Showing 78001 words to 81000 words out of 124209 words

Chapter 27 - FURAR DANKO PART 1

Unknown   

12 Nov 2024

8779

sanyi suka shiga bama Abban haƙuri, tare da masa alƙawarin yin zaman meeting na musamman akan bikin. Albarka ya saka musu tare da sallamar kowa. Smart ne kusan ƙarshen fita, dan haka Abba yace masa bayan sallar isha'i ya samesa. Kai kawai ya jinjina masa ya ƙarasa ficewa cikin dauriya.. Fitowar tasa ta bama wasu da ga cikin ƴan uwan nasa damar tayashi murnar da suka gagara yi a ɗazun. Murmushin kawai yake musu da amsawa cikin dauriya, da ga haka ya wuce ɗakin Ammah. Ya samu Aunty Bilkisu da ƙanwar Ammah da tazo gidan babu jimawa suna tattauna abinda su Ummar sukai yanzu a gaban Abba. Yayinda su Asma'u ke ta faman murnarsu sukam finally Yayansu yayi aure shima gorin Umma ya ƙare. Gaban Ammah yaje ya zauna, yayinda Gwaggo Sa'adah ƙamwar Ammahn ta muƙe tana masa ghuɗa da kirari kasancewar sunan mahaifinsu ne ya ci, dan duk ƴan gidan su Ammah Babangida suke kiranshi ko suce Hydar, shiyyasa ma ko'anan gidan nasu Hydar ɗin ta bisa, Abba ne kan kirashi da Aliy shima wani lokacin yakance masa Baba. Idanunsa ya rumtse da sauri dan har cikin tsakkiyar ƙwalwar kansa ghuɗar nan ke ratsashi. A take kansa ya fara juyawa ya ringa ganin kamar ɗakin na juya masa shima. Ɗayan hannunsa ya kai ya ƙara dafe kan da hannu biyu. Hawwah ce ta lura da hakan, da sauri ta ce, “Yaya Hydar lafiya kuwa?”. Yanda tai maganar cikin zaburowa ya sa Gwaggo Sa'adah dakatawa, Ammah ma ta haɗiye murmushin fuskarta ta maida dubanta garesa. Aunty Bilkisu ma da ke ta faman turama dangi saƙo ta wayar Ammah ta miƙe zumbur. Ammah da ke kusa da shi ce ta samu nasarar taroshi jikinta, dan gaba ɗayansa ya tafi zai zube damma a zaune yake......

________________★

    Ƙololuwar ɓacin rai Alh. Sulaiman ya shiga sakamakon kiransa da akai masa cewar ga Tajuddeen a asibiti sakamako auren Lulu da mahaifinsa ya ɗaura yau da shegen tsageran yaron nan da yakema kallon abin alhaki. Abu mafi ɗaure masa kai shine ta yaya Baban yasan da shirinsa har yaje ya ɓata masa shiri haka? Ya san dai da ga shi sai Tajuddeen suka ƙulla hakan. Dan ko mahaifiyar Tajuddeen ɗin bata san komai ba akai. To kodai cikin waɗanda ya aika sumasa waliccin auren ne? Kai bayajin hakan zata kasance ai. Dan Kawu Laminu mutum ne makwaɗaici yasan kuɗin da ya shaƙa masa bazai barsa buɗe baki ya faɗama wani ba. To ko Tajuddeen ɗinne yay ɓaranɓarama a gaban wani? Shima dai hakan bai kama hankali ba gaskiya dan yasan yanda Tajuddeen ke son auren nan bazai taɓa bari wani ya samu ƙofar rusa masa shi ba. Tattare komai yay ya ajiye gefe yabar maɓoyar tasa zuwa asibiti. Dan yazo nan ɗin ne ya ɓoye saboda Baba har sai ƙura ta lafa zuwa gobe kamar yanda ya tsara idan an ɗaura aure da Tajuddeen. Lokacin da ya isa ya samu Tajuddeen ko farfaɗowa baiyi ba ma. Ga shi labari yazo masa su baba na government house ana liyafar cin abinci bayan a gabansu Jikansa ya faɗi amma ya shure saboda bai ƙaunarsa shi da ɗansa. Sosai zuciyarsa ke ƙara tafasa, yayinda yake saƙa abubuwan alkaba'i da zai rusa rayuwar Smart da duk wanda ke tare da shi. Dan a ganinsa duk shine ya ruguza masa shirinsa, sai yanzu ma yake nadamar bayyana masa fuskarsa a waccan ranar... Farfaɗowar Tajuddeen babu jimawa mahaifiyarsa ta iso, sai dai daga zuri'arsu kaf babu wanda ya leƙo asibitin dan Baba ya hana. Ya kuma tabbatar musu duk wanda yaje sai ya ɓata masa rai fiye da yanda yake zato ko tsammani..........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

