Showing 21001 words to 24000 words out of 36102 words

Chapter 8 - MATAR SHEGE HAUSA NOVEL

28 Mar 2025

3648

ki yi ta yawon naki a can,wallahi na ji ba daidai ba sai ranki ya b'aci".

Na sunkuyar da kai na yi shiru,ya wuce ya na fad'awa Mama ai ina ciki bacci nake yi.


Wajan k'arfe goma na dare ina kwance,kamar a mafarki sai ga kiran Salim,hannuna na rawa na d'aga har da in'ina wurin gaishe shi.Bai amsa ba ya ce"ke nutsu dalla,tambayar ki zan yi"

Na ce"to,ina jinka"

Ya ce"me ya kai ki shagon k'anwata yau?"

Gabana ya fad'i,na yi saurin fad'in"kitso na je".

Ya yi wata y'ar dariya ya ce"kitso ko? To ke da ita d'in ku iya takun ku,don duk abin da kuke yi a tafin hannuna yake".

Ya katse kiran,ba tare da ya bani damar wata maganar ba.

Na dafe k'irjina da har yanzu bai daina bugu ba,maimakon na yi nazarin maganar sa,da kuma tunanin yanda ya san na je wurin Baby,ina! Sai na fad'a wani shauk'in son shi,na ji kamar ba ni da wata damuwa a duniya,muryarsa ta mantar da ni duk wata matsala da take tunkaro ni.





KU NA GANIN MAFITAR DA BABY TA KAWO ZA TA SAMU SHIGA KUWA?

AKWAI WANI K'ALUBALE BABBA A KOMAWAR ZINATU GIDAN ANTI NA'IMA.

Ku dai ku biyo ni🥰
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_


BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_


*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*


Page 14



K'arfe goma na safe na kammala shirin tafiya gidan anti Na'ima,na yiwa Mama sallama ta amsa kamar gaske.Sai da na biya ta gidan Ummi na gaishe ta,ta kwaso min kayan kitchen da zannuwan gado,labulaye da dai sauran tarkace wai duka nawa ne,a to tarkace mana! Tunda su suke ta shirin su,watak'il dai sun tanadi wata matar da za su aura wa Habib,don ni Zinatu na yi masa nisa

Ban jima ba na yi mata sallama na tafi,bayan ta yi min nasiha sosai wadda ba ta fashi indai zan zo gaishe ta.

Fuska babu yabo babu fallasa na shiga gidan Antin,don ina tunanin yanda zaman gidan zai zo min,indai za ta hana ni fita harka ta to fa tabbas tafiyar mu ba za ta yi nisan zango ba,domin kuwa ba na jin zan iya yin sati hud'u ban bawa idona hakk'insa ba,wato kallon Salim

Gidan nata b'angare biyu ne,don ta na da abokiyar zama,ita ce amarya,uwargidan babba ce har ta na da manyan y'ay'a guda uku,Nazifi shi ne babba,kuma mu na shiri da shi sosai,kun dai sanni da maza...sai k'annen sa Hafiz da Umar.Ita Anti Na'ima Allah bai bata haihuwa ba har yanzu,su na zaune lafiya babu wata matsala,shiyasa idan na je ma muddin Nazifi ya na nan,to na fi zama a shahen su,mu yi ta shan firar mu ta duniya.

Don haka yau d'in da na je,bayan ta nuna min kayan gyaran da yanda za ta yi min,na ce mata sai gobe a fara,na tashi na yi sashen su Nazifi,na yi sa'a kuwa ya na nan,a can muka zauna mu ka sha firar mu har la'asar

Na yi zaton ma Anti za ta min fad'an zama na a can, sai na ji ta yi shiru,na taya ta girkin dare muna yi ta na yi min bayanin wasu dabarun girkin,ni dai jinta kawai na ke,ina bin ta da ido.Washegari aka fara yi min gyaran jiki,tun daga ranar kuwa fatata ta fara kyau, cikin sati d'aya na zama kamar ba ni ba,kullum mu na waya da Baby, ko ba ta kira ni ba,ni zan kira ta mu gaisa,haka ma ta b'angaren Salim ba ta canza zani ba,domin kuwa kullum sai na jera masa kira,amma ba ya d'agawa.Lokaci zuwa lokaci bawan Allah Habib ya na fad'o min a rai,don tun ranar da muka yi wannan maganar...bai sake kiran wayata ba, bare ya zo,har Anti sai da ta yi min maganar sa,na ce mata mu na yin waya kullum,ba ni da matsala a zaman gidan,sai dai na fara k'osawa da rashin fita ko k'ofar gida,tunda ko aike na ba a yi,sau d'aya ma na ce zan raka Nazifi kasuwa,maman su ta ce na yi zama na,idan ana gyara ba a shiga rana.

