Showing 36001 words to 39000 words out of 124209 words
na samu zata fita shine na bita”.
“Ya Arrahaman harma ta sha kenan?”. Uncle Yousuf ya faɗa cikin matsanancin damuwa.
Tausayi sosai ya bama Smart, ya ɗan cije lips da faɗin, tana buƙatar saka ido sosai dan koba wannan halayyar bai dace ace mace kamarta tana fitar dare ba haka Alhaji”.
“Gaskiya ka faɗa Aliyu, na kuma gode sosai da ƙoƙarinka, duk laifin na yaya ne da bazai iya tsawata mata ba a duk sanda yaga zatai fitar, amma inasha ALLAH zan ɗauki mataki ni da kaina. Sai dai abin damuwar nima ɗin wani lokacin bana nan tunda ina tafiye-tafiye, da zaka min alfarmar dawowa kusa da mu da naso haka Aliyu, wlhy na yarda da kai, ina jinka tamkar ɗan uwana na jini, zan iya bar maka amanar Mawaddat batare da jin ko ɗar ba a zuciyata....”
“Nagode sosai da wannan karamci Alhaji. Sai dai maganar dawowa nan kam abun ne mai wahala gareni, dan Abba ma bazai yarda ba balle kuma Ammah. Sannan nima inada ƙanne, kuma suna buƙatar saka ido duk da dai ba wayona ke tsaremin su ba ko jajircewa. ALLAH ne gafurin rahimun”.
Duk da Uncle Yousuf ya gamsu da bayanin nasa amma bai so hakan ba. Dan yana matuƙar buƙatarsa tare da su. Yaron nada wata nagarta mai matuƙar ƙayatarwa. Ga nutsuwa da cikar kamala tamkar ba talaka ba. Godiya yay masa tare da fiddo Lulu da ke sharɓan tana ɗan surutanta jefi-jefi a cikin barcin, wanda ba komai bane sai zagin Hon. Baita. Shi dai sallama yay masa zai wuce. Dakatar da shi yay da faɗin, “Kaga dare yayi yanzun. Kaje da motar gida dan abin hawa zai iya maka wahala”.
Kamar zai ce a'a sai kuma ya tuna maganar Uncle Yousuf ɗin gaskiya ce. Dan haka ya gyaɗa kansa tare da godiya. Saida ya ga ya shige ciki sannan shima ya shiga motar ya tayar ya bar gidan. Mubarak kawai ya samu a waje alamar dai shi ake jira, cikin washe baki Mubarak ɗin ya taso yana masa sannu da zuwa da shafa motar har ya kasheta ya fito yana lucking. “Yaya ka sayi mota ne?”. Mubarak ɗin ya faɗa cikin zumuɗi. Karan farko yayma yaron ɗan murmushi. Cikin deep voice ɗin nan tashi da ta gaurayu da gajiyar son yin barci ya ce, “Daga ganin sarkin fawa sai miya tai zaƙi Mubarak? Ta mutane ce”. Kamar an zarema Mubarak lakar jiki ya ɗan rausayar masa da kai gefe kawai. Daga haka suka shige ciki gidan shiru alamar duk anyi barci, sai wasu a ƴammatan dake waya da samarinsu, idan ka cire Asma'u da Maryam dako wayar Yayansu yama hanasu riƙewa sai ta Ammah suke ɗan ɗauka. Ɗaki kawai ya shige dan kwanciya yake matuƙar buƙata.......
