Showing 27001 words to 30000 words out of 36102 words

Chapter 10 - MATAR SHEGE HAUSA NOVEL

28 Mar 2025

3650

da na fito ba na ce"unguwa za su kai ni".

Ya ce"e,ki fito ni na kai ki".

"A'a, na gode" Na fad'a ina shirin rufe k'ofar.

Ya rik'e murfin ya ce"to ki zo,ina son magana da ke ko ta minti biyar ce".

"Ba zan samu dama ba gaskiya, idan na dawo sai ka dawo mu yi". Na fad'a ina rufe murfin motar,su ka ja mu ka tafi,mu ka bar Habib tsaye kamar an dasa shi.


Sharad'an mu ka dosa,can wajejen su Salim d'in,don kuwa gidan da na ga sun faka motar babu nisa da gidansu Salim.

Mu ka fito muka shiga,amma banda abokin Nazifi,na dinga bin matsakaicin gidan da kallo, d'akuna uku ne a ciki,sai band'aki,da wani wuri da nake kyautata zaton kitchen ne,ya shiga wani d'aki ya ce na shigo, na shiga da sallama

Babu komai a ciki sai katifa da kayan kallo,da wasu akwatunan kaya a gefe,da alama dai d'akin saurayi ne.Na rab'a gefe na zauna duk a tsarge nake

Muna nan zaune da Nazifi ya na yi min bayanin yanda aikin zai kasance,sai ga abokin nashi da na ji ya na ce masa Sabi'u ya dawo rik'e da ledoji.

Ya zube su a gabana,ya kalli Nazifi ya ce"to ta so mu wuce ko?"

Nazifi ya kalle ni ya ce"to Zinatu,bari mu je,anjima za mu dawo d'aukarki,kafin nan an fara fatin,ga abinci nan ko za ki ji yunwa".

Na ce "to,sai anjima".

Bayan sun fita na bud'e ledar,na ga abinci ne a takeaway, sai lemuka har kala uku, ba na jin yunwa amma sai na ji sha'awar shan lemon

Na bud'e d'aya,na sha kusan rabi,na matsar gefe,na d'akko wayata ina kallon hotunan Salim da sak'e-sak'e,ko minti goma sha biyar ban yi ba,na fara jin bacci-bacci,abu kamar wasa tun ina daddaurewa har dai abun ya rinjaye ni,na kwanta a nan k'asa,na yi fulo da gefen katifa tuni wani bacci me shegen dad'i ya sure ni muka tafi...
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_


BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_


*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*


Page 17



Saukar ruwa me sanyi da na ji a fuskata shi ne ya farkar dani daga nannauyen baccin da na yi,na farka a firgice ina k'ok'arin bud'e idanuna da nake jinsu kamar ba nawa ba,wani irin yanayi nake jin jikina kamar dai wata ce aka saka zuciya da tunanina a jikinta

"Ke! Uban waye ya kawo ki d'akina!?"

Duk da ban gama wartsakewa ba,amma ba na jin akwai halin da zan shiga wanda zai mantar da ni muryar Salim,na bud'e idona sosai na kalle shi,sai na ga kamar ba Salim d'ina bane,don kuwa gani na yi kamar an canza idanunsa,ta idonsa kawai za ka fahimci ya na cikin tashin hankali mara misali.Lokaci d'aya na fara tunanin ta yanda su Nazifi suka kawo ni d'akin Salim,a iya sani na bacci na kwanta a d'akin da suka ajiye ni,kuma ban farka ba sai yanzu,kenan hakan ya na nufin cak suka d'auke ni? Kuma har ta ya ma suka shigo da ni nan d'in wani bai gan su ba?

Ban gama tunanin ba na ji muryarsa cikin hargagi,kamar mak'ogoronsa zai fice "me ya kawo ki nan? Kuma waye ya miki haka!?" Ya yi maganar ya na nuni da kayan jikina

Sai na kai duba ga jikina,gabana ya yi wata mummunar fad'uwa ganin alamun jini a farin yadin jikina,na doguwar rigar da ta kwanta a jikina,kasancewar ta roba.Nan take na tuna ni fa atamfa na saka daga gida,kuma duka ma ba ni da irin rigar nan,hankalina ya yi matuk'ar tashi fiye da yanda za ku yi tsammani,k'irjina ya dinga lugude kamar ana daka a ciki

Sai da na maimaita innalillahi wa inna ilaihiraji'un kusan sau biyar sannan Salim ya sake katse ni,ta hanyar buga min wata gigitacciyar tsawa ya ce"ke Zinatu! Kar fa ki raina min hankali,tambayarki nake yi waye ya kawo ki nan!?"

