Showing 15001 words to 18000 words out of 36102 words

Chapter 6 - MATAR SHEGE HAUSA NOVEL

28 Mar 2025

3645

kuma ya ce shi zai jira har lokacin da za ta nutsu,ta amince da aurensa,ba zai tab'a yin aure ba,saboda ta ce muddin ya yi aure to ta rabu da shi har abada! A cewar shi dai yanzu ya rabu da ita,amma duk ba mu yarda ba,sai dai daga lokacin da na ga jakarki a d'akinsa na fara zargin wani abun kuma na da ban.Wannan shi ne labarin Junaina,sai ki cika alk'awari ki fad'a min gaskiyar tsakanin ki da Yaya".

Hawayen da ban tantance ko na meye ba suka shiga zubo min,tun ina gogewa har na fashe da kuka sosai.Wata k'aunar Salim da tausayin shi suka yiwa zuciyata dirar mikiya,har na ji idan ba shi na aura ba ni ma har abada ba zan yi auren ba.

Baby ta tsaya ta na kallona da alamun mamaki,sannan ta ce"Allah yasa dai ba zatona bane ya ke shirin tabbata!".

Na yi shiru ina saita kaina,na ce"ko kad'an,Baby kar ki zargeni ko d'an'uwanki,yanda ya fad'a miki d'in na san gaskiya ne...". Na kwashe labarin tun farkon had'uwarmu har izuwa ranar da na bar jakata na fad'a mata.

Ta yi shiru kamar me tunani,sannan ta kalleni ta ce"Zinatu tsakanin ki da Allah da gaske ki ke son Salim?"

Na yi saurin fad'in"wallahi har zuciyata nake k'aunar Salim,tunda na yi masa kallo d'aya,idan so ya na zama k'addara to son Salim shi ne tawa k'addarar". Na fashe da kuka

Cikin sanyin murya ta ce"ayya! Ki bar kukan haka,ba zan yi miki alk'awarin auren Salim ba,amma zan yi iya yi na ganin na had'a alak'ar ku,ke ma sai ki had'a da addu'a, da kuma y'an dabarun ki".


Na ce"na gode sosai y'ar'uwa,amma a ganina me zai hana na shiga jikin Junaina,na karanci halaye da d'abi'unta,ko koyi da ita zai sa Salim ya maye gurbinta da ni?"

Baby ta yi murmushi ta ce"Zinatu gurbin ido ba ido bane,kuma shi so babu ruwan shi da halayya,tunda ita d'in yake so,to fa ko za ki yi birgima a tab'o ki koma kamarta sak,bai zama lallai ya so ki ba".

Na jinjina kai na ce"hakane,amma duk da haka ina son ganin ta dai,ki taimakeni da lambarta don Allah".

Ta ce"wa!? Ni kam me zan yi da lambarta,kin san yanda na tsaneta kuwa? Zan dai kwatanta miki wurin sana'arta idan ki na so".

"Ina so!" Na fad'a da sauri.

Ta kwatanta min,babu nisa ma sosai,a zoo road ne wurin,kuma siffanta min kamannin ta

Na rakata har bakin titi ina ta kwarara mata godiya kamar ba gobe.
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_


BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_


*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*


Page 11



Ina dawowa daga rakiyar Baby,na zauna na kira lambar Salim,har ta katse bai d'auka ba,sai da na kira sau uku sannan ya d'aga cikin fushi ya ce"ke! Lafiya kike kira na?"

Na d'an ji fad'uwar gaba,amma na dake na ce"lafiya lau,na kira ne kawai na gaishe ka,kuma na ji lafiyarka".

Bai bani amsa ba,kawai ya kashe wayar.Na had'a kai da gwuiwa,hawaye suka min sallama,na jima a haka ina nazari kafin na tashi cikin sauri,kamar an tsikare ni

Wanka na yi,na shirya cikin dogon hijjabina har k'asa,na zari jaka da wayata na fice.Sai dai ina tsayawa a bakin titi don jiran abin hawa,kawai na ga Baba ya sakko daga adaidaita,na d'an ji fargaba da kunyar sab'a umarnin sa sun kama ni,amma na dake cikin zuciyata na ce"sai dai ka yi hak'uri Baba,addu'ar ce dai za ka yi ta min".

