye wanka na shiga na fito na d'aura alwala,ina dab da shiga d'aki na ji sallamar Mama ta shigo cikin gidan,ban amsa ba sai tsaki da na ja,ina mamakin irin halin Mama Saude,wai ta san sarai bacci na ke yi amma sai ta yi ficewar ta,ba ta ko karo k'ofar gidan ba,yanzu idan wani ya shigo ya yi min sata kuma fa?
"Allah ya kyauta" Na fad'a ina k'ok'arin shigewa d'aki
Ban kai ga shiga ba na jiyo muryar ta"ke! Uban wa ki ke fad'a wa hakan?"
Banza na bawa ajiyar ta na shige d'aki,don idan na kula ta sai mu kai magriba mu na yi,ko kad'an ba ta gani ta kyale,kuma ba ta gajiya da mita ni ma yau d'in Allah ya sa ba y'an rashin kunya bane a kaina,da haka zan biye mata mu yi ta yi,wannan ya zama jiki kusan kullum sai mun yi,kamar kishiyoyi ko facaloli haka mu ke ni da ita,shi ya sa ma ban fiya zaman gidan ba na gwammace na fita yawona,idan na dawo na sha fad'a a wurin mahaifina.
*Zinatu* kenan,matashiyar budurwa mai ji da kanta,y'ar kimanin shekara ashirin cif,ta kammala secondary tun shekaru uku da su ka wuce,islamiyya kuwa tun tuni ta ajiye ta a gefe,babu yanda ba ta yi da Baban ta ba kan ya bar ta,ta cigaba da karatu ko y'ar digiri ta samu,amma ya ce sam ba zai yi wu ba,a rashin jin maganar ta bai ga dalilin da zai sa ta je makarantar gaba da sakandari ba,don kuwa ya na jin tsoron had'uwar ta da maza,da kuma gogaggun mata,saboda Zinatu ba ta jin magana.Allah ya yi wa Zinatu farinjinin masoya,don duk inda ta shiga sai wani ya k'yasa,ita kuma mutum ko kad'an ba ta sauraron maza,don duka ma ba ta yarda da soyayya ba,wahala kawai ta d'auke ta,haka ne ya sa ta dad'e ba ta tsaida mijin aure ba.
Ba ta da k'awa ko d'aya,sai abokai maza sun fi a k'irga,ita kowa nata ne in dai namiji ne,hakan ne ya sa mutane su ke yi mata kallon ballagaza,wasu ma har su na zargin ta da wani mummunan halin.
Ban gama tsinkewa da lamarin Salim ba,sai da dare ya yi na zo bacci,don kuwa yau duk saurin bacci na sai na neme shi na rasa,hoton fuskar Salim ya yi ta dawo min kamar dai maza bak'ina ne? Sai da na tashi na d'akko k'ur'ani na fara karatu,kafin na fara jin baccin.
Kiran sallar asuba a kunnena,na tashi na yi sallah na koma na kwanta,don baccin yau bai is he ni ba.Shuuu! Na ji Baba ya kunna rediyon sa me hanani komawa baccin safe,na ja tsaki ina shirin sake yin juyi na jiyo muryarsa
"Zinatu! Ke Zinatu!".
"To fa! Babu lafiya,Allah ya yi dare gari ya waye". Na fad'a a bayyane ina tashi na saka hijjabi na fito
Zaune na tadda shi a k'ofar d'aki,Mama kuma ta na ta gyare-gyaren wurin sana'arta,da ya ke ta na saida wainar shinkafa da k'uli kullum da safe.Na gaisheta ta amsa a d'ak'ile,na kalli Baba da ya ke nuna min gefen sa,alamar na zauna.
"To ni Zinatu! Allah ya fitar da ni!". Na fad'a a zuciyata,don kuwa in dai ka ga Baba ya min irin kiran nan da zai bani wurin zama to akwai magana,ko dai zai min fad'a ko kuma nasiha,ille kuwa! Ban gama tunanin laifin da na yi ba,na tsinkayi muryarsa
"Yanzu Zinatu irin rayuwar da ki ka za'bawa kanki ki na ganin za ta kai ki tudun tsira?"
"Subhanallah! Baba me na yi kuma? Ko dai an sake had'ani da kai ne?". Na yi maganar ina yiwa Mama kallon gefen ido.
Tuni Baba ya tsuke fuska,ya fara magana" yanzu a masallaci a ke fad'a min an ganki jiya wai maza su na koya miki keke,haba Zinatu! Ke me yasa ba kya gudun bakin duniya wai? Kullum burinki ki jawo min abin magana ko,a yi ta nuna ni a gari a na ga mahaifinki ko? Don Allah ki rufa min asiri na aurar da ke lafiya,sauran y'anuwanki dai ba mu yi haka da su ba".
Yanda ya k'are maganar da sanyin murya sai ya bani tausayi,don ni kaina ina tausayin Baban yanda ya ke ta k'ok'arin ganin na nutsu
"Ka yi hak'uri Baba,zan daina in sha Allah, sai a yi ta saka ni cikin addu'a".