[9/18, 12:38 PM] +234 703 706 8372: 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣5️⃣



.......Shigowar Abba da Asma'u ta fita ta kira da sauran ƴan uwansa maza da basu kai ga fitaba yasa matan darewa. Tallafosa Abba yay da ga jikin Ammah da ke tofa masa addu'a a nutsenta, duk da a rikice take amma a zahirinta babu alamar ruɗewa dan mace ce kamila mai tarin nutsuwa akan komai. Faisal ne yay hikimar matso da fanka kusa da su yana faɗin, “Ku ɗan matsa a kansa yasha iska mugani”. Fita duk matan sukai a ɗakin, sai Ammah da su Umma da suka shigo. Aunty Amarya ta ce, “Ko dai a masa hayaƙin maganin nan dan yanayin nasa kamar na matsalar can ne da ke bugunsa”. Cikin gamsuwa Gwaggo Sa'adah ta ce, “A kawo ɗin sai a gwada a gani. Rushin wuta Hawwah ta ɗibo, Maryam ta ɗakko maganin a ɗakin Ammah aka saka masa, yayinda Ammah da Abba ke cigaba da tofa masa addu'a su da sauran ƴan mazan gidan. Kusan minti talatin ana abu ɗaya kafin ya fara motsawa. Sai kuma ya fara wata irin atishawa mai ƙarfin gaske. Yayi tafi sau bakwai sai kuma ya dafe kansa yana mai ambaton sunan ALLAH da faɗin, “Ammah kimin addu'a kaina kamar zai fashe. Wayyo Ammah kaina kimin addu'a”.
      Da ƙyar Ammah ta danne hawayen da suka cika mata idanu, ta kamo hanunsa cikin hannunta ɗayan kuma ta ɗaura a saman goshinsa da faɗin, “Kayi haƙuri Hydar gani nan kusa da kai ina maka addu'an in sha ALLAHU zai bari, kai dai cigaba da ambaton ALLAH”. Addu'a ya cigaba da yi a ransa, tare da sake kai hannunsa saman goshinsa ya ɗaura kan na Ammah data dafe masa... Cikin amincin ALLAH a haka aka samu barci mai nauyi ya ɗaukesa kusan gab da magrib. Abba ne ya saka ƴan mazan ɗaukarsa aka maida ɗakinsa dan zai fi samun ƙarancin hayaniya a can ɗin kasancewar nan akwai yara (jikokin gidan). Aunty Bilkisu da Hawwah ne sukaje can suka zauna da shi. Itama Ammah bayan ta idar da salla sai ta nufi ɗakin nasa da ruwan addu'oi da tayi a kofi ita da Gwaggo Sa'adah dan su Aunty balikin su samu suzo suyi salla suma......

        
         ★...........