Kafin ma ya k'araso inda nake,har na fad'a adaidaita,ban zarce ko'ina ba sai Zoo road, Allah ma ya taimake ni me mashin d'in ya san wurin,don haka ban sha wata wahala ba aka kaini har k'ofar shagon Junaina.Babu laifi wurin da girman sa,ya burgeni tun daga k'ofar,na saita kaina na k'ara nutsuwa ina kallon kaina daga sama har k'asa,wai na tabbatar babu wata makusa,kamar dai wadda zan gana da shugaban k'asa ko wani sarki

Tun kafin na k'arasa ta glass na hango wani matashi daga ciki,ya kafeni da ido kamar ya sanni,na tura k'ofar na shiga sallama d'auke a bakina,shi kad'ai ne a ciki don iya hange na ban ga alamar Junaina ba,ko kuma masu siyan kaya,matashin ya tashi da sauri ya amsa sallamar,ya fara washe baki ya na min sannu da zuwa,da alama dai ya na da rawar kai kuma sam bai burgeni ba,don haka na had'e gira na ce"Junaina nake nema".

Ya turo min kujera tare da fad'in"wallahi yanzu ta fita,amma ba za ta jima ba,ki zauna bari na kira ta a waya".

"Na gode" Na fad'a bayan na d'osana na zauna a kujerar,sannan ya d'auki waya ya kirata.Ya dinga k'ok'arin ja na da fira ni dai kawai ina bin sa da e,a'a,a haka har kusan minti ashirin,ni dai har na fara k'osawa sai ga ta ta shigo da sallama

Na yi saurin d'agowa daga kallon wayata,na zube idona a kanta,fara ce tass,ba don kar ace kishi nake ba ma da na ce har da k'arin mai a hasken,ba ta da wani dogon hanci,sai manyan idanu kamar k'wai,bakinta d'an k'arami don nawa ya fi nata girma,wando ne a jikinta da riga iya gwuiwa,ta nad'e kanta da mayafi,sai wani uban glass da ta maida shi goshinta,y'ar siririya ce kamar yanda Baby ta fad'a min

"Wa alaikumus salam" Na amsa ina yi mata murmushi

Ta k'araso ta ja kujera ta zauna,ta na kallo na ta ce"ke ce me nema na?"

Na ce"ni ce".

Ta ce"to Allah yasa dai lafiya"

Na yi murmushi na ce"in sha Allah ".

Ta jinjina kai ta na sake kallo na daga sama har k'asa ta ce"to ina sauraron ki"

Na d'an kalli matashin nan,na ga mu ya ke kallo, sai na ji nauyin yin magana a gabansa,don haka na kalle shi na ce"bawan Allah ko za ka iya bamu wuri?"

Junaina ta ce"Sani jira mu a waje mana". Ya tashi ya fita ya na waige na.

Na maida hankalina kan Junaina na ce"sunana Zinatu,don Allah wata tambaya na ke son yi miki da farko".

"Uhm" Ta ce kawai.

Na ce"na san duk tarihin soyayyarku da Salim.Don Allah me yasa kika k'i amincewa da auren shi har yanzu? Ko ba ki san yanda yake k'aunar ki ba?"

Sai ta yi shiru na y'an sakanni ta na kallo na,sannan ta yi murmushi ta ce"shi ne ya turo ki da wannan tambayar?"

Na ce"a'a,Salim ba shi da masaniyar zan zo wurin ki,kuma ba a bakinsa na ji tarihin soyayyarku ba".

Sai ta jinjina kai ta ce"ina son Salim, amma ni ban shirya yin aure yanzu ba,shi ne kawai dalili"

"To me yasa?" Na yi saurin tambayar ta

Ta ce"saboda ban shirya kashe rayuwata ba".

"Kisa kuma?" Na tambaye ta da mamaki

Ta yi y'ar dariya ta ce"e mana! Ai ita mace da zarar ta yi aure to rayuwarta ta zo k'arshe,shi ya sa nake son na gama cin duniyata da tsinke kafin aure,tunda ina da dahir d'in me yi min son gaskiya,kuma zai jirani duk tsawon lokaci".

Na yi shiru ina mamakin kalaman ta.Ta d'ora"menene dalilin zuwanki wurina?"

