Showing 24001 words to 27000 words out of 36102 words

Chapter 9 - MATAR SHEGE HAUSA NOVEL

28 Mar 2025

3644

aikata zina ba.Mutuncina na mijina ne in sha Allah, ba ma Salim ba,duk wani namiji da ya aureni ko da ba na son shi shi kawai zan mallakawa kaina.Zan dai nemi wata hanyar ba wannan ba,zan yi shawara".

Ya ce"to,amma ki yi da wuri,kin ga lokaci ya na k'urewa"

Na ce"in sha Allah! Sannan maganar get fas,na samu guda biyu, anjima zan k'arb'o a wurin Baby".

Ya ce"yawwa! Ya yi kyau,idan na dawo da daddare sai ki taho min da shi sashenmu".

Ranar haka na wuni ina ta tunanin ta inda zan samu wannan kud'in,to ni kam indai ba kayan lefena zan siyar ba ta ina kud'in za su fito? Ga shi sai hanya-hanya ya ke min,ya k'i sanar min yanda aikin ya ke,da dubu hamsin ne ma da tsaf zan shafawa idona toka na tambayi Habib,don na tabbata zai bani,amma gaskiya dubu d'ari biyu ya yi yawa,da me zai ji? Ga duka ga tsinka jaka!

Dab da magriba na tambayi Anti zan je gida na d'akko wasu kayana,sai da ta yi min fad'a kafin ta bar ni,wai meyasa tun safe ban je ba sai da magriba? Haka dai na shirya na tafi shagon Baby,sai dai ina zuwa na tarar ba ta nan,wai lokacin tafiyarta gida ya yi.Na kirata a waya na sanar mata na zo mata nan,ta ce sai dai na k'araso gidansu tunda babu nisa,ta kwatanta min na kama hanya.

WANI KUSKURE...

Ban san zuwa na gidan su Salim a lokacin kuskure bane sai daga baya,da na je na tarar da megadi,amma bai hana ni shiga ba,ina dai tunanin Baby ta sanar masa za ta yi bak'uwa,lokacin har an shiga masallaci ana sallar magriba,a tsakar gida na tadda Baby,ta tareni da farinciki,mu ka k'arasa ciki,ta na ta murna

Mu na zama sai ga wata matashiya ta zo ta kawo min abun motsa baki,na tambayi Baby wace ita? Ta fad'a min me taya su aiki ce,sunanta Habiba.

Na sha lemon da ta kawo min,sannan mu ka gaisa da Baby na ce"yi sauri ki d'akko min,kin ga magriba ta yi".

Ta ce"Tabb! Ai ki tashi ki yi sallarki,yau sai kin ci abincin dare a gidan nan".

Na ce"rufa min asiri Baby,kunyar Ammi na ke ji wallahi".

Ta kwashe da dariya,har da rik'e ciki ta ce"wato ga surukarki ko? Aikuwa dole sai kun gaisa,don ta san da zuwanki,sallah take yi shiyasa ba ta fito ba"

Na tashi tsaye na ce"don Allah Baby ki rufa min asiri,wallahi sauri na ke yi".

Ta yi murmushi ta ce"to bari na nuna miki abun d'ebe kewa".

Kafin na yi magana ta ja hannuna,ta nufi wani d'aki da ni,ta tura k'ofar ta bud'e mu ka shiga,ni na yi zaton ma d'akinta ne,amma ina shiga sai na ji irin k'amshin da nake ji a jikin Salim ya daki hanci na,ga wani k'aton hotonsa a bangon d'akin,ya yi kyau sosai yana sanye da k'ananun kaya,a d'ayan bangon kuma na shi ne,shi da Baby,ta rirrik'e shi su na dariya,sun yi kyau sosai,kamar rak'umi da akala haka ta ja ni har kan gadonsa.

Ta ce"ga d'akin angon ki nan,na san ba za ki gaji da jiran Ammi ba ".
Na zauna a bakin gadon,kamar wata amarya,tuni na ji wata kasala ta rufeni,k'amshin sa duk ya cika d'akin,har na fara zargin ko dai ya na ciki?

Na kalli Baby na ce" k'amshin Salim duka ya cika d'akin,ko dai ya na nan?"

