Showing 48001 words to 51000 words out of 124209 words

Chapter 17 - FURAR DANKO PART 1

Unknown   

12 Nov 2024

8790

ta ambata mata. Sannu-sannu ta fara sassauta damƙe kujerar da rumtse idanun nata da tai, sai kuma ta buɗesu gaba ɗaya sunyi jajur matuƙa kamar wadda tasha wani abu a lokacin.
“Shigomin da ita”.
    Ta faɗa ƙirjinta na ƙara ƙarfin sukar da yake mata. Ga jikinta bai daina tsumar da yake ba. Da ace tanada ilimin addini da addu'a tafi cancanta da harshenta a irin yanayin. Amma sai aka samu akasin hakan a gareta. Da sauri sakatariyar ta ta fice cikin matuƙar sassarfa. Minti biyu basu rufaba sai gasu sun shigo. Matar dai da ka ganta kaga wadda ke'a cikin mawuyacin hali, sai dai da zata samu kulawa ƙyaƙyawar mace ce dirarriya. A lamarin Lulu da talaka a teburin aikinta kawai suke iya shan inuwa ɗaya, shima akan abinda ya shafi aikintane kawai babu ruwanta da rayuwarka. Har ƙasa matar ta kai ga alamun ciki da ya turo a jikinta zata gaida Lulu. Bata hanata durƙusawar ba amma dukkan hankalinta na gareta, sai kuma katseta da ga gaisuwar data fara da tai...
        “Kinga wannan gaisuwar baida amfani faɗamin ina yarinyar take?”.
    Cikin gyaɗa kai da share hawaye matar ta ce, “Tana gidan ƴar uwata da ta rakoni nan jiya, saboda yanda jikin nata yake ne ƴar uwar tawa tace na dawo yau ita ta kula min da ita”.
            “Wane police station kukaje domin kai ƙarar?”.
       “Na nan unguwarmu ne sai kuma da mukazo nan wajen ƴar uwar tawa itama ta kaimu na nan ɗin. Sai dai shima basu ɗauki abin da muhimmanci ba shiyyasa ta ce zata rakoni nan inda take da tabbacin za'a share mana hawaye. Hajiya dan ALLAH ki taimakeni kamar yanda ALLAH ya taimakeki. Yarinyar nan marainiya ce mutuwar mahaifinta ta sani auren wannan tsinannen da tunda na aure shi ban sake farin ciki a rayuwata ba......”
     Cikin jan tsaki da takaici Lulu ta katseta da faɗin, “Kika zauna da shi kuma har ya miki ciki. Malama ni ba rayuwar aurenki nake buƙatar ji ba. Ki tashi kuje zan haɗaki yanzu da wanda zaku sameni a asibiti”. Ta ƙare maganar tana miƙewa cikin matsanancin ɓacin rai. Waya takai kunnenta, da ga can aka ɗaga. Kirari aka fara mata ta katse da faɗin, “Musa ka sameni a office yanzu kai da Shu'aibu Please inada emergency case.”
          “An gama ranki ya daɗe”.
Musa ya faɗa ransa fes dan yasan yau aljihunsu zai kasance a cike. Dan aiki da Lulu yafi masa zaman cikin station aita kayan hamma balle tsaiwar kan titi amsar na goro. Ɗan rubutu tai a takardar data yago ta miƙama sakatariyar ta dake tsaye har yanzu. “Idan sun zo ki basu wannan, suje da ita sai su sameni a wannan asibitin dana rubuta. Kibasu 5k da zasu saka mai a mota”. Daga haka ta fisgi hand bag dinta da ɗayar wayarta da key tai waje...
Batako kalli sauran mutanen da ke zaune a inda table ɗin sakatariyarta ya ke ba ta fice. Taja ƙaramin tsaki lokacin da take dana unlock ɗin motar tunkan ta ƙarasa gareta. Bazata iya jure wannan zirga-zirgar tuƙin ba fa gaskiya. Dan tun farko ita dama ba gwanar sonyi driving bace. Cikin ƙara jan tsaki lokacin da take ficewa a gate ɗin ta dannama Uncle Yousuf kira. Sai da ta shiga ta tuna abinda ya faru jiya da wasan ɓuyan data ƙudiri aniyar farayi da shi. Da sauri ta rarumi wayar zata katse sai dai harya ɗaga. Babu alamar wasa a muryarsa ya ce, “Lafiya?”.
      Kamar ta fasa ihu haka taji, amma sai ta dake cikin pretending da ƴar shagwaɓa ta ce, “Uncle Barka da safiya. Dama no ɗin mutumin nan zaka turamin koka kiramin shi Please ya sameni a Shira's hospital”.
       Ɗan jimmm yay kamar bazai amsa mata ba sai kuma cikin dakewar da takan bata tsoro a Duk sanda yayita ya ce, “Wane mutumin?”.
           Yanzu kam sai da taji bugawar zuciya. Da ɗan rawar harshe ta ce, “Driver fa my papa”.
    Har zaiyi yi mata tambayar yaya akai bashi ya kaita office ba sai kuma ya fasa saboda tare ya ke da abokinsa Hameed. “K kina ina yanzu?”. Ya faɗa cikin goce tunaninsa.
       “Ina hanyar Shira's hospital ɗinne ”.
     “Sai kin ƙaraso”.
Ya faɗa kawai yana yanke kiran.......✍️
         



