Showing 30001 words to 33000 words out of 36102 words

Chapter 11 - MATAR SHEGE HAUSA NOVEL

28 Mar 2025

3646

katifar na rab'a,sanyi ya na ratsa sassan jikina

Ba a jima ba Babyn ta dawo,da sallama na amsa ina son ganin cikin idonta,amma ba ta bani dama ba,ta ajiye min riga da sket na atamfa,ta juya ta na shirin fita na ce"zan samu hijjabi don Allah? "

Ba ta juyo ba ta fice kamar ba ta ji ni ba,amma kuma ba ta dad'e ba ta dawo ta jefo min hijjabin ta koma

Na tashi na shiga band'akin cikin d'akin,don dama fitsari nake ji sosai ya d'aure min mara.Sai dai na yi mamakin rashin ganin jini a jikina,don a iya rigar kawai ya tsaya,na jima a tsugunne ina son na gano halin da nake ciki,da gaske anyi min fyad'e ko a'a? Amma na kasa ganewa,don haka na hak'ura na tashi na yi wankan tsarki,tunda ban gama yarda da kaina ba,na wanke farar rigar,ko nace na d'auraye ta tunda ban ga clean ba,haka dai na cukuikuye ta na barta a band'akin,na fito na saka kayan da ta kawo min na saka hijjabin na tada sallah,margiba da isha'i na yi don su ake bi na,haka na zauna na yi ta istigfari tun kafin na san yanda za ta kaya goben.Wata yunwa ma nake ji sosai,amma sanin a yanzu ba ni da gatan samun abinci na kwanta a haka na lullab'a da hijjabi,tuni bacci ya kwashe ni.

Washegari da na farka har an idar da sallar asuba,gari ya fara haske,kuma a hakan ma fa baccin bai isheni ba,na tashi na yi sallah na kwanta a kafet d'in ina jin yanda babban yatsana na k'afa yake zugi,wani baccin ya sake kwasa ta.

"Zinatu,Zinatu" Na ji muryar Baby cikin baccin nawa

Na farka na ganta tsaye a bakin k'ofa. "Ki fito inji Abba" Ta fad'a, sannan ta fice

Na tashi,na saka hijjabin na fito cikin jin kunya,kaina a k'asa,a falo na tadda su duka har da Salim d'in,na saci kallonsa ta gefen ido,sanye ya ke da bak'ar shadda da kofin shayi a hannunsa,ya na juyawa da cokali,sai na ga ya yi min kyau sosai.

Na k'arasa na duk'a na gaida Abba,ya amsa ya na yi min ya jiki,ban amsa ba saboda kunya,na juya wurin Ammi na gaisheta,ita kam ba ta ma nuna ta san da halitta ta a wurin ba,na juyo kan gogan nawa na ga ni ya ke kallo, na ce "ina kwana?"

"Lafiya lau" Ya amsa min,ban yi zato ba. Na koma gefe na rakub'e kamar yajin k'osai

Habiba y'ar aikin gidan ta shigo falo ta kalleni ta ce"ki zo ki karya".

Na tashi na bi bayanta da d'an d'ingishi,don har na fara zaton na yi targad'e ne a jefoni da ya yi,daga cikin bahon wanka.A nan dinning d'in na tadda Baby ta na karyawa,na kalle ta na ga hankalinta na kan farantin dankalin dake gabanta

"Baby,an tashi lafiya?" Na fad'a ina k'irk'iro murmushi.

Sai ta yi kamar ba ta ji ba, ta tashi ta bar wurin.Cikin d'ari-d'ari na had'a shayi,don ba dan ina jin yunwa ba ma ba zan ci komai ba,na zuba dankalin kad'an na karya,sai na yi zama na a wurin,don duka kunyar su nake ji wallahi, na dinga tunanin halin da gidanmu yake ciki a yanzu,watak'il ana can ana ta nema na,na fara fargabar kada Habib ya ji labari,tunda shi ne kawai ya ga lokacin da aka d'aukeni a mota,kuma babbar matsalar ma ya ga wanda ya d'auke ni d'in.

