Showing 33001 words to 36000 words out of 36102 words

Chapter 12 - MATAR SHEGE HAUSA NOVEL

28 Mar 2025

3643

na nan zaune Salim ya shigo da sallama,Mama ta amsa ta na yi masa sannu,ni kuwa binsa da kallo kawai na yi,ina jin wata k'aunar shi, Kai! Gaskiya ina son Salim fiye da zaton ku.

Kallo d'aya ya yi min ya kauda kai,ya kalli Mama ya ce"kun ci abincin kuwa?"

Ta washe baki ta ce"mun ci abinci mun k'oshi".

"Ok! Za mu wuce gidan". Ya fad'a ya na d'aukar kwandon kayan abincin.

Ya fita,muka bi bayansa,sai kallon shi nake yi.Muna shirin shiga motar wannan likitan ya dakatar da mu,ta hanyar k'walla min kira,na dakata,shi kuwa Salim ya shige motar bayan ya bud'ewa Mama ta shiga gidan baya.

Likitan ya ce" kin ba ni mamaki".

"Na me kenan?" Na tambaye shi.

Ya ce"akan irin yanda na fad'i abin da ba haka bane,kuma ba ki nemi jin dalili ba".

Na ce"to meye dalilin?"

Ya ce"saboda ba na son tarayyarku da Habib". Na yi masa kallon mamaki

Ya d'ora"Sam! Habib bai dace da mace irinki na,ya na da hak'uri da halaye masu kyau,mace me hankali da hak'uri ce kawai ta dace da shi.Ya na yawan ba ni labarin irin yanda ya ke son ki,ke kuma ba ki damu da shi ba...".

"Kai dakata malam! Idan ka yi ne don ka raba ni da shi,to ka sani shi ka cuta ba ni ba,kuma tunda ka ga tun farko ban nemi jin dalili ba,idan da tunani ai za ka gane hakan dad'i ya yi min.Ba ni da lokacin ku!".

Ina gama maganar na wuce wurin motar na bud'e gidan gaba na shiga, ya ja muka tafi.


Gidan Babana mu ka je,na ji wata sabuwar fargaba ta kamani,Mama ta bud'e ta fita,ina shirin bud'ewa na fita,babu zato kawai na ji Salim ya...
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_


BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_


*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*


Page 20



Na ji ya kira sunana a sanyaye,na juyo na kalle shi ina jiran abin da zai fad'a,sai kawai ya tsaya ya na kallo na,ni ma na zuba masa ido son shin na ratsa duk wasu jijiyoyin jikina,wajan minti biyu muna a haka,sannan ya jinjina kai ya d'auke idonsa a kaina ya ce"je ki".

"Na gode" Na fad'a,sannan na fice na rufo masa motarsa,tsaye na yi ina kallon motar har sai da ya b'acewa gani na,na sauke ajiyar zuciya na shiga gida da fargaba.

A tsakar gida na tadda Mama,anti Na'ima,anti Halima,da kuma yayata ta Rijiyar lemo anti Maimuna,na yi sallama na k'arasa inda suke a sanyaye,da na gaishe su ma babu wanda ya amsa,ni dai na d'auki buta na shige band'aki,ina shiga na duba wayata,na dannawa Nazifi kira,bugu biyu ya d'auka ko sallama ban jira ya yi ba,na fara magana
"Nazifi me kuka yi min?"

Ya ce"ya ya? Da fatan komai ya tafi daidai,ban kira ki bane saboda kar a samu matsala".

"Wai da gaske an yi min fyad'e?" Na tambaye shi,cikin zafi-zafi.

Ya yi dariya ya ce"haba Zinatu! Zargi na kike yi?"

Na ce"ka ga kawai ka sanar min!"

Ya ce"wallahi Zinatu babu wani fyad'e da aka yi miki,kuma cikin mu babu wanda ya tab'a ki".

Na d'an ji dama-dama a raina, na ce"ta ya zan yarda da kai,bayan na ga kun canza min kaya?"

"Wallahi mace ce ta canza miki kaya,ba mu ba". Ya fad'a

Sai na yi mamaki,na ce" to wace ita? A ina kuka samo ta? Kuma jinin jikin rigar fa!?"

Ya ce"k'anwar abokina ce,kuma ta ina za mu samu jini? Zob'o ne muka zuba".

