Showing 21001 words to 24000 words out of 34206 words

Chapter 8 - Tsutsar-nama-book-2

29 Jun 2024

6934

zata fara kulaki. A'in ce kamar mai aljanu wlhy".
Murmushi nayi yayinda ita kuma ta ?are maganar da sakin ?aramar dariya. Daga haka ta cigaba da fa?in, "Ya danganta da yanayin aikin da zamu tarar. Musamman ma ni, dan iyayen gidan nawa mutuncinsu ragaggene bare ma idan akace miki Aunty Azizat. Tana abu kamar mai jin warin mutane. Bari naje dan in nayi latti zan sha maruka gashi ?a'idarta ne iyanzu take wankan yamma".
Kasa cewa komai nayi, sai kaina dana ?aga mata kawai sunan wadda ta kira na min kai-kawo a rai batare dana san dalili ba. Bayan ficewarta na saki nannauyar ajiyar zuciya. Sai kuma na mi?e cikin kasalar jiki zuwa gadon da tace nawa dake a farkon shigowa. Na can ?arshen bango na A'i, na tsakkiya nata. Sai ni a bangon ?arshe na farkon shigowa.....

??¡ï¡ï¡ï??

Tsakanin Halime da Dady dai tun wannan ranar ba'a sake ha?awa ba. Dan washe gari uban aiki taci kamar kurar wasa. Dan kaf girke-girken da aka tanadama Alhaji Rufa'i itace tayi su. Tayi kuma gyaran gidan musamman falon tarar ba?i da Mom ta sakata ?al?alewa kamar za'a canja bangonsa. Ita dai bata san dalilin uban aikin da taci ba sai da yammaci take ji a bakin auta wai Baby ce tayi ba?o. An kuma ce ta saka hijjab da ni?ab takai masa abinci falon ba?i. Bata da yanda zatai dole tabi umarnin Mom tayi shigar da akace taje takai komai. Da ?unbin mamaki ta fito mara misali. Yayinda taketa jarumtar danne dariyar dake cinta har sai da ta shiga ?akinta. Bata tsaya a tsakar ?akin ba ta shiga toilet ta rufe kanta duk dan kar a jita sannan ta fara kwasar dariya harda hawaye. "Kambu ta?ashin nan. Yanzu ni Halime ina Baby ta samo wannan tulun giyar, wlhy cikinsa kamar an kifa masakin Baba Lauren gidanmu na Daudawa. Gashi san?ameme kamar samudawan da suka zo mana a labari. Tab ?i jan, daga dai ganin wannan kasan sai dai a so shi dan ku?i duk da dai ?ya?y?yawa ne a fuska." kiran da Mom ke ?wala mata ya sata fita a guje dan tasan idan tai na uku sai ta sha maruka a wajenta.

Gab da magrib taji ihun Bibaa da Abbas ya cika gidan. Ta kitchen ta kasa kunne sai ta jiyo ihun nasu wai duk murna ne akan Alhajin nan ya bama Baby makulin mota, tare da al?awarin kujerar maka gareta da Mom da Dad da kuma Abbas, su kuma su Bibaa da Auta da Nabil yay musu ?yautar wayoyi iphones. Hakan dai na nufin su duka banda Yaya Musaddiq bawan ALLAH kowa ya samu alkairi daga Alhaji Rufa'i. Baki ta ya?e ta cigaba da aikinta. Daga haka bata sake bi takansu ba sai washe gari da kakarsu tazo take jin har ?yautar ku?i yay ma yaran gidanta itama wai naira miliyan ?aya. Itama kuma kakar tasu harda ita a zuwa saudia, da yaje gidanta kuma ya bata waya mai ?yau ?ar dubu ?ari biyu harma ta sayar da ita yau. Sosai Halime ta jinjina kwa?ayin wannan mutane da mamakin maganganun da taji suna tattaunawa. Dan sai da Mom ta farga da ita sannan tasha maruka aka korata waje, daga haka bata san mi suka ?arasa tattaunawa ba.

WASHE GARI kuwa bata ma san lokacin da Mom ta fita a gidan ba tare da Baby. Sai Bibaa da Auta da suka wuce makaranta. Shi dama Abbas ba'a sakashi a lissafin gidan. Yaya Musaddiq kuma ta lura jiya kamar bai kwana a gida ba. Tana a falo tana shara da raira wa?arta cikin zazza?ar muryar nan tata taji kamar ana kallonta. ?an jim tayi cikin nuna tsarguwa. Sai kuma ta cigaba da shararta amma ta daina wa?ar da take rerawar ta (kwanana ya kusa ?arewa a gidanmu zan tafi ?akina. A gidan mijina zan rayu zaman ka?aici ya kusa yankewa).
Cikin sauke ajiyar zuciya da rashin jin da?in daina raira wa?ar tata Abba ya ?arasa fitowa daga jikin ?ofar ?akin barcinsa da yake ma?ale.........??



