Showing 54001 words to 57000 words out of 124209 words
ba. Bayan sallar la'asar gaba ɗaya kuma sai zaman gidan ya gunduresa. Hakan ya sashi miƙewa ya kimtsa. Yayi ƙyau cikin ƙanan kayan duk da shi bawai ya saka don kwalliya bane ba. Ƙamshin turarensa yake mai sanyi da sakama zuciya nutsuwa. Sai da ya fito ya fara tunanin inama ya dace ya nufa? Duk da har yanzu yana jin jikinsa babu kuzari sosai. Rashin mafitar ina ya kamata ya nufa ya sashi kallon agogo, yasan yanzu bata tashi aiki ba, bara ya gwada zuwa idan ta huce sai ya maidata gida kawai, yafi ya tafi yawo mara dalili. Napep ya tare ya shiga.
Zuwa yanzu gaba ɗaya yanayinta ya sake birkucewa, ta zame ribbon ɗin data ɗaure dogon gashinta da ya sauka har kafaɗarta. Sosai idanunta sunyi jazur haɗe da kumburowa. Surutai take ita kaɗai da gaba ɗayansu na bege ne ga mahaifiyarta. Sai kuma zagin mijin matar nan da yay fyaɗe tare da ɗaukawa kanta alƙawarin koya masa hankali da duk ire-irensa. Hawaye take da murmushi a lokaci ɗaya, yayinda ta ƙurama hoton mahaifiyarta da ta ɗakko saman decks ɗinta dake a cikin wani ɗan ƙyaƙyƙyawan fram ita da Daddynta, hoton anyisa ne bayan aurensu a ƙasar Mexico lokacin sunje honeymoon. Su dukansu suna sanye ne a cikin ƙanan kaya suna kallon juna da murmushi mai nuna tsantsar soyayya da sukema juna. Hannunta ta kai ta shafa fuskokinsu, sai kuma ta rungume hoton tana mai komawa kwance rigingine ta ƙurama p.o.p ɗin office ɗin ido. Ƙwayar tata ce ta fara gaya mata shirme ga mahaifiyarta a wajen cikin farin tufafi tana mata kallo mai kama da tausayi.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣2️⃣
........Motar taima key ta cigaba da tafiya duk da ta fara jin kanta ya ɗauka. Da ƙyar ta iya kai kanta office saboda abinda tasha ɗin ya fara aikinsa. A yanda ta shiga duk da bawai tana layi bane yasa mutane da yawa ɗan binta da kallo. Office kawai ta faɗa tare da maidashi ta rufe harda saka key. Tai jifa da handbag ɗinta da key da takalma har ma da mayafi da ɗan kwali. Zama tai jikin kujera ta dunƙule jikinta waje guda tana mai tura kanta data dafe da duka hannu biyu tsakanin ƙafafunta. Surutai takeyi ƙasa-ƙasa irin wanda idan ba kusa da ita kake sosai ba bazaka taɓa iya fahimta ba...
_(Kai jama'a shaye-shaye baiyi ba. Shaye-shaye kan zubar da mutuncinka kowane matsayi ka taka. Yana maidaka baya komai ƙarfin ikon ka. Yana ƙasƙantar da kai komai darajarka. Ga lafiyarka kaima da ɓarnar kuɗi. Miyasa ƴan uwa? Mike birgemu? Mike ruɗarmu?. Kuɗi? Ƙawaye? Abokai? Samari? Gata? Kokuwa son zuciya?. Idan duk sune mu tabbata masu ƙarewa ne kamar ba'ai ba. Masu zama labarine kamar basu zo ba. Shaye-shaye wafce mana dukkan muhimman damammaki yake na cigaban rayuwarmu ta duniya da lahira. Kuduba ku gani, duk shekaru irin na Mawaddat bama tasan minene addininta ba, duk da tarin damammakin rayuwa da ALLAH ya bata wannan illar ɗaya take ta shaye-shaye da ke tare da rayuwarta na ƙoƙarin maidata baya. Tun tana ganin tana kiyayewa akan aikinta gashi ta fara kuma a cikin lokacin aikin, mi kuke tunani? Wataran aikin ma sai ta gagara yinsa gaba ɗaya. Da ga sanda ta rasa wannan damar kuma shike nan ta ƙarasa rushewar baki ɗaya sai jiran ta fara bin bola kuma duk da gatan ta😭. ALLAH ka shiryemu ka shiryar mana da zuri'armu da duk masu wannan mummunar ɗabia)._
★★.....