Ranar da na cika kwana goma sha biyu a gidan, wata rana da yamma ina zaune sai ga kiran Salim,Allah ya sa ni kad'ai ce a wurin,don haka na d'aga da hanzari ina yi masa sallama.

"Wa alaikissalam" Ba saban ba yau ya amsa sallamata.

"Da fatan ka na cikin k'oshin lafiya?" Na fad'a,ina dafe k'irjina da ya ke ta bugu kamar na ga abin tsoro

"Kwatanta min gidanku" Ya fad'a, ba tare da ya amsa ni ba.

Sai na ji kamar a mafarki ne ba zahiri ba,yau Salim ke cewa na kwatanta masa gidanmu? Aikuwa sai zuciyata ta fara ayyana min watak'il ya yarda da soyayyata ne,har zai zo mu fara fahimtar juna.

Cikin zumud'i na ce"e...am...yanzu ba na gidanmu"

"Ki na ina? Koma ina ne ki kwatanta min,ga ni nan zuwa yanzu" Ya fad'a cikin d'an fad'a-fad'a.

Jikina ya yi sanyi,na fara tunanin zuwan na shi na lafiya ne ko akasin haka? Amma na fi kyautata zaton alkhairi ne, tunda na san ban yi masa wata kwab'a ba a y'an kwanakin nan.Don haka tiryan-tiryan na kwatanta masa gidan Anti,bai ce komai ba ya katse kiran,ni kuwa na tashi da sauri na shiga band'aki na yi wanka,duk da na yi d'azu na yi kwalliya,na saka doguwar riga,na yafa k'aramin mayafi,na yi zaman jiran shi.

Anti da ke ta hada-hadar girkin dare ta kalleni ta ce"to! Ke kuma ina zuwa haka,ki ka yi shiri ki ka kame a falo?"

Na ce"Anti Habib ne zai zo".

Ta ce"to! Ai da sai ki ce ya shigo,ku yi firar ku a cikin gida ko?"

Na ce"a'a,sauri ya ke yi,abu zai bani ya wuce".

Ta ce"to ai shikenan,ki gaishe shi".

"Zai ji" Na fad'a ina tashi don Salim ya k'ara kira,na san ya k'araso ne.

Sai da na fita na d'aga kiran,ban ma kai ga yin sallama ba na hango shi tsaye a kusa da motarsa,ya na sanye da farar shadda da bak'in glass,ya yi kyau sosai, sai na ji kamar na je na rungume shi na bud'e zuciyata,ya ga irin k'aunar da na ke yi masa, da kuwa babu shakka sai ya tausaya min ko da ba zai karb'i soyayyata ba.

A slow na dinga taku,har na k'araso inda ya ke a tsaye,na yi masa sallama na sunkuyar da kai,ganin yanda ya kafeni da ido tunda na taho

Bai amsa sallamar ba ya fara magana"Zinatu sunanki ko?"

Na ce"e,haka ne"

Ya ce"me ya sa kike son shiga rayuwata?"

Na d'ago na kalle shi,sai na ga tsakanin sa da Alllah ya ke tambayata, na maida kaina k'asa na ce"Allah ne ya jarabceni da son ka,wallahi ba yin kaina bane,kuma da alkhairi nake son ka ba sharri ba"

Ya ja dogon tsaki ya ce"me ya kaiki wurin Junaina?"

Gabana ya fad'i,don ban shirya k'aryar da zan yi ba,tunda ban tsammaci tambayar ba,don haka na ce"ni? Yaushe na je?"