Har raina na yarda da zancen sa,ashe ya b'oye min wani babban abu,sai nan gaba za ku ji illar da suka yi min!

Na ce"to amma meyesa duka jikina yake ciwo? Kuma maganin bacci kuka bani ko?"

Ya yi dariya ya ce"ai dole jikinki ya yi ciwo,tunda ba ki tab'a shan irin k'wayar ba,ke ta ma fa sake ki da wuri".

Na ce"amma Nazifi meyasa kuka ba ni k'waya?"

Ya ce"to Zinatu gani na yi idan idonki biyu za ki iya kawo cikas wurin gudanar da aikin,ko kuma bayan mun kai ki,ki ji tsoro daga baya ki lalata aikin,amma wallahi babu abin da aka yi miki".

Na sauke ajiyar zuciya na ce"to shi ke nan,Nazifi na gode sosai, Allah ya biya ku".

"Amin matar oga J.S" Ya fad'a yana dariya. Na yi murmushi na kashe kiran.

Bayan na fito aka tisa ni a gaba,da fad'a kamar za a min ciki da hak'ora,ni dai ban wani damu da hayaniyar su ba,tunda dama na san ta zama wajibi,kuma ko dukana za a yi tunda burina zai cika ba zan damu ba.Bayan sun gama bambamin su,sai kuma suka sakko suna tambaya ta a inda na had'u da Salim har ya min fyad'e,na fad'a musu dama can saurayina ne,kuma ba halinsa bane,shi ma tsautsayi ne ya afka masa.

Anti ta katse ni da fad'in"to idan ma halinsa ne cutar y'ay'an mutane ai yanzu ya yi wanda ba zai kub'uta ba,don kuwa yanzu sati d'aya aka tsayar auren ku".

Na ji zuciyata ta motsa,sai na rasa farinciki zan ji ko akasin sa? Ni dai abu d'aya da na tsana yanzu bai wuce yanda y'an'uwana su ke yiwa Salim kallon macuci ba,na san alhaki a kaina,sai dai na kan ji dama-dama idan na tuna da anyi auren komai zai wuce...

Na tashi na shige d'aki,na kwanta,ina jiyo tattaunawar su,har aka kira la'asar.

Ina idar da sallar la'asar Baba ya shigo,ya kira ni,na zo na tsugunna kaina a k'asa,to shima dai fad'an ne babu k'akk'autawa,kuma ya tabbatar min ranar Asabar za a d'aura aurenmu da Salim, kamar yanda mahaifinsa ya tsara, ya ce min shi ma kuma ya amince don shi ne kawai mafita a gareni.

Washegari da safe Anti Maimuna yi min waya, ta ce na je gidan Ummi yanzu, na shirya na tafi ina ta fargaba.A d'akin Umma na same ta,na zauna na gaishe su suka amsa babu yabo babu fallasa,na yi shiru ina jiran ta inda za su fara tasu tijarar,jin shirun ya yi yawa na ce"Ummi ga ni".

Ta ce"ai na gan ki, me zan yi miki? Ko na kira ki ne?"

Na ce"Anti Maimuna ta ce na zo".

Ta ce"to ki kira ta ki tambayi wurin wanda za ki je,ni dai ban kira ki ba".

Na sunkuyar da kai na ce"don Allah Ummi ki yi hak'uri".

Ta ce"hak'uri ai ke ya kama Zinatu,ke da za ki zama MATAR SHIGE...".

Babu wanda ya sake yi min magana, har dai na gaji da zama na,na tashi na koma gida. Tun daga nesa na hango Habib a k'ofar gidanmu,na k'araso na yi masa kallo d'aya,ina niyyar shigewa ya zo ya tare hanya,sannan ya ce"Zinatu zan yi magana da ke".

Ban ce komai ba,na tsaya sauraron shi

Ya ce"yaushe ku ka had'u da J.S,har kuka yi nisa a soyayya ban sani ba?"

"Ba mu dad'e ba" Na ba shi amsa.

Ya ce"kuma da gaske ne ya yi miki fyad'e?"

Na ce"to kai meye matsalar ka da hakan?"

Ya ce"amma ai kin san ya kamata na sani ko?"

Na ce"saboda me?"

Ya ce"saboda ni zan aureki,kin ga kuwa ya dace na san komai game da matsalar".

Na yi shiru ina mamakin sa.

