Showing 18001 words to 21000 words out of 36102 words

Chapter 7 - MATAR SHEGE HAUSA NOVEL

28 Mar 2025

3649

da jarumta na ce"Yaya Habib, ina son magana da kai ta fahimta,Allah yasa za ka fahimce ni".

Ya sake tattara hankalin sa wurina,alamun damuwa k'arara sun bayyana a fuskarsa ya ce"me zai hana? Zan fahimce ki Zinatu, ki fad'a min don Allah"

"Idan na tambaye ka,ka na so na ban yi maka adalci ba, na san duk duniya babu wani namiji da ya ke so na sama da kai Yaya Habib,amma a wane mataki ka ajiye so na a zuciyarka?"

Ya sauke numfashi har yanzu dai da alama bai nutsu na ya ce"Zinatu,ba iya son ki nake ba,har da k'aunarki,k'auna me tsanani ma kuwa,kuma kin kai mataki na k'arshen k'arshe a zuciyata".

Na d'auke kaina daga kallon sa na ce "idan na fasa auren ka ya za ka ji? Ma'ana idan k'adddara ta sa na auri wanin ka..."

Ban k'arasa ba ya katse ni,a sanyaye"amma me ya kawo wannan maganar?"

"Ka fara bani amsa kafin ka ji dalili" Na fad'a har yanzu ban kalle shi ba.

Cikin raunin murya ya ce"Zinatu ni musulmi ne,na yarda da k'addara me kyau da akasin ta,wallahi ina tunanin irin yanda zan ji,da kuma yanda rayuwata za ta kasance idan ban aure ki ba, saboda ke kad'ai nake so.Amma hakan ba zai sa na kasa yarda da k'addara ba,tunda na sani wani ba ya auren matar wani,kuma duk da ke kad'ai ce a zuciyata,amma a kullum ina sake neman zab'in Allah".

Jikina ya yi wani mugun sanyi,gaskiya Habib ya na da hankali,kuma na san har da ilimin addini a wannan kyaun zuciyar nasa,ina ma ace shi ne Salim! Da zan bugi k'irji cikin dubunnan mata na ce na fi kowace mace dacen miji,sai dai kash! Zanen k'addara ba ya gogewa,don kuwa har yanzu ban ji son Habib a raina ba,sai dai tausayin shi,kuma wallahi ba zan iya sadaukar da farincikina ba akan shi,sai dai ya yi hak'uri ya d'auki tasa k'addarar kamar yanda nake shirin rungumar tawa

"Akwai wata matsala akan maganar aurenmu ne Zinatu?" Ya tambaye ni

Kamar na yi masa k'arya sai dai na daure na ce"Yaya Habib ko a cikin maza kai namiji ne,ka had'a abubuwa da dama wanda duk mace me hankali za ta so ta same ka a matsayin abokin rayuwa,sai dai ni har yau na kasa jin son ka a zuciyata saboda ba ni da hankali..."

Ya yi saurin katse ni da fad'in"a'a Zinatu,kar na sake jin haka daga bakinki,ki na da hankali,wannan ba laifinki bane laifin zuciyarki ne,shi ya sa ake son mutum ya dinga addu'ar Allah yasa ya fi k'arfin zuciyarsa,zuciyarki ta fi k'arfin ki,da ace kin fi k'arfin ta za ki iya yi mata tilas ta so abin da hankalin ki ya ke baki daidai ne".

Wasu hawaye suka zubo min,na share na ce"wallahi har zuciyata,na so na yi wa mahaifana biyayya don na faranta musu,su yi alfahari da ni ko da sau d'aya ne a rayuwa,amma rafkananniyar zuciyata ta gaza bani had'in kai.Ka yi hak'uri Yaya Habib na fasa auren ka,saboda ko da na aure ka ba zan tab'a iya baka farincikin da ya dace namiji nagartacce irin ka ya samu daga matarsa ba".

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Ya furta kawai

Shiru na tsawon lokaci sannan ya ce"Zinatu na sani dama can ba kya so na,amma na tabbata yanzu akwai dalilin ki na fasa aurena,me ya sa? Don Allah kar ki b'oye min".