    A gaban su Baba Mawaddat (Lulu) zaune bayan ta gaishe da Baba da tunda ta shigo yake Binta da kallo fuskarsa ƙawace da murmushi. Kusa da shi da ya nuna mata ta zauna takai zaune gab da ƙafafunsa. Kanta ya dafa yana mai saka mata albarka da addu'oin zaman lafiya da mijinta da zuri'a masu albarka. Saurarensa kawai take amma ba komai take fahimta ba a halin yanzu. Sai da Baba ya gama Addu'oinsa su Uncle Yousuf na amsawa da Amin sannan ya kirayi sunanta cike da kulawa. Amsa masa tai batare data ɗago ba. Bai damu ba ya cigaba da faɗin, “Mawaddat ƴar Mawaddat yau kema kin zama babba mai kima da darajar da aure kawai ke Bama kowacce ɗiya mace a duniya. Dan daga yau zuwa ko yaushe kema za'a iya kiranki da suna UWA. Alhamdullah kin kawo mana mijin aure a jiya kuma a jiyan babu sanya muka saka akai mana bincike a kansa muka kuma ɗaura muku aure a yau kasancewar rayuwarsa cike take da abubuwan birgewa daban sha'awa irin wanda duk wasu Iyaye na gari zasuji alfaharin kasancewarsa ɗan su ko suriki. Na tayaki murna matuƙa da mu kammu ma ahalinki. Ina fatan zaki zama mace tagari da shima tashi zuri'ar zatai alfahari da ke da tarbiyyar da muka baki. Ina sake tayaki murna da tsintar dami a kala. Dan irin waɗan nan nagartattun yaran kamar Aliyu tamkar tsintar dami ne a kalla musamman idan mukai la'akari da lalacewar zamanin yanzu da matasanmu suka saka baɗala ta shaye-shaye da neman mata a gaba fiye da cigaban rayuwarsu. Fatanmu ki kasance mai biyya da haƙuri, Mun kuma ɗaura aurenki ne a wannan gaɓar babu shiri sakamakon son kwantar da ƙurar da ke son tashi, fatanmu bazakiga laifinmu ba. Sannan munyi alƙawarin shirya miki biki kamar na sauran ƴan baya da akayi hakama iyayenki gasu nan a shirye suke da shirya biki domin farin cikinki next week a kaiki ɗakin mijinki kamar kowace ƴar gatan dangi. ALLAH yay muku albarka ya jiƙan mahaifiyarki da namu iyayen muma baki ɗaya”.
       Uncle Yousuf ne ya amsa da Amin shi da Uncle Khamil da Uncle Amin da suka rako Baba, sai Daddy da shima yake a falon. Uncle Khamil da Uncle Amin ma sun mata tasu nasihar. Ita dai batace komai ba saurarensu kawai take. Sai dai a ƙasan zuciyarta ayyanawa ta ke, (Grandpa kenan, kuma bar wahal da kanku ko ɓarnata kuɗinku auren wata ɗaya ne kacal. Biki kuma ko kiɗan ƙwarya babu mai mana a gidan nan). Babu wanda ya lura da halin da take ciki sai Uncle Yousuf da ke hankalce da yanda take ta faman taɓe baki duk da kanta a ƙasa yake. Dariya da tausayi ta bashi, amma sai ya kanne bai nuna ko ɗaya ba a ciki har akai zaman mata nasihar da ya san ba wai shigarta take ba suka miƙe. Rakkiya tama Baba har mota, hakan ya sake bashi tabbacin lallai tana matuƙar son wannan yaro. Sai hakan ya ƙara masa kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya dan abinda yafi fata kenan. Shi babu ruwansa da wai ɗansa ko jika sai sunyi auren ƙwarya tabi ƙwarya ɗin nan. Duk wanda kika kawo ko ka kawo iyakarsa dai yasa ai bincike. Inhar yaro ko yarinya sun fito da ga gidan tarbiyya kuma suma masu itane babu abinda ya shallesa zai bada goyon baya ya kuma sanya albarka a ciki. Hakan kuma na sake ɗaga darajarsa da kimarsa ga al'ummarsa.
       Bayan wucewarsu Lulu tai komawarta ciki babu alamun wata damuwar auren tattare da ita. Daddy dai mamakin hakan yake, yayinda shi Uncle Yousuf ya san bata ɗauki abin da muhimmanci bane saboda yace mata auren contract ne. Sannan fa dama Lulu a wasu lokutan shahararriyar ƴar I don't care ce ta bugawa a jarida duk da masifar nan tata.......
      “Ita ko damuwa ma batai ba”.
  Cewar Daddy cikin nuna mamaki yana kallon Uncle Yousuf. Ƙaramar dariya Uncle Yousuf ɗin yay da ɗage kafaɗu duka. Yace, “Nima abinda keban mamaki kenan”.
           “Amma auta baka tsoron ko wani abu take ƙullawa. Kasan fa wacece Mawaddat akan rashin ji”.
     Dariya Uncle Yousuf yayi da faɗin, “Kwantar da hankalinka babu abinda take shiryawa face sanin cewar auren na wucin gadi ne”.
         “Da wannan kuma”.
    Cewar Daddy cikin samun ƴar nutsuwa. Daga haka suka shige ciki dan ganawa da Mommy da yaran gidan suma duk da sudai duk sun san mike faruwa dan tun a jiya da dare Daddyn ya sanarma Mommy, Uncle Yousuf kuma ya sanarma ƴan biyu shiyyasa tunda safe suka iso Kano. Haka ma su Mubeen duk Mommy ta sanar musu a yau da safe. Sun sha matuƙar mamaki yanda auren yazo damma dai basu san dawa za'a ɗaura ɗin ba har ita Mommy ɗin sai da sukaje wajen ɗaurin auren ne suka sani, bayan sun dawo ɗinne sukai zaman jinjina al'amarin.
