Showing 75001 words to 78000 words out of 124209 words
yay tayi kasancewar duk wanda zai ɗauki hoto sai an jajubosa musamman ma manyan mutanen nan da ke nanuƙe da Alh. Sufi Garko. Shigowar lokacin sallar la'asar ne yay belinsa. Da ga salla kuma kowa zai kama gabansa..........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
[9/15, 4:50 PM] +234 906 439 3116: 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣3️⃣
......Sam Lulu bata san wace waina ake toyawa ba. Dan yau ma dai tashi tai da ciwon kai har da zazzaɓi sakamakon mura da ta mata ɗaurin kazar kuku. Da ƙyar ta iya tashi kusan 12 da Mommy ta tasheta akan tai wanka. A sannan ne ma suka san bata da lafiyar. Bayan ta ɗan samu tai wankan ne ta sha tea da Mommy ta haɗa mata da kanta mai kayan ƙamshi sosai. Wani irin faɗuwar gaba takeji ga rashin lafiyar da ta kadata. Da ƙyar ta samu ta ɗanyi waya da Zainab dan jin yaya ake ciki a office, sai kuma Sha'aibu ɗan sanda da yay kiranta yay mata albishir ɗin cafke mijin matar nan da suka sami nasarar yi. Hakan ya ɗan faranta mata rai da jin zazzaɓin nata ma ya sauka har ta fito falo. Anan taci karo da yayunsu su Twins sun zo. Sama-sama sukai gaisuwa ita da su dan sam babu jituwa tsakaninsu. Fasa zaman falon tai ta juya ta koma ciki ranta na ƙara dagulewa. Ta rasa mitai ma ƴan uwan nata suke jin zafinta irin haka. Hira da ta samu sunayi da sauran ƙannensu har da dariya, amma ita tana fita duk suka gimtse fuska sai Suhaib da Nazeer ne suka gaisheta, sai kuma Amrah da tai mata yaya jiki. Wannan abun ya jima yana damunta, sai dai rashin riƙe abu a rai kansa ta watsar ta cigaba da al'amarin ta musamman idan tasha wani abu haka. Gadonta ta koma ta kwanta dan da jikinta yay mugun zafin zazzaɓi, barci ne mai nauyi ya ɗauketa batare data shirya hakan ba. Hakan yasa har su Abba suka fita massalaci tare da yayunta da Mubeen da su Suhaib bata sani ba. Ba kuma ta farka ba har bayan la'asar da ƴar hayaniyar da gidan ya ɗauka ya farkar da ita da ga barcin da take mai cike da mafarkin mahaifiyarta da take matuƙar bege, sai drivern ta da bata san daga ina kuma mafarkin nata ya yayo mata shi ba dan ita dai bata kwanta da tunanin ko mai kama da shi ba balle ace. A hankali ta ɗan ja tsaki da murza goshinta da yay mata nauyi. Zazzaɓin nata ya sauka, sai dai nauyin da kan nata yay mata da rashin jin ƙwarin jiki. Landline phone da ke saman bed side drawer ɗinta ta ɗauka tai kiran sashen masu aikin gidan. Batare da jiran jin waye ya ɗauka ba balle amsa sallamarsa tai umarnin ganin Iya Tabawa ta yanke wayar ta ajiye. Cikin mintuna kaɗan kuwa sai ga iya Tabawa na faman washare baki. Kallo ɗaya tai mata ta ɗauke kanta cikin bada umarni kamar yanda ta saba ta ce ta haɗa mata ruwan wanka.