Ya d'ora da fad'in"saura fa sati biyu ya rage,zuwa gobe na ke son a buga invitation,sai ki lissafi abin da ki ke buk'ata,na baki kud'in,lokaci ya na k'urewa".

Daga haka ya tafi,ya bar ni tsaye da mamakin sa.



SALIM

Tunda ya maida su Zinatu ,gida ya dawo ya kwanta,zuciyarsa fal bak'inciki,ya san dai ko giyar wake ya sha bai isa ya kalli Abba ya ce masa ba zai auri Zinatu ba,shi a yanzu ba ma auren nata ne damuwarsa ba,yanda Junaina za ta d'auki lamarin kawai ya ke ji,ace aure nan da sati d'aya? Anya kuwa za ta yarda da shi?

Ya tashi zaune jin k'irjinsa ya yi masa nauyi,ya je ya d'akko lemo a fridge ya yi had'in k'wayoyin sa,ya fara kwankwad'a.

Ya na cikin wannan yanayin Baby ta zo ta same shi,kasa ajiye jarkar ya yi,saboda burinsa kawai ya shanye ya samu bacci ko zai samu nutsuwa.

Ta na k'araso wa,ta warce jarkar ta jefar,ta zauna ta fashe da kuka, ya dafe kansa ya na furzar da iska. Ta ce"Yaya..."

Ba ta k'arasa ba ya katse ta"wallahi Baby Zinatu sharri ta yi min,ban san komai ba".

Ta ce"na sani,kuma ko na sakan d'aya ban tab'a zarginka ba Yaya,wallahi na yarda shiri ne kawai,saboda son da take yi maka,ga shi har son ya na nema ya zama k'iyayya".

Ta d'ora da fad'in"Yaya shaye-shaye ba mafita bane,da wannan abun da ka zauna ka na sha da alwala ka yi,ka tada sallah ki ka yi ta karatun k'ur'ani,idan ma ba ka da nutsuwar karaton ka kunna ka yi ta saurara,za ka ji sauk'i a zuciyarka".

Haka ta yi ta kwantar masa da hankali har sai da ya nutsu.


HABIB
Da daddare Baba ya kira Habib,ya zo gidanmu,bayan sun gaisa Baba bai b'oye masa komai ba,ya zayyane masa halin da ake ciki,tunda a zaton sa shi bai sani ba,ya d'ora da fad'in "Habib na san ka na son Zinatu,amma a irin yanayin da ta shiga yanzu ya zama dole ka hak'ura da ita,shi wanda ya yi b'arnar shi ya dace ya aure ta,ya zauna da ita".

Habib ya ce" Baba,son da na ke yiwa Zinatu na tsakani da Allah ne,ba gangar jikinta na ke so ba,kuma idan ni d'an'uwanta bai yarda da aurenta a halin da ta shiga ba,waye zai yarda?"

Baba ya ce"ai shi mahaifin yaron ya tilasta masa auren ta,don haka babu wata sauran matsala".

"Shi ne ma babbar matsalar Baba" Habib ya fad'a.

Ya d'ora "wallahi Baba ina jin tsoron kar ayi masa tilas ya aure ta,ba da son ransa ba,kuma ya zo ya na k'untata mata daga baya.Ni fa na ce,na ji na yarda,zan aure ta a hakan kuma mu zauna lafiya ba tare da na nuna mata alamar na sani ba".

Baba ya sauke numfashi ya ce" wata sabuwa! To a gaskiya da farko na yi zaton idan ka ji haka za ka fasa aurenta,shi ya sa ma har na amincewa mahaifin yaron,amma yanzu zan sanar masa da na janye maganar,shikenan komai ya wuce,tunda itama ai da nata laifin".

Habib ya ce"to Baba na gode,Allah ya saka"

"Amin Habibu,ni ne da godiya, ka je ka cigaba da shiri" Baba ya fad'a.


Ina kwance na ji shigowar sak'o wayata,na duba da sauri ganin sak'on Habib ne

_"Zinatu son gaske nake yi miki ba na k'arya ba,don haka ba na jin wannan k'aramar matsalar za ta sa na fasa aurenki.Ki kwantar da hankalin ki,har yanzu akwai maganar aurenmu"_.

_"Habibu! Ba na son ka,kuma ba zan aure ka,Salim zan aura in sha Allah!"_ Na maida masa da amsa.