_Masoya ina ?ara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR??????ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE??_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ????_*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing??_*








*_??TSUTSAR NAMA....!!??_*
_(Itama nama ce)_




_?????????? ???????????? ????????_



_???????? ??????_
_???????? ????????????????_


_____________

_Koda ku?inka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ?an kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sau?i da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin bu?atunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ?an yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ?ai-?ai zamu tsaya ba harda sari ga mai bu?ata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sau?i da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. ?an kasuwa masu sari da masu sayen ?ai-?ai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*??_

https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG



https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5

_____________

......Daga ni har Mama Balki ?asa muka zube gaban Alaja dake zaune cikin kujera ?afa ?aya kan ?aya tana da?ilar tab. Gaisheta na shiga yi, batare data ?ago ba ta amsa min. Kusan mintuna biyu muna zaune kamar masu neman gafara sannan ta ?ago tana cire eyeglasses ?in idonta da bana raba ?ayan biyu na ?ara gani ne. A kaina ta zube idanun nata, sai kuma ta ?an saki murmushi. "?ammata sorry fa. Tunda mukazo ban sake waiwayarki ba ko? Nayi busy ne da yawa."
"Ba komai Mama".
Na fa?a kaina a ?asa ina wasa da yatsun hanuna ta cikin hijjab.
"Ohkay, yanzun ma bani da isashen lokaci. Maman Nana kije da ita wajen Sunusy ya gwadata a ?inka mata uniform itama. Sauran kayan da zata iya bu?ata kuma sai ki shirya zuwa anjima kuje shopping. Zata cigaba da zama a hannunki kafin tasan aikin da zatayi".
"To Hajiya in sha ALLAHU yanda kikace haka za'ayi. ALLAH ya ?ara nisan kwana da rayuwa mai albarka".
A hankali ta amsa da amin. Jin godiyar da Mama tayi nima sai nayi godiyar. Duk da kuwa wani irin abune mai masifar nauyi ke neman ri?e min ?irji. Ban san a wace kalar rayuwa kuma na jeho kaina ba. Lallai na tafka kuskure. Inama Kano na nufa abina. Kai anya kuwa kuskuren nawa ba daga baro asibiti bane da nayi. (Tun daga baro gidan mijinki dai a Kano) wani gefe na zuciyata ya ayyana min. Jinai tsigar jikina yay wani irin tashi sama. A saman lips na maimaita kalmar "Miji". (Kai ina ai bazan ta?a zama matar kowa ba sai Mansoor in ALLAH ya yarda)..

"K! waye wannan kika hayo mana har sama da shi?!". Muryar dana tabbata naji irinta a jiya ta fa?a cikin daka mana tsawa dai-dai muna sauka steps na biyun ?arshe. Ganin yanda Mama Balki ta dakata da sauri cikin nuna shakka ya sani mamaki. Cike da girmamawa da sauke kai ta furta "ALLAH ya huci zuciyarki Aunty Azizat. Dama mun cika umarnin Aunty Mama ne. Dan itace ta bu?aci ganinmu".
Fuska ta wani yamutse tana balla mana harara. Da alama dai bata da abincewa. "K kuma uwar miye kike wani kallona? Shegiya mai kama da mayu!!". Ta sake fa?a a fusace tana wani ware idanu a kaina sosai cike da nuna tsagwaran tsanar da ban san laifin dana mata ba. Duk yanda naso jin na bata girma a matsayin wadda na shigo gidansu da kuma girmata da tayi a shekaru dan zata iya kaiwa sa'ar Yaya Musaddiq amma sai naji hakan ya gagareni. Sai ma tsareta nai da idanu ina ?are mata kallo daga sama zuwa ?asa....
Tauuuu!!! Naji saukar wani shegen azabebben mari asaman fuskata babu zato babu tsammani. A take ta rashin jin ya yun?uro, bamma san lokacin dana ?aga nawa hannun ba na sauke mata nawa yatsun biyar nima a saman fuskarta dake fara sosai a dama da haggu kuma. Daga gani kasan akwai ?arin farin kanti dan har wani yellow-yellow takeyi. Tamkar mutuwa ta ratsa gidan haka yay wani irin tsittt na wuccin gadi. Kafin tai wani irin zuba min ido like wadda tai suman tsaye. Bama ita ba hatta da Mama Balki wani irin waro idanu tayi da ?aura hannuwa duka a saman kai bakinta bu?e. Cike da dakiyar nan tawa da taurin kai na watsar da su tamkar banga komai ba na ra?a zan wuce. Dai-dai nan ta wani saki kururuwa da girgiza tamkar tsohuwar dodanniya ta dam?o min hijjab ta baya. Sai kawai ji nai an sha?ureni tare da jawoni baya. Tabbas da banyi azamar dam?e hijjab ?in ta gaba ba da zamesa da sauri babu abinda zai hanata kaini ?asa a wajen. Idan kuwa na fa?i zan iya buguwa, idan ma da tsautsayi zan iya rasa rayuwata. Gaba nayi gaba ?aya, dan yanda ta fisga ni kuma na fisge sai yay kamar an hanka?oni ne. Na gama sallamawa babu makawa a wannan ga?ar sai na kai ?asan mayen marbles ?in nan mai tsananin she?i da ?aukar idanu tamkar zakaga fuskarka a cikinsa. Dan haka na runtse idanuna gaba ?aya ina mai ambaton sunan ALLAH da sallamawa baki ?ayana......