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

[9/8, 10:18 PM] +234 813 110 8969: 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣9️⃣



........Kaɗan ya rage ta bugama motar gabanta. Tai saurin take birkin da ƙarfi. Ganin yanda mai motar ya dakata shima da alama fitowa zaiyi ya sata sake mata key tabar wajen da saurin dan ba wannan ne a gabanta ba yanzu. Tana hango zagin da mai motar ke mata cikin daƙuwa da wanda wasu ke mata na gefen titi. Oho basu bane a gabanta. Furucin Uncle Yousuf ne ke mata kai da kawo. Ji take kamar ta koma su canja asibiti sai dai ta riga kuma tace su Sha'aibu su sameta a can. Sannan yanda uwar ke nuna yarinyar na cikin mawuyacin hali maganar sakaci daga gare ta ma bata taso ba, dan a yanzu al'amarin su drivern ta ya shafe a zuciyarta yanda zata yaga rayuwar mijin matar nan kawai take ƙullawa. A wannan fanin ba'a gayyacesu ba ma taka rawa suke balle sune da bikin. Ai rawa sai kalar wadda sukaso takawa wlhy.....
         “Da gaske dai Uncle You na asibitin nan? To mi ha kawoshi?”. Ta faɗa a fili tana parking idanota akan motar Uncle Yousuf dan babu ta yanda za'ai motocin gidansu su ɓace mata. Cikin rashin sanin abinda take buƙatar sani ta fito a motar. Sai da ta leƙa motar Uncle Yousuf ta tabbatar babu kowa a ciki sannan ta bar wajen zuwa cikin asibitin. A reseption kuwa suka haɗu da Uncle Yousuf ɗin. Karan farko a rayuwa taji bazata iya haɗa ido da shi ba, tsoron ma haɗuwar tasu take yi. Musamman kuma yanda ya zuba mata idanun nasa duk sai ta nema daburcewa. Shi ya fara ɗauke idanunsa da ga kanta yana kai wayarsa da aka kira kan kunne. Hakan ya bata damar nufar inda ake yankar kati, sai dai kuma fa ko sunan yarinyar bata sani ba ma fa ashe. Cikin ɗan yarfar da hannu da juyawa gaba ɗayanta tai facing ƙofa ta ke faɗin “Ouhhh! Saurin banza ma ashe nake”. Dai-dai nan motar ƴan sanda mai ɗauke da matar nan da yayarta da yarinyar suka iso. Shigowar Musa ya sata sauke ajiyar zuciya, shi ya sanar da nurses cewar akwai mara lafiya a waje kafin ya ƙaraso gareta. Kallo ɗaya da Lulu taima yarinyar ya sata rumtse idanunta takalminta har yana gullewa sai da ta dafe kantar reseption ɗin.......