Ta yi dariya ta ce"turarukan shi dai su na nan,ko na ba ki d'aya?"

Na zare ido na ce"rufa min asiri,idan ya tambaye ki Wanda ya d'auka fa?"

"Sai na ce ke ce" Ta fad'a ta na d'age kafad'a.Na yi murmushi na tashi, na ce,
"Don Allah mu fita,ni dai gida zan koma".

Ta d'akko wani turare a gaban mudubi ta damk'a min a hannu ta ce" ni ce na ba ki kyauta".

Na karb'a na ce"na gode".

Da mu ka fito ba Ammi ba ta dawi falon ba,sai ta ce bari ta kira ta mu gaisa,ni dai duk sai na ji kunyar matar tun kafin na ganta,haka dai na zauna don kar Baby ta ji babu dad'i

Wayata ta fara ringing na ga Nazifi ne me kira,kamar kar na d'aga sai dai na d'aga,get fas ne ya ke tambaya ta,na ce ya ba ni mintuna ina cikin gidan

Ina gama wayar Ammi ta na k'arasowa tare da Baby,babbar mace ce y'ar gayu,fara ce tass! Don da gani ma hasken ta Salim ya yi

Ta k'araso da murumushi a fuskarta ta zauna a d'aya daga cikin kujerun

Na ji ta yi min wani kwarjini,na sakko na zauna a k'asa,kaina a duk'e na gaishe ta

"Lafiya lau Zinatu,ta shi ki koma kujerar" Ammin ta fad'a

Bam koma ba,kuma ban d'ago na kalle ta ba

Baby ta ce"Ammi sauri take yi,bari na raka ta".

Ta ce"to! Rowa za ki ma k'awar taki,ba za ta ci abinci ba?"

Na yi saurin fad'in"na k'oshi Ammi,na gode". Na tashi na yi hanyar fita,ina ta wasa da kwalbar turaren ta cikin hijjabina.

Kafin Baby ta fito daga d'akinta har na fice tsakar gida,bayan na yi wa Ammi sai da safe.Baby ta fito hannunta rik'e da leda,ta mik'o min,sannan ta ba ni get fas d'in guda biyu.

Na amsa na ce"ke! Wannan ledar ta meye?"

Ta ce"Ammi ta ba ki".

Na ce"to ki taya ni godiya,Allah ya saka".

"Ameen" Ta fad'a, ta na murmushi.Sai da ta raka ni har k'ofar gida sannan ta koma

Ina tsaye a bakin titi ina jiran adaidaita sahu,na ga hango wani mashin tun daga nesa ya dalle min fuska da hanke,ni ma shi na ke kallo don ina son sanin ko waye,amma hasken ya kashe min ido har na kasa gane shi,ya zo ya wuce ni.Na shiga adaidaita,bayan na zauna na bud'e ledar,da kud'i na fara cin karo,na yi mamaki don haka na yi saurin d'akko su,na k'irga dubu biyar ne cif,sai wata atamfa me kyau,da mayafi,sai wani saitin turare a kwali,na ji dad'in kyautar sosai,na kai kwalbar turaren Salim hancina,na shak'a har da lumshe idona,sai na ji kamar ina tare da shi ne,na jefa shi jakata tare da kud'in,na kuma fara tunanin yanda zan yi idan Anti ta tambaye ni wanda ya ba ni.

Ina shiga gida mu ka had'u da Nazifi,ya tare ni da fad'in"yawwa kin samu abun?"

Na ce"an samu" Na d'akko get fas d'in na ba shi duka,sannan na yi masa bayanin kayan da Ammi ta ba ni
Ya ce"tab! Aikuwa Anti ta na falo, don yanzu haka daga can na ke".

Na ce"yanzu me zan ce mata?"

Ya yi dariya ya ce"ai kawai ki bar min,dama yau zan je zance,kin ga sai ayi kyauta akan kyauta,ita ta ba ki,ke kin ba ni,ni kuma na bawa wata".

Na harare shi na ce"kyautar surukar tawa? Ina so ni ma"

Allah ya taimake ni hijjabi ne a jikina,na saka saitin turaren cikin jakata,na soke sauran kayan a jikina,na shiga d'akin.