¡ï¡ï¡ï¡ï

Cikin mintuna ?alilan Halime ta dawo ?auke da tray. Haka kawai take ji bazata iya tsallake umarnin Abba ba. Duk da tana jin shakkar uwar ?akinta tasan ta ?etare umarninta. A hankali ta dire tray ?in a gaban Abba dake zaune a dining. Tun fitowarta kuma yake famar binta da kallo ta gefen ido tamkar zai cinyeta. ?o?ari barin wajen take yi tamkar mai ra?a ya furta, "Baza'a zuba min ba?".
Duk shirmen Halime sai da taji zuciyarta ta tsarga. Hannunta na rawa ta shiga zubama Abba abincin. Ta kammala tana ?o?arin barin wajen ya katseta da fa?in, "Uhhm Kinga zo mana". Nan ma ?iri tai tana kallonsa, kafin cikin sanyin jiki tai ?o?arin dur?usawa a ?asa. Amma sai yay saurin girgiza mata kansa da mata nuni da kujera. Gabantane ya sake fa?uwa. Tai masifar waro idanu waje tana jijjiga masa kanta alamar dai bazata iya ba. ?yaleta yay, cikin gyara yanayinsa ya ce, "Minene sunanki?". Ganin yanda yaci serious ya sata nutsuwa itama. Kanta a ?asa tana wasa da yatsun hannunta ta amsa masa da, "Halime".
"Halimatussa'adiyya kenan?".
"Eh ta fa?a a hankali".
"Ina ne garinku?".
"?an tumaki". Ta bashi amsa kai tsaye.
"?an tumaki?". Ya maimaita da ?an waro idanu a kanta a tunaninsa sha?iyanci ne. Amma sai a mamakinsa yaga ta jinjina masa kai na tabbatarwa. Kasa ha?uri yayi sai da ya furta "A wane state ne?". Girgiza masa kai tayi da fa?in, "Katsina ne. Amma dai muna kusa da Musawa". Jin sunan Musawa ya sashi fahimta Katsina state kenan ?in dai da gaske. Humm mutanenmu da ganganci, ka turo yarinya mai cikar halitta jiki kamar wannan aikatau har wata jiha. Cigaba yay da fa?in, "Miyasa kike aikatau?".
Idanunta ne suka ciko da ?walla. cikin rawar murya ta ce, "Inna ce tace Baba ya turani na samo ku?in kayan ?akin aurena".
"Ita Innar mamanki ce?".
"A'a gwaggona ta rasu tun ina ?arama. Matar Babana ce, amma uwarsu ?aya ubansu ?aya da Gwaggona. Bayan ta rasu aka aurama Babana ita dan ta ri?emu ni da ?anina. Sai dai kuma ta tsanemu, kullum cikin mana mugunta take, gadonmu ma da Gwagginmu ta barin mana duk ta cinye. Gashi Baba baya iya cemata komai, shima tsoron masifarta yake ma".
Haka kawai yaji wani abu mai nauyi ya tsikarar masa zuciya. Tamkar wal?iya hoton Maman su Samraah yazo masa a cikin idanu. Da sauri ya ture zancen zucin gefe ya cigaba da fa?in, "ALLAH ya gafarta mata. Toke kina da saurayi ne da aka turoki samun ku?in kayan ?aki?".
?asa ta ?ara yi da kanta sosai alamar jin kunya. Wasa ta farayi da yatsunta sannan cikin in ina ta ce, "Duk wanda yazo wajena Inna korarsa take yi. Tace saina haihu a gida ?an shege ko zata bari nayi aure. A hakan ma sai su Lami sun gama yin nasu auren".
Sosai zuciyar Abba ta sake raunana da tsinkewa. Da ?yar ya iya furta, "Wacece ita Lami ?in?".
"?anwata ce ita ta haifeta da su Lailah".
Kasa sake magana Abba yayi tsahon lokaci. Sannan yace ta tashi taje ta cigaba da aikinta. Shima sai ya mi?e dan ya gagara cin abincin kuma ya koma ?aki. Shirin fita yayi zuciyarsa na masa kaikawo. Bai wani jimaba ya kammala ya bar gidan batare da ya sake neman Halime ba....