Da k'yar na bud'e baki na ce"don Allah waye ya yi min haka? Allah yasa kai ne ka min fyad'e ba su ba,kai ne?" Na fashe da kuka.

Sai dai na yi saurin dakatar da kukan jin ana buga k'ofar d'akinsa da k'arfi.Ya zaro ido had'i da d'ora hannunsa a kai,alamar ya shiga tashin hankali,murya k'asa-k'asa kamar zai yi kuka ya ce"na shiga uku! Zinatu me na yi miki za ki yi min haka?"

Ni ma hawayen nake yi,amma ba na tausayin shi ko nadamar abin da na yi masa ba,ni kukan nawa na tunanin wanda ya yi min fyad'e ne

Aka sake buga k'ofar,wannan karon har da kiran sunan shi,muryar namiji ne,ina dai zargin mahaifinshi ne.Ya zo da sauri ya ja hannuna ya na fad'in "don Allah tashi ki b'uya,ki rufa min asiri kar wani ya ganki,wallahi ba zan iya wanke kaina ba,tashi don Allah!" Ya kai k'arshen maganar ya na k'ok'arin d'agani

Sai ya ba ni tausayi don haka na fara tunanin janye wannan mummunan k'udurin nawa,na yi masa sharrin fyad'e, na yunk'ura da nufin tashi,amma me? Sai na ji na kasa tashi,jikina kamar ba nawa ba nake ji,aka sake buga k'ofar ana kiran sunan shi,ban yi aune ba sai gani na yi ya sungume ni cak ya yi wata k'ofa da ni,band'aki ne kamar yanda na zata,cikin hanzari ya shiga ya wurga ni cikin bahon wanka,har k'uguna ya bugu,ya rufe k'ofar ya fita

Ban san yanda suka yi da me buga k'ofar ba,can dai na ga ya sake dawowa,har yanzu ba ya cikin nutsuwarsa,sai zare ido ya ke ya na huci

"Zinatu Allah ya isa tsakani na dake! Me na yi miki wai? Ta ya kika zo d'akina?" Ya fad'a ya na d'ora duka hannuwansa a ka.

Tausayin shi ya kama ni sosai,na yunk'ura na tashi zaune na fashe da kuka sosai kamar ya min umarni da kukan.Sai ya zaro duka idanunsa kamar za su fito ya ce"kuuut! Wai har damar kuka ma ki ka samu? Ni da zan yi kuka ban yi ba,sai ke? Zo ki fice daga gidan nan tun ban yi miki dukan mutuwa ba!". Ya kai k'arshen maganar muryarsa na rawa kuma cikin fad'a.

"Ina wayata?" Na tambaye shi.

"Ta na gidan ubanki!" Ya fad'a,sannan ya fusgoni daga cikin bahon ya warb'ar da ni a k'asa,k'afata ta bugu har na ji kamar babban yatsana ya karye

Da k'yar na tashi tsaye don fita na tafi gidan kamar yanda ya ce,amma da k'yar na samu na iya taku uku,wani irin juyi na ga garin ya na yi min,haka na yi ta layi ina dafa bango a k'ok'arina na fita daga band'akin,kallo d'aya dai za ka min ka san ba na cikin hayyaci na,ina fitowa daga band'akin na zube a k'ofar cikin mutuwar jiki,don k'arfina ya k'are duka,ba na jin zan iya wani takun

Salim ya zube shi ma a inda na fad'i murya na rawa ya fara jijjigani ya na fad'in"na shiga uku! Zinatu ki rufa min asiri kar ki mutu a d'akina don Allah!"

Ya tashi a guje ya d'akko robar ruwa ya watsa min,don shi a zaton sa suma na yi,na bud'e idona da suka yi jawur na ce"Salim... Don Allah Salim ka ji?"