_"Wallahi sai kin aureni Zinatu,ko kuma ki yi danasani, da nadama mabayyabiya!"_

Ya maido min da amsa.
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_


BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_


*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*


Page 21


*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
10GB@===2,600
15GB@===3850
20GB@===5000
40GB@===9900
Dial *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR
Call 08066268951*



Na tashi zaune ina sake kallon sak'on da d'umbin mamaki,lallai Habib ya na son wargaza min shirina,aikuwa yanzu ne zan d'aura d'amarar zabga masa madarar rashin mutunci,don wallahi ba zai sani na yi wahalar banza akan Salim ba,na kira shi bai d'auka ba,sai sak'on da ya sake turo min me d'auke da kalamar _"I love you "_. Ban samu bacci ba a daren har sai da na samawa kaina mafitar da ta dace.

Washegari da sassafe na tafi gidan su Ummi,na samu dai yau ta kula ni,ta yi ta min nasiha a tsanake,na tambaye ta Kawu Sabi'u,ta ce ya na d'akinsa ba ya jin dad'i,ta ce jiya ma shi ya yi ta tausar Kawu Ummaru,don cewa ya yi sai ya zaneni,na yi farinciki kuwa don dama wurin sa na zo,na ce mata zan shiga na duba shi.

Ina fitowa tsakar gidan na ga Kawu Ummaru ya na shirin fita,ya zabga min wata kafirar harara,na sunkuyar da kai na gaishe shi,bai amsa ba sai k'wafa da ya yi ya fice,na tab'e baki ina bin bayansa da harara sannan na yi sallama a d'akin da Kawu Sabi'u ya ke.

Ya amsa,ya min izinin shiga,na shiga da sallama kaina a k'asa,ko fuskata ba na son ya gani,saboda nauyin zancen da na zo masa da shi, kamar amarya haka na nemi wuri na rakub'e,ina sake jawo hijjabina,na gaishe sa na yi masa ya jiki,ya amsa,na yi shiru na d'an lokaci kafin na ce" Kawu dama wata magana ce nake son yi maka"

Ya ce"to Zinatu,ina jinki".

Na ce"dama akan zancen aurenmu da Habib ne".

Ya ce"to,wani abun ne kuma ya taso? Ba an ce ya yarda zai aureki a hakan ba?"

Na ce"e,amma ni Kawu wallahi na fi son na auri shi Salim d'in".

Ya ce"meyasa?"

Na yi kalar tausayi na ce"wallahi Kawu ni ina tsoron wulak'ancin da zai biyo baya,wannan abun da ya faru k'addara ce,kuma ni a yanda nake gani Habibu zai aureni ne kawai saboda mugunta,wallahi yanzu ba so na ya ke ba...".

Sai na ga ya had'e rai,ya ce"shi ya fad'a miki yanzu ya daina son ki?" Na girgiza kai,alamar a'a.

Ya ce"to kul! Na sake jin haka daga bakinki,babban rufin asirinki shi ne ki auri Habibu,don kuwa shi ne kawai zai iya zama da ke ba tare da wata tsangwama ba,saboda irin yanda ya ke son ki,kuma ke ma sai bayan auren za ki fahimci abin da ake fad'a miki".

"Ba za ku gane ba!" Na fad'a a zuciyata.Wani takaici ya rufeni,nan take kuma wata dabarar ta fad'o min,wadda nake kyautata zaton ita ce ma babbar mafita,amma ni da na tsaya duhun kai ban aiwatar ba.

Na tashi na fita daga d'akin,ina jin takaicin su na rashin fahimtata,sallama na yi wa Ummi,na tafi,kai tsaye bakin titi na yi,na siyi sabon sim na saka a wayata,na yi gida.

Ina zuwa k'ofar gida na tadda motar Salim ta na k'ok'arin tsayawa a k'ofar gidanmu.Na ji irin abinda na ke ji idan na gan shi a y'an kwanakin nan,tsayawa na yi har ya daidaita fakin ya fito,mu ka tsaya muna kallon kallo na tsawon minti biyu kafin na k'arasa inda yake,na gaishe shi ina sunne kai,ya amsa fuska babu yabo babu fallasa,sannan ya mik'o min y'ar jakar da take hannunsa ya ce"congratulation Mrs Muhammad Salim!".