         “★“★ ∆ ★”★”

       “Ranka ya daɗe yaron nan fa daka tada hankalinka kansa ba wani ɗan kowa bane face wani mutum da ake kira Malam Mika'il Idris Mawashi a anguwar fagge. Shi kansa mahaifin nasa a iya layin nasu kawai aka sanshi balle shi. Kuma da gaske drivern yarinyar ne kwata-kwata bai ƙulla sati huɗu da fara aiki gidan Alhaji Isma'il Jiƙamshi b.....”
      “Kace Alhaji wa?!!”.
   Alh. Baita yay saurin tarar numfashin yaronsa da suke kira Goga a kamar razane da jin sunan Alhaji Isma'il Jiƙamshin. Bashi kawai ba hatta Hon. Nakowa da ke tare da shi dan tunda suka baro gidan MM Atik Kumo da ya basu aro anan gidan hutawar Alh. Baitan suka ƙarasa kwanan nasu. Shine tun da farar safiya kuma suka nemi babban yaronsu na bangar siyasa Goga suka sakashi binciko wanene Smart ta hanyar ɗan bayanai da suka samu ga Nadiya wadda itama ta samune ga Lulu randa taje saloon shagonta....
        “Alhaji Isma'il Jiƙamshi nace ƙwarai da gaske oga. Dan shine mahaifin ita yarinyar ma ai.”
      “Babbar magana ƴarsa ta cikinsa?”. Hon. Nakowa ya faɗa wani irin abu mai ma'anoni da yawa na tsirga masa tun daga saman kai har tsakkiyar ƙafafunsa. Cikin tabbatarwa Goga ya gyaɗa masa kai. Tare da masa ƙarin bayanin da zai gaskata hakan duk da shi bai san dalilinsu na jinjina sunan ba tunda shi dai a ɗazun yaga hankalinsu akan yaron yake ba ita yarinyar ba.
      “Kaga jeka”.
Honorable Babale ya faɗa cikin katse masa tunani. Dai-dai Goga na miƙewa ya sake faɗin ka jiramu a waje nan zamu nemeka.” shi dai da to ya amsa musu ya fice kamar yanda suka buƙata. Yana kuwa fita Hon. Nakowa ya firta, “Tabɗi jan inji mata. Dama ƴar iskar yarinyar nan ɗiyar Isma'il Jiƙamshi ce? Haba shiyyasa bata zubar a banza ba.” sai kuma ya wani ƙyalkyale da dariya alamar hakan ya masa daɗi ƙwarai da gaske. Shima Alh. Baita dariyar ya fara. Sai kuma ya buga ƙafa da faɗin, “In kere na yawo zabo na yawo tabbas faɗar masu iya magana watarana za'a gamu. Honorable Please kira mana Hon. Misau mana. Dolene ai wannan shagalin da shi”.
      “Ƙwarai ma kuwa”. Cewar Hon. Nakowa yana wani bula-bula da babbar riga wajen laluben wayarsa. Cirota yay tare da yin danne-danne ya kai kunnensa......

      Tofa masu karatu wata sabuwa kenan. Mi'a haɗin Daddy kuma da su Honorables?🤔.

          ∆★∆★∆★∆

    Tun bayan wucewar ɗan nasa yake ta faman kai kawo a lafiyayyen office ɗin nasa. Abubuwa da yawa ne ke masa sukur-sukur a brain game da buƙatar autan nasa a karo na biyu. Tabbas zai fi kowa farin ciki da ƙulluwar wannan auren dan koba komai dai Mawaddat ɗiyar ƴar uwarsa ce Mawaddat. Ƙanwarsa mafi soyuwa garesa a duk cikin ƙannensa. Wadda yasha bama sirrin al'amuransa batare da tunani ko jin ɗar ba har ALLAH ya ɗauki ranta. Zai kasance mai yin farin cikin ganin jininsa da nata sun zama abu ɗaya. Sai dai kuma matsalar itace Isma'il. Isma'il shine babban bakangizo mai razani da ya gitta a tsakkiyar wannan ƙaunar zumunta mai cike da ababen burgewa ga duk wanda zai iya jin asalinta da wanzuwar ta. Dan tarihin ratsawar Isma'il a cikin labarinsa dana ƴar uwarsa uwa ɗaya uba ɗaya ya juya akalar waccan ƙayataccen labarin zuwa ɗimautacce mara armashi a yanzu. Ata wani fanin kuma kamar zai zo da sabon armashin kansa da kansa dan labarin zai canja ne da ga na shi da ƴar uwarsa zuwa na shi da Isma'il Ibrahim Jiƙamshi mijin ƴar uwarsa da ƴarsa. Ƴarsa da yasan yana matuƙar ƙauna fiye da komai a rayuwa. Kafin yau da faruwar matsalar farko na tusguɗewar aure tsakanin Mawaddat da Tajuddeen labarin ba a haka ya tsarashi ba, sai dai yana ganin wata dama ce da zai masa editing dan ya zauna dai-dai da zamanin nan na 2023 a ajiye wancan ƙarnin dan ya koma tsohon yayi. Ya wani lumshe idanu da dunƙule hannunsa ya ce, “Yess!! Sulaiman Sufi Ado Garko kai mai nasara ne akoda yaushe. Isma'il Jiƙamshi sabon game, sabbin players and sabon stadium ka zama cikin shiri”.

