Showing 33001 words to 36000 words out of 124209 words

Chapter 12 - FURAR DANKO PART 1

Unknown   

12 Nov 2024

8755

kuma an tabbatar masa da tazo wajen awa biyu baya da suka shuɗe. Waya ya ciro yay kiran Nadiya, an jima ba'a ɗauka ba dan har tana batun tsinkewa sannan aka ɗauka. Cikin wata irin murya ta ce, “Ranka ya daɗe barka da dare”. Sai da ya ɗan cije leɓen haushi kafin ya amsa mata da “Ta iso ne?”. Cikin muryar nan na wadda ta gama buguwa da shiga yanayin masha'a ta amsa masa da “Tazo amma shegen driver ɗin nan nata ya kwasheta sun tafi”.
      “What!!” MM Atik Kumo ya faɗa da ƴar tsawa. Bai jira cewar Nadiya ba ya yanke wayar ransa a ɓace. Mota ya shige ya zauna tare da kwantar da kansa kan steering. A karo na biyu ya rasa damarsa akanta, tunda yake wata mace bata taɓa shiga ransa irin haka kamar yanda Lulu ƙamshi ta shiga ba. Da gaske sonta yake, yana kuma tsananin buƙatar mallakarta. Bai damu ace sai da aure ba, dan shi a halin yanzu babu maganar aure  ma a gabansa duk da kullum faɗan momynsa kenan shine yay aure. Sai dai da to kawai yake amsa mata a duk sanda ta titsiyesa. Tun randa suka haɗu da Lulu a airport ya kasa hutawa da tunanin surar yarinyar da tsiwarta, burinsa kawai ya gusar da ƙishinsa gareta dan kowace mace tama daina birgesa a dalilinta yanzu. Sake kaiwa steering duka yay tare da tashi zaune yayma motar key a fusace ya bar gidan......

       ★★
    Driving ɗin yake cikin ɓacin rai da takaici, yayinda ita kuma ta keta faman surutai da zaginsa akan ya maidata sai ta koyama Hon. Babale Misau da Nadiya da suka haɗa baki hankali. Faɗi take ita ba ƴar iska bace, duk wanda yace zai mata iskanci sai ta wulaƙanta shi.....
    Wani irin baƙin ciki ne ya sake turniƙe zuciyar Smart dan surutanta sun ishesa, sake tunzura fushinsa suke zuciyarsa na ƙuna. Wani shegen birki ya taka a harzuƙe har sai da tai gaba ta bugu da kujerar gabanta ta sake buguwa da jikin ƙofa sannan ta koma ta zauna daɓar. Dafe kanta tai dan azaba kamar zata fasa kuka, sai kuma ta harzuƙo cikin fushi da masifa ga rashin kasancewa a hayyaci da ya ƙara hauhawar masifar tata ta ce, “Kai wai miyasa baƙauye ne akoda yaushe? Mugu so kake ka kasheni ka gudu da motan ko? Illiterate kawai, ba abinda ya iya sai shashashanci baƙauye”.
       Idan motar nan ta motsa Smart to shima ya motsa, yakai matuƙar wuya so yake ya mata masifa dan maƙogwaronsa sai kaikawo ya ke a wuya amma yanata ƙoƙarin hana kansa, sai ma wayarsa da ya ɗauka ya fara danne-danne abinsa. Hakan ya sake fusata Lulu, da ma yaya lafiyar kura balle ta tsinke. Tana ƙalau ma yaya aka ƙare da jaraba balle yanzu da ya haɗa da maye. Sosai ta cigaba da zazzaga masa masifa ko haɗiyar yawu ma batayi, ganin badai zai kulata ba ta kama murfin ƙofar zata buɗe ta fita amma sai taji yayi lucking motar. Wayyo azabatun azaba. Yau dai kam yaga masifar ƙare dangi, dan bakinta baiyi shiru ba har sai da barci ya fara rinjayar mata idanu. Da wahala kaga Lulu tasha abu ya sakata barci, shiyyasa ko cikin abokanta ake ji da ita da kwarzanta ƙarfin kanta, amma yau da yake wani mugun haɗine MM Atik yay mata batare da ko Nadiya ta sani ba yasa abinda yafi ƙarfin kanta kala-kala wani ma bata taɓa shansa ba. Tun randa suka haɗu a airport bai huta ba, biye yake da ita yana ninƙaya cikin al'amurranta har sai da ya gama sanin ita ɗin wacece. Dan haka ya jawo Nadiya a jikinsa ya dinga jiƙata da kuɗaɗe harta amince da shi bawai yazo dan ya cutar da aminiyar tata bane son gaskiya yake mata. Ita da shi suka haɗa plan ɗin wannan phaty na samun lafiyarta, ya kuma saya musu duk kayan shaye-shayen tare da basu gidan hutawarsa da ya gama ginawa kwanan nan, shi yayi hakane dan ya rutsa Lulu a can, yayi imanin in har ya sameta sau ɗaya da kanta zata cigaba da nemansa kamar sauran ƴammatansa tana kawo masa kanta. Sai dai kuma kash, bayan ya gama wahalar haɗa dukkan plan ɗinsa wani shegen driver ɗinta ya zo ya rusa masa komai.........✍️