Ina nan zaune Baby ta dawo cikin shirinta,har da hijjabi,ta kalle ni ta ce"ki taso muje asibiti.Kuma ki sani ko kin auri Salim ba za ki tab'a samun wani farincikin rayuwar aure ba,saboda Ammi ba za ta tab'a k'aunarki ba,ta san tsakaninku da Salim,tun ranar da kuka gaisa a gidan nan,na bata labarinki duka.Sannan ko da kin yi nasarar shigowa dangin mu,za ki yi rayuwa ne ke da mijinki kawai,saboda har ni ma ba na tare da ke!". Ba ta jira cewata ba ta bar wurin

Ba ni da zab'in da ya wuce na bi bayanta,don haka na tashi jikina duk ya yi sanyi,na nufi falon,har Abba ya so bani tausayi,yanda yake kallo na cikin kulawa da tausayi a idonsa,na fita kamar yanda na ga sun yi.

Muka shiga mota,Salim ne a mazaunin direba,Abba a gaba,sai ni da Baby muka shiga baya,sai da na ga an tada motar na gane banda Ammi za a je.

"Ina ne gidanku?" Abba ya tambaye ni.

"Hotoro ne" Na fad'a a sanyaye.

"Wace unguwa?" Ya sake tambaya ta.

"Abba na fa san gidan" Ya fad'a da murya ciki-ciki.

Abba ya ce"to ka ga Salim,in har ka san da gaske ka yaudari yarinyar nan ka fad'a min,ba sai mun je asibiti mun tonawa kanmu asiri ba".

Salim ya ce"wallahi Abba gaskiya na fad'a maka,ni ban yi mata komai ba".

"To amma ta ya ka san gidansu?" Ya tambaye shi.

Salim ya yi shiru,kamar bai ji shi ba.Motar ta yi shiru,har muka k'arasa k'ofar gidan Anti Na'ima,bugun zuciyata fa sai ya k'ara tsananta,Abba ya ce na shiga na yi masa sallama da Babana,na yi masa bayanin nan d'in gidan Yayata ne,sai ya ce na kira yayar tawa,ko mijinta.

Na fito daga motar jiki a sanyaye na shiga gidan,ina shiga na tadda Anti a falo,ta tashi tsaye ta ce"Zinatu a ina ki ka kwana? Hankalinmu duka ya tashi muna ta nemanki,kuma kin bar wayarki a gida!"

"Ina wayar tawa?" Na tambaye ta.

Ta ce"ban sani ba! Na ce a ina ki ka kwana?"

Na sunkuyar da kai ban bata amsa ba na ce"ana sallama da ke a waje".

Cikin mamaki ta ce"sallama kuma? Waye?"

"Mahaifin Salim ne" Na bata amsa.

Ta ce"waye kuma Salim?"

"Anti suna jiranki,ba fa k'ananun mutane bane" Na fad'a cikin k'osawa da tambayoyin ta.

Sai ta d'akko hijjabi ta saka ta ce na ce su shigo ciki kawai. Su ka shigo,amma banda Baby da ta zauna a motar,bayan sun gaisa Abba ya tsara mata yanda komai ya faru,sannan ya shaida mata yanzu wani nasu ya shirya aje asibitin tare.

Anti Na'ima ta dinga jera salati babu k'akk'autawa,sannan ta fara k'walla ta ce"wallahi Alhaji aurenta saura sati biyu,ashe ita yarinyar nan shirin ta da ban!"

Abba ya jinjina kai ya ce"duk abar maganar,aje asibitin kawai".

Anti ta ce ta na zuwa,ta shiga d'aki.Ba ta jima ba ta fito,ta mik'o min wayata,tana min wata kafirar harara, mu ka tafi. Hanyar asibitin Aminu Kano muka d'auka,Anti ta ce gwara aje Nasarawa akwai likitoci mata ta wannan fannin,Salim ya juya kan motar muka yi Nasarawa,ni dai gabana sai fad'uwa ya ke yi,shi kuwa Salim ban san abin da yake ransa ba.

Muka shiga asibitin,Anti ta ce ta san b'angaren da ya kamata mu je,kamar an san da zuwanmu mu na zuwa aka nuna mana inda za mu shiga,Anti ce ta yiwa wata nurse bayani a tak'aice,sai aka yankan min kati,babu jimawa aka nuna min d'akin da zan shiga a dubani.