"Uban me zan ji? Me za ki fad'a min? Ai har gani ma na yi ba ji ba,wannan shi ne sakamakon son da kika ce ki na yi min? Allah ya isa!"

Kawai sai ya jingina da bango ya fara share hawaye.Na daddafa na tashi da k'yar,idona ya na rufewa saboda har yanzu da sauran bacci a ciki na fara takawa a hankali nima ina share hawayen,ni dai hawayen tausayin kaina da nadama nake yi, shi kuma ban san ko na meye ba.

Har na kai bakin k'ofa na ji ya daka min tsawa ya ce"dawo!".

A maimakon na dawo sai na zauna a bakin k'ofar,idona ya na lumshewa,ya tashi ya fita daga d'akin.

Babu wani zafi ko zugi da nake ji daga k'asana,wanda zai tabbatar min da fyad'en da aka yi min,amma ko ban ji zafi ba dole na yarda tunda ga jini nan ya zama shaida,da kuma canza min kayan da aka yi,ni yanzu babbar damuwata na ga wayata kawai,don na kira Nazifi na ji wanda ya yi min fyad'e da kuma dalilinsa na yi d'in.

Bai jima ba ya dawo d'akin,ya bud'e sif ya d'akko kayan shi,ya buga min harara ya shige band'aki,ya fito sanye da k'ananun kaya ba na d'azu ba,ya zo ya tsugunna a gabana har ina jin hucin numfashin sa,ya ce"Zinatu! Don girman Allah waye ya kawo ki d'akina?"

Na kalli k'wayar idonsa da na ke karantar damuwa k'arara na ce"son ka ne Salim! Wallahi son ka ne k'addarata...".

"Ni ma kin zama k'addarata Zinatu,kuma ban yafe miki ba" Ya katseni

Na share hawaye ina lumshe ido,wata sabuwar k'aunar shi na dagargazar zuciyata wallahi burina kawai na ganni a kwance ina bacci,da ya san yanda nake ji a halin yanzu da tuni ya rungumeni na yi bacci a jikinsa.

"Da ki ka zo d'akin nan kin d'auki wata k'wayar kin sha ne?" Ya tambaye ni,ya na nuna min lokarsa

Na girgiza masa kai,alamar ban sha ba. Ya ce "ok dama can ki na shaye-shaye kenan?"

Na yi banza da shi

"Ki tashi na kai ki gidanku,gobe zan zo mu yi magana". Ya fad'a ya na d'akko mukullin mota.

Na tashi da k'yar, ina tangad'i idona na lumshewa,amma duk iya k'ok'arina sai na kasa tafiya,saboda tsabar jirin da nake ji

"Wuce mana!" Ya daka min tsawa

Ina d'aga k'afata na tafi luuu,na fad'a kanshi gabad'aya

"Bura'uba!" Ya fad'a da k'arfi,sannan ya hankad'e ni,Allah ya taimake ni a gado na fad'a, sai kuwa na gyara kwanciyata na lumshe ido.

"Yau na shiga uku ni Muhammad!" Na ji muryarsa sama-sama

Babu zato na ji ya shek'a min ruwa a jikina,Ina bud'e ido na gan shi tsaye da bokiti ya na huci,na tashi a firgice na ce"ka yi hak'uri don Allah, zo ka raka ni gida,ko kuma ka bar ni,na kwana anan wallahi gobe zan tafi".

Ya dafe goshinsa ya na wani irin huci.Can dai kamar wanda aka yiwa umarni kawai ya zo ya sungume ni,ya sab'a a kafad'a,dama ba wata k'iba ce da ni ba,bare na yi nauyi,ya yi waje da ni.Don dole na wartsake saboda wani sanyi da nake ji,sakamakon rigar jikina da ta jik'e jak'ab,sad'af-sad'af haka ya dinga tafiya da ni a kafad'a,ya na jera min Allah ya isa,har mu ka kusa fita daga falon.

"Salim!" Ya tsaya cak! Jin muryar mahaifinsa.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ya furta a sanyaye,sannan ya dawo ya ajiye ni a kujera ya durk'usa,ya saka gwuiwowinsa a k'asa. Taku d'aya bayan d'aya mutumin ya k'araso har gaban shi, murya a sanyaye ya ce"Salim yaushe ka fara satar mutane a cikin gidana?"