       Kallan kallo aka shigayi tsakanin Mommy da ƙannen Lulu jin wai da Smart drivern ta akai ɗaura mata aure yau. Karan farko Hussain yay murmushi har haƙoransa na bayyana bayan Mubeen ya gama basu labarin yanda take yaga Smart ɗin. Duk da ganin harar da Daddy ke masa bai iya haɗiye abinda ke bakinsa ba sai da yace, “Uncle You kuma itace tace tana son sa da kanta?”.
             Murmushi Uncle Yousuf ɗin yayi shima da faɗin, “Hussain ai matar mutum kabarinsa inji hausawa. Fatan alheri yanzu suke buƙata garemu baki ɗaya. Sannan kuma sai kuyi himmar naku auren dan zamanku haka ya ishemu. Dan haka na baku da ga nan zuwa ƙarshen shekara inba haka ba kuma mu koma Jiƙamshi a duba a cikin dangi ni babu ruwana”.
       Dariya Mubeen ya shiga tuntsurawa, su Amrah na tayashi ƙasa-ƙasa dan suna tsoron ta fita aci ƙaniyarsu. Da ga haka kuma aka cigaba da hira, ganin hirar na daɗi babu Lulu kuma Uncle Smart ya aika Suhaib yay kiranta. Koda ta fito taga har da su twins sai tai kamar zata koma. Sai dai kiran da Uncle Yousuf yay mata ya sata dole ƙarasawa. Kamo hanunta Mommy tai ta zaunar a kusa da ita tana murmushi. Ta ce, “Haba yarinyata miyasa zaki koma kuma?”.
        Kasancewarta ba mutum mai ɓoye-ɓoye ba ta ce, “Mommy to bakowan kesan ganina anan ɗin ba. Kinga babu amfanin na zauna ko”.
    Karan farko Mommy taji wani iri a ranta, dan yanda Lulu tai maganar cikin rashin sakewa zai tabbatar maka halin ko'in kula da ƴan uwan nata ke nuna mata yana cimata rai matuƙa musamman su manyan. Shi kansa Uncle Yousuf wani tunani ne ya fara zo masa a rai akan furucin nata. Daddy kuwa tuni fuskarsa ta nuna ɓacin rai, ya bi su Hassan ɗin da wani irin mugun kallo. Sai kuma ya miƙe tare da zuwa har gaban Mommy ya kama Hannun Lulu ga miƙar. “Tunda basu son ganinki sai suzo su kasheki ai Mawaddat, sannan su haɗa da ni nima” ya jata suka fice a falon. Babu wanda ya iya cewa komai sai Uncle Yousuf ne da ya kafe su Twins ɗin da kallo ya furzar da iska. “You see wannan shine abinda nake ta so ku fahimta tun ba yanzu ba. Amma sai kuka kasa fahimtar tawa saboda idonku ya rufe da cewar Yaya baya son ku sai Mawaddat. Anji shi kan kuskure yake, amma koyaya dai mahaifi sunansa. Amma ita minene laifinta tunda ba itace tace yay mata hakan ba tun bata san kanta ba. Sannan har yanzu Mawaddat bata san minene ya faru kafin haihuwarta ba, ta yaya zaku dinga hukuntata da laifin daba ita tayi ba. Duk da rashin jinta da ake gani a ranta tana matuƙar son kusanci da ku, sai dai rashin damar da kuke bata yasa ta zaɓi kaɗaice kanta bata da wani amini sai Yaya a gidan nan”.
        “Amma Uncle ai Mommy ta jata a jiki Daddy yay katanga ma hakan saboda yana ganin zata cutar masa da ƴar gwal”.  Hassan ya faɗa cikin ɓacin rai dan yanada zafi. Murmushi mai ciwo Uncle Yousuf yayi, “Yes Aunty Khareema ta jata Yaya yay ƙoƙarin hana hakan, amma ai ba Mawaddat bace ta ƙi aunty Khareema ko. Ku zauna kuyi nazari akan wannan matsalar kuma Kanada taku gudunmawar a ciki, sannan a yanzu na ƙara fahimtar a fanɗarewar Mawaddat harda dalilin ɗaukar kanta ware da kuke nuna mata. Ku manyanta ne, kun fita hankali da sanin ya kamata, ku kuma ajiye halin Yaya gefe ku zauna kuyi nazari akan duk abinda ke faruwa a tsakaninku da ita kuyi alƙalanci tun kafin kuzo kuyi nadama da ga baya”.  Da ga haka ya miƙe batare da jiran cewar kowa ba yay ficewarsa. Shiru falon kowa ya kasa cewa komai, dan hatta Mommy kalaman Uncle Yousuf ɗin sun shigeta. Sai take gani kamar itama tana da nata kamshon mai girma da bata taɓa zama wajen matsa musu canja abinda suke kallo ba yanda yake faruwa ba tunda Mawaddat dai ba ita yace Daddy yay mata irin wannan rikon ba, sannan yarinyar bata taɓa ƙin ƴan uwan nata ba, barta dai da tsiwarta sai kuma gatan da Daddyn ke nuna mata na fitar hankali sama da sauran yaran a komai na rayuwa.........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
[9/18, 12:38 PM] +234 703 706 8372: 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣6️⃣