K'irjina fa ya tsananta bugu,na dinga taku d'aya bayan d'aya kamar wahainiya,fargaba fal raina

Da na shiga d'akin kusan fad'uwa na yi,saboda wani tuntub'en bazata da na yi,sakamakon ganin Habib sanye cikin uniform d'insa na asibiti,ya hard'e hannu a k'irji,fuskar nan babu walwala,shi kad'ai ne a d'akin,da alama dai shi ne likitan da zai duba ni.
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_


BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_


*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*


Page 19


*Ni fa na san so,kuma na yarda k'addara ne.Don haka ina team d'in Zinatu,idan kuna zaginta Allah zan tafi hutun typing na sati biyu,kafin nan zuciyarku ta yi sanyi,sai mu d'ora😉*



Habib ya yi min wani firgitaccen kallo,da alama dai bai tsammaci gani na ba.Ni kuwa kusan mutuwar tsaye na yi,ganin wannan tonon sililin da ya tunkaro ni,ko kuma na ce na jefa kaina a ciki,amma sosai na yi mamakin ganin shi a b'angaren,don a iya sani na Habib likitan ido ne,to me zai kawo shi nan b'angaren? Ban gama raba d'ayan biyu ba na ji muryarsa

"Zinatu! Kar dai ki fad'a min ke ce wadda za a duba yanzu!" Ya yi maganar ya na k'ank'ance ido da alamun b'acin rai.

Na ji wata kunyarsa ta rufto min,na kasa magana,kawai sai na fara zub da hawaye ba tare da na shiya ba. Ya yi huci me zafi ya nemi kujera ya zauna,sannan ya d'akko wayarsa a aljihu ya yi danne-danne ya kara a kunne

Na yi shiru ina sauraron wayar tashi,ban san da wanda yake wayar ba,na dai ji ya na cewa"ka ga doctor, ka k'arasa a tsanake,ni ma na ari office d'in naka na y'an mintuna,idan na kammala zan kira ka".

Ya ajiye wayar ya kalle ni fuskar nan murtuk kamar ba shi ba ya ce"maganar fyad'en da ake tantama a kansa,ina so ki fad'a min gaskiya anyi miki,ko ba a yi miki ba?"

Na yi shiru,kaina a k'asa.Ya buga teburin da k'arfi ya ce"ke! Ina tamabayarki ne fa as your doctor, ba Habibun da kika sani ba,ki d'auka ban ma tab'a ganin ki ba sai yau,saboda haka idan kin shirya ganin likita sai ki bud'e bakinki,idan ba ki shirya ba ki fice min daga office!"

Na d'ago na kalle shi, sai na ga tabbas wannan ba Habib d'ina bane,da gaske ya ke yau a gaban doctor Habib nake,sai na saka a raina ban san shi ba d'in,don haka na ce"ni ma ban sani ba".

"Kamar ya ba ki sani ba? Shekarunki nawa?" Ya tambaye ni,idonsa a kaina

"Ashirin" Na ba shi amsa.

Ya ce"ko y'ar shekara biyar aka yi mata fyad'e dole ta sani,bare ke da kin isa zaman aure! Ki na kokwanton anyi miki fyad'e,ta ya ki ka tsaida wanda kike zargi?"

Na lura dai da gaske Habib ya ke son k'ure ni,gwara ni ma na dawo masa Zinatu,don ya na shirin canza min suna da wata banzar barazanar sa,wai shi likita!

Na had'e rai na gyara zama na ce"kafin na shigo wurin nan ce min aka yi likita zai duba ni,ba lauya ba,kuma a zatona da doctor Habib na ke magana,ba barrister Habib ba".

"E hakane,amma wannan tambayar duka cikin aikina ne". Ya fad'a ya na had'e gira.

Na ce"tunda ka ga har sun kawo ni nan,ai ka san an zo gab'ar raba gardama kenan.Idan za ka duba ni bismillah kawai". Na k'arasa maganar zuciyata na bugu,don ina fargaba da takaicin wani gardi ya ga tsaraicina,musamman ma Habib d'in,wannan rashin darajar ina zan kai shi? Amma a fili ba za ka tab'a kawo haka nake tunani a raina ba.

Ya yi shiru ya na kallo na,tsawon sakanni,sannan ya jinjina kai ya ce" bismillah! Ga gado can je ki hau".

Gabana ya fad'i,duk da har yanzu zuciyata ba ta amince da zai iya duba ni d'in ba,ban nuna ba na dake na tashi na yi inda gadon ya ke,sai dai zama na yi ba kwanciya ba

Na d'an jima da zama,har na fara k'aguwa sannan ya k'araso wurin,ya janyo kujera ya zauna ya fuskance ni,ni kuma na sunkuyar da kai, don ba na son ya kalli k'wayar idona.