Na karb'a ina mamakin maganar sa,tun kafin na bud'e jakar ya shige mota ya bar unguwar. Na shiga gida,har ina tuntub'e saboda sauri,ina shiga d'aki na bud'e jakar,wani abu ya caki zuciyata ganin abin da yake ciki,invitation ne me kyaun gaske,d'auke da sunana da na shi,na duba date d'in na ga kwanaki biyar ya rage aurenmu.

Na fad'a katifata ina yin siririyar dariyar farinciki,can kuma na rungume katin na fara hawaye.

Na jima a haka,sannan na zabura kamar an tsikare ni,na d'auki wayata na saka sabon sim d'in,na nemo lambar mahaifiyar Habib,sai dai duk rashin kunyata sai na ji ba zan iya aiwatar da abin da na yi niyya ba,na yi shiru ina nazari,kafin na d'auki jakar invitation d'in na fice daga gidan.

Kai tsaye wurin da na san zan samu Anas na yi,na yi sa'a kuwa ya na nan,sai na ja shi gefe,bayan mun gaisa na yi tsara masa duk abin da ya faru tun daga farko har k'arshe, sannan na fad'a masa abin da na ke so ya yi min yanzu.

Tunda na fara jawabi ya ke jinjina kai,ina kai aya ya ce"lallai Zinatu ke ma fa babban kai ce".

Ya d'ora"yanzu da gaske wannan gayen ne zai aureki?"

Na yi wani murmushi na ce"har ka ga invitation ai ya raba tantama".

Ya gyad'a kai ya ce"kawo wayas!".

Na mik'a masa wayata bayan na kira lambar mahaifiyar Habibu,bugu biyu ta d'auka Anas ya k'aro k'arar wayar ta yanda har na ke iya jin muryarta

Bayan ya gaishe ta ta tambaye shi me magana,ya yi gyaran murya ya ce"abokin Habibu ne".

Ta ce"to ya aka yi? Ai Habibun ma yau bai fita ba,ba ya jin dad'i ".

Anas ya ce" kin san kuwa Zinatu ce dalilin rashin lafiyarsa?"

Ta ce"kamar ya?"

Nan fa ya kwashe k'arya da gaskiyar da muka had'a ya zayyane mata tsaf,tun kafin ya kammala take jero salati da sallallami,sannan ta yi masa godiya,ya katse kiran ya mik'o min wayar,na yi masa godiya sosai ba shi invitation d'in har da na samarin unguwa,na koma gida,zuciyata fal da farinciki.

Ashe na yi wani kuskuren ban sani ba,za ku ji nan gaba...

Ban jima da komawa ba,yaro ya shigo wai ana sallama da ni,duk a zato na Habib ne,amma ina fita na yi saranda ganin Junaina tsaye a kusa da motarta

Na ji wani kishi ya rufe ni,na had'e rai na k'arasa inda take na ce"lafiya dai ko".

"Ita ce ta kawo ni" Ta fad'a,sannan ta zuge jakarta ta fito da wani envelope ta mik'o min.

Na kalle shi a k'yamace ina tab'e baki na ce"wannan kuma fa?"

Ta ce"me ki ke jin tsoro? Tunda har ki ka samu nasarar sace zuciyar Salim ai kin cika jaruma,ba na jin akwai abin da kanki ba zai iya d'auka ba".

Na karb'a,ina yi mata kallon daidai nake da ke.

Ta na k'ok'arin shiga mota ta ce"wancen tsohon layin nawa fa ya daina tafiya,idan ki ka buk'aci gani na sai dai ki zo wurin sana'ata".

Ba ta jira cewa ta ba ta shige mota ta tafi,na shiga gida,ina auna maganganunta,to uban me zai sa na nemi ganinta? "Mahaukaciya!" Na furta ina k'ok'arin bud'ewa,don ta lik'e da gam

"Innalillahi wa inna ilaihi ra'jiun!" Na furta ina fito da duka idanuna waje,wani tashin hankali me bugar da zuciya ya rikito min,ganin abin da ya ke ciki.

Jagwab! Na zube a wurin,ina dafe k'irjina,ba dan na san ba ni da ciwon zuciya ba da zan ce yanzu tashi zai yi,to ta yaya?

Gaskiyar Junaina,dole na neme ta!.


*LAST FREE PAGES*

KADA KU MANTA ZINATU TA CE TAYI KUSKUREN RASHIN GANIN SHAYE-SHAYEN SALIM A MATSAYIN

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login