Washegari da safe sai ga sak'on Salim a wayata,hannu na rawa na bud'e,duk da na san ba ya nema na sai na yi masa wani laifin,ko sallama babu a sak'on,tambaya ta kawai ya ke yi,wai da fatan dai jiya ba gidansu na je ba.


Na maida masa da amsa _"idan na je gidanku zai zama matsaka ne?_

Ina ta jiran amsa na ji shiru,na tashi na d'akko turaren da daga jiya zuwa yau na shinshina shi ya fi sau shurin masak'i.
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_


BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_


*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*


Page 16


*O'o! Fans😂,ni fa ba matar shege sunan littafin nan ba🤦🏻‍♀️Matar shige ne,(shi)na ke sakawa ba (she) ba,matar shige ba ta daraja,ni na isa na ce matar shege ba ta daraja? Shi ma shegen ai ba shi ya zab'awa kansa kasancewa a haka ba*


Yau kwanaki uku kawai suka rage min na biyan kud'in da za a yi min aikin nan,kuma har yanzu dubu goma sha uku ne a hannuna,ni da nake buk'atar dubu d'ari biyu,duk iya tunanina na kasa gano ta yanda wannan kud'i za su shigo min,har wata rama na yi a y'an kwanakin.Tun Nazifi na yi min magiyar na kawo har ya gaji ya daina yi min zancen

Kuma har yanzu Habib bai kira ni ba,bai kuma zo gidan Antin ba,bare na saka ran wani abun daga wurin sa.Kullum sai na yi sana'ar tawa,ta kiran Salim amma sam! Ba ya d'agawa.Junaina ta kira ni jiya take tambaya ta ya batun bayanan Salim d'in? Don haushi ban san lokacin da na k'unduma mata zagi ba,na dinga surfa mata ruwan ashar kamar zan ari baki,kuma na ce idan ba ta yi recoding ta kunnawa Salim ba, ba ta haifu ba! Ba ta tanka ni ba dai, ta katse kiran,na danna shegiya a blacklist na yi wurgi da wayar.


Ranar Asabar ne ya kama birthday d'in,don haka ranar Juma'ar nan duk wanda ya kalleni sai ya gane ina cikin damuwa,Anti kuwa tun kwana biyu da suka wuce ta zaunar da ni ta tambaye ni,na yi mata k'aryar babu komai,ko d'azu mun yi waya da Baby ta sake tambaya ta,na tabbatar mata da zuwa na goben.

Da yamma mu ka keb'e da Nazifi a k'ofar gida,ya kalle ni da kyau ya ce "Zinatu! Yau ce fa rana ta k'arshe da ya kamata a kammala duk wani shiri! Kuma kin ga dole sai da kud'i, wanda za mu yi aikin tare ya na da wasu uzururrukan fa".

Na yi huci me zafi,ina kalmashe hannayena a k'irji,na ma rasa abun fad'a

Ya ce"kin yi shiru".

Na yi jim! Sannan cikin sanyi na ce" Nazifi a bar shi kawai na hak'ura,idan Salim rabo na ne zai aure ni".

"Wai duk saboda kud'in ki ka hak'ura?" Ya tambaye ni

Na ce"e! Tunda na yi duk yi na,ban samu hanyar samu ba,kuma lokaci ya k'ure".

Nazifi ya yi shiru kamar me nazari,can ya jinjina kai ya ce"ina zuwa". Ya ja gefe can nesa da ni,ya ciro wayarsa a aljihu ya kara a kunne

Wallahi ban san da wanda ya yi waya ba,ba na jiyo muryarsa bare na fahimci wayar,kuma ya juya baya bare motsin bakinsa ya d'an yi min k'arin haske,wajan minti biyar ya na waya,sannan ya dawo inda nake ya na fara'a,har abun ya so bani mamaki.

Na ce"kuma murmushin na meye?"

Ya washe baki ya ce"ke na ke tayawa".

"Ni kuma?" Na tambaye shi

Ya gyara wuyan rigarsa ya ce"wanda za mu yi aikin tare ne ya ce ki bar kud'in kawai,dayake na yi masa bayanin ba ki da kud'i, shi ne ya ce tunda ya na da shi kawai zai taimake ki.Yanzu dai aiki zai yiwu gobe in sha Allah!".