Gaskiya ban ji zan iya ba shi labarin Salim ba,don haka na girgiza masa kai alamar a'a sannan na ce"ka d'auka hakan k'addara ce kamar yanda ka sanar da ni ka yarda da ita.Ni dai yanzy alfarma d'aya nake nema a wurin ka, wannan alfarmar idan ka yi min ita ce kawai za ta sani na tabbatar da k'aunar da kake yi min,kuma zan rik'e ka a zuciyata masoyi na gaskiya,na yi maka alk'awarin duk sallolina biyar na kowace rana zan yi maka addu'ar Allah ya baka mace ta gari,kuma Allah ya cire maka so na a zuciyarka".

"Wace alfarma ce wannan?" Ya tambaye ni,jikinsa duk ya yi sanyi

Na gyara zama ina fuskantar sa na ce"Yaya Habib so na ke ka fad'awa manya ka janye maganar aure na,don Allah ka yi min wannan".

Ya saka yatsan sa a baki ya ciza kafin ya ce"haba Zinatu! Me yasa ki ke da son kanki da yawa? So ki ke ni aga laifina fa kenan,ki na so a saka ni a jeren masu sab'a alk'awari kenan? Kuma da wane idon kike so na kalli mahaifanki?"

"Ka na nufin ba za ka iya yi min wannan alfarmar ba,a matsayina na wadda ka ke kira farincikin ka?" Na tambaye shi muryata na rawa.

Ya tashi tsaye ya ce"e,ban yi miki k'arya ba Zinatu,ke ce farincikina,amma ba zan iya yi miki wannan abun da kika nema ba,gaskiya sai dai ki yi da kanki.Kuma ki yi tunani kafin ki yanke hukunci,so da yawa mutane su na son abu kuma abun ba alkhairi bane a rayuwarsu,kuma sai su k'i abun da shi ne alkhairi a duniyarsu da lahirarsu,shi ya sa istihara take da amfani,ki je ki yi ta istihara ki nemi zab'in ubangiji,idan still kin ji ba za ki iya aurena ba,sai ki sanar musu da abin da kika yanke,ni ma zan saka ki cikin addu'o'ina in sha Allah, Allah ya mana zab'in alkhairi".

Ya na gama maganar ya buga mashin d'insa ya tafi,ni kuma na tashi na shiga gida ina kukan rashin gaskiya.

'Dakina na shiga na fad'a a katifa,na fashe da kuka sosai,ni ma na san ban yi wa Habib adalci ba,to amma ya zan yi? Haka k'addarar mu ta zo mu duka ukun,da ni, da shi da Kuma Salim,duk Allah ya jarabce mu da son maso wani.

Bayan na gama kuka na sai tunanin sharad'in Junaina ya dawo min,a gaskiya ina son Salim kuma ko da na ke ganin zan iya yin komai a kansa abun bai kai na aikata zina ba,to na saida mutunci na don ya aure ni,na je masa fanko kuma na saka ran zan yi wata daraja a idonsa? Ai idan na yi hakan na yaudari kaina,kamar an ba ni umarni na d'akko wayata na dubo lambar Junaina na doka mata kira

Ta d'aga da sallama ta na kiran sunana,ban amsa ba na fara magana"Junaina wannan sharad'in ya yi min girma,gaskiya ba zan iya ba,idan akwai wani ki fad'a".

"Za ki yarda da romance? Ina nufin ki yarda ya biya buk'atarsa ba tare da ya kusance ki ba". Ta fad'a kai tsaye kamar me bani shawarar na yi azumi ko sallah

Na yi shiru,ina tunani duk zina ai sunan ta d'aya ne,ko ta ido ma an ce ana zina bare kuma wannan babban abun

"Idan fa kin ga ba za ki iya ba,babu dole" Muryarta ta katse ni.

Mu na cikin wayar kiran Baby ya shigo,na yi saurin ce mata"zan kira ki anjima".

Na katse kiran,na d'auki na Baby na k'irk'iri murmushi me sauti na yi mata sallama.

Ta amsa sannan ta ce"da fatan kina lafiya matar Yaya Salim"

Na ji zuciyata ta motsa,na yi y'ar dariya na ce"Baby kenan,to Allah ya tabbatar".