Sai ya ciro wayarsa a aljihu ya yi y'an danne-danne,ya nuno min fuskar wayar, gabana ya fad'i ganin hotona a wayar,ina zaune a shagon Junaina.Na shiga mamaki da tunanin yanda a ka yi har ta min hoto ban lura ba,da kuma tunanin yi min hoton ma duka,lallai wannan Junainar makira ce ashe.

"Me za ki ce game da wannan hoton?" Ya tambaye ni,bayan ya maida wayar aljihu.

"Duk sanadin ka ne Salim,kai fa musulmi ne,don Allah ka tausaya min,ina son ka". Na yi maganar hawaye na zubo min

Ya ce"saboda ki na so na sai ki nemi cin mutuncin macen da na ke k'auna? Kin san matsayin ta a wurina kuwa?"

Na dafe k'irji,cikin firgici na ce"na shiga uku! Cin mutunci kuma? Ni d'in? To wallahi sharrin ta yi min,Allah ya isa tsakani na da ita!"

Ya daka min tsawa"ke! Kin ga dakata,ni ban zo don ki min rantse-rantse ba,na zo yi miki gargad'i ne da jan kunne,don wallahi ko ta waya ki ka sake zagin ta sai kin yi kwanan prison!"

Na saki baki ina kallon shi da mamaki,Allah ne kad'ai ya san irin k'aryar da ta had'a masa.To amma me yasa Junaina ta yi min haka?

"Idan kunne ya ji...!" Ya fad'a, ya shige motarsa ya tafi,ya bar ni tsaye,ko k'wak'kwaran motsi na kasa yi,kamar na had'iyi tab'arya.



"Zinatu!" Nazifi ya kira sunana da alamun mamaki

Na yi saurin kallon shi,sai na ga fuskarsa sam babu walwala,na ja k'afa,na k'arasa inda ya ke tsaye a k'ofar gida.

Ya kalleni da kyau ya ce "kukan me ki ke yi?"

Oho! Ni ban ma san ina hawaye ba sai da ya fad'a, na kai hannu na share na ce"babu komai".

Ya ce"ban yarda ba! Waye wannan d'in Zinatu?"

Na ce"yayan k'awata ne fa,ya zo ya ke fad'a min ta rasu tun wancen satin".

"Kuma kun shak'u da k'awar sosai ko?" Ya tambaye ni,ya na maida fuskarsa kalar tausayi

Na share wasu hawayen,ina shirin yin magana ya rigani

"K'aryar ki ba ta samu shiga ba.Me ya had'a ki da J.S har ya zo wurinki? Ba ma wannan ba,me ya fad'a miki da ya saka ki kuka?"

Na ce"a ina ka san shi?"

Ya ce"fara ba ni amsa,kafin ki tambaye ni".

Haka kawai na ji na yiwa Nazifi yardar da zan ba shi labarin gaskiyar abin da ya had'ani da Salim.Ashe rabon ayi ne ya ja ni...


Mu ka shiga ciki,a tsakar gida mu ka zauna kamar an jona min batir haka na zayyane wa Nazifi tun had'uwata da Salim har izuwa abin da ya kawo shi wurina yanzu.Ya sauke ajiyar zuciya ya na murmushi ya ce"lallai ke ma Zinatu sai a barki! Yanzu ana ta shirye-shiryen aurenki,ke ashe ki na can ki na naki d'an bikin? To wallahi ki na ruwa!" Ya kwashe da dariya

Takaici ya rufeni,na ji dama ban sanar masa ba,na ce"dama don ka yi min dariya ka so jin sirrina?"

Ya daina dariyar ya ce"to ai ki na bada labarin tun kafin ki k'arasa,mafita ta zo min raina,wannan dariyar da kika ga ina yi,har da ta mugunta"

"Mugunta kuma?" Na tambaye shi,ina had'e gira.

Ya ce"yes! Salim na ke yiwa dariya,don kuwa muddin ki ka yarda da sharad'ina to fa ki sa a ranki kawai kin zama matar Salim,ko da za a kira ki da MATAR SHIGE...
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_


BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_


*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*


Page 15



"Zan amince da sharad'in ka kowane iri ne,muddin babu sab'awa Allah a ciki" Na fad'a jikina na d'an yin sanyi,don na tsorata da jin kalmar sharad'i,tunda ga dai yanda mu ka yi da Junaina

Nazifi ya yi murmushi ya ce"babu wani sab'on Allah a ciki,zance ake yi na kud'i muddin ki na da kud'i to kuwa ni zan shige miki gaba har sai kin samu shiga.Ke ni fa ban ga laifinki ba,wallahi yaron ya had'u ga kyau ga kud'i".