Salim ya runtse ido bai yi magana ba. Ya daka masa tsawar da ni kaina sai da na firgita na wartsake sosai,na gyara zamana, ya ce "da kai na ke magana!"

Salim ma ya firgita ya ce"na rantse da Allah Abba..."

Bai k'arasa ba ya katse shi da fad'in"rantsuwa na tambaye ka?"

Ya sunkuyar da kai ya ce"wallahi Abba ban san wanda ya kawo yarinyar nan d'akina ba,ai ka ga dai tare muka shigo gidan da ku,ina zuwa na tadda ita a kwance,na rantse da Allah Abba".

Abba ya ce"to to to, wato aljanu ne su ka kawo ta ko? Idan gaskiya ne ai tun lokacin da ka ganta za ka zo a guje ka sanar mana,ba ka yi tunanin ko aljana bace yanzu da ka kinkime ta? To ina ma za ka kai ta da ban fito ba?"

Kafin Salim ya kai ga magana Ammi ta fito ta na fad'in "wai hayaniyar me nake ji cikin dare?"

Sai ta zaro ido ta na kallona ta ce"wacece wannan?"

"Amsar wanda ya kawo ta na ke jira!" Abba ya fad'a, ya na zama a kujera

Ammi ta kalle ni da kyau,sannan ta dafe k'irji ta ce"mun shiga uku! Wannan ai k'awar Baby ce,Nuratu ko?"

"A'a Zinatu,ita ce,k'awar Baby ce" Cewar Salim da rawar murya.

Abba ya ce"zance ya fara fitowa,ashe har sunanta ka sani?"

Ammi ta koma da sauri,sai ga ta sun fito tare da Baby,ta na murtsuke ido,alamar ta fara bacci.Turus! Ta ja ta tsaya,ba tare da ta k'araso inda muke ba, ta nuna ni da yatsa ta na fad'in "Zi zinatu?"

Na runtse idona hawaye suka zubo,sannan na sunkuyar da kai

"Tambayar ka mu ke yi,me ya kawo mace d'akinka?" Cewar Abba

Salim ya ce"wallahi Abba ba ni na kawo ta ba,kuma ban san wanda ya kawo ta ba".

Sai Abba ya juyo da kallonsa gareni ya ce"ke maganar da ya fad'a gaskiya ce?"

Na d'ago,mu ka yi ido hud'u da Baby,da ta k'ank'ance ido ta na kallona,na maida duba na ga Salim,na ga idanunsa taf da k'walla

Na sunkuyar da kaina k'asa na ce"ba gaskiya bane,shi...shi ne ya kawo ni" Na fashe da kuka

Wallahi da na san haka abun zai kasance babu yanda za a yi na yarda da wannan aikin,ban gama tunani ba na ji muryar Abba "to kidnapping d'inki ya yi?"

Salim ya kalle shi da sauri ya ce"haba Abba!"

"Yi min shiru!" Cewar Abban

Sannan ya kalle ni ya ce"biyan kud'in fansar aka yi,shi ne zai maida ki gida ko?"

Na girgiza kai alamar ba haka bane.

Abba ya ce"to me ya yi miki?"

Na kalli Baby,na ga sai share hawaye take yi,na kalli Ammi na ga ta rik'e k'ugu,fuskar nan murtuk kamar kunun kanwa,na kai duba ga gogan nawa,shi ma ni ya ke kallo kamar idanunsa za su fito

Sai kawai na maida kaina k'asa,gabana na tsananta fad'uwa.

Ammi ta ce"tambayarki fa ake yi!"

Sai da na yi wasu huci masu zafi har uku a jere sannan na ce"Fyad'e ya yi min".

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Duka suka d'auki salati,har da Salim d'in.





#Team Salim
#Team Zinatu

Waye abin tausayi wai?😥
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_


BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_


*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*


Page 18



"K'arya take,wallahi ban yarda ba!" Cewar Ammi ta na nuna ni da yatsa.

K'irjina ya dinga lugude,tuni nadama ta rufe ni, kai gaskiya ranar na yi danasani,na ji haushin kaina sosai. Salim ya kalle ni ya ce"Zinatu ki ji tsoron Allah! Yanzu saboda na k'i karbar soyayyarki sai ki saka min da wannan?"