“An gama ranki ya daɗe”. Iya Tabawa ta faɗa tana nufar bathroom cike da farin cikin abinda su Daddy suka shigo da shi gidan cewar an ɗaurama Lulu aure. Harga ALLAH da gasken gaske son yarinyar take da ƙaunarta. Duk halayyar Lulu a gidan ta taka ma'aikata baisa taji ƙinta ba. Dan duk wulaƙancin da take musu hakan bai hanata ƙyautata musu randa ta so ba kuma musamman ma ita. Ba kuma komai ya ƙara girmama farin cikin ta ba sai jin wanda Lulun ta aura, dan ita sam bataga hakan komai ba duk da sauran ma'aikatan gidan na can na dariya da gulmar wai alhakinsu ne ya kamata ta ƙare da auren drivern ta. Dan su sosai abin yay musu suga da kallon cewar Lulu tayi faɗuwar baƙar tasa. Tana ƙoƙarin shiga wankan ta bama Iya Tabawan umarnin haɗa mata farfesun kifi mai yaji sosai dan Lulu na matuƙar son kifi a rayuwarta. Harta nufi ƙofar fita Lulun ta dakatar da ita.
“Wai lafiya ne a gidan aka ishi mutane da hayaniya? Kema naga sai wani washare baki kike”.
Iya Tabawa da murmushi ya kasa barin fuskar tata ta ce, “Muma dai bamu san mike faruwa ba Aunty, munga dai su Alhaji ƙarami (Uncle Yousuf) nata farin ciki inagama aure dai ya ƙara”.
“What?! Uncle You ɗin ne ya ƙara aure ki kike nufi?”.
“Bani da tabbacin hakan Aunty, hasashen dai kawai nake”.
Tsaki Lulu taja cikin taɓe baki ta nufi bathroom ɗin cikin ƙunƙuni take faɗin, “Kai wannan tsohuwa da neman masifa kike. Haka kawai da ranar nan tsaka ace amma Aunty Saliha kishiya ai akwai ƙura. Dan koni nan na korar mata shegiya”. Daga haka ta shige.
Ta fito a wankan tana cikin shiryawa da kaya marasa nauyi na wando da riga akai mata knocking ƙofa. “Waye?” ta faɗa tana fesa turarrukanta. Uncle Yousuf ya amsa mata da cewar shine. Ƙofar ta nufa da sauri tana faɗin, “Uncle You!”. Amsa mata yay yana turo ƙofar ya shigo, dan haka suka kusa cin karo. Baya taja da sauri tana mai zuba masa ido. Cikin kasa danne abinda ke bakinta ta ɗan waro manyan idanunta ta da faɗin, “Oh god wai da gaske ne kenan?”.
“Da gaske mi?”.
Ya faɗa idonsa a kanta. Fuska ta ƙwaɓe da wani yamutseta. “Kishiyar kaima aunty Salihar mu Uncle?”. Yanda tai tambayar da wani tsuke masa fuska taso bashi dariya. Amma sai ya dake ya ce, “Eh haramunne?”.
“Kutt! Wai da gaske ne ma?”.
Kasa jurewa yay yanzu kam sai da ya dara. Dan a masifaffiyarta ta sake tambayar. Ya ce, “Kinga maida wuƙar Daughter ba haka bane. Ai auntynku ita da kishiya sai a aljanna”.
“Oh har na samu relief”.
Ƴar dariya yayi yana kaiwa zaune a kan sofa. Ya nuna mata wajen zama itama. “Kinga zauna bani da lokaci magana nazo muyi.”. ganin yanda yaci serious ya sata kaiwa zaunen cikin bashi dukkan attention nata. Shima sake gyara yanayinsa yay da nutsuwarsa ya ce, “Mawaddat!”.
“Yes Papa”.
Ta amsa cikin sake nutsuwa. Cigaba yay da faɗin, “Kin san daga ina muke?”.
“Massallaci”.
Murmushi yayi da jin jina mata kai. “Yes daga massalaci muke, sai dai bayan yin sallar juma'a an ɗaura aure. Auren kuma bana kowa bane sai naki”.
Wani shegen dariya ta saki a lalace. Tace, “Uncle You ALLAH ka iya tsokana, sai kace wata babyn roba ”.
Murmushinsa ya sake faɗaɗawa da gyara zamansa. “Mawaddat ba wasa nake ba. Kema kuma kin san bana miki kalar wannan wasar ai”.