Bayan sallar la'asar Daddy da Uncle Yousuf suma suka shiga jerin ƴan sannu da zuwa ga Alhaji Sufi Garko. Ya nuna farin cikin ganinsu. Dan mutum ne da ya san mutuntawa. Kallo yake musu suma irin na ƴaƴa tun kan aurattayya ta shiga tsakanin ɗiyarsa da Daddy balle yanzu ga Mawaddat ta ratsa duk da babu ɗiyar tasa data zama sanadi a duniya. A hirarsu ne ma suke jin cewar Mawaddat ce ta ɗakkosa da ga airport, yana ƙyautata zaton ma har yanzu tana a gidan tare da ƴan uwanta. Daddy yaji daɗin hakan har Uncle Yousuf ma kansa. Basu nemeta bata suka cigaba da hirarsu hankali kwance. Shigowar Alhaji Sulaiman (mahaifin Tajuddeen) ce ta saka Daddy yin shiru, sai kuma ya dubi Alh. Sufi Garko da suke kira da Baba cikin girmamawa ya ce, “Baba inaga bara mu wuce ALLAH ya ƙara lafiya yasa kaffara ne”.
Alh. Sufi ya tsatstsare Daddy da idanu batare da ya amsa ba, sai kuma ya maida dubansa ga ɗansa Alh. Sulaiman da ya koma can gefe zai zauna. Cikin bada umarni ya ce, “Isma'il koma ka zauna”. Babu musu Daddy ya koma ya zauna ɗin. Ya maida dubansa ga Alh. Sulaiman da faɗin, “Kaima zonan”. Gaba ɗayansu a gabansa sukaje suka zauna kowa na hararar ɗan uwansa kamar wasu ƙananan yara.
“Ku yanzu kuna ganin wannan rayuwar bazaku ajiyeta ba. Ko a tinaninku har yanzu ku yarane? Ku duba gashin kawunanku furfura duk ta gitta a ciki. Tunda kun gagara faɗamin matsalarku a tsahon shekarun nan ni bazan cigaba da damuwa da sai na sani ba. Sai dai ku sani idan har abinda ya shafeku kuka bari ya shafi zuri'arku bazan yafe ba. Ku shaida hakan ko bayan ƙasa ta rufe idanuna ne”.
(Anzo wajen) cewar Alh. Sulaiman a zuciya. Dan haka ya gyara zama cike da makirci ya sake raunana muryarsa. “Baba ni ba laifina bane, tunda kowa shaidane na biyo hanyar da zamu sasanta da shi a shekarun baya amma ya koma bayan fage ya zuge yarinya komai ya sake rushewa. Shine ya sakama ransa ni maƙiyinsa ne kawai. Shiyyasa naso haɗin auren Tajuddeen da Mawaddat dan ya tabbatar ba hakan bane ba. Kuma ko a yanzu in har zai amince ya cire komai a ransa ni a shirye nake komai ya zama labari. Mu kuma dunƙule ƴaƴanmu waje guda matsayin ma'aurata dan ƙara danƙon zumincinmu”.
Wani irin kallon ɓacin rai Daddy ke masa. Sai dai baice komai ba. Alh. Sulaiman da ke masa kallon ƙasa-ƙasa ya saki wani irin makirin murmushi da kashe masa ido ɗaya. Ƙara tunzura zuciyar Daddy tai amma sai ya danne dan jin Baba ya fara faɗin, “Ni kaina zanso wannan haɗin zumincin, zan kuma so ya zama sanadin canja wannan gabar taku. Sai dai kuma bazan so ya rikiɗe daga manufarmu ya koma abinda bashi muke fata ba zumincin ya taɓarɓare ma fiye da yanzu....”
“Amma Baba ai yaran suna matuƙar son junansu. Dama tun farko matsalarmu ce ta tilastasu haƙura a wancan karon ma”. Alh. Sulaiman ya faɗa yana sake sakin makirin murmushi. Baba da ba ganin abinda ke faruwa yake ba ya kai dubansa ga Daddy da baice komai ba. “Isma'il bakace komai ba. Abinda ɗan uwanka ke faɗa gaskiya ne?”.