"Kai!" Abba ya daka tsawa ya kalli Salim ya ce"Salim! Ka san ni dai ba sa'anka bane,bare ka tsaya yin wasan kwaikwayo a gabana,don haka ka fad'a min gaskiyar yanda abin ya kasance".

Salim ya cije leb'e da alama dai ya na jin zafi a zuciyarsa,ya ce"wallahi tallahi Abba ban yi mata komai ba,sharri ta yi min kawai!".

Ammi ta ce"amma lallai yarinyar nan ke makira ce! Kenan saboda ya ce ba ya son ki sai ki nemi jifansa da sharri? To plan d'inki bai samu shiga ba!".

Abba ya d'aga mata hannu ya ce"kin ga Rahma! Ba a shaidar d'an yau,kuma ki yi tunani idan Khadija aka yiwa haka ya za ki ji? To wallahi ba zan bar maganar nan haka ba,dole na tabbatar da adalci a ciki".

Ni dai hawaye kawai nake sharewa,yanzu kam na fi tausayin Salim fiye da kaina.Baby dai har yanzu ba ta ce komai ba,ban kuma san abin da shurunta ya ke nufi ba,jikina ya mutu murus nadama ta haifar min da kasala sosai.

"Don Allah Abba ka yi bincike,wallahi wannan yarinyar sharri ta yi min, ban san wanda ya kawo ta d'akina ba,kuma tun farko fargabar yanda za ku d'auki zancen ne yasa na kasa fad'a muku,na yi yunk'urin fitar da ita daga gidan nan". Salim ya fad'a murya na rawa.

Abba ya ce"alfarma d'aya zan yi maka! Gobe za mu je asibiti da yarinyar nan,likitoci su duba ta muddin aka tabbatar an yi mata fyad'e to na yarda da zancen ta,na watsar da naka,don kai ne ka yi kenan. Idan kuma aka tabbatar da babu wani fyad'e da aka yi mata,to zan yarda da zancen ka,kuma ba zan bar duk wani me hannu a sharrin da aka k'ulla maka ba".

Salim ya ce"amma Abba..."

"Na gama magana,kuma ban buk'aci jin komai daga bakin kowa ba". Ya katse shi da fad'in haka.

Gabana ya fad'i da jin furucinsa,nan take na fara tunanin anya kuwa na yiwa Salim adalci? Ni dai a halin yanzu ban san a wane hali nake ciki ba,an yi min fyad'e? Ba a yi min? Wallahi ba ni da masaniya,idan aka je asibiti ya tabbata anyi min,shikenan fa na had'a Salim da mahaifinsa,kuma bani da tabbacin hukuncin da zai yanke min zai yi daidai da burina,hukuncin tilastawa Salim aurena na ke nufi.Idan kuma ba a yi min fyad'en ba duk cikin plan d'in su Nazifi ne fa? Wane irin hukunci zai yanke akan mu,bayan asiri ya tono? Na dinga jero salati a zuciyata, da na tuna yanzu duk inda hankalin Anti Na'ima ya ke ya tashi,na rashin dawowa ta,watak'il har Ummi da Baba duk sun ji.

Abba ya kalli Baby da ke share hawaye ya ce" Khadija,je ki bata d'akin da za ta kwanta kafin goben".

"Ki biyo ni" Baby ta fad'a, ba tare da ta kalli inda nake ba.Shi kuma Salim har yanzu ya na nan a durk'ushe kamar me neman gafara,kodayake kusan hakan ne ma ai

Na tashi jiki ba k'wari na bi bayan Baby,tun ban yi nisa ba na ji Abba ya saki salati,na yi saurin juyowa sai ya juyar da kai ya ce"sannu kin ji? Khadija ki bata kayanki ta canza wad'annan".

"Salim ka na da imani kuwa? Da har ciwo ka ji mata haka,amma shi ne za ka fita da ita a haka?" Na ji muryar Abba, hakan ya tabbatar min ya ga jinin jikin rigata ne.

Ban ji amsar da Salim ya ba shi ba na shiga d'akin da na ga Baby ta shiga,ta kunna haske sannan ta fita.Na bi d'akin da kallo,fess yake,babu wani shirgi daga katifa madaidaiciya,sai mudubi lik'e a jikin bango,na samu gefen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login