Showing 6001 words to 9000 words out of 34206 words
ke faman maimaita kansu a cikin kaina cikin matu?ar amsa kuwwar data zarce ?arfin muryar daya sanar min su. (Idan nan ne GARIN AUREN ni ne MIJIN fa?) Kalamansa suka shiga min amsa kuwwa a cikin kunne tamkar wadda akema shelarsu. Gaba ?aya ma brain ?ina ta toshe, sai nake jin kamar na kasa fahimta ko fassara su a bigiren daya dace. (Kai ina wannan gangan ne) wani gefe na zuciyata ya ambata. (Samraah dawo cikin hankalinki mana) sashen zuciyar tawa dai ya sake maimaitawa. Hannuna dake a saman kaina na sauke tare da kaisa saman kumatuna na ?an bubbuga, dan nafi tunanin mafarkine kawai. (Kai amma wannn mummunan mafarki da muni yake) na sake fa?a ina bubbuga fuskar sosai da ?arfin gaske kozan farka. Zafin daya ratsata ya sakani rumtse idanun da ?arfi. A masifar jigace da ?o?arin ha?iye hawayena na ce, "Wai kai minene ala?arka da ni ne? Mi kaje ka ?ulla? Miye matsalarka dani?".
Idanunsa ya ?auke da ga kaina gaba ?aya. Sai kuma ya ?an ta?e baki alamar yanzun ma bazai tanka min ba. Rainin wayonsa ya gama zuwa min ko ina. Dan haka na fisgi ?an ?arfen dake cikin tasar asibiti a gefena na ?ago ina kaisa saman cikina cikin soyewar ido data zuciya. "Dana zauna da kai a matsayin miji gara na kashe kaina na san ban mori komai a rayuwata ba."
Idanunsa dake min wani kallon ?asa-?asa ya sake ja luuu kamar zai rufesu gaba ?aya. Sai kuma ya bu?esu warr cikin yanayin i don't care manners ya furta, "So! Ai ba hanaki zan ba. Abinda kawai nake bu?ata kafin ki mutum ki bani video".
Wani irin sakartaccen kallon tsana da takaici nake masa. Na cije lips ?ina da masifar ?arfi. "Har abada kuwa bu?atar taka bazata biya ba. Dan wannan videon bazai ta?a zuwa hannunka ba har gaban abada."
"Ashe kuwa ko kin mutu gawarki zata cigaba da zama a gareni. Ahalinki kuma zasu cigaba da amsar hukuncin laifinki".
"Idan kuma kai na kashe fa?". Na fa?a ina jefar da ?arfen cike da tsantsar fusata da tafi ta ?azun. Idanunsa ya ?an zuba min, sai kuma cikin nuna rashin damuwa ya janyesu yana wani shegen annamimin murmushi daya ?ona min rai.
"Oh are you threatening me? Ai game dani ba wasan yara bane ba. Har yanzu bamu fara wasan ba, balle ki tunanin samun game over. Zan iya baki damar kwanaki domin shiryawa. Ba kince kinfi ?arfin la?ewa bayan wani domin fa?an sun?uru ba. To gana gaba-da-gaba nan kin samun bissmillah. Matsoraciya kawai. Kwana uku kacal har kin fara banbance tsakanin aya da tsakkuwa".
Bamma san lokacin da wani irin ?arfin zuciya yazo min ba. Cikin tsantsagwaron ?aukar alwashi da tsawa na ce, "Har abada nafi ?arfin yin laushi a hannun matsoraci irin ka. Dan ni har yanzu banga MAZANTAKA ba anan tunda sai da ka la?e a bayan aure yanzun ma. Kasaka a ranka daga yau ni Samraah bint Abdul-wahab Gwarzo, sai na sakaka lissafin lissafa kwanakin rugujewarka daga yau har zuwa ranar dana ?eba maka da zan kuma koma ga masoyina. Ni nan sai na sakaka gudu, gudu irin wanda babu wajen zuwa a tsakkiyar sahara mai tsananin zafi rana da ?arancin ruwa. Wlhy sai kasan ka ?akko KARA DA KIYASHI. zakuma kasan TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE". Daga haka na ture wayar ?asa batare da na jira jin abinda zaice ba. Sai ma wani irin izza da ?arfin iko da naji yana ratsa ga??aina, duk da sara min da kaina yake tamkar zai rabe biyu. Sai kuma hawaye sharr suka shiga kwaranyomin masu zafin gaske....
(????tofa irin wannan alwashi haka Sam-G).
????????????
"Magana ta gaskiya Alhaji yaronka Mansoor na cikin ha?ari. Sai dai akwai mafitar da in na baku shawara kuka gamsu da ita ina fatan za'a dace......"
Cikin tarar numfashi da taune harshe Dad ya furta, "Ka fa?i ko minene mu masu baka goyon bayane Doctor. Bama son rasa Mansoor dan ALLAH ka taimaka mana".