Ban san dalili ba,amma sam ban ji farincikin maganar ba,duk da ina ta fatan me bani wannan kud'in,na k'agi murmushi na ce"na gode sosai Nazifi,Allah ya saka da alkairi,ka yi masa godiya".

Ya ce"kar ki damu,goben k'arfe takwas za a fara fatin nasa,ke kuma sai ki shirya k'arfe biyar na yamma,za mu zo mu tafi da ke,inda za mu fake kafin lokacin ya yi".

"Kai Nazifi! Ya fa kamata ace kun yi min bayanin aikin nan,ya za a yi min abu kuma ayi ta yi min dabaibayi,na rasa gane inda kuka dosa".

Ya yi murmushi ya ce"to me kike ci na baka na zuba? Gobe ne fa".

"Ni dai kawai ka fad'a min malam" Na yi maganar ina had'e gira.

Ya ce"to gaskiya wani zarge za mu yi wa Salim,ko dai na ce tuggu za mu had'a masa,mu yi masa d'aurin goro,yanda bai isa ya ware ba,kawai dole ya aureki".

Na yi jim sannan na ce"ina jinka,wane irin tuggu kenan? Ya za mu yi?"

"Ya za ku yi za ki ce,ke aikin ki sai mun kammala namu,mu ne masu aiki ba ke ba". Ya fad'a ya na dariya.

Na ce"duk da haka ka sanar min yanda abun zai kasance"

Ya ce"d'akin Salim za mu kai ki,a wani irin yanayin da duk wanda ya gan ki zai ce ya yi miki fyad'e..."

Na yi saurin katse shi "ban gane wani yanayi ba!".

Ya ce"za ki gane bayan komai ya tafi daidai.Idan muka yi nasarar shigar da ke,ke kuma sai ki yi k'ok'arin tabbar wa iyayensa abun gaskiya ne,ki nuna musu Salim sato ki ya yi,don ya miki fyad'e".

"Amma idan na yi masa haka anya na yi masa adalci kuwa?" Na fad'a, jikina duk ya yi sanyi

Ya ce"idan ba za ki iya ba babu dole,sai ki hak'ura,ko kuma ki samo wata hanyar da ki ke ganin za ta tilasta masa aurenki".

Na kama baki ina nazari,don gaskiya na san idan na yi wa Salim sharri,ban yi daidai ba,yanzu ko darajar Baby ai bai dace na yi hakan ba,da wane ido zan kalle ta? Kuma ko kowa ya yarda Salim zai sato ni ya min fyad'e banda Baby,tunda ta san duka tsakaninmu da shi,amma na yarda hakan ne kawai zai sa ya aureni a y'an tsakanin nan,ina jin tsoron jinkirtawa har a d'aura aurena da Habib ban ankara ba,sai dai na san ko na yi nasara ya aureni ba lallai na samu wata daraja daga gare shi ba,saboda MATAR SHIGE BA TA DARAJA!
Amma na yarda ni mace ce, don haka na saka a raina shiga gidan nashi ne babban aiki,karkato da hankalin sa gareni,da cusa masa soyayyata shan ruwa ma zai fi shi sauk'i,matuk'ar na zama matarsa.Don haka na yarda da wannan aikin na su Nazifi,amma na saka a raina zan yi ta istigfari daga baya,kuma bayan komai ya zama normal zan nemi yafiyar Salim

Idan aikin ya yiwu fa kenan!

Nan na fad'a wa Nazifi na amince,kuma goben zan shirya kamar yanda ya ce d'in,na yi masa godiya ya tafi,ni kuma na shiga gida. Ashe wani babban kuskuren na sake tafkawa! Idan banda ragon tunani irin nawa,ta ya zan yarda da zancen wai wanda zai min aikin,ya biya min kud'in? Shi da ya na da kud'in da zai yi kyautar dubu d'ari biyu,amma ya tsaya a wannan aikin wanda idan aka kacaccala kud'in bai fi ya samu hamsin ba? Na sake kuskuren da ya hanani zaman lafiya. Nan gaba dai za ku ji...


