Showing 123001 words to 124209 words out of 124209 words
shima, alamunsa sun nuna yay wanka dan sanye yake cikin ƙananun kaya da sukai matuƙar amsarsa sai ƙamshinsa mai sanyi da ke tashi. Zaune ya kai idonsa a kanta sai dai fuskarsa babu walwala, duk da taji motsin nasa ko sau ɗaya bata nuna alamar hakan ba balle ta ɗago, lap-top ɗinta kawai take ƙoƙarin kunnawa. Shi kuma sai ya tsira mata idanun nan nasa na macizai da take kira, ƙin ɗagowar tata bai hanata jin kaifin idanun nasa a kanta ba, amma ta dake ta cigaba da abinda take yi.
“Break fast fa?”.
Ya faɗa a dake still dai idanun nasa a kanta. idan kujerar da ya ke zaune ta motsa to itama ta motsa. Cije lips ɗinsa yay yana wani sake ƙanƙance idanunsa a kanta. Kusan minti ɗaya yana kallon nata kafin ya miƙe tsam zuwa inda ta ke, lap-top ɗin ya ɗauke da ga jikinta ya ajiye gefe, karon farko ta ɗago ta kallesa da idanunta da suka kaɗa saboda kukan da tayi, fuskarta na nuna matuƙa ranta a ɓace. Nunawa yay kamar baiga kallon da take masan ba, kafin ta furta abinda ke bakin nata ya kwasheta gaba ɗayanta a cikin hannunsa yayi sama da ita kamar wata ƴar baby, (🤣dama abu ba abu ba sai masifa).
“Bana son wulaƙanci malam miye haka? Dalla sauke ni”. Ta faɗa cikin matsanancin ɓacin rai tana kai masa ƙananun duka a ƙirji, amma ko gezau kansa tsaye ya nufi hanyar kitchen da ita, saman cabinet ya direta, ya juya ya sakama ƙofar key. Dai-dai ita kuma tana dirowa da ga inda ya ɗauratan ta iso ga ƙofar. Wani shegen kallo ta watsa masa da faɗin, “Matsa min”.
“Idan kinyi abinda nace kenan”.
Ya faɗa cikin halin ko'in kula yana saka key ɗin cikin aljihun wandonsa da jingina da ƙofar yana mai harɗe ƙafafunsa waje guda. Ƙarshen ɓacin rai Lulu ta gama kaiwa, dan haka cikin kaushin murya ta ce, “Kasan na iya fiye da abinda kake tunanin ka'iya na rashin mutunci ko. Aliyu! Ka buɗe ƙofar nan ka bani hanya na wuce kafin na saka dana sanin sani na”.
Jikin ƙofar ya bari da ɗan taɓe baki batare da yace komai ba ya nufi frizzier ɗin da ke kitchen ɗin ya buɗe, sai da ya ƙarema kayan ciki kallo sannan ya rufe ya nufi store. Daga sama har ƙasa yake bin store ɗin da aka tsatstsage da kayan abinci kala da iri da kallo shima, har da su doya da airish da ruwa da kayan miya da akaima ajiya irin wadda bazasuyi saurin lalacewa ba. Shi sai abin ma ya so bashi mamaki da dariya, to su da suka jibge waɗan nan kayan matar gidan ta iya abinci ne?....
Shigowar Lulu a fusace ya saka tunaninsa yankewa, ya juyo gaba ɗayansa yana dubanta, huci take sosai idanunta sun juye gaba ɗaya har wani tara ƙwallan masifa sukeyi. Gashi yanda yaga sun ɗan kumburo tun ɗazun ya fahimci kuka tayi, yaji ba daɗi a ransa, dan sam baya son ganin wani ya shiga damuwa a dalilinsa, sai dai dolene yay abinda yayin dan ya fahimtar da ita da da yanzu ba ɗaya bane, yanzu komai sai da izini... Da sauri ya dubeta jin tana ƙoƙarin saka hannu a aljihunsa alamar son zaro key. Hannun nata ya riƙe yana ɗan waro idanu waje, duk yanda taso fisgewa bai sakar mata ba sai da ya zare key ɗin da ga aljihun nasa, sai kawai ya maƙalashi jikin belt ɗinsa ta inda yasan bazata ce zata ɗauka ɗin ba yana sakin wani shegen murmushin mugunta. Da sauri ta ɗauke kanta da ga dubansa gaba ɗaya tana jin kamar ta fasa ihu, a zuciyarta kuwa tace (ɗan iska).