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*


[9/1, 12:11 PM] +234 913 709 3201: 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣2️⃣



........Anan kam tasan basa barin ƙofa a buɗe, dan haka ta zagaya ta window ɗin ɗakin Iya Tabawa. Tana kuwa zaune tana addu'oi tun bayan idar da salla. Ba yau Lulu ta fara mata haka ba, shiyyasa koda ta kirata bata firgita ba. Sai ma miƙewa da tai a ɗan ɗarare. A kausashe Lulun ta ce, “Dalla Malama ki buɗen ƙofa kin wani tsaya kallo na”. Haƙuri Iya Tabawa ta bata ranta fal wasi-wasi. Zuciyarta ta fara raya mata ko dai yawon banza Lulu ke fita ne, tunda ba taɓa ganinta cikin maye tai ba. A ƙasar Hausa kam mafi yawan al'umma sukan fassara yawon dare na ɗiya mace da tazubar ne kawai, da wahala hasashensu ya wuce haka har su hango wasu abubuwa masu illa a rayuwar ƴaƴanmu mata bawai zina kawai ba. Sun manta a rashin ji duk abinda namiji yasa kansa iyawa wasu matan kan kwatantashi ba wai sai iskanci kawai ba. (Ya rabbi ka shiryar damu da zuri'armu baki ɗaya).
     Tana shiga ɗakinta a saman katafaren gadonta ta zube tana mai sauke numfashi, lamo tai cikin lallausan bedsheet da duvet ɗin gadon masu ltaushin tsiya da ƙamshi. Tunanin matakin da zata ɗauka akan tsageran driver ɗinta takeyi, da su Hon. Nakowa, sai dai kuma barcin da bai gama fita idonta ba ne yaci ƙarfinta......
     