★★★ ∆∆ ★★★
Da asuba Uncle Yousuf da kansa ya shiga ɗakin aunty Saliha da ya kai Lulu dan ita a ɗakinsa ta kwana ya tadata yin salla. Sam bata da nauyin barci, damma yau akwai na maye tare da ita, da alama kuma ya bugar da ita da yawa, dan ma tana da jini mai ƙarfi, da ace tana da saurin buguwa ma abubuwan da MM Atik Kumo ya harmutsa mata zata iya ƙara shanye yinin yau bata san inda kanta yake ba. Amma sai gashi Alhamdullah ita da sauƙi ya saketa. Zata fara masa gardama ya daka mata tsawa. A firgice ta tashi zaune zumbur jin Muryar Uncle Yousuf tana mazurai. Sosai take zazzaro idanun mamaki, shiko ya watsa mata harara da faɗin, “Karna dawo Massalaci na tadda baki tashi kinyi salla ba, zan matuƙar ɓata miki rai”. Kai kawai ta gyaɗa masa mamaki fal ranta akan ganinta nan ɗin. Sai kuma abinda ya faru a daren jiya ya shiga dawo mata ɗaya bayan ɗaya. Cikin wani irin takaici da jin ƙuna a rai ta dafe kanta tana jan tsaki. A fili ta furta, “Sai nayi maganinka wlhy, illiterate kawai ko wa yace ya kawoni nan? To wai ubanwa ma ya nuna masa can ɗin da har ya bini?” Anya mutumin nan baida iskoki bisa kai ko? To inba mai iskoki ba itako mizata kirashi? A jiya dai tasan ya tashi a aiki ai da wuri ma. Amma kuma sai gashi ta gansa a inda babu wani mahaluki da yasan zataje. Kai wannan lamari da mamaki, dole ne tasan yanda ma akai ya bita can, kuma sai ta koya masa hankali akan shiga abinda bai shafesa ba. Nadiya ma sai ta shuka mata rashin mutuncin da bazata taɓa mantawa da shi ba da ga ita har su Hon. Baita ɗin. Jin ana neman idar da salla ya sata sauka a gadon dan tasan Uncle Yousuf babu wasa ne, ba ruwansa rufe ido zaiyi yaci mata uwa babu ruwansa da shirin da sukeyi. Wanka ta farayi sannan ta ɗauro towel Dan tana so ta sake wattsakewa. Batako zaman jiran tsanewar jikinta ba ta zura abayar Aunty Saliha. Sallar tai babu wani nutsuwar a cikinta, tana zaune a inda ta idar tana kulla mai fishseta Uncle Yousuf ya leƙo, gaidashi tayi, sama-sama ya amsa mata duk da yaga yanda ta koma kalar tausayi. Ba yanzu ya shirya mata magana ba dan haka yay ficewarsa. Ji Lulu tai gaba ɗaya hankalinta ya gama tashi, sam bata ƙaunar fushin Uncle You a rayuwarta, har gara ma Daddy yay fushi da ita dan shi tasan abu ɗaya zata masa ya rikice ya dawo lallaɓata. Kuka take so tayi, sai dai ita mai juriya ce da shegen taurin kai, ba a komai take iya kuka ba komai ƙololuwar ɓacin rai ko tashin hankali da zata tsinta kanta a ciki. A karan farko taji kunyar haɗuwa da mutanen gidan, tashi tai jikinta duk babu ƙarfi, bata ko nemi jakarta da takalminta ba ta fice cikin sanɗa, taji daɗin rashin samun kowa kuwa, da sauri tabi ta ƙofar kitchen ta baya. Tunda ta fito bayin fulawoyi ke mata kallon mamaki da ga nesa, dan shi dai bai san sanda tazo gidan ba kam, ƴar tsawar da tai masa ta sakashi dawowa a hayyacinsa. “Wawa mi kake kallo ne? Dilla buɗe min ƙofa!!”. Jikinsa har kakkarwa yake duk da kuwa a girme ma zai iya girmarta shima, kuma ba aikinsa bane, ta watsa masa harara lokacin da take ficewa tare da jan tsaki. Yasan laifinsa dan haka ma baiji haushi ba. Mawaddat ta tsani taga ana kallonta, gashi kuma yau shi ta kamasa dumu-dumu. Ya san dai bala'i bai ƙare ba, dan duk randa ta dawo gidan zai sha masifa. Ƙila ma harda zagin ƙare dangi za'a haɗa masa.
Da ƙafa ta isa gida, kasancewar garin da sauran duhu ga ɗan sanyi-sanyin da aka fara na lokacinsa. Acan ma sai da maigadinsu ya samu rabonsa na zagi. Dan shima dai galala yay yana mata kallon mamaki. Amma tunda ta fara danna masa na maguzawa sai ya nutsu ya koma gaisheta a daburce. Bata amsa ba tai shigewarta tana jan tsaki..........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
[9/4, 7:59 PM] +234 813 876 4648: 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣3️⃣
.........“Waya aike ka inda ka sameni jiya? Miye ma dalilinka na bina?”.