       Wata sabuwar kuma dai🤔.

★★★★★

         Duk da a yanda take jin matuƙar gajiya bata huta ba har sai da doctors suka rufu akan yarinyar nan da lamarinta ya taɓa duk wanda ya ganta a cikin asibitin. Dan hatta Uncle Yousuf tuni ya ajiye batun takaicin Lulu gefe da shi akai komai na ganin likitoci sun tsaya a kanta. Abin tausayi ita uwar ma zuciyar ta bushe ko kukan zahiri ta kasa sai na zuci. Ganin komai ya natsa dan ana neman  uku na rana ma Uncle Yousuf ya kai dubansa ga Lulu da alamunta suka nuna gajiyarta matuƙa. Dan sai faman yamutse fuska take. Tausayi ta bashi, dan haka ya cigaba da kallonta a kaikaice cikin tausasawa da mata addu'ar shiriya akan halayenta marasa ƙyau. Isowar Ahmad wajen ta sakashi maida hankali garesa. Fuskarsa da murmushi yay ma Lulu magana, amma sai ta amsa masa a ɗan ɗage. Bai damu ba dan ya santa ya san halinta. Hasalima ya taɓa nuna sonta amma ta taka masa burki lokacin tana farkon dawowarta da ga Uk. Uncle Yousuf da yanda tai masa ɗin ya bashi takaici ya harareta, sai kuma ya maida hankalinsa ga Ahmad ɗin da ke faɗin, “Yaya ya farka, doctor ɗin ma ya sallamemu dan ya matsa zaije gida. Kasan Mawashi fa sam bai son asibiti.”
       Murmushin Uncle Yousuf yay, cikin yanayin tsokana ya ce, “Kai haba kamar wani yaro ko mace”.
          Dariya Ahmad yayi, dai-dai nan Smart ya fito a wani ɗaki da ke kusa da inda suke. Coach riƙe da hanunsa kamar wani ƙaramin yaro sai ɓata fuska yake. Dan da gasken fa bai son asibiti shi sam a rayuwarsa. Kuma bai san allura. Yanzu ma ba ƙaramar badaƙala akasha ba kafin ai masa shine ma Ahmad yay fushi ya fito. Ilai kuwa hararar Ahmad ɗin yayi tare da ɗauke kansa duk a lokaci guda, cikin rashin sa'a ya saukesu akan Lulu da tai kicin-kicin da fuska saboda kasancewar Ahamd a wajen, ita ala dole kar a kawo mata raini, dan duk wanda ya taɓa furta cewa yana sonta ko ya nuna basa ƙara shan inuwa ɗaya kuma. Ƙoƙarin janyewa yake sai kuma yay dai-dai da ɗagowarta cikin shirin miƙewa tabar wajen. Ta wani yamutse fuska fiye da yanda take sai kace wadda taga kashi. Shima ƙara tsuke tashi fuskar ya ɗanyi tare da ɗauke kansa gaba ɗaya irin bai ganta ɗin nan ba ma....
         “Ga Aliyu nan babu lafiya sai ki masa sannu. Dama ina son ki gama da wannan kai kawon ne muje ki dubashi ashe ma zasu sallamesa yanzu”. Uncle Yousuf ne yay maganar cikin katse hanzarin Lulu dake niyyar barin wajen abubuwa masu yawa na mata kai da kawo musamman ganin drivern nata a nan. Dakatawar tai, sai dai ta kasa cewa komai sai ɗan hararsa da take ƙasa-ƙasa.
     “Wai nikam bada Mawaddat nake ba?!”. Uncle Yousuf ya faɗa cikin ɗan kaushin murya dan ya san taurin kanta na tsiya da gadara. Sosai taji haushin hakan, amma babu yanda zatai dan Uncle Yousuf ne. Ta ɗan sake ɗagowa ta kallesa, a taƙaice ta furta, “ALLAH ya bada lafiya”.
        Coach ne ya amsa da “Amin”. Cikin murmushi. Shi kam a zuciya ya amsa mata. A zahiri kam ya ɗauke kansa gefe kamar bai san da shi take ba. Sosai ta sake tunzura da salon rainin nasa. Tana mai tabbatar ma kanta a zuciya sai ta koya masa hankali da sauke masa wannan girman kan nasa. Batare da ta sake kallon kowa ba ta ce, “Uncle You ni na koma Office. Uncle Hameed ka gaidamin Aunty Rukayya sai nazo gaisheta”.
        Coach yay ɗan murmushi da faɗin, “Zan sanar mata idan da gaske kike Daughter. Dan na sanki ke da sabgoginki marasa ƙarewa.” karan farko da ta saki sassanyan murmushinta da kan ƙawata ƙyawun fuskarta, sai dai batayinsa sai ta gadama. Kai Ahmad da zuciyarsa tai wani irin tsargawa ya ɗauke gefe. Dan Lulu cikakkiyar mace ce da kan iya jan hankalin mafi yawan maza musamman irin matasanmu na yanzu masu fifita ƙyale-ƙyale ga mace fiye da nagarta. Sai kuma ka kwasa ka kai gida ka samu fanko ce ko addininta bata sani ba sai duniyar kawai aka saka a gaba da son birge al'ummar cikinta....
       Suma a tare suka fito su huɗun, Coach da Ahmad da Smart suka shiga motar Ahmad da ya koma ya ɗakko. Uncle Yousuf kuma ya shiga tasa motar dan Lulu kafin su fito ma har ta bar asibitin. Babu wanda ya sake bi takanta. Godiya Smart yay ma Uncle Yousuf sosai tare da su coach ɗin ma gaba ɗaya. Da ga haka kowa yaja motarsa. Har gida suka kaisa. Ahmad yay masa rakkiya har cikin ɗakunan kasancewar ba baƙonsa bane ɗakin dama. Bai wani zauna ba saboda Yayansa dake jiransa a mota. Yay masa ALLAH ya ƙara lafiya ya tafi.......✍️