Na d'an fara fargaba,don ban san ko nawa zai buk'ata ba,kuma ni yanzu kud'in hannuna ba su haura dubu takwas ba,na ce"kamar nawa kenan?"

Ya ce"ki tanadi dubu hamsin,kafin nan da kwana takwas".

"Dubu hamsin!?" Na fad'a ina zare ido,saboda na yi mamaki,kuma uwa-uba ban ga ta inda zan samu dubu hamsin ba.

Ya yi y'ar dariya ya ce"e,dubu hamsin kuma a hakan ma fa bai zama lallai ta isa ba,kin ga ba ni kad'ai zan yi aikin ba,dole sai mun siyi wani na kusa da Salim,wanda zai taimaka mu samu damar gudanar da komai cikin sauk'i,sannan dole na sai get fast..."

Na yi saurin katse shi da fad'in"dakata! Wai wane irin aiki ka ke magana akai? Kuma get fas na meye?"

Ya ce"aiki ne mai wahala kuma me hatsari,amma muddin aka yi sa'a ya wakana babu tangard'a,to ni na tattabar miki kin samu Salim kin gama,sai dai idan ba ki so ba.Shi kuma get fas na shiga wurin da zai yi birthday na ke nufi,nan da sati d'aya ne,haka na ji a bakin wani abokin sa".

Na jinjina kai na ce"na san da maganar birthday d'in,amma ban san ya kusa ba,zan yi wa Baby zancen na ji ko zan samu get fas d'in".

Ya ce"to indai za ta ba ki,kawai idan ki ka karb'a ki bani saboda ke ba sai kin shiga wurin ba".

"Kamar ya!?" Na fad'a ina b'ata rai.

Ya ce"kin ga dai yanzu ki fara tanadin kud'in kafin mu gama tsara komai,amma in sha Allah komai zai zo da sauk'i".

Na ce"Allah yasa".

Jikina duk ya yi sanyi, ina tunanin ta inda zan samu dubu hamsin,ya fita daga gidan ni kuma na shiga sashen Anti

A falo na tadda ita ta na kallo,ta kalle ni ta ce"har ya tafi?"

Ni sai yanzu ma na tuna da k'aryar da na yi kafin na fita,na ce"e ya tafi"

Ta ce "ai da ya shigo mun gaisa,yaushe za a bugo invitation?"

Ina shegewa d'akin da aka bani a gidan na ce"kai Anti,ai da saura".

Zama na yi na kira lambar Baby,ta d'auka,bayan mun gaisa na ke ce mata"ashe birthday d'in mutumin nawa ya zo,ko gayyata ko?"

Ta yi dariya ta ce"ya ma zama naki ko? Ai ban yi zaton za ki je ba,in dai za ki je gobe ki zo ki karb'i katin,jiya ya bani guda uku"

Na ce"me zai hana ni zuwa? Wani ma ya yi rawa bare d'an makad'a? To amma sauran biyun na waye?"

Ta ce"a'a,ai dama ya bani ne kawai ko da wanda zan gayyata,tunda kin ga ni ba sai da get fas ba,tare za mu shiga da shi".

Na ce"kuma Junaina ta na zuwa?"

Ta yi guntun tsaki ta ce"wai ke meye damuwarki da wannan banzar? Me zai kawo ta?"

Na yi dariya na ce"ke dai kawai ba kya son ta,abu nasu me zai hana ta zuwa?"

Ta ce"ai sai ta zo mu gani".

Na ce"to suwa za ki bawa? Guda biyu nake so,ina son gayyatar wata k'awata ne".

Ta ce"ok! Ba matsala,ko gobe sai ki zo ki karb'a ai,don dai yau yamma ta yi ne ma".

Daga haka na yi mata godiya muka yi sallama.


Washegari da safe Nazifi ya kira ni a waya,ya ce min sun riga sun shirya komai da yanda abun zai kasance,amma fa babu yanda za a yi dubu hamsin ta isa,don haka dole na samo hanyar da kud'i za su shigo.