       ★Kasancewar alerm data saita ƙarfe takwas ta farka badan barcin ya isheta ba. Sai dan tana da shari'a mai zafi a yau ɗin da zata gudanar wadda a yau ɗin take fatan alƙali ya yanke hukuncinta. Cikin rashin kuzari ta tashi ta faɗa toilet, sai da ta gamsu da gyara jikin nata a fannin wanka sannan ta fito. Shiri tayi tsaf da ita cikin suit na mata kalar baby pink, rigar cikinta fara. Dan ƙyau kam tayi ƙyau, ga shegun takalmanta masu dogayen dudduge ɗin nan da tsabar ƙwarewa a sakasu yasa ko gargada batayi a tafiya da su. Yau dai anyi abun arziƙin saka ƙaramin baby hijab fari da yay mata ƙyau sosai, sai dai iyakarsa kafaɗarta dan ƙaramine. Ƙamshin nata na fitar hankali ta bulbula a jiki har ita da kanta tanajin ƙamshin na hawa mata kai, sai dai haka take buƙatarsa. Cikin takun nan nata na isa da gadara ta fito, illahirin jikin nan na motsa kansa kamar wata tarwaɗa a ruwa. Mubeen kawai da Daddy ta samu a dining suna breakfast, sai Mommy tana tsaye a tsakkiyarsu da alama abincin take haɗa musu.
       “Good morning Daddy & Mommy!”. Ta faɗa kanta tsaye babu wani alamar respect gareta matsayinsu na iyayenta. Musamman ma Daddy dake amsa sunan mahaifi. Kowa dai yasan yanda ƴaƴa ke shakkar iyayensu maza fiye da mata a ƙasar hausa. Mommy dai kallonta kawai tai ta girgiza kanta. Shiko Daddy fuskarsa a washe da murmushi, duk da dai kamar alamunsa na nuna yana cikin damuwa ne yake dannewa.
        “Morning sweet heart. Kin tashi lafiya? Yaya ƙarfin jiki”.
          “Komai normal Daddy”. Ta faɗa tana ɗaukar shayin gabansa da yake sha ta kurɓa da ga tsayen da take. Da kallo ya bita har yanzu da murmushi a fuskarsa. “Babyna zauna mana kisha ba ƙyau shan abu da ga tsaye ai”.
     “No Daddy, hakan ma it's ok for me. Ina sauri ne 9:30 inada Shari'a”.
   “Allah yay miki albarka, ya kare munke ga duk wani sharrin maƙiya na gida dana waje”.
           “Amin sweet Papa na”.
     Sarai Mommy ta fahimci harda ita a addu'ar tasu. Hakama Mubeen. Dan tuni sun gane abinda mahaifin nasu kema Mommy akan ƴar uwarsu. Sai dai ko sunce zasu ɗauki mataki hanasu yin hakan Mommyn take yi. Babu yanda suka iya dole suke haƙura. Amma badan jajircewarta a kansu ba ba ƙaramar tsanar Lulu sukeji ba a rai. Wani lokacin ma hatta shi Daddy ɗin takaici yake basu  shiyyasa su ƴan biyu sam basu son zaman gidan. Harta ɗan sha shayin na Daddy kusan sau bakwai ta ajiye Mubeen bai mata magana ba itama batai masan ba. Batama nuna tasan da zamansa a wajen ba kamar yanda shima ya nuna. Tana shirin sauka a ɗan steps ɗin hawa dining ɗin Daddy ya dakawa Mubeen ɗin tsawa.
       “Kai dan uwarka ita ɗin sa'arka ce da bazaka gaishe ta ba?!”.
     Kallon Daddy ɗin Mubeen keyi zuciyarsa a bushe, sai kuma yaja numfashi mai nuna zuciyarsa na yunƙurowa, sai dai kallon gargaɗi da Mommy ke masa ya hanashi cewa komai da ga tarin abubuwan faɗar da ke cikin bakinsa game da mahaifin nasu. A hankali ya furta “Daddy kayi haƙuri” kawai yaja bakinsa ya tsuke.
            Tsaki daddy yaja dai-dai Lulu na ficewa a falon gaba ɗaya. Bata jira jin abinda Daddyn ke shirin faɗa ba. Karo na farko a rayuwarta taji kamar babu daɗi akan abinda Daddy ɗin kema ƴan uwanta saboda ita. Har ga ALLAH tana ƙaunar ƴan uwanta, hasalima bata haɗa son su da komai ba. Hatta su Yaya Hassan batajin daɗin rayuwar doya da manjan da ke a tsakaninsu. Dan ko gidan su ƴan biyun sukazo basa kulata bata kulasu, saboda sun riƙe abubuwan da mahaifiyarsu ta fuskanta da ga mahaifinsu dalilin mahaifiyarta da ita kanta. Goshinta da yay mata nauyi saboda abinda ta sha jiya bai gama sakinta da ƙyau ba ta ɗan shafo tana furzar da iska. Ba ƴan uwanta kaɗai ba hatta Mommy tana jin ƙaunarta, dan kallon uwa take mata a zahiri da baɗinin rayuwa. Ta sani duk wanda yasan gidansu ma ya sani Mommy bata taɓa cutar da rayuwarta ba koda da harara, idan dai tayi laifi yanda take ma yaranta faɗa itama haka take mata. Shiyyasa duk rashin mutuncinta har abada bazata taɓa kwatantashi ga Mommy