Kai tsaye na ce"son Salim nake,kuma na zo ne na rok'eki ki bani wasu shawarwari don na samu kan Salim cikin sauk'i".

"Me!?" Ta fad'a da d'an k'arfi ta na zaro ido.

"Shi Salim d'in ya san ki?" Ta tambaye ni

Na sauke numfashi na ce"ki nutsu don Allah, Salim ya san ni,amma bai amince da ni ba.Ni ki yanke kud'in da zan biya ki kawai ki fad'a min abin da ki ke yi masa ya ke k'aunar ki don Allah".

Sai ta jinjina kai,amma da alama dai hankalin ta ya tashi,ta ce min"ok! Gobe bayan magriba ki dawo,kafin nan na yi shawara".

Na yi mata godiya na fito daga wurin,kaina duk a d'aure,ni dai ban yi zaton Junaina ta na son Salim ba,amma a yanda na gani a idonta kam tabbas tana kishin Salim sosai.Na hau mashin na koma gida,gidan Ummi ma na wuce,don ina jin tsoron had'uwata da Baba, na yi sallahr azhar na ci abinci,na kwanta sai bacci.



Yau da wuri ya dawo daga kamfani,ransa duk a b'ace ya ke, don ya san Baby ce ta je ta kaiwa Zinatu wayarta,yau da wani ne ta yi masa haka ba ita ba,babu abin da zai hana ya yankar masa tikitin rashin mutunci,fuska a murtuke ya shigo gidan,bai tadda kowa a falo ba,ya fi zaton suna kitchen, don haka ya shiga kai tsaye da sallama,a zaune ya ga Baby ita kuma Ammi ta na tuk'a tuwo,ya d'an saki ransa bayan sun amsa sallamar ya ce"Hajiya Ammi,ke da y'arki ne ku ke yin tuwo?"

Ammi ta yi murmushi ta ce"na ke yin tuwo dai,fira kawai take taya ni,kuma ni na ce ta zauna ta huta".

"Aaaa,lallai y'ar gatan Amminta" Salim ya fad'a da d'an murmushi.

Baby ta kalle shi,ta na nazartar sa ta ce"sannu da dawowa Bros,ya aiki?"

"Aiki babu dad'i,zo mana sister mu yi sirri" Ya fad'a ya na shirin fita daga kitchen d'in.

Ammi ta ce"lallai fa sirri,idan ta yi tsami dai za mu ji".

Baby ta tashi ta na dariya ta ce"ai Ammi babu abin da zai yi tsami,indai tsakanina da my bro ne". Daga haka ta fito ta yi hanyar d'akinsa,kamar yanda ta ga ya yi can.

A zaune ta tadda shi,ya had'e rai ba kamar d'azu ba,ta k'araso jiki a sanyaye ta zauna nesa da shi,don ta lura da yanayin sa tun shigowar sa gidan,ta share ne kawai

"Akwai matsala ne bros?" Ta tambaye shi

Ya ce"ina wannan jakar?"

"Na kai mata abun ta" Ta yi maganar ta na bud'e hannu alamun ko a jikinta.

Ya sauke numfashi ya ce"haba Baby! Me yasa za ki kai mata da kanki? Kuma idan ma dole sai kin je da kanki ai sai ki takura min na kaiki"

Ta turo baki ta ce"to ba kai ka ce ba ka san gidansu ba?"

Ya yi shiru ya na kallon ta,ya na shirin magana ta riga shi "don Allah Yaya zan rok'e ka wata alfarma,duk da na san ba zan samu ba ma". Ta k'arasa a sanyaye

Salim ya ce"ina jinki"

Ta tashi ta dawo kusa da shi ta zauna,don nuna masa muhimmancin maganar,ta fara"ni dai a yanzu burina kayi aure,ka samu nutsuwa,ka manta da Junaina.Yaya! Zinatu ta na matuk'ar k'aunar ka,wallahi irin wannan macen ya dace ka aura,don na san a yanda take son ka ko ka auri Junaina daga baya za ta jure komai,Yaya Junaina fa ba son ka take ba,wallahi cutar da kai kawai take yi,da za ka bawa wata macen dama ta hanyar auren ta za ka tabbatar da hakan...".