Idanu ya lumshe tare da buɗewa a lokaci guda. Kamar yanda yay magana ɗazun a tausashe yanzu ma haka yayi. “Baki so asan kina aikata abinda na gano ɗin ne?”.
“Kai ɗin banza da zanji ina son ɓoye maka abu. Shiga abinda ban saka ka bane ya sa nake neman ba'asi dan bana son shiga sharo. Idan kuma kace zaka cigaba da shiga min hanci wlhy zan saka ka dana sani kai da duk wanda ma yake maka kallon arziki. Tsabar kai ɗan haɗin masifa ne ka ɗauke ni ka kai gidan Uncle you.., wlhy kasan mima zaka faɗa masa, in ba haka ba sai naje har gidanku kaima na maka ƙullin da har gaban abada baka isa ka kwancesa ba ɗan sa ido kawai. Idan kuma kaji ƙarya mu zuba ni da kai mai shishshigin tsiya, kai a dole sai ka shiga jikin iyayena dan maular tsiya irin ta talaka”.
(Maula! Talaka!) Zuciyarsa ta maimaita cikin jin ƙunar kalmomin. Kamar zai yi magana sai kuma ya haɗiye abinsa dan ya fahimci al'amarinta na buƙatar sai da uzuri, idan yace zai biye mata sai ma su zama ɗaya. Yanda bata sake magana ba tana ta faman duba takardun nata shima bai sake kallon inda take ba, sai dai ƙamshin turaren data bulbula ya addabesa har yana hawar masa kai kamar yanda itama nashi ke cizon can ƙasan zuciyarta. A cikin tsare-tsaren da Uncle Yousuf ya bashi nata ya sashi sanin inda zasu je a yanzu ɗin, dan haka kai tsaye babbar kotun da muke kira da (kotun ALLAH ya isa) dake a jiha ya nufa. Tamkar ba safiya ba harabar court ɗin cike da mutane, hancin motar na kunna kai cikin gate ɗin wasu gungun ƴan jarida suka yomusu caa, isowar securitys da ke son hana ƴan jaridar isowa garesu ya ɗan maido hankalin mutane kan motar suma. Kafin ya gama kashe motar har an buɗe mata. Fuska a yamutse da ɗan jan tsoki ta kalla harabar court ɗin. Wanda ya buɗe matan ta miƙama tarkacen hanunta tare da rigarsu ta lauyoyi. Ita kuma ta ɗauki handbag ɗinta bayan ta toshe fuska da wani shegen gilashi mai tsananin ƙyau ta haɗa da hular, dai-dai tana ficewa ta balla masa harara da faɗin, “Saura nan ma kace zaka biyoni kaga yanda zan baka mamaki”.
Da kallo kawai ya bita, sai kuma ya ɗan furzar da iska ransa fal mamakin yanda bata gajiya da masifa. Da ga can ƙasan ransa kuma yanda ake ta bata wani girma da kariya da ga security ɗin da zallon da ƴan jarida ke faman yi na son isowa gareta ya ƙara ɗaure masa kai da jin takaicin da sun san wacece a zahirinta da ko kallon mutuntawa bata cancanta a garesu ba. Bai iya ɗauke idanunsa garesu ba dan takaici har suka shige wata ƙofa ba ainahin ta Court ɗin ba. A take ya ga gurin ya sake ribcaɓewa, mutane sai faman ɗura kai suke cikin court ɗin. Maganar wasu samari da ke wuce motar cikin ƙaucin shiga kotun ta ɗan ja hankalinsa. Na farko mai riƙe da camara ke faɗin, “Yaufa akwai ƙura, dan na tabbatar barrister Mawaddat Jiƙamshi ba ƙaramin sabon shiri tayo ba duba da yanda Barrister Marafa ya nema zubar da ita a wancan zaman. Kasan fa ita bata taɓa bari a kaita ƙasa musamman a kan irin wannan case ɗin na fyaɗe, ga shi tasan aikinta lawyers ƴan uwanta da yawa har tsoron karawa suke da ita, dan ita ko waye ma ubanka akan fyaɗe sai tayi kutu-kutun turaka jail dan haka kullum ita bata kare mai laifi sai wanda aka zalunta musamman ƴan uwanta mat.......”