ɗin ba. Musamman ma idan ta tuna nasihar da Kakanta Alh. Sufi Garko kanyi mata a duk sanda taje garesa game da Mommy ɗin da halaccinta ga zamantakewarta da mahaifiyarta. Duk da dai itafa har yanzu bata taba jin labarin ainahin zaman da Mamanta tayi da Mommy ɗin ba...... Gaisuwar da ma'aikatan gidan ke mata ce ta katse mata tunani, batare data kalli ko guda a cikinsu ba take wucewarta kawai da takun nan nata na yauƙi da isa. Tana gab da isa motar da take buƙatar hawa idanunta suka sauka akan Smart da ke zaune wajen maigadi kamar kullum hankalinsa a waya yana buga game ɗin ball da yake matuƙar bege. Sake tamke fuska tai da ɗauke kanta, abinda ya faru jiya ne ya shiga mata kaikawo cikin kai. Sosai taji ɓacin rai ya sake baibayeta da takaicin su Nadiya da suke son jamata rainin nan wajen wannan shashashan, ta jima tana shaye-shaye, amma duk wanda yay mata sani na haƙiƙa bai san wannan halayyar tata ba, a koda yaushe cikin ƙoƙarin binne sirrinta take, amma sai gashi a haɗuwarta da mutumin da tafi tsana fiye da kowa a duniya shi ya ganta a yanayin. Ƙwafa tai da balla masa harara, cikin borin kunya ta cilla masa key da sake jan tsaki. Idanunsa da ke nuna alamun barci bai ishesa ba ya ɗan lumshe ya sake buɗewa, batare da ya kalleta ba ya miƙe zuwa gaban Motar data ɗakkoma key ya buɗe mata bayan, sai da ta shiga ya maida ya rufe sannan ya koma mazaunin driver, motace mai tsadar gaske da ɗaukar hankali, kasancewarta ƴar gatan gidan hatta Daddy tafi yawan motoci. Dan motarta biyar kuma duk ƙosassu, sai ƙarama ɗaya da sha'awa kawai ya sata matsawa Uncle ɗinta Khamil ɗan uwan mahaifiyarta dake Abuja saya mata ita. Dai-dai suna barin kan titin layin nasu ya miƙa mata handbag ɗinta ta jiya da key ɗin mota, a hankali ta ɗago da ga duba takardun da takeyi ta ɗan sake hararsa sannan ta kalla kayan a yamutse. Murya a dake sai dai acan ƙasan maƙoshi ta furta, “Waya gayyaceka inda nake jiya?”.
        Sarai ya jita, amma sai yay kunnen uwar shegu da ita ya haura kan babban titin bayan motar da ya dakatama ta shige layin da ya fito. “Malam da kai nake yi”. Ta sake faɗa cikin zafin rai da borin kunya. Karan farko ya ɗan ɗago idanu ta cikin mirror ya dubeta. Ido suka haɗa, tai saurin kauda nata zuziyarta na tsirgawa. Itafa komi za'ai ayi amma kar ya kalleta da wannan shegun idanun na macizai (kamar yanda ta raɗa musu😂🥱). Yanda tai ɗin sai ya so bashi dariya, amma sai baiyi ba ya ɗan saki murmushin gefen baki da maida hankalinsa ga titi cikin salon lumshe idanun nasa kamar yasan suke razanata, babu alamar zai bata amsar da take buƙatar son ji. Ba ƙaramin takaicinsa bane ya kume Lulu, ga wayarta ta isheta da ruri. Nadiya ce keta faman kiranta tun ɗazun, sai dai taƙi ɗagawa dan tai alƙawarin sai ta koyama ƙawar tata mafi kusanci hankali. Tsaki taja a karo na babu adadi, ta fisgi wayar da ke kan rigarta ta lauyoyi ta kashe tare da sake cillar da ita kan rigar da ke a gefenta. Haushin Nadiyar dana sharetan da yay ta tattaro gaba ɗaya ta nufesa da shi.
      “Wai kai mika ɗauki kanka ne da har ina maka magana kana wani cika da batsewa?”.
    Yanda tai maganar muryarta har tana zuga kamar wadda kuka ke son yunƙuromawa sai dai ƙarfin halinta na dannesa ya sashi sake dubanta a karo na biyu ta cikin mirrorn. Sake maida kansa yay ga titin sai kuma ya ɗan muskuta zamansa da furzar da iska. Ƙasa-ƙasa na rashin kuzarin da kasala irin na wanda barcin bai ishesa ba cikin deep voice ɗin nan ta shi ya ce, “Mi kike son sani?”.
           Wata irin kasala muryar tasa ta nema saukar mata saboda yanda yay maganar cikin sanyi da tausasa lafazi, sai dai cikin yaƙi da kai da nuna juriya irin ta masifaffun mutane ta watsa masa kallon banza da yin ƙwafa tana maida kanta ga takardun da take dubawar. Kamar bazata ce komai ba sai kuma bayan kusan minti ɗaya ta ce.........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
[9/1, 12:11 PM] +234 913 709 3201: 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣1️⃣