"Baby kin san yanda nake ji a zuciyata kuwa? Ke ba ki san so k'addara bane ko?" Ya katse ta

Ta yi murmushi ta ce"alhamdulillah! Tunda har ka riga ni sanin k'addara ne,to kamar yanda ka ke ji d'in nan,ita ma Zinatu haka take ji fa,yanda Junaina ta zama k'addarar ka,haka itama ka ke k'ok'arin zama tata k'addarar..."

Ya katse ta da fad'in"a'a,ban yarda ba,ita ce ta d'orawa kanta!"

Ta yi saurin fad'in "kenan kai ma kai ka d'orawa kanka? Idan amsar e ce kenan mutum shi yake zab'arwa kansa k'addara ko? Kai me yasa ka zab'o wadda za ta wahalar da kai?"

Ya yi shiru, ya rasa abin fad'a,sai ta cigaba"wallahi Yaya na ga k'aunar ka k'arara a idon Zinatu,har kuka ta dinga yi duka saboda kai,me zai hana ka gwada saka ta a rayuwarka ko na d'an lokaci ne ka gani?"

"Na riga ki wannan tunanin" Ya katse ta.

Da mamaki ta ce"to amma me ya sa ba ka aiwatar ba?"

Ya ce"na gwada aiwatarwa,sai na tadda matsala,yarinyar ba ta dace da ni ba gaskiya, ba ta da hali".

Baby ta ce"subhanallah! Wane hali ne da ita? Kuma Yaya kai da ka ce ba ka san ko gidansu ba,ta ya ka san halinta?"

Ya yi guntun murmushi ya ce"bari na fad'a miki gaskiya, yarinyar nan akan gab'a ta zo min,dama ina son in yi aure, ba don ina buk'atarsa ba,sai dan na farantawa Abba rai,yanda yake ta lallab'a ni akan zancen auren nan,shi yasa na yanke shawarar zan yi,amma sai na samu me so na sosai,yanda bayan auren za ta iya jure kowane irin k'alubale,don Junaina ko cewa ta yi na saki matata zan saketa".

Ya nisa,sannan ya cigaba"a ranar da ta bar jakarta a d'akina,a ranar na yanke hukuncin auren ta,kuma ta na barin wurin bayan ta mari manager na shiga adaidaita sahu na bi bayanta,a gabana ta kira d'an daba ya zare wuk'a zai cakawa me mashin d'in,Allah ya taimake sa suka k'yale shi,kuma dama marin da ta yi ma ya sa ni kokwanto akan tarbiyyar ta.Washegari na dawo unguwar,na yi bincike akan yarinyar,na farko da na tambayi manyan unguwa mutum biyu,suka tabbatar min da yarinyar ba ta da tarbiyya,ta na mu'amala da maza..."

Baby ta katse shi"maza kamar ya?"

Ya ce"maza dai wanda kika sani,kuma na tambayi wasu samari su ma sun tabbatar min da hakan,to tun lokacin na san yarinyar ba matar aure bace,shi yasa na fasa". Baby ta yi shiru ta na nazari,sannan ta ce,
"Amma Yaya babu wani taimako ko nace uzuri da za ka yi mata? Ta na son ka"

Ya ce"ni kuwa na yi mata taimako,kin san matakin da managerna ya so d'auka kuwa? Da na samu labari,na gargad'e shi indai ya sake na ji wani abu ya same ta,sai na yi shari'a da shi".

Sai ta rasa abin cewa,ta ce"Yaya sallar magriba". Ta bar d'akin jiki a sanyaye,amma sam ba ta yarda da zancen yayan nata ba,kuma za ta yi bincike.



Sai bayan la'asar na koma gida,na tadda Baba a k'ofar gida shi da wani mak'ocinmu,na gaishe su,kaina a k'asa na shige gida,na zauna ina ta tunanin k'aryar da zan yi masa idan ya ritsa ni.Ga mamaki na,sai na ga Baba ya bawa banza ajiya ta,aikuwa na ji dad'i sosai na ce watak'il ya sassauta hukuncin ne.