Gabana ya fad'i cikin sauri na ce "yanzu kana ina?"

Ya ce"ina d'akina,amma yanzu zan fita".

Na ce"to idan ka fita ka jirani a k'ofar gida,sai na fito mu yi magana".

Haka kuwa aka yi,ya na fita ni ma na fita,na yi sa'a ma Anti ba ta falo. "Wai Nazifi dubu hamsin d'in ma ka san da yanda zan samu,da har ake neman k'ari?"

Ya ce"to Zinatu me zai hana a hak'ura? Tunda babu dole, wai ni dama taimakon ki zan yi,ganin halin da kike ciki,kuma da ina da kud'i wallahi ni me iya biya ne ayi miki komai ba tare da ko sisinki ba".

Na sauke ajiyar zuciya na ce"to yanzu nawa ake buk'ata?"

"Dubu d'ari biyu" Ya fad'a kai tsaye.

Na dafe k'irji tare da zaro ido na ce"haba Nazifi! Ko sata na fara ai ba na jin zan had'a dubu d'ari biyu nan da kwana bakwai".

Ya yi dariya ya ce"wa ma zai aike ki sata? Ki na mace,macen ma buduruwa,buruwar ma me kyaun suffa irinki Zinatu amma ki dinga tunanin ta inda za ki samu dubu d'ari biyu acikin kwana bakwai? Wallahi sai dai rashin niyya!"

Cikin son gano inda zancen sa ya dosa na ce"ban fa gane ba,ka yi min dalla-dalla".

Bai yi magana ba ya d'akko wayarsa a aljihu,kafin na ankara ya k'yasta min hoto,sannan ya ce"ba ni minti biyar ki gani".

Ya cigaba da danne-danne a waya,kafin ya kalle ni ya ce"na fad'a miki ba ni kad'ai zan yi aikin ba,dole sai mun had'a da direban sa,duk da ma na ji ance bai fiya son tafiya da direban ba,sai in mahaifinsa ya matsa masa.Sannan wanda zai kula da abinci da kuma abun sha a wurin,shi ma dole sai mun biya shi,ke megadin gidansu ma sai mun biya shi,sannan shi ma abokina da za a yi aikin tare da shi sai an biya shi,ni kuma na yafe, na miki saboda Allah".

Na ce"ni fa duk ba wannan ba,so na ke na fara jin yanda aikin zai wakana,idan na ji ba mai yiwuwa bane gwara na hak'ura kawai".

Sai ya duba wayarsa da na ji shigowar sak'o ya ce"kin gani ko!? Dama na fad'a miki ai ki na da kadara" Ya yi maganar ya na murmushi

Cikin rashin fahimta na ce"wai mene?"

Ya ce"yanzu na turawa wani gaye hotonki,na ce masa haja ce sabuwa dal,nawa zai siya? Shi ne ya ce ya siya dubu d'ari biyar kwana biyu".

"Nazifi ni ce hajar!?" Na fad'a da k'arfi,zuciyata na zafi

Ya yi shiru ya na kallo na. Na d'ora"tun farko sai da na fad'a maka zan yarda da sharad'in ka ne kawai idan babu sab'on Allah a ciki..."

Ya katse ni"wannan ba ya cikin sharad'i ai,idan ki na da hanyar samun kud'in an wuce wurin".

Na ce"Nazifi,ban tab'a Zina ba,kuma ba zan fara ta ba saboda Salim,idan na bada kaina ka na da tabbacin abun da za mu shirya d'in zai yiwu? Idan ba mu yi nasara ba fa? Na yi biyu babu kenan fa,ko kud'in za su siyo min wani mutuncin? Idan ma aikin ya yi kyau,da wane ido zan kalli Salim bayan ya aureni? Me zan fad'a masa?"

"Gaskiya ne!" Ya fad'a da d'an rauni a muryarsa

Sannan ya ce"ni dama na yi tunanin ba ki da hanyar samun kud'in ne,shi ya sa na yi hakan".

Na yi huci me zafi na ce"tabbas! Ba ni da wata hanya da zan samu dubu d'ari biyu,amma hakan ba zai sa ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login