Na fad'a ina tashi na koma d'akina,ba tare da na jira abin da zai ce ba.
"Kar ma ki daina! Ni kam shi ya sa na matsu ki bar gidan nan ko na huta,da ganin takaicinki"
Mama Saude ta yi maganar ta na jan tsaki.
Katifa na fad'a ina murmushi,tunowa da Anas da ya ke fad'a min tunda na fad'i sau uku ba zan ta'ba iya keken ba.
"Allah ya shiryi y'an gulma" Na fad'a ina rufe idona,tuni bacci ya sureni.
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_
BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_
*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*
Page 2
Ringing d'in wayata ne ya tasheni,na wartsake da hayaniyar masu siyan waina,ban fara kawo tunanin komai a raina ba sai na Salim,rintse idona na yi ina sake tuno yanda na ganshi,na d'an jima a kwancen ina sak'e-sak'e kafin na tashi,ban kalli wayar ba bare na duba me kiran,na saka k'aramin hijjabi na fita don shiga wanka.
Karin kumallo bai dameni ba,to ina ma na ke da gatan da za a bani? Mahaifiyata ce kawai me min tilas na ci abinci,ko na rana ma ni ce na ke yin girkina,don tuni na samawa kaina y'anci daga wulak'ancin Mama akan abinci,idan na rage kuma na mik'a mata,babu kunya ta ke kar'ba ta ci,don babu laifi ta na da kwad'ayi.
Hoda kawai na shafa,bayan na shirya cikin doguwar riga ta atamfa,na yafa wadataccen mayafi,na saka takalmi, na d'auki jaka,ina dab da fita na sake jin ringing d'in wayata
"Y'ar wahala,har na manta da ke". Na fad'a ina d'akko ta,kamar yanda na zata Habib ne me kiran
"Wahala ta aure ka,tunda ka nace". Na yi maganar kafin na daga kiran.
"Hmmm!". Ya sauke ajiyar zuciya,kafin ya ce,
"Saura k'iris zuciyata ta fashe Zinatu".
"Har dagargajewa sai ta yi" Na fad'a k'asa-k'asa.
"Me ki ka ce?" Ya tambaya
Na yi guntun murmushi na ce"me ya hana ka zuwa jiya...?"
"Wane ni da taka umarnin ki? Na kira ba ki d'aga ba, kuma kin gargad'e ni na daina zuwa sai na sanar miki".
Na yi murmushi na ce"hakane fa! To ya kake?"
"To gani nan dai,lafiya ba lau ba,wallahi Zinatu ba na jin nutsuwata za ta dawo idan ban mallake ki ba,wata biyun nan jin sa na ke kamar shekara biyu,kuma..."
Na yi saurin katse shi da fad'in"kai! Dakata,na ga ka d'ebo fira,ni kuma wani uzurin na ke ka katseni,ka zo yau da daddare sai mu yi zancen ko?"
Ban ma jira cewar sa ba na katse kiran,na jefa wayar a jaka,na fito na na rufe d'akina da mukulli.
"To sai ina kuma?" Mama ta yi maganar daga y'ar rumfar da ta ke suya.
"Inda Allah ya nufa". Na bata amsa ina ficewa daga gidan.
Kai tsaye gidan su mahaifiyata na nufa,a d'aki na tadda ta ta na shara,na zauna ina gaishe ta bayan na kar'bi sharar na k'arasa mata.
"Zinatu!" Ta kira sunana a nutse
"Na'am Ummi" Na amsa ina maida hankalina wurin ta.
Sai ta ce min"anya da gaske za ki yi auren kuwa?"
Na yi d'an murmushi na ce"me ki ka gani Ummi?"
"Na ga kamar ba kya shiri,ga abu sai matsowa ya ke". Ta fad'a ta na tashi ta d'akko min leda wai tukwane ne ta siya min,za ta had'a da wancan kayan.
Sai na yi murmushi na ce"Na gode Ummi,Allah ya saka".
Ba ta amsa min ba ta tashi ta had'a min shayi,ta mik'o min,na sha fin rabin kofin,sannan na tashi ina yi mata sallama.
"Ba za ki gaida kakar ki ba?" Ummi ta tambaye ni.
Na d'an cukume,don ba ma shiri da mahifiyar Ummi,ni fa duk wanda zai fad'a min gaskiya bayan mahaifiyata,to fushi nake yi da shi.Labulen d'akin na d'aga ko sallama ban yi ba,zaune na ganta ta na linkin kaya,na saki labulen kawai na juya,duk da mun yi ido hud'u da ita,sai na d'an d'aga murya ina fad'a wa Ummi bacci take yi.
Na d'an jima tsaye a bakin titi,ba wai abin hawar na rasa ba,a'a kawai ina jinjina wurin da zuciyata take bani umarnin zuwa ne,daga baya dai na yi shahada na tari adaidaita na antaya,ina fad'a masa inda zai kai ni.