Bai ƙarasa jin abinda saurayin ke son faɗa ba dan sun masa nisa. Da farko baiyi niyyar shiga wajen ba, sai dai saboda gargaɗinta ya ƙudiri shigar dan yaga mizata iya masan. Ƙoƙarin fitowa yay a motar kira ya shigo wayarsa. Kamar zai share sai kuma ya cirota da ga aljihu. Ƙanwarsa ce mai bimasa Hawwah dake auren abokinsa. Ɗagawa yay, sai dai yana kaiwa kunnesa yay saurin janye wayar yana mai lumshe idanunsa. Buɗesu yay a hankali zuciyarsa na wani irin zallo. Cikin motar ya koma tare da sake kiranta. Ringing ɗaya ta ɗauka. Cikin matsanancin kuka ta ke faɗin, “Yaya dan ALLAH ka barni na taho gida. Wlhy na gaji da wannan rayuwar bazan iya ba. Inko ba haka ba wataran sai mahaifiyar Abban Nasreen ta kasheni a gidan nan....”
Iska ya ɗan furzar mai ɗaci, tare da faɗin, “Miya kuma faruwa?”. Sake fashe masa tai da kuka, da ƙyar ta iya faɗin, “Mai fa da nake suya airish ma Nasreen da zata wuce school ta kusa kwaramin yau a jiki Yaya. Ban san wane irin rashin ƙauna matar nan take min ba. Wlhy bazata taɓa canja halinta ba nima na gaji da haƙuri da ita.”
“Shi ina Sa'id ɗin yake?”.
“Yaya yana fa a gidan, gashi can ya jata wai yana bata haƙuri saboda ni ba'a san ciwona ba. Yanzu Yaya data sameni da man nan haka zai tsallakeni ya bita ke nan....”
“Kinga ya isa. Ki jirani gani nan zuwa gidan yanzu”. Da ga haka ya yanke wayar batare da ya jira abinda zata ce ba. Fitowa yay a motar ya kulle. Da ƙafa ya fita a habar court ɗin da ta yi tsittt alamar an fara shari'ar ko za'a fara. Yana fitowa a gate ɗin ya samu napep zuwa Daurawa anguwar da gidan ƙanwar tasa take. Kasancewar safiya ce basu wani samu matsala ba, dan haka suka iso da wuri. Bayan ya biya mai napep ɗin maimakon shiga gidan kai tsaye ko yin knocking sai ya ɗaga waya yay kiran abokin nasa Sa'id Ibrahim da sukai karatu a jami'a tare. Yanda Sa'id ɗin ya ɗaga wayar ta isa tabbatar da a rikice yake. Dan duk ya daburce sallamar ma da in ina yayi ta. Sai kuma ya shiga kame-kamen gaisuwa. Katsesa Smart ɗin yay da faɗin, “Gani a ƙofar gidanka ka turo min Hawwah zamu wuce gida”.
“G...g...gida kuma Mawashi? Miya faru ka...k...kake wannan maganar haka? Ko itace ta kira ka ta faɗ......”
“Sa'id!!”.
Ya dakatar da shi a harzuƙe. Sake tsurewa Sa'id ɗin yayi dan yasan halin abokin nasa sarai. Bai da yawan magana ko hayaniya, dan bai taɓa ji ko ganin abokin faɗan Smart Mawashi ba a rayuwa. Amma shi kaifi ɗaya ne akan komai da kowa. Duk yanda yake da kai bai yarda ka latsashi ba ko gasu abokai. Yanda ya rikice ɗin sai ya harzuƙa ran mahaifiyarsa da ta hanashi fita duba matarsa. Dan ta rantse ko bakin ƙofa yaje domin Hawwah ɗin sai ta tsine masa. Cikin masifa ta wafce wayar, kunnenta ta kai da faɗin, “To ɗan mulkin mallaka wai shin nikam ko kai ne ka haifa min Sa'id ne ban sani ba? To bazai zo ɗin ba, nace bazai zo ba idan ka isa kai duk abinda kake jin zaka iyayi, ko ita ƙanwar taka autar mata ce da in ya rabu da ita zai kasa cigaba da rayuwa har ya auro wasu huɗun. Aikin wofi kawai anga kuɗi an nanema yaro na”.