Ta ce "Amin".
Sannan ta yi jim ta ce" amm...Zinatu ina son ganin ki gobe,akwai magana me muhimmanci da za mu yi da ke akan Salim,ina tunanin na samo mafitar da za ta shigar da ke wurin shi ta hanya me sauk'i".

"Da gaske kike!?" Na fad'a da d'an k'arfi,farinciki ya mamaye zuciyata

Ta ce"e,goben ki zo shagon gyaran jikina da yamma"

Na yi mata godiya na ce zan zo mu ka yi sallama.Tun kafin na ajiye wayar na ji muryar Baba ya na k'wala min kira

Gabana ya fad'i,don na san yau dama tara ni ya ke yi,na saka hijjabi na fita kaina a k'asa kamar malama,na je na tsugunna nesa da shi a tsakar gida na ce"Baba ga ni".

Ya ce"Zinatu da gaske dai ban isa da ke ba ko?"

Muryata na rawa na ce"a'a,wallahi ka isa da ni Baba".

Ya ce"to indai kin yarda ni ne na haifeki,daga yau kada ki sake fita ko k'ofar gida sai da izinina!"

Ban ce komai ba,sai gyad'a kai da na yi alamar na amince,na tashi na koma d'ak'i na fashe da kuka.




HABIB😥
Babu me son Habib don Allah?
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_


BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_


*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*


Page 13



Bacci kad'an na samu a daren,ina ta tunanin yanda zan yi na yiwa Baba biyayya,ba na son b'ata masa rai,amma kuma Baby ta buk'aci gani na goben,kuma na san ba zai yiwu na ce ita ta zo ba,tunda k'aruwa ta ce ba tata ba,na so ma na ce ta fad'a min ta waya sai kuma na ga rashin dacewar hakan,ta na ta k'ok'ari a kaina,ai sai ta ga kamar ma ban damu ba,itama ta janye jikinta.Ga tunanin yanayin da na saka Habib a ciki,watak'il ya na can a cikin damuwa ta dalili na.Ita dai Junaina na ajiye buk'atar su a gefe,don ta yi kad'an ta saka ni aikata zina,ta dad'e ba ta bani bayanan Salim d'in ba don uwarta!.


Washegari da ciwon kai na tashi,ina d'aki tun safe,na kira Salim har sau biyar bai d'aga ba,na tura masa sak'on fatan alkhairi,ina nan kwance ina ta juye-juye da sak'a da warwara na ji sallamar yayata anti Na'ima,na yi farinciki da zuwanta sosai kuwa,na fito tsakar gida inda suke zaune da Mama Saude ni ma na zauna mu ka shiga shan fira,don babu laifi anti Na'ima su na shiri da Mama,cikin firar take fad'a min alfarma ta zo nema a wurin Baba

Da mamaki na ce"alfarma kuma anti?"

Ta ce"e mana,so na ke ya bani ke mu tafi gidana,na fara yi miki gyaran jiki".

"Kuma tun yanzu ake yi?" Na tambaye ta.

Ta ce"to Zinatu sai yaushe? Sati biyar ne fa ya rage,sai na miki na sati hud'u,ki dawo idan bikin ya rage sati d'aya".

Jikina ya d'an yi sanyi na ce"to Allah yasa ya yarda".

Mama ta ce"zai ma yarda,ai ko ni sai na saka baki ya amince,to wa ya k'i gyara?"

Anti ta ce"a to! Idan ma Habib d'in kike ji ai ya san hanyar gidana,sai ya dinga zuwa kuna gaisawa".

"Uhm!" Kawai na ce,don ni fa ganin lamarin aurena da Habib na ke kamar almara.Na rasa ta yanda zan sanar da su na fasa,kowa na kalla sai na ga ya yi min kwarjinin da ban isa na tunkare sa da wannan batun ba,to amma fa na ga hakan ba mafita bace,tunda abu ya na ta k'ara matsowa,ya zama dole na samu mafita kafin sati biyun.

Bayan la'asar ta koma gidan Ummi, ta ce idan Baba ya dawo na kira ta a waya,kuma na shirya idan ya amince a yau za mu tafi Hotoro,k'arfe hud'u da rabi Baby ta yi min waya ta na tambayar zan shigo kuwa? Na ce mata ina nan tafe.