A take fara"ar fuskarta ta ɓace ɓat gaba ɗaya. Ta tsirama Uncle Yousuf ɗin ido kamar wadda tai suman wucin gadi. Fahimtar yanayin data shigan ne ya sakasa riƙo hanunta a cikin nashi yana girgiza mata kansa. “Kinga calm down sweet heart. Wannan aure ya tafi ne kamar yanda muka tsara da ke. Abinda yasa kuma akayisa yanzu ba tare da saninki ba kema shine a jiya da yamma......” ya kwashe komai game da ƙudirin su Tajuddeen da mahaifinsa ya sanar mata. Ya ɗora da hukunci baba dama abinda ya faru yau a massalaci yanzu haka ma Tajuddeen na asibiti an kwasheshi.”
A hankali ta lumshe idanunta. Sai kuma ta koma jikin kujera ta lafe dan ƙirjinta wani irin bugawa yake da sauri-sauri. Da'ace ta iya addu'a ita ya kamata ace ta karanto a wannan halin, sai dai kash hakan bai samu ba. Taja wasu mintuna a haka kafin Uncle Yousuf ya dawo da ita a hankalinta.
“Mawaddat Please relax. A yanzu haka fa tare muke da Baba a gidan nan. Kuma son ganinki sukeyi. Ina so. Ki nutsu kisa hankalinki waje ɗaya dan kar kije ki canja abinda muka tsara kuma ta ƙwaɓe, dan idan Baba ya fahimci shirinmu bake ba hatta ni da Yaya da bai san komai ba sai ranmu ya ɓaci. Ki dake zuciyarki ki nuna jin daɗinki ga hukuncinsa ta haka ne kawai zai kauda kai akan ki mu samu cikar burinmu dan zuwa dare zan nemo Aliyu yazo ayi komai a rubuce ma”.
“Uncle karfa ya bamu matsala. Wlhy guy ɗin nan yanada taurin kan masifa fiye da yanda kake tsammaninsa”.
“Karki damu insha ALLAHU babu abinda zai faru. Komai bazai canja ba da ga yanda muka tsara in har kin yi abinda ya dace yanzu a gaban Baba ta yanda bazai fahimci komai ba”.
Kanta ta jinjina masa muryarta a shaƙe ta ce, “Shikenan zanyi yanda kace. Amma Please bana son ganinsa yau sam”.
Murmushi Uncle Yousuf yayi yana miƙewa. “Baki da matsala da hakan tashi kisa mayafi muje. Koma dai ki canja kayan nan zuwa atamfa haka ki lass ok”.
Badan taso hakan ba ta gyaɗa masa kai kawai. Ya fita yana sake jadadda mata ta kiyaye dai ta kuma kula kar wanda ya fahimci halin da suke a ciki......
★.....
A ɓangaren Smart kam tunda suka bar government house hannunsa riƙe yake da kansa. Tun su Ahmad na masa shaƙiyanci da wasu a cikin teammate ɗinsa da suka biyosu a motar Ahmad ɗin har suka fahimci shirun nashi bana lafiya bane. Dan duk da dama shi bamai yawan magana bane koyaya ne zai musu murmushi ko yace wani abu koda sau ɗaya ne, balle wannan ranar a gareshi ta musamman ce, tunda su dai basu san komai game da auren ba.
“Mawashi lafiya dai?”.