Tun kafin ya fara magana wani likita ya shigo,wanda na ke kyautata zaton shi ne me office d'in.

"Doctor ka kammala?" Ya tambaye shi,idonsa a kaina

Habib ya yi wani huci ya dafe kansa da duka hannayensa biyu.

Likitan ya janyo wata kujerar ya zauna a kusa da shi,ya ce"na fa kasa fahimta,a iya sani na ba ka harka da mata,wacece wannan?"

Kamar ba zai ba shi amsa ba,sai can ya ce"ita ce Zinatu".

Ko idona ne oho! Sai na ga kamar lokaci d'aya yanayin likitan ya canza,zuwa ga b'acin rai,ya yi min wani kallon da na kasa fassra shi a lokacin,sai daga baya,sannan ya kalli Habib ya ce"to me ya kawo ta nan d'in?"

Habib ya tashi ya je kan teburin ya d'akko masa takarda ya ba shi.Ko me aka rubuta a takarda tawa oho! Na dai ga ya kalle ni da sauri,kuma da alamun b'acin rai

Ya kalli Habib ya ce"yanzu ka duba ta d'in?"

Ya girgiza masa kai alamar a'a.Sai ya ce"ok,ka je kawai zan saita komai".

Habib ya yi masa wani kallo me wuyar fassrawa ya ce"kai! Matar da zan aura d'in za ka duba!?"

"Ai cikin aikina ne" Ya ba shi amsa ya na d'age kafad'a.

Habib ya kalle ni ya ce"ke tashi ki fita! Sai dai ku canza wani asibitin wallahi,ta ya wanda na sani zai duba min mata?"

Likitan ya dafa kafad'arsa ya ce"ok! Na fahimce ka Habib,amma ka sani ko wani asibitin aka kai ta ba ka da tabbacin mace ce za ta duba ta.Na yi maka alk'awarin ba zan duba ta ba,zan lallab'a ta ta sanar da ni gaskiya".

Habib ya yi shiru kamar me nazari. "Ka yarda da ni abokina,ka je d'in".

Habib ya kalle ni,sannan ya maida facemask d'insa ya fice.Na sauke ajiyar zuciya a b'oye,har yanzu zaune nake a bakin gadon

Likitan ya kalle ni da kyau ya ce" ke anyi miki fyd'en ko ba a miki ba?"

"Ni ma na kasa tantancewa fa" Na fad'a, ina juyar da kai gefe

Sai ya tab'e baki ya ce"yanzu ya kike jin jikinki?"

Na ce"ya na yi min ciwo kad'an,sai bacci da nake ji".

"Tun yaushe abun ya faru?"

"Jiya da daddare" Na ba shi amsa.

"Waye wanda ake zargi" Ya tambaye ni.

"Wani ne" Na fad'a

Ya ce"ko Salim da na gani a waje?"

"Shi" Na fad'a a tak'aice.

Ya ce"ok! To yanzu zan canza miki d'aki,sai na saka miki drip,idan ya k'are za a sallame ki".

Ina shirin yin magana ya tashi,ya na cewa na biyo shi.

Ba ni da zab'in da ya wuce bin umarnin shi.Zazzaune muka tadda su Abba,da alama har sun k'osa da jira,na tsaya daga d'an nesa,yayinda likitan ya k'arasa wurin su,Abba ya tashi da sauri ya mik'a mishi hannu suka gaisa ya na tambayar sa ya ake ciki?

Likitan ya kalli Salim sannan ya maida duban shi wurin Abban ya ce"fyad'en dai ya tabbata,sai dai Allah ya rufa asiri".

"Ban yarda ba! Wallahi akwai k'ulla-k'ulla a wannan abun!" Muryar Salim ta karad'e kunnuwanmu.

Gabana ya fad'i. Likitan cikin nuna rashin damuwa ya ce"me ye ya ba ka tabbacin hakan?"

Salim ya ce"duba yarinya ba sai likitoci biyu ba,likitan farko da ya dace ya duba ta ya jima a ciki,sannan ya fito kuma ina kallon shi,sam ban yarda da yanayinsa ba,kai ma kuma da ka shiga ka jima a ciki,to meye dalilin dad'ewarku a duba mutum d'aya kawai?"