Murmushin mugunta Daddy dake ƙulla murtanin da zai maida ga Alh. Sulaiman ya saki. Cike da sake girmamawa ga surukin nasa kuma ogansa ya jinjina kansa. “Baba duk ina saurarensa. Sai dai na tafi wani tunani ne, kenan Mawaddat ƙarya tamun ko kuwa rashin jin nata ne ya sata kawo min wani a matsayin miji alhalin suna tare da Tajuddeen har yanzu...”
“Miji?”.
Alh. Sulaiman ya faɗa kamar a ɗan razane. Shiko Baba murmushi yayi da faɗin “Miji Mawaddat ɗin ta fitar?”.
“Eh Baba. Dan dama dawowarka muke zaman jira muzo maka da batun. Saboda yanata ma damuwar turo magabatansa amma ina dakatarwa da cewar har sai ka dawo tukunna”.
“Wlhy ƙarya kake Isma'il! Wannan makirci ne ka ƙulla dan kar Mawaddat ta auri Tajuddeen, an gaya maka tsoronka nakeji wai ne da na gagara ɗaukar mataki a kanka tun a baya”. Alh. Sulaiman ya faɗa yana miƙewa zumbur. Gaba ɗaya falon suka zuba masa ido. Sai kuma duk ya daburce dan fahimtar yana neman yin ɓaran ɓarama fa.
“Ka ɗauki mataki a kansa! A wane dalili Sulaiman?”. Baba ya katse shirun. Kame-kame Alh. Sulaiman ya fara, hakan ya bama Daddy damar sakin murmushin mugunta. Sai kuma ya dubi Baba. “Baba ƙyalesa kawai shirmensa ne. Kasan shi Sulaiman idan ya fusata akan abu baida fahimta. Sannan ya iya sakin duk maganar da tazo masa a baki koda ba hakan bane a ransa. Ni dai ba ƙin haɗin auren Mawaddat da Tajuddeen nake ba. Kawai shashancin da tayi ne na kawo min wani matsayin miji da har na sanar da nawa dangin dama jiranka kawai muke ka dawo a tsaida biki alhalin tana tare da Tajuddeen kuma ne yasa ma harna faɗa. Amma ayi haƙuri ni zanje ga babanta Yousuf mu sameta a nutse na mata tambayoyi dan nasan halinta bajin magana take ba. Kaga idan Tajuddeen take so ni bazan hana ba, sai nasan dabarar yi wancan ya janye a rabu lafiya mutuncin kowa bai zube ba....”
“Mizai hana w kirata yanzu ayita ta ƙare”.
Cewar Alh. Sulaiman. Shiru kamar Baba bazaice komai ba. Sai kuma ya nisa a hankali da faɗin, “Ku dukanku kunzo da shawara mai ƙyau kuma duk na gamsu da maganarku. Sai dai muyi haƙurin goben sai a zauna a nutse kan maganar. Amma yanzu ina son a kiramin Mawaddat da Tajuddeen”.
Sosai hankalin Daddy ya tashi, amma ya danne a ransa yana mai addu'ar ALLAH yasa kada Mawaddat ta watsa masa ƙasa a ido. Dan shifa bazai taɓa yarda ya haɗa zuri'a da Sulaiman ba. Shi kansa Uncle Yousuf zancen Yayan nasa ya sakashi a ruɗani. Duk da yasan akwai ƴar tsamar da har yanzu bai san tushen ta ba tsakanin ɗan uwan nasa da Alh. Sulaiman bai san dalilinsa na ambaton wani ba matsayin Mawaddat ta kawo bayan yasan ba hakan bane ba. Kusan a tare suka saki ajiyar zuciya shi da Daddy lokacin da ɗan aiken ya dawo ya tabbatar musu ai Mawaddat ance ta tafi tunma ɗazun. Alh. Sulaiman kuwa bai so haka ba. Amma baice komai ba, sai dai a ransa yana ƙudurta duk Daddy yayi ya gama a wannan karon sai Mawaddat ta zama matar Tajuddeen.....
😂Anayi muna cin tuwon masara miyar kuka🤪.