Da na gama shiri ma na jima ina nuk'u-nuk'u a d'aki,don ina shakkar taka umarnin Baba yau d'in,sai da na ga Mama ta shiga band'aki,sannan na zo na fice sad'af-sad'af,ba tare da na rufe k'ofar d'akina ba,na je na hau adaidaita,sai Sharad'a.

Muka gaisa da Baby cikin fara'a,ta bani wurin zama ta na tsokana ta da matar Yaya,ni kuwa sai murmushi nake ina jin kamar ya tabbata.

"Zinatu kin je wurin Junaina?" Ta tambaye ni

Kamar na yi mata k'aryar ban je ba sai na ga rashin dacewar hakan, "e na je" Na bata amsa

Ta gyad'a kai ta ce"to ya ku ka yi? "
Na yi jimm! Don ba na jin zan fad'a mata irin sharad'in da Junaina ta bani,don haka kawai na ce"cewa ta yi na je na tambaye shi,shi ya san dalilin da yasa ya ke son ta".

Baby ta tab'e baki ta ce"ai dama na fad'a miki kar ki je".

"Kin san mafitar da na samo miki?" Ta tambaye ni,na girgiza kai alamar ban sani ba

Ta ce"kin ganni nan! Duk gidanmu an fi so na,ana ji da ni,kuma ana gudun b'acin raina sosai, musamman Yaya,don ni kad'ai Allah ya jarabta da ciwon zuciya,idan ya tashi ina shan wahala sosai,su na mugun lallab'a ni don kar ciwon ya tashi,to kin ga kuwa idan na so za ki iya shigowa rayuwar Salim ta dalilin ciwona".

Na yi jim! Na y'an sakanni,kafin na ce"amma Baby ki na ganin hakan zai yiwu? Kuma ke d'in tada ciwon naki za ki yi saboda ni?"

Ta yi murmushi ta ce"Zinatu,ina son Yayana sosai,ina yi masa sha'awar ya auri macen da take mugun son shi kamar ke,saboda ban San lokacin da zai daina shaye-shaye ba,kuma kin San zama da me shaye-shaye sai wanda ya jure,sai mace me mugun hak'uri, ko kuma wadda take bala'in k'aunar mijin".

Na jinjina kai alamar gamsuwa,ina dai sauraron ta,amma ni har mantawa nake da shaye-shayen Salim,don a ganina ba komai bane,wannan k'aramar matsala ce.Hmmm! Ashe na yi kuskuren fahimtar da ya kusa jefa ni a rijiya gaba dubu,nan gaba dai za ku ji...

Baby ta d'ora da fad'in"zan nuna masa kawai indai yana son farinciki na to ya aure ki,idan ya k'i amincewa sai na fara nuna ina cikin damuwa,na daina walwala a gaban kowa,hakan zai tashi hankalin kowa na gidan,har su nemi jin ba'asi,to a sannan ne zan sanar musu da na zab'a mishi ke kuma idan bai aureki ba mutuwa zan yi..."

Ta na kawowa nan na tuntsure da dariya,ta saki baki ta na kallo na,sai da na yi me isa ta sannan ta rik'e hab'a ta ce"mene ya sa ki dariya?"

Na ce"haba Baby! Na ji ki na zance ne sai kace a shirin films, yanzu kawai sai ki cewa iyayenku kin yiwa Salim zab'in matar aure? Kuma don kin ce za ki mutu idan bai amince ba sai su yi masa dole?"

Baby ta yi murmushi ta ce"ki na mamaki ne? Da ace yau zan bawa Abba da Ammi labarin ki,na ce musu na yi k'awa ina son ta sosai,wallahi gobe idan ki ka zo gidanmu sai kin yi mamakin yanda za su karb'e ki,don har Abba ba zai fita aiki ba saboda ku gaisa".

Na jinjina kai na ce"a lallai na yarda ke y'ar gata ce".

Ta yi dariya ta ce"yanzu kin san yanda za a yi? Zan cewa Ammi na samu k'awa,na san za ta yi farinciki sosai"

Na katse ta da fad'in"to wai ke d'in ba ki da k'awaye?"