Bacci na kad'an ne a wannan daren,ina ta tunanin yanda wannan wasan mara kyau zai kasance gobe,yanzu idan abun ya b'aci ai na tabbata ni da su Nazifin duka sai mun yi zaman gidan d'an Kande.Gefe guda kuma ina tunanin irin halin da zan jefa gogan nawa a ciki,idan aikin ya yi kyau,ai zan b'ata masa suna a idon danginsa,kuma ba ni da tabbacin Baby za ta rufa min asiri a yanda take k'aunar d'an'uwanta.Sannan ina tunanin irin yanayin da iyayena za su shiga,idan suka ji wannan babban lamari,da kuma yanda Habib zai ji.Amma fa hakan ba zai sa na janye ba,saboda ina son Salim gaskiya

Na janyo turaren shi,na kafa hancina na lumshe ido,ina neman bacci.


Washegari da safe duk a sanyaye na tashi,har Anti ma sai da ta gane hakan,ta kalle ni da kyau ta ce"wai ni kam Zinatu meye damuwarki a y'an kwanakin nan? Har fa kin fara ramewa,ko tunanin auren ki ke yi?"

Haka nan na ji saukar hawaye,na share ina gyad'a mata kai alamar e tunanin ne

Ta ce"ki kwantar da hankalin ki,za ki auri namiji me hankali kamar Habib shi ne har ki ke tada hankalin ki? Maza ba su da tabbas,amma ina kyautata zaton Habib ba zai sa ki kuka ba Zinatu,ki kwantar da hankalin ki".

Na gyad'a mata kai,ina share hawaye,sannan na sanar mata da yamma zan je gidan k'awata,don mu tattauna akan bikin.

Wajan azhar ina zaune kamar a mafarki sai ga kiran Habib,kamar ma kar na d'aga,don sharenin da ya yi ya ba ni haushi,na d'aga ina sallama murya a dak'ile

Shi ma ba kamar yanda ya saba yi min wasa da kalamai masu dad'i ba,yau kai tsaye ya ke yi min magana "Zinatu zan shigo da yamma za mu yi magana".

"Ni fa bana gidanmu" Na fad'a,cikin jin haushi

Ya ce"e na sani,kuma gidan Na'imar zan zo dama".

"Ban baka dama ba" Na fad'a cikin ba shi umarni

"Dama ban nemi izininki ba ai" Ya fad'a,kuma ya datse kiran bai jira cewa ta ba.

Na bi wayar da kallon mamaki,a bayyane na ce"e lallai Habibu ka samu dama,ka dad'e ba ka zo ba kuwa!".



"Yanzu Baby ki na ganin wad'annan kayan sun yi?" Salim ya fad'a ya na kallon kayan da ta zab'a masa,na zuwa wurin birthday

Baby ta narkar da kai ta ce"oh! Bros Allah sun fi wanda ka zab'a kyau fa,ni na fi son na gan ka da manyan kaya ne".

Ya yi murmushi ya ce"to shikenan,zab'inki shi ne nawa sisi".

Ta juyar da kai ta yi shiru,alamun ta shiga damuwa da tuna wani abun.

Ya ce"to y'ar rigima,me kuma ya faru?"

Ta ce"rok'on ka zan yi alfarma Yaya".

"Zan yi miki ko ta mene" Ya fad'a.

Ta ce"don Allah kar ka sha wani kayan maye,kamar yanda ka yi waccan shekarar,ka ga wannan karon Abba ya na nan,kuma zai je wurin".

Ya kama hannunta ya ce"wannan shi ne damuwarki?"

Ta gyad'a kai. Ya ce"na yi miki alk'awarin ba zan sha komai ba in sha Allah".

"Na gode" Ta fad'a ta na ficewa daga d'akin.


K'arfe shida daidai na kammala shirina,kuma ya yi daidai da kiran wayar Nazifi,ya na jirana a waje,doguwar riga na saka ta atamfa da wadataccen mayafina,na yi kyau sosai,na zabga turaren Salim kamar zan k'arar da shi,na yiwa Anti sallama na fita.

Sai dai ina fita na ga Habib ya na k'ok'arin gyara packing, zai fito daga motarsa,na yi saurin shigewa motar abokin Nazifi da suke ciki suna jira na,amma kafin ya ja mu tafi,Habib ya yi saurin zuwa inda muke,fuska babu walwala ya ce da abokin Nazifi "kai bud'e yarinyar nan ta fito".

Na bud'e,ba tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login