Cewar Ahmad yana gangarawa layin anguwar su Smart ɗin. Kansa ya nuna masa da hannu kawai. “Subahanallahi ciwo yake maka kan?”. Kan ya sake gyaɗa masa. Shiru motar tai na ɗan lokaci duk suna kallonsa, sai kuma suka shiga jera masa. Kusan tare motar tasu ta tsaya da ta su Abba suma. Dan haka suka firfito a tare, dole ya sake daurewa dan a cikin ƙanƙanin lokaci ƙofar gidan shima ya fara tara mutane ƴan taya murna, dan al'amarin kamar busa usur zancen auren ya dinga shiga kunnuwan mutane, dama gashi juma'a ce yawancin mutane duk sun dawo gida..........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
[9/15, 4:50 PM] +234 906 439 3116: 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣4️⃣
........Gayyar yayunsa da ƙanne su Salim da sai da sukaje wajen ɗaurin aure suka san dawa aka ɗaura kusan ransu duk a ɓace yake, dan gani suke kamar Abban ya rufe zancen ne dan yafi son Hydar ɗin a gidan kamar yanda iyayensu kan faɗa. Komai ya sake tsaya musu a rai jin ƴar wanda ya aura da kuma Gwamna da yay waliccin auren. Zuwa walimar cin abincin ma a gidan gwamnati sai da Abba ya nuna ma wasun su ɓacin rai sukaje. Su dai su Mubarak ƙanana ko'a jikinsu, sai ma farin ciki suke ballema yau gasu a cikin government house. Sune suka fara isa gida da labarin wannan aure na bazata, dan sun riga su Abban tahowa, sune kuma suka baza batun auren a anguwar.. Smart yayi dauriyar tsayawa amsa gaisuwar mutane da taya murna kafin su shiga ciki. Sun tadda gidan a ɗan harmutse, dan kamar kowa jiran shigowar Abba yake. Shiko Abba da yasan da hakan a tsumensa ya shigo, dan haka dole kowa ta kama kanta sai dai ƴar ƙus-ƙus a ɗaki tare da yaransu dan har na ma'auri matan yau suna gida kasancewar hakan kamar ɗabi'ar yaran gidan ce duk juma'ar ƙarshen wata anan suke yini su da gayyar ƴaƴansu..
Umarni Abba ya bama Smart ya biyoshi falonsa. Ya kuma aika Musaddiq tattaro sauran jama'ar gidan suma. Cikin ƙanƙanin lokaci kowa ya hallara har falon na neman musu kaɗan. Dan kuwa dai ALLAH ya azurta malam Mika'il Idris Mawashi da baiwar ƴaƴa. Matan ne suka shiga gaisheshi da sannu da dawowa dan sanda wasunsu suka iso shi ya fita. Ya amsa musu da tambayarsu mazajensu dama yaran duk da yasan sukam duk suna tare da su anan. Zakuma su zo gaisheshi. Duk da ran wasun su a dagule yake haka suka dinga amsawa mahaifin nasu kamar yanda suka saba. Shima ya lura da yanayin wasun su ɗin, amma sai bai damuba dan yasan iyayensu mata ne suka gama kunnosu, ya kuma san bai wuce akan wannan aure na Hydar da ya sirrinta ba. Yayi gyaran murya da sake tsare gida yana maida kallonsa ga matan nashi duka huɗu.
“Zan fara da ku matsayinku na iyaye. Alhamdullah da farko zan fara da sanar muku yau dai ALLAH yayi an ɗaurama Aliy aure. Nasan abin zai iya zama abin mamaki a gareku har ma da ka-ce-na-ce. To bazan hana hakan ba, sai dai zan fahimtar da ku muma a haka al'amarin yazo mana. Ga mahaifiyar sa nan ita kanta sai a safiyar yau na sanar mata cewar zamu kai kuɗin auren Aliy domin iyayen yarinyar da yake so ɗin sun buƙaci haka sakamakon ɗan rikici da abokan neman auren nasa suke son kawo wa a ciki. Ni kaina kuma a yau ɗin munje ne da batun kai kuɗin aure sai suka buƙaci kawai a ɗaura domin hakan ya zama masalaha ya kuma bama kowa kwanciyar hankali. Sosai hakan yamun daɗi, dan ganin auren Aliy a yanzu yana ɗaya da ga cikin abinda ke damuna, bayan mun dawo naso zaunar da ku na muku bayanin halin da ake ciki sai ya zam guri ya ƙure, dan haka nace bari mu bari har sai mun dawo. To Alhamdullah yanzu dai ta ƙare, shima Aliy ya shiga sahun ƴan uwansa, sai muyi masa fatan alkairi da zaman lafiya da zuri'a mai albarka kamar saura, an ɗaura aure ne kawai sai zuwa wani satin insha ALLAHU za'ai biki duk da mu hakan dai yazo mana a ƙure amma ALLAH muka riƙe mun san kuma bazai bamu kunya ba....”