Likitan ya kalle shi na y'an sakanni,har na fara fargaba sai ji na yi ya ce"amma dai ina tunanin ka san irin b'arnar da ka yi mata ko?"

"Ban gane ba!" Salim ya fad'a a hasale.

Likitan ya ce"likitan farko da ka ga ya fita,shi ne ya fara duba ta,kuma ya ga b'arnar da ka yi mata,shi yasa ya kira ni saboda na fi shi k'warewa a fannin d'inki,yanzu dai an gama gyarata,za mu saka mata ruwa,idan ya k'are kuma sai a sallame ta.Akwai magungunan da zan rubuta".

"Dank'ari!" Na fad'a a zuciyata.Amma lallai wannan likitan idan ya shiga wasan kwaikawayo zai samu abinci sosai, na ji wani farinciki ya rufe ni,sai dai fa na yi mamakin abin da ya sa shi wannan k'aryar har haka,kuma na sa a raina ba sai na ji dalili ba,ko ma menene ni kam ya taimake ni.

Salim ya ce"kai ka ga! Kada ka sake danganta ni da wannan,can za ta nemi wanda ya yi mata b'arna ba...".

"Kai!" Abba ya daka masa tsawa,Salim ya koma ya zauna fuskar nan kamar bai tab'a murmushi ba.

Abba ya ja likitan gefe,ban san dai me suka tattauna ba,ni kuma wata nurse ta zo ta rik'e hannuna muka shiga wani d'akin. Aka bani gado,ta saka min drip,ta ba ni magani na sha,har da lulllub'e ni da bargo,aikuwa bacci ya ce min mu je.

Ba ni na tashi ba sai bayan azhar,na duba wayata dake kusa da ni,na ga k'arfe biyu da minti ashirin,na tashi zaune,yanzu kam na ji dad'in jikina sosai,babu wani sauran bacci a idona,na tashi na shiga band'aki na d'auro alwala.

Ina fitowa na tadda Mama Saude a d'akin,ta dinga kallon k'afata kamar wadda aka ba ta aikin k'irga taku na,na san dai tsabar gulma ce take cinta,na had'e rai na k'araso na gaishe ta.

Ba ta amsa ba ta ce"oh! Zinatu ashe haka abu ya faru?"

"Uhm!" Kawai na ce,na d'auki d'ankwalina na shimfid'a a k'asa,na tada sallah

"To kin yi wankan tsarki ne?" Na ji tambayar tata a bazata.

Na juyo na kalle ta na sakan uku,sannan na tada sallata.Kafin na idar ta fita ta shigo da kwando me d'auke da kuloli,ta had'a shayi kofi biyu, ta ja d'aya gabanta,ta mik'o min d'aya,haka abincin ma ta zuba faranti biyu, ta gyara zama ta fara antayawa ba tare da ta min magana ba.

"Mama a ina aka samu wannan abincin?" Na tambaye ta,ina d'aukar kofin shayin

Ta ce"daga gidansu yaron aka kawo.Ai ya na nan ma,ya na jira a sallame ki, ya maida mu gida,wallahi yaro kyakkyawa me hankali da kirki,ni na san k'addara ce kawai kifta".

Na ce"Baba da Ummi sun sani?"

Ta na yagar naman kaza ta ce"yo kema dai zancen ki ke so,idan ba su sani ba ni taya zan ji har na zo jinya? Ai har da mahaifin yaron ma baban naki sun zauna,ban dai ji abin da suka tattauna ba tukun,sai mun koma gida".

"Ummi ta zo?" Na tambaye ta.

Sai ta tab'e baki ta ce"ta zo ina? A gabana Na'ima ta kira ta ta sanar mata,amma wallahi bud'ar bakin matar nan,sai cewa ta yi Allah ya ba ki lafiya.To dama waye dolenki idan ba ni ba? Wallahi na san na fi mahaifiyarki shiga tashin hankali,ke ni yanzu fargabata d'aya ,kar Habibu ya ji labari".

Ni dai na yi shiru ban sake tanka mata ba,ta na ta surutun ta,ni kuwa tunanin yanda za mu yi da mahaifana kawai na ke yi. So na ke ma ta bani space na samu damar kiran Nazifi a waya,amma ta zaune min.

Mu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login