Duk yanda Abba ke son ya?ar zuciyarsa game da abinda take ?wa?aita masa hakan ya gagara. Tun yana iya danne al'amarin har yana son fin ?arfinsa. Yakan rasa sukuni a duk ranar da baiga Halime cikin idanunsa ba. Al'amarin tun yana bashi mamaki har ya koma bashi tsoro. Dan haka kawai yanzu rana tsaka zai baro kasuwa yayo gida dan kawai yaga Halime. Tun Mom na masa uziri idan yace mantuwa yayi harta fara tsarguwa da tunanin ya saka mata ido ne akan yawan yawon da take kwana biyun nan. Hakan ya sakata ?an nutsuwa a waje guda. Yayinda shi kuma Abba zaman nata a gida ya zame masa takura. Dan idan tana nan ko giccin Halime baya gani saboda yanda take jin tsoron sa?a umarninta. A haka da ?yar akai kwana hu?u. A daren cikar na biyar ya gagara ha?uri ya nufi gidan abokinsa Alhaji Sadisu mai-agogo. Tsaff ya kwashe komai ya sanarma Alhaji Sadisun. Shiko ya dinga dariya yana tsokanar Abba har sai da yaga ya ?ulu sannan ya bashi ha?uri tare da bashi shawarar yanda ya kamata suyi dan ganin komai ya tafi dai-dai. Sosai shawarar tayima Abba kuwa. Ya tafi gida cike da farin ciki....

¡ï¡ï¡ï

Wata irin ajiyar zuciya na sauke mai ?arfi jin na fa?a kan abu mai taushi sa?anin inda na gama sada?arwa zan fa?i. Rawar tsorata dana riga nayi jikina keyi, dan haka na sake ?an?ame abinda na fa?awar ina mai sake matse idanuna dake a kulle. Sai dai me, wani kalar wakitawa ?itjina da zuciyata sukayi a lokaci guda, a take tsigar jikina ta fara mimmi?ewa. Gabana ya sake fa?uwa jin yanda wajen ya koma tsitt tamkar babu wani rai mai numfashi. Gaba ?ayan numfashina ne ya ?auke daga illahirin gangar jikina nima, tare da wata irin girgizawar zuciya taban mamaki. Sake ?an?ame abinda na fa?awar dai na sake yi. Wani irin jifff!! ?irjina ya sake bugawa a karo na biyu jin tabbacin mutum ne, mutum ?in kuma daga ji ba jikin mace bane, sannan ?amshin dana sha?a na neman jirkice min tunani gaba ?aya. Ga tsitt ?in da wajen ya ?auka lokaci ?aya tamkar an tsaida numfashin kowa da komai na gidan. Sassauta ri?on da naima koma minene na fara yi, sai kuma na shiga ?ago kaina a hankali ina ?o?arin bu?e idanuna. Akan farin riga armless ta sport wear fara tas na fara saukewa. Sai ?aton damtsen hannu dake a mur?e sosai fari mai ?an duhu ka?an dan fatar batai irin tas ?in nan na mahaukacin fari ba. (Jikin namiji) zuciyata ta ayyana min, dai-dai da bugar hancina da ?amshin turarensa ya sake yi. Cikin wani irin sauri da shiga tsananin tashin hankali na ?ago gaba ?ayana na sauke idanuna akan fuskarsa.........??



_????Hukumar tawada da al?alami tace a tafi yajin aiki.??_



_Masoya ina ?ara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR??????ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE??_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ????_*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing??_*








*_??TSUTSAR NAMA....!!??_*
_(Itama nama ce)_




_?????????? ???????????? ????????_



_???????? ??????_
_???????? ????????????_

__________


Toh Nazo maku
Da kayan arziki
Kudai kunsan mata sai da gyara
Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta
A katafaren kamfanin mu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login