“Tofa bazawara ce kenan?”.
Cewar Umma a gatsine. Murmushi Abba yay da kafeta da idanu, sai kuma ya janye yana jinjina kansa. “Yarinya ce budurwa ba bazawara ba, ɗiya ce ga Alhaji Isma'il Ibrahim Jiƙamshi, sannan jika ga Alhaji Sufi Ado Garko”.
Kusan duk falon musamman matan babu wanda bai zabura da jin sunayen guda biyu ba. Dan daga Alhaji Isma'il Jiƙamshi har Alhaji Sufi Garko babu sunan da bai zama mai shura ba a cikin Kano da wajenta musamman ma shi Alhaji Sufi Garko ɗin. Ƙwarai da gaske sun girgiza har mazan a yanzu dan suma dai basu san kuma amaryar tanada alaƙa da Alhaji Sufi Garko ɗin ba sai yanzu. No wander dole gwamna yay walicci kam ashe. Ƙus-ƙus ɗin da falon ya ɗauka ne ya saka Abba yin gyaran murya, a take duk sukai tsit. Abba ya cigaba da faɗin, “Kamar yanda na faɗa muku sati mai zuwa za'ai biki amarya ta tare, sai kowa yaje kamar yanda tsarin wannan gida yeke kowa ya kawo gudunmawarsa, a kuma kasance cikin shirin biki.”
“To amma yanzu Abbansu a sati guda ɗin nan har wane shiri za'ayi? Bayan kowa yasan Hydar bai ajeba bai ba ma wani ajiya ba. Gashi ya kinkimo ƴar babban gida da su komai sunfi buƙatar ganin dozin”. Mama ce da wannan magana itama dai da alama ranta a jagule yake, dan fa jin Smart ya samo ƴar babban gida ransu fal kishi da hassadar ba ƴaƴansu bane.
Caraf Umma ta amshe da faɗin, “Kema kike ta wannan ai ga zancen gudunmawa da yaywa yaran nan. Maganar gaskiya ba'ace gudunmawa ba kuma a irin wannan ƙurarren lokacin Abban su. Yanda abubuwa sukaima mutane yawa kowa na fama da kansa da iyalinsa, shi Hydar ɗin yasan bai shirya ma auren ba ya kinkimo ƴar masu hannu da shuni shi ba sana'a ba ba komai ba. inba dai sune zasu masa komai ba dan da'alama ma sadakin sune suka biya masa ko?”.
Kallonsu kawai Abba yake yi, su kansu kuma a cikin yaran duk sai sukaji kunyar abinda iyayen nasu keyi kamar wasu ƙananun yara sun kasa ɓoye baƙin cikinsu. Abba ya maida kallonsa ga Ammah da tunda ta shigo kanta a ƙasa yake baiwar ALLAH. Ajiyar zuciya ya sauke da sake maida idonsa kansu Mama ɗin. “Yalwati da Yahanasu nasan dai kun san da Aliy da yaran nan duk nawa ne ko? Kuma ni ne na bada umarnin haɗo gudunmawa kamar yanda nake basu akan kowacce hidima anan gidan tunda ba yau na fara ba. A kaf ɗinsu kuma ba gori ba babu wanda Aliy bai taka rawar gani a hidimar aurensa ba a bashi da aikin yin dai. Maganar kuma sati guda yay kaɗan ba'a shirya ba wannan komai na ALLAH ne babu ruwanku. Sannan sadaki ga ƴaƴanku nan ku tambayesu a duka aurensu ni ne na biya musu sadaki, ko akan Aliy ne zan canja abinda nake tun farko?. Ƴar babban gida kuma data tsole muku ido ALLAH ne ya bashi kasancewarsa mai ƙyaƙyƙyawar zuciya da nagarta, fatanmu ALLAH ya taya shi riƙo dan shi bai auri ƴarsu dan kuɗinsu ko sunansu ba”.
Sosai murtanin Abban ya hana kowa sake yin motsin kirki. Sai ma a cikin yaran ne maza jikin wasu yay