........Wayar da yake faman daƙila ya ajiye, dan dama yana dannawar ne kawai badan yana fahimtar komai ba da yake yi. Ta cikin mirror yake kallonta, sai kuma kamar wanda aka tsikara ya janye yana jan tsuki. Da sauri ya furzar da iska zuciyarsa tana masa kai-kawon tunanin ina ya dace ya dosa da ita. Gidansu ko gidan Uncle Yousuf?. A gidansu tana da ƙanne, kuma basu san halin da take ciki ba bayan iyayensu, ganinta a haka garesu zai ƙarasa zubar mata da mutunci ne a idonsu har ma da ma'aikatan gidan nasu da take takawa kamar ƙasa a duk sanda taso. Gidan Uncle Yousuf kam yaransa basu da wayo sosai kasancewarsu ƙanana, zai ma iya yiwuwa yanzu sunyi barci, ajiyar zuciya ya ɗan sake ja da kallonta ta mirrorn sai kuma ya janye idanunsa a lokaci ɗaya. Har ya ɗauki waya da nufin kiran Uncle Yousuf ɗin sai ya fasa, key yayma motar kawai ya cigaba da tafiya. Kaɗan-kaɗan sai ya dubeta ta mirror har suka iso gidan. Horn yay maigadi ya buɗe ƙofa ya fito, dan ba'ace masa wani zaizo gidan ba a irin wannan lokacin dan ƙarfe sha ɗaya saura. Ƙarasowa yay jikin motar sosai, Smart dake kallonsa shima yay ɗan murmushi da faɗin “Baba Barka da dare yaya aikin?”.
      Murmushi shima maigadi yayi, dan ya ganesa. Cike da kulawa ya ce, “Mazan fama kaine yanzu da dare haka?”.
     “Eh baba na kawo wannan ne”. Yay maganar yana nuna baya, ɗan leƙawa baba maigadin yayi, ganin Lulu kwance a bayan ya sashi ɗan yin baya yana dafe baki dan shi a zatonsa ko barcin isa ne take yi. Da sauri ya koma ciki ya buɗe gate ɗin. Har gaban ƙofar shiga falon gidan Smart yay parking. Sai da ya kashe motar ya fito sannan ya ɗaga waya ya kira Uncle Yousuf. Ba'a jima ba aka ɗauka. Shi ya fara gaidashi dan a girme dai ya girmesa. Uncle Yousuf ya amsa da ƴar fargaba, sai yay saurin tambayarsa badai wani abu ya sake haɗasa da Mawaddat ba?.
         “A'a Alhaji komai bai faru ba. Itace dai na kawo nan ɗin gamu a ƙofar falo”.
     Da mamaki Uncle Yousuf ya miƙe zumbur, Jallabiyarsa ya ɗauka ya zura dan har sun kwanta ma. Ko amsa tambayar lafiya da Aunty Saliha ke masa baiyi ba ya fice cikin sassarfa yana faɗin, “Ina zuwa”. Shi da kansa ya buɗe motar ya leƙa, ƙirjinsa yay matuƙar bugawa, ɗagowa yay yana kallon Smart kallo na neman ƙarin bayani. Fahimtar hakan shi kuma ya sashi furzar da iska kaɗan. “Bayan tafiyata ta fita, jin hirarsu da ƙawarta a ɗazun ya sani sake dawowa, sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login