.......Gaba ɗaya hankalinta a tashe yake, duk yanda take ta son dannewa hakan na neman gagara. Ga shi Kasancewar ƴaƴanta na nan ta rasa ta yanda zatai kiran aminiyar ta su tattauna wannan ruɗani da ke neman kaita ƙasa a yinin yau. Ganin hankalin duk jama'ar gidan ya koma kan halin da Smart ke a ciki ya sata sirarewa ta koma ɗaki. Can ƙuryar ɗakinta ta shige ta rufo. Takaicin yanda wayar keta ringing anƙi a ɗauka ya sata jin kamar ta kaima bango naushi. Sake kira na biyu tai bayan katsewar na farkon. Yanzu ma har ta fidda rai da za'a ɗaga ɗin, amma jin an ɗauka ya sata sakin wata wawuyar ajiyar zuciya. Cikin haushi da ƙosawa ta ce, “Haba Hajiya Naqiba ina kika shigane ke kuwa inata kiran waya..”
“Yi haƙuri ina falo ne da mutuniyarki, wai munafukan tazo tana faɗa min tsolon ƴar nan tata ragowar ciwo ta samu miji amma Alhaji ya ƙi saurarenta, acewarsa sai ta gama makaranta fa maganarsa ba canji”.
“Mtsoww aikin banza. Banda haukarta ma wannan sikila ɗin ko auren tai dawo mata zatai”.
“Hhhhh ashe kin gane Aminiya. Shiyyasa mafa ni yarinyar sam bata cikin lissafina wlhy........”
“Aminiya ina cikin tashin hankali wlhy yau ɗin nan, tun ɗazun na rasa taya zan kiraki ɗaki cike da Ƴaƴa kin san yau juma'ar ƙarshen wata”. Umma ta katse ƙawar tata Hajiya Naqiba.
“Tofa mike faruwa kuma Aminiya. Ke da kin gama kame gida tsaf baki da wata matsala a yanzu, banda ma waccan shegiyar sirikar taki matar Salim na neman buɗe mana aiki itama....”
“Aminiya masu son buɗe mana aikin ai sun ƙaru. Kin san shegen yaron da muka cimmawa da ƙyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login