★★..★★
Yau gaba ɗaya a gida ya yini saboda tun daren jiya Uncle Yousuf ya ce masa karfa ya fito aiki yau ɗin ya bari har sai yaji ƙarfin jikinsa. Hakan ya saka shi yin zamansa tunda dama sunyi faɗa da ogar tasa. Ɓoye kansa yay a ɗaki ya sha barci, hakan yasa babu wanda yasan yana gidan ballema ya tuhumesa tunda bai sanar musu abinda ya samesa ba. Bayan sallar la'asar gaba ɗaya kuma sai zaman gidan ya gunduresa. Hakan ya sashi miƙewa ya kimtsa. Yayi ƙyau cikin ƙanan kayan duk da shi bawai ya saka don kwalliya bane ba. Ƙamshin turarensa yake mai sanyi da sakama zuciya nutsuwa. Sai da ya fito ya fara tunanin inama ya dace ya nufa? Duk da har yanzu yana jin jikinsa babu kuzari sosai. Rashin mafitar ina ya kamata ya nufa ya sashi kallon agogo, yasan yanzu bata tashi aiki ba, bara ya gwada zuwa idan ta huce sai ya maidata gida kawai, yafi ya tafi yawo mara dalili. Napep ya tare ya shiga.
Zuwa yanzu gaba ɗaya yanayinta ya sake birkucewa, ta zame ribbon ɗin data ɗaure dogon gashinta da ya sauka har kafaɗarta. Sosai idanunta sunyi jazur haɗe da kumburowa. Surutai take ita kaɗai da gaba ɗayansu na bege ne ga mahaifiyarta. Sai kuma zagin mijin matar nan da yay fyaɗe tare da ɗaukawa kanta alƙawarin koya masa hankali da duk ire-irensa. Hawaye take da murmushi a lokaci ɗaya, yayinda ta ƙurama hoton mahaifiyarta da ta ɗakko saman decks ɗinta dake a cikin wani ɗan ƙyaƙyƙyawan fram ita da Daddynta, hoton anyisa ne bayan aurensu a ƙasar Mexico lokacin sunje honeymoon. Su dukansu suna sanye ne a cikin ƙanan kaya suna kallon juna da murmushi mai nuna tsantsar soyayya da sukema juna. Hannunta ta kai ta shafa fuskokinsu, sai kuma ta rungume hoton tana mai komawa kwance rigingine ta ƙurama p.o.p ɗin office ɗin ido. Ƙwayar tata ce ta fara gaya mata shirme ga mahaifiyarta a wajen cikin farin tufafi tana mata kallo mai kama da tausayi.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏
_*
[9/11, 1:35 PM] +234 913 709 3201: 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣3️⃣
.......Bai san ainahin Office ɗin nata ba, sai dai ganin motarta a harabar wajen ya sake tabbatar masa da tananan bata wuce ba. Tunanin zaman jiran fitowarta yayi, hakan ya sashi samun wajen zama a gurin securitys. Bayan gaisuwa a tsakaninsu bai sake kula kowa ba ya shiga sana'ar tasa ta game ɗin ball a waya. Biyar dai-dai babu alamar zata fito, tun yana ɗan ɗagowa ko zai hangota har ya fara sarewa ganin biyar da rabi har ta gota ma. Ga mafi yawan ma'aikata sun wuce dan motarta da wasu biyu ne kawai suka rage a harabar wajen. Ɗaya da ga cikin security ɗin ne ya dubesa tare da faɗin, “Abokina wanda kake jira har yanzu bai ƙaraso bane? Dan shida dai-dai ake rufe wajen nan fa”.
Wayar ya ajiye tare da ɗagowa ya dubi security ɗin fuskarsa a ɗan sake, sai dai ba murmushi yake ba. “Wadda nake jira tana ciki dan ga motarta nan, nima ina tunanin ko lafiya har iyanzu bata fito ba”.
“Kana nufin Madam Mawaddat Jiƙamshi?”.
Kai ya jinjina masa alamar ita. Shima security ɗin cikin nuna jimami ya ce, “Inaga dai yau aiki ne yay mata yawa gaskiya, dan a kullum zakaga idan bata zama ta farkon tashi ba to zata zama ta biyu. Nima kaina nayi mamakin rashin fitowar tata yau duk da dai naga wani aiki tasa a gaba kwana biyun nan mai muhimmanci. Amma bari na duba maka maybe bata san kana zaman jiranta bane”.