"Wannan duk na ALLAH ne Alhaji. Idan kuma muka cigaba da ro?onsa shi mai amsawa ne. Shawarar dama itace ai gaggawar barin ?asar nan da shi zuwa India. Akwai ?wararren likita dana sani game da ciwonsa. Kuma inada ya?inin in sha ALLAHU zai basa dukan kulawar da muke bu?ata koma fiye da ita. Sannan ku shirya ya?i na gaskiya game da nisanta komansa da abinda ya sake jawo wannan matsalar tasa da mukai tunanin ta barsa tun a shekarun ?uruciya. In ba hakaba akoda yaushe komai zai iya faruwa magana ta gaskiya".
Sosai zukatansu suka ?ara raunana da zancen Doctor. Dan duk dakiyar Attahir sai gashi yana share hawaye. Basu wani yi ja'inja ba dan basa fatan rasashi, tun ma yana yaro sanda matsalar ke da zafinta basu nutsu ba balle yanzu. A take aka fara shirye-shiryen fita da Mansoor zuwa India. Abinka da masu hannu da mai?o, cikin kwana ?aya da yini komai ya gama kammala. A cikar kwana na biyar da ?aura auren Samraah da Maash aka wuce da Mansoor. Da ga shi sai doctor da Attahir ne suka wuce. Su Dad kuwa sai nan da kwanaki biyar saboda tsaiko da aka ?an samu game da visa ?in Amal. Duk wani masoyinsu ya bisu da fatan alkairi. Yayinda tausayin Mansoor ya sake cika zukatan wasu. Wasu ko nama iyayen nasa ALLAH ya ?ara kasancewar koma a wane hali yake sune suka jaza masa. Dolene kuma sakayyar Samraah ya bisa. Dan gashi itama ance babu lafiya har an wuce da ita asibiti. Dan tun a randa aka wuce da ita Abuja labari ya shiga kunnuwan mutane sakamakon shegen surutun Mom da ita take fa?a cike da nuna jin da?i. Dan itafa jinta take fes uwa ya zuciyar sabon jariri haihuwar yanzu. Har fa?ama mutane take ai mijin Samraah ?in dama irin kwatakwalin yaren nan ne shiyyasa ma ya wuce da ita Abuja ?in dan ya kaita ga danginsa a bata ji?e-ji?ensu amma babu wani asibiti duk joni ne dan kar ai mata dariya. Wasu dai sun hau sun zauna, yayinda wasu ke fassara al'amarin nata da hassada kawai. Duk da dai mutane ba ganin mijin Samraah ?in sukayi ba. Kowa dai batun an ?aura aure da sunan wanda aka ?aura ?in mai suna Muhammad Mu'azz kawai sukaji. Sai kuma waliyayyansa da kowa ya gani ?uru-?uru da ido dan wasu ma harda video sun ?auka domin ya?awa a media kasancewar Sam-G ?in cele ce, yanda auren nata ya canja akala cikin ?an?anin lokaci sun san zai jawo magana. Ya kuwa jawo ?in, dan har a yau da yake cika kwana biyar cif da ?aurawa ba'a daina yawo da hotunanta da ?ananun magana ba harma dana Mansoor. Sai dai duk bin ?wa?w?wafin mutane na son ganin sabon ango da iyayenta sukai mata auren huce haushi da shi har yanzu babu wanda ya gani. Duk da anata editing hotonta da maza daban-daban matsayin ita da angon nata. Masu ?arancin hange sun yarda, masana da hangen nesa sun ?aryata. Daga baya ma dai abokan aikinta da yawa sun fito sun ?aryata ba ita bace editing ne..
¡ï¡ï¡ï¡ï
Gwaggo dan ALLAH ki daina kukan nan hakanan. Ni wlhy ba wai ba zanji shawararki bane ko maganar ki. Ba kuma ina tsoron Jalilah bane da har zan gagara ?ara aure. Kawai dai ni ra'ayina kenan zama da mace ?aya."
"Ra'ayinka ?in banza da wofi Imamu. Har ni zaka gayama wani ra'ayinka can na yahudanci. Mika rasa ko wane shara?ine baka cika ba na ajiye mace fiye da ?aya? Kaje bazan sake magana ba. Amma ka sani wlhy in dai na haifu cikin Balkisu da Usama bazan sake shiga sabgar zuri'arka ba. Sannan ina so daga yau ka sa?e hannunka daga ?a?an ?ar uwarka. Dan ba sai gobe ba a yau ?in nan Musaddiq zai dawo wajena da zama. Shima Hafizun yana gama makarantar nan zai dawo. Kaje ka cigaba da rayuwarka da naka ?a?an da matarka tunda dama haka take so kai ma kake so ku rayu daga ku sai ku batare da wani ya ra?eku ba saboda kada mu rage muku jin da?in duniyarku.."
"Amma Gwaggo dan ALLAH k....."