         


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
[9/8, 10:18 PM] +234 813 110 8969: 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣0️⃣



.......Bayan yay sallar la'asar barci ya sake sha har kusa da magrib batare da kowa yasan yana a gidan ba. Dan sanda su Ahmad suka maidosa basu ga kowa a ƙofar gida ba. Wanka yay da alwalar magrib ya fito. Yanayin yanda yake jin jikinsa babu ƙarfi ya sashi yin sallarsa a ɗaki. Bayan ya idar ya fita zuwa cikin gidan. A kallo ɗaya zaka iya fahimtar baida lafiya ƙarfin hali ne kawai. Sai dai hakan bai hanashi leƙa duk ɗakunan gidan ya gaida su Mama ba. A ɗakin Umma ya samu babban yayansu Salim yazo gidan shima. Sama-sama suka gaisa Salim ɗin na wani cika da batsewa shi adole mai naira a gida. Ko'a jikin Smart dan shi ba wannan shirmen ne a gabansa ba. Yana juya baya zai fita Salim ɗin da Umma suka raka bayansa da harara. Oho baima san sunai ba shi dai.
        A falo ya samu ƙannen nasa duka. Sai Nasreen dake ta faman tsalle-tsalle ita da autar Aunty Amarya. Gaisheshi suka shigayi, ya amsa yana zama tare da ɗan dafe kansa da har yanzu bai gama saki ba. Ammah da tun shigowarsa take kallonsa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login