Kafin Smart ya samu damar cewa wani abu security ɗin yay gaba. Minti kusan uku sai gashi ya dawo. “Abokina inagafa kamar akwai matsala”.
“Matsala kuma? Tami fa?”. Smart ya faɗa ƙirjinsa na bugawa da sauri-sauri. Amma sai ya dake abinsa kamar babu komai. Security ɗin ya cigaba da faɗin, “Bawai matsalar bace a zahirance, na samu sakatariyarta ce kawai zaune cikin damuwar wai tun ɗazun data fita ta dawo ta shige office ta rufe kanta har yanzu bata fito ba. Ta mata knocking kuma yafi sau ashirin batako ji motsinta ba sai yanzu babu jimawa taji maganarta kamar cikin surutai”.
Ƙirjinsa ne yaji ya ƙara bugawa, ya kai yatsunsa biyu saman goshi ya ɗan murza. Basai ya nema ƙarin bayani ba yasan wani abu tasha. Sai dai bai taɓa tunanin har a wajen aikinta ma tana shan abubuwan nan ba. Ɗagowa yay idanunsa har sun kaɗa da ɓacin rai. “Kozan iya shiga office ɗin nata?”. Ya tambayi security ɗin.
“Ah eh mana mizai hana. Ai gara a je a duba mike faruwa ko?”.
Miƙewa kawai yay, security ɗin yay masa jagora har office ɗin. Sun samu sakatariyarta tsaye jikin ƙofar tana knocking da faman kiran “Aunty! Aunty Please ki buɗe ko kiyi magana dan ALLAH.”
“Kinga ƙyaleta idan da key bani”. Ya faɗa cikin dakewa. Cikar kamala da kwarjininsa yasa Zainab jin bazata iya musa masa ba. Duk da kuwa yau ne karo na farko data taɓa ganinsa anan ɗin. Sai kuma ganin harda security ya ƙara mata ƙarfin gwiwa. Muryarta a sanyaye ta ce, “Sai dai na duba ko zanga extra keys dan ta shiga da key ɗin ciki”. Kansa kawai ya jinjina mata, ta koma wajen table ɗinta domin bincikawa. Shi kuma ya jingina da bango tare da harɗe hannayensa a ƙirji ya lumshe idanunsa. Kusan mintina huɗu tana ta binci-bincike har dai ta samo keys ɗin da ƙyar. Gabansa tazo ta miƙa masa cikin girmamawa.
“Thanks” yace a hankali yana amsa. Koda ya buɗe ƙofar bai yarda ita da security ɗin sun biyosa ba sai da ya leƙa. Saurin rumtse idanunsa yay tare da yo baya, cikin ɗan furzar da huci ya gyara yanayin fuskarsa yanda zasu fahimcesa. “Inaga bata da lafiya ne, kun san halin ogar taku kuma maybe bata buƙatar kowa ya sani shiyyasa taya rufe kanta a ciki, ku barni da ita kar ku samu rabon faɗa kuma”. A yanda yay maganar dole ne ka gamsu, dan haka security ɗin yay murmushi dan kuwa masifar Mawaddat kowa ya santa, idan sukai sanya wajen buɗe mata gate kota saka wani aikin kai mata wasa sai ta tsefeka tas. Balle ma Zainab da tafi kowa sanin wacece uwargijiyar tata. Sallama security yay ya fita, Zainab kuma ta koma mazauninta ta zauna duk da ya kamata ace ta tashi, amma dai tafi yarda taga sai Mawaddat ta fito lafiya sannan. Ƙofar ya sake turawa ya shiga ya maida ya rufe tare da jingina jikinta kansa a ƙasa bai yarda ya sake kalloba. Kamata yay ya kira Zainab, sai dai baya son ta ganta a yanayin. Har yanzu tana kwance a tsakkiyar sofas ɗin da aka shirya dan zama bayan ta zamanta da wanda ke a gaban table ɗin nata. Ta ture Centre table ɗin tsakkiyar kujerun tana kan carpet ɗin gashinta yaɗan barbaje. Har yanzu idanunta na kallon p.o.p