Ta yi wani murmushi ta ce"yanzu ba ni da k'awa ko d'aya,da dai ina da k'awa,sai ta ci amanata, na yarda da ita sosai ina son ta,amma ta cuceni,ta raba ni da wanda na ke masifar so,da tuni shi zan aura,yanzu haka har an yi auren su.Tun daga lokacin ban kuma sha'awar yin wata k'awa ba,kowa sai dai mu gaisa sama-sama,amma banda k'awance".

Cikin tausaya mata na ce"Allah sarki,Allah ya saka miki cin amanar da suka yi miki".

Ta yi murmushi ta ce"manta da su kawai.Za ki fara zuwa gidanmu as mun shak'u da juna,ni ma zan dinga zuwa gidanku,to daga nan sai na fara nuna wa Ammi kyaun halinki,idan na ga ba ta gane inda na dosa ba,sai na yiwa Salim zancen kai tsaye,tunda ya san komai,idan bai amince ba sai na yi plan d'in da na shirya"

Na ce"amma ki na ganin hakan zai yiwu kuwa?"

Ta ce"yes! Abu me sauk'i,amma fa gaskiya sai nan da sati uku".

Gabana ya fad'i da na tuna saura sati biyar bikina,ga shi ta ce sai nan da sati uku za a fara wasan,kuma ban san sati nawa game d'in zai d'auke mu ba.

"Me yasa sai nan da sati uku?" Na tambaye ta

Ta ce"e,saboda nan da sati uku Salim zai yi birthday, ya na girmama birthday d'insa,shi ya sa ba na son rage masa farinciki kafin zuwan ranar,don indai ina cikin damuwa shi ma ba ya tab'a walwala".

Hmmm! Na sauke ajiyar zuciya na ce"to shikenan Baby,na gode sosai da kulawarki".

Ta ce"kar ki damu,ai yi wa kai ne".

Ta rakoni har bakin titi na shiga adaidaita sahu na kama hanyar gida.Na yi ta tunanin halin da na jefa rayuwata a ciki,gefe guda kuma na gamsu da mafitar da Baby ta kawo d'ari bisa d'ari,sai dai ina gudun k'urewar lokaci,ace sai aurena ya rage sati biyu za a fara wasan? Yanzu idan komai bai yi daidai ba a sati biyun ya zan yi? Don ban ga alamar Habib zai sanar musu da na fasa auren shi ba,ni kuma gaskiya ina jin tsoron abin da zai biyo baya idan na furta na fasa auren.Kuma ita kanta Baby ban yi kuskuren k'in sanar mata an kusa aurena ba kuwa? Amma gaskiya ba zan fad'a mata ba,don ina jin tsoron ta janye taimakon ta,ta ce na hak'ura da Salim


Da wannan tunane-tanayen na k'arasa gida,lokacin ana shirin sallar magriba,don haka ina shiga gida na d'aura alwala na shiga d'aki,aikuwa Baba ya na dawowa ni ya fara k'wallawa kira,ina jin muryar Mama ta na fad'in,

"Wai wace Zinatu ka ke kira? Ai ba ta gidan nan tun d'azu".

Baba ya ce" Zinatun ce ta fita yau? Amma ai ga d'akinta a bud'e ko?"

Mama ta ce"zancen kake so,ai sai ka shiga d'akin ka d'akko ta".

Ina jin haka na kwanta akan sallayar kamar me bacci,don na san Baba akwai ganin k'wak'waf!

Aikuwa sai da ya zo ya d'aga labulen kamar yanda na zata
"Ke Zinatu!" Ya kirani da k'arfi

Na tashi firgigit kamar wadda aka tasa daga bacci na ce"uhm!"

Ya ce"wane irin shashanci ne haka bacci da magriba?"

Na tashi zaune na ce"kaina ne ya ke ciwo"

Ya ce"to Allah ya sawak'e,yanzu Na'ima ta kirani a waya,wai kun yi zancen za ki je gidanta ki kwana biyu,ta jirani kuma sai mijinta ya mata waya ga shi nan a hanyar shigowa garin,to yanzu dai ta riga ta tafi gidan,ke kuma gobe sai ki shirya ki je".

Na ce"to Baba".

"Ai ba to ba,saura ki je

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login