Daidai wurin da na ga Salim ya faka motar sa jiya na tsaya ina waige-waige,amma ban ga ko mai kama da motar ba,cikin k'arfin hali na shiga wurin ina had'e gira,don kar ma wani ya kawo min raini.Ma'aikacin da na fara cinkaro da shi na tambaya"don Allah Salim ya shigo?"
Sai ya zaro ido ya ce"waye ya ce miki kullum ya ke zuwa?"
Na sake had'e rai na ce"mun yi da shi ne za mu had'u a nan,na yi mamakin rashin zuwan shi"
Na yi maganar ina daddana wayata,na kara a kunne,tsaki na ja na ce"ka gani ko? Tun d'azun na ke kiran shi a kashe,kuma shi ma yau ya na son ganina dole,kai Salim matsala ne!".
"Mu ga lambar?" Ya tambayeni.
Na d'an ji dam,amma ban nuna ba,na maze na ce"mu ga ta wayarka?"
Babu musu ya mik'o min wayar bayan ya nemo lambar,na ji wani farinciki na kalli lambar na ce"ka ga kuwa ba ita bace a wayata,shi dai ban san adadin lambobin shi ba,kamar d'an kidnapping".
Tass! Na kwafe lambar,na bashi wayarsa ina yi masa godiya.Cikin farinciki na fita daga wurin kamar an yi min albishir d'in cikar wani babban burina.
Saving d'in lambar na yi da Salim na jefa wayar a jaka ina murmushi.
Kai tsaye kasuwa na nufa,na yi siyayyar abin da ba ni da shi na kayan abinci,na yi cefane na har da kaza,saboda yau ina cikin farinciki.A tsakargida na tadda Mama ta na tsintar shinkafa,duk sallamar da na yi ta rangad'awa ba ta kalle ni ba,bare ta amsa,da alama dai yau tambotsen take ji,murmushi na yi na shige d'akina,ba tare da na yi mata magana ba.
Tunda na fara aikin girkin Mama ba ta kalli inda nake ba,ta na ta fama da hura murhu,ga shi bakinta ya k'i mutuwa sai mita take yi,wai ita ta gaji da wannan bala'in na girki a murhu,na gama abin da zan yi na shige d'aki,don risho d'ina a d'aki yake saboda gudun satar kalanzir da Mama take yi min.Dab da kammala soya miyar na ji Mama ta na k'wala min kira "Zinatu! Zinatu!"
"Ya aka yi?" Na tambaya daga inda nake.
Sai gata ta bankad'o rik'e da roba ta na fad'in"wai da na ga kin fita ba ki karya ba...shi ne na ce to bari na rage miki waina"
Ta min maganar ta na ajiye min wata sandararriyar waina,had'i da lek'a tukunyar miyar da ke kan risho.
Na yi wata dariyar rainin hankali na ce"kin ga Mama...to ina ruwanki da cikina? Yau na saba fita ban ci komai ba?"
Sai ta gyara d'aurin d'ankwali irin na marasa gaskiya ta ce"ai wai da na ga yanzun aure za ki yi..."
"Idan ba na karyawa auren ba zai yiwu ba ko?" Na katse ta.
Sai ko ta had'e rai ta ce"ke ba fa na son raini,don ma kin ga ina lalla'ba ki? To kar ki ci d'in!"
Na yi murmushi ina d'aukar kwano na zuba mata abincin,na mik'a mata"k'amshi dai ki ka jiyo,shi ne ba za ki iya fad'a kai tsaye ba"
Ta k'ar'ba,ta fice ba tare da ta tankani ba.
Bayan na gama cin abinci na yi sallah,sai na kwanta na janyo wayata,wadda ta fara yi min kwarjini saboda bak'uncin lambar Salim da ta samu.Na jima ina kallon lambar kafin na yi k'undunbala na danna kira.
Har ta katse bai d'auka ba,hakan ya sa na sake kira a karo na biyu,nan ma dai amsar d'aya ce,aikuwa aiki ya ce min muje! Nan na yi ta jera masa kira,kamar ba gobe,sai kace wani game aka bani,ina jira in yi over.
Sai da na yi guda tara cif! Ina shirin yin na goma na ga shigowar sak'on shi.
Da hanzari na duba don na ji ko wani uzurin zai bani na rashin d'agawar shi
_"Waye ne?"_ Abin da ya ke rubuce a sak'on kenan.
Na yi saurin mayar masa da amsa kamar ya sanni na ce _"Zinatu ce"_.
_"Wace kuma haka? Daga ina?"_ Ya sake tambaya ta.
Tsaki na yi na sake kiran lambar ko zai d'aga,na yi sa'a kuwa ya d'aga,na wani kashe murya don gaskiya ba ni da zak'in murya na ce"Assalamu alaikum".
Tsaki na ji ya ja,a maimakon amsawa ya ce"malama tafi kai tsaye ba ni da lokacin shirme!".
"Subhanallah!" Na fad'a a zuciyata,da alama dai zai yi wulak'anci.
Sai da na yi gyaran murya sannan na ce"Zinatu ce".