“Yanzu mi zaki dafa mana? Dan yunwa nake ji nikam ga shi nace su Ammah kar su ƙara aiko abinci injiki.”
Harara ta watsa masa cikin gatsali ta ce, “Ashe zaka mutu da yunwa kuwa a gidan nan”.
“Zadai mu mutu, dan kema dai duk tsiya dole ki nema ai. A yanzu ma haka idan kina son fita da ga kitchen ɗin nan ki nema mana abinci, inba hakaba ALLAH anan zamu yini”. Ya ƙare maganar yana fitowa da ga store ɗin. Ɗaya da ga cikin kujeru huɗun da aka sakama table a tsakkiya yaja ya zauna. Hankalinsa kwance ya jawo wayar ya fara buga game ɗin ball, ya kuma ƙure ƙarar yanda ta cika kitchen ɗin da hayaniya. Lulu data gagara fitowa a store kanta ta dafe, sai faman haɗiyar rai take zuciyarta na ƙuna. Ta rasa yaushe ne guy ɗin nan yay mata irin wannan rainin har haka, bata taɓa haɗuwa da mutumin da ke latsata a yanda yake so da gadararsa irinsa ba, ya bala'i bala'in shigar mata hanci da yawa. Gadararsa da son nuna shi ɗin wani ne da iya taurin kai na cimata zuciya. Fitowa tai a bisa shawarar da zuciyarta ta bata, ta cije lips ɗinta tana jin kamar idan ta ƙarasa garesa ta shaƙesa kawai, amma sai ta ture tunanin gefe. Kujerar dake kallon wadda yake zaune ta dafa cikin ɗan sassauta zafinta dan ta fahimci ihun da take masan kamar tunzurashi yake da jin daɗin latsata. “Aliyu kafa san aiki nakeyi ka ɗakkoni ka kawo nan, kai miyasa baka bambance lokacin shiririta dana serious?”.
Batare da ya ɗago ya kalleta ba hankalinsa ma akan game ɗin sa ya ce, “Yima mijinki girki ne ba serious ba?”.
“Kai kasan mijin ma, Ka bani key na wuce, idan abincin kake so ai kasan gidan abinci, dan in har abinda zan girka zakaci ka siyama kanka wahala dan ban iya ba ma sai kabi wani sarkin”.
“Hummm ashe kuwa in dai ba zakiyi abinda nake so ba kuma ya dace ga matar aure to aikin ma zai gagareki yi ne, duk da a farko banda wannan niyyar. Dan haka kina da zaɓi kenan, yin yanda nake so kuma na tsara a gidana, ki samu yanda kike so kema. Ko ƙin yi, kema ki ƙi samu. Abinci kuma duk yanda kika iya kiyi zanci a hakan ko baiyi ba”.
Luuuu tai da idanunta kamar zata lumshe su sai kuma ta buɗe, komai ma ya gundireta, tama rasa yaya zatai da mutumin nan mai shegen taurin kai da gadara. Wai miyasa ma ta amince ne da wannan tsarin da shi? Miyasa bata bada damar a nema wani ba?. Tsaki taja mai ƙarfi da kai hannu ta dafe kanta, sai kuma ta janye tana mai watsa masa hararar zaka banbance tsakanin aya da tsakkuwa ta bar wajen. Da kallo ya ɗan bita ganin ta nufi hanyar store, tana shiga yay mata gwalo da sakin murmushi nan nasa da take kira na mugunta yana kashe ido ɗaya a hankali ya ce, “2-0 Madam”........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*