"Na gama magana ta Imamu, tashi kaban waje. Ka dai tabbatar min bani na haifeka ba kuma na amince da hakan. Sai dai Alhamdullah bakai ka?ai bane ?a balle hakan ya dameni, gasu nan bila'adadin harda jikoki duk mun godema UBANGIJI". Daga haka ta mi?e ta bar masa falon. Da kallo kawai Abba ya bita zuciyarsa na kai-kawo tamkar zata fito. Babu abinda ke dawo masa a rai sai furucin mahaifiyarsu a lokacin da take gargarar barin duniya dan jinya tayi mai tsanani, kuma Gwaggo Gudidi itace ta kula da ita har ta koma ga ALLAH. (Imamu kona bar duniya nayi imanin baku rasa uwa ba kai da ?ar uwarka. Dan haka in har kuka bijirema umarnin ?ar uwata ban yafe muku ba. Kuma in har ina da hakki a kanku a matsayina na mahaifiya nasan bazaku ta?a ganin dadai ba. Ku ?yautata mata, ku bita tamkar yanda zaku bini in sha ALLAHU zaku ribantu da hakan ba kuma zakuyi kukan rashina ba). Sosai tsigar jikinsa yaji ta tashi da tuno wannan magana. Dan tamkar a yanzu ne mahaifiyarsu ke fa?a masa shi da ?ar uwarsa mahaifiyar su Musaddiq. Bayan rasuwar ta kuma Gwaggo Gudidi itace ta cigaba da ri?e su. Itace tai musu aure da ga shi har ?ar uwarsa. Bata ta?a kuma gazawa ba a ?awainiyarsu data ?a?ansu har zuwa yanzu da tsufa ya risketa. Anya kuwa idan ya butulcewa wannan baiwar zai ga dai-dai? Bakin mahaifiyarsu kuwa bazai kamashi ba? Dan yana ?yautata zaton shine ma ya ta?ashi a yanzu abubuwa ke masa gangal-tangal uwa ya motar tirela mai ?auke da siminti akan gadar icce dake tsakkiyar teku, dan yasan wasu kaso na rashin mutuncin da Jalilah ta dinga ma Gwaggo nasa a baya. Sai dai baisan miyasa baya iya tsawatar mata ba duk da abin na masa matu?ar ciwo a zuciya. Sannan yana matu?ar ?aunar Gwaggo Gudidi, yana kallon fuskar mahaifiyarsu ne akan tata fuskar saboda tsananin kamannin da sukeyi. ya rabba yana a cikin tsaka mai wuya, dan baya jin zai iya ma Jalilah kishiya, yana kuma tsananin tsoron bijirema Gwaggo Gudidi bakin mahaifiyarsu ya kamashi.........??
_??To Abba adai sake tunani._
_Masoya ina ?ara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR??????ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE??_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ????_*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing??_*
*_??TSUTSAR NAMA....!!??_*
_(Itama nama ce)_
_?????????? ???????????? ????????_
_???????? ??????_
_???????? ????????_
____________
Toh Nazo maku
Da kayan arziki
Kudai kunsan mata sai da gyara
Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta
A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE
Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne
Muna da
Shedaniyar gumba
Gumba mai saying
Garin mai kabbara
Mai dalalan miyau
Wayyo dadi
Mai bunsuru
Dan jarida
Soyayya dole
Bakin kyalle
Tadire ta girke
Gumba mai likkafani
Maza taye
Zumar kwakwa
Zumar ridi
Zumar dabino
Zuma mai ma'ul ijaba
Farin jini
Mallakoki
Gumba kalla kalla da dai sauran su
A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba
Ga kuma maganin slimming
Gyaran nono
Maganin hips
Maganin Kara kiba
Da dai sauran su
Kayan mu tested and trusted ne
Muna maraba da masu siyan Daya ko sari
Muna Nan cikin garin kaduna
Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah
Ni ce taku har kullum
AMINA GACHI
07034404975
CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE
KADUNA
Phone no 07034404975
_____________
......."Alhamdulillah, I am very happy today we will send you off. I am very happy with the way you calmed down and gave us your cooperation. May God give you good health and protect the future".
Murmushi na saki ka?an ina jinjina kaina. Kafin a hankali na furta. "Thanks you doctor".
"Ni ya kamata nayi godiya".
Dariya yanda ya ha?a hausar da yanayin fitar kalaman ya bani, amma sai banyi ba nai murmushi kawai. A ?asan raina ina jinjina karamcinsa gareni duk da kasancewarsa ba ?abilata ba, sai dai ya nuna min kusancin musulunci dake tsakaninmu yafi na ?abilancin. A kusan tare muka mi?e ni da shi, a dai-dai nan akai knocking ?ofar ?akin jiyyar tawa. Kai tsaye ya bada izinin shigowa. Cikin gur?atacciyar hausa hamsha?iyar mace fara tas ?ar duma-duma tayi sallama ta shigo. Kallon cikin ido mukaima juna. Sai kuma matar ta janye nata tana maidawa kan doctor tare da rissinawa tana gaisheshi irin dai girmamawar ?abilu. Ya amsa mata da kulawa. Sai kuma ya nuna mata ni. Hankalinta ta sake