Har tayi ta gama bai ce uffan ba, sai da yaji tayi shiru ya yanke kiran. Yanda yake huci zai baka tabbacin sanin ran ƴan maza ya kai ƙololuwar ɓaci. Number Hawwah yay kira, bugu ɗaya ta ɗaga. Kafin tace komai ya ce, “Ɗakko mayafinki ki sameni waje”. Ya yanke kiran. Minti shida kuwa bata gama cika ba sai ga Hawwah da ƙaton akwati da Nasreen ƴar shekara huɗu biye da ita. Tana ganinsa ta cilla da gudu garesa tana faɗin, “Oyoyo Uncle”. Kaɗan ya saki murmushi, tare da duƙawa ya ɗauketa ita da school bag ɗin da ke goye a bayanta alamar an gama mata shirin makaranta ne. Sau ɗaya ya kalla ƙanwar tasa ya kauda kansa. Batare da yace komai ba ya amshi akwatin hanunta yay gaba tabi bayansa. Napep ya tare musu suka shiga, Nasreen nata zuba masa surutu dan yarinyar ko akku haka ta ganta ta bari kamar ƴar ƙwa-ƙwa akwai wayon jaraba. Dan bakinta ya girmi shekarunta. Sai da ya kaisu har gida sai dai bai shiga ba yace taje ta jirasa zai je ya dawo. Bata musa ba ta fita, shi kuma yace ma mai napep ya juya da shi babban kotun dake jaha. Ya samu har an fito da ga shari'ar, yanda harabar kotun ke'a harmutse da ƙayataccen murmushin da ya hango a fuskar Lulu ya sashi tsira mata idanunsa. Tsaye take a tsakkiyar lauyoyi ƴan uwanta wanda da alama duk ƴan ɓangare ɗaya ne a shari'ar, dan yanda fuskokinsu ke a washe kamar ita saɓanin waɗanda ke gefensu kaɗan zai baka tabbacin hakan. Ƴan jaridar da suka zagayesu ya sashi daina iya hangota, ɗauke kansa yay tare da buɗe motar ya shiga, a kallo ɗaya zaka fahimci damuwar dake zagaye da fuskarsa, dan babu abinda ke faman masa kai kawo sai batun ƙanwarsa Hawwah, shi shaida ne Sa'id na matuƙar son Hawwah, sai dai matsalar mahaifiyarsa da tun farko ta nuna bata son auren saboda ƴar ƙanwarta da taso ya aura shi kuma yaƙi tsayawar mahaifinsa ta sa ta janye ta amince ya auri Hawwah, sai dai tunda take gidan mahaifiyar tasa ke nuna mata hantara da ƙyara musamman idan Alh. Ibrahim mahaifin Sa'id ɗin baya gari. Tasha marin Hawwah ɗin dayi mata abubuwa masu cin zuciya shi yana zuwa ya sasanta bada sanin iyayensu ba. Sai dai a wannan karon ya fahimci dole ne fa a tauna tsakkuwa dan aya taji tsoro. Dan tsohuwar na buƙatar sanin Hawwah nada gatan iyaye da dangi itama, sannan dukiya ba itace rayuwa ba kawai akwai muhimman abubuwa da suka fita a zamantakewar rayuwa. Kai dai kai fatan kawai ALLAH ya rufa maka asiri kafi ƙarfin yau da gobenka. Idan kuma ya azurtaka da dukiyar ka bida ita ta hanyar da kai a karan kanka zakai alfahari da kanka watarana da zaka amsa tambaya akan dukiyar kwabo bayan kwabo........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
[9/4, 7:59 PM] +234 813