Washegari ko minti biyar ban k'ara ba akan lokacin da Junaina ta bani,yau ta na nan kuma ita kad'ai ce a wurin babu wannan matashin,bayan mun gaisa ta kawo min lemo da ruwa,ni dai ban sha ba,burina kawai na ji ta bakinta.

Ta nisa ta ce"ke dai yanzu idan na fahimce ki,ki na son sanin duk abin da Salim ya ke so,da kuma wanda ba ya so,abin da yake burge shi,da wanda ba sa burge shi ko?"

Na ce"e hakane,idan da dama ma har kalar abincin da ya fi so,da wanda ba ya so".

Ta yi wani murmushi ta ce"za ki ji komai,amma fa akwai sharad'i".

Na ce"na amince da sharad'in ki,fad'a min kawai".

Sai ta yi y'ar dariya ta ce"y'an mata da sauri haka?"

"Zan iya yin komai don Salim ya aureni" Na fad'a ina murmushi

Ta gyara zama ta ce"kin ga yaron da ki ka gani jiya anan? Abokina ne, shi yake taya ni jire wurin nan,kuma gidanmu d'aya da shi,to jiya ya fad'a min ya na son ki,kallo d'aya ya yi miki ya ji sha'awar ki ta kama shi"

Sai ta yi murmushi ta ce"ai ban ga laifin sa ba,kin had'u Zinatu.To a tak'aice dai ya na son kwanciya dake ko sau d'aya ne,wannan shi ne sharad'in idan kin amince ko yau a shirye yake,ni kuma da kun kammala zan ba ki bayanai".

Tunda ta fara magana wani abu ya zo ya tokare k'irjina,na ji kamar na tashi na yi ta fesa mata mari.Ni kam ko da wasa ban tab'a sha'awar aikata wannan mummunan abun ba, to ta zarge ni ne ma wai da take kawo min wannan tayin?

"Ki bani lambar ki,idan na yi shawara zan kira ki" Na fad'a ina mik'a mata wayata.

Ta saka min lambar na karb'a na yi mata godiya na tafi.
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_


BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_


*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*


Page 12



Lokacin da na k'arasa gida har an yi sallar isha'i,tun daga nesa na hango Habib zaune a bencin k'ofar gidanmu,na rage sauri na dinga d'aga k'afa kamar ba na so,kallon shi kawai nake yi cikin tausayawa,indai abin da na ke ji a zuciyata game da Salim,shi ma Habib haka ya ke ji game da ni,to kuwa tabbas zan tausaya masa,sai dai ba zan iya sadaukar da farincikina akan na wani ba.

"Barka da zuwa gimbiyata". Ya fad'a bayan na zo dab da shi

Na zauna a bencin nesa da shi na ce"daga ina haka?"

"Daga gida nake" Ya bani amsa

"A yi hak'uri dai a min uzuri,na karya dokar sarauniya,ina fatan za a tausayawa raunanniyar zuciyata wurin yi mata hukunci. Na ji kin ce kin tafi hutun amsa kira,kuma ban sani ba ko har yau ba ki dawo ba,shi yasa ban kira ki ba na yi gaban kaina na zo". Ya k'arashe maganar a raunane,wai a dole na ji tausayin shi

Na k'ura masa ido tun daga kanshi,har yatsun k'afarsa,har yau na kasa gano makusar Habib,ya na so na sosai ga shi d'an'uwana,ko bai b'ata bakinsa ya fad'a min ba,na san zai kula da ni da soyayya idan ya aureni,ya na da hak'uri sosai duk wani laifi da nake yi masa da gangan ya na sani ya ke sharewa,ko wani bai fad'a min ba na san idan na aure shi zan ji dad'i.Amma sai dai kash! Kwata-kwata Allah bai d'iga min son shi a zuciyata ba,a da na amince da shi ne saboda ina ganin ni fa duk duniya babu wani namiji da zan so da aure,ashe lokaci ne bai yi ba,ni kuma GAJEN HAK'URI na ya sa ni saurin zab'ar Habib, ashe sarkin zuciyar tawa ya na dab da bayyana,gaskiya na yi garaje.

Ban san hawaye na ke yi ba sai da na ji muryarsa ya na fad'in "subhanallah! Zinatu lafiya kuwa? Me ya ke damun ki? Ko ba ki da lafiya ne?"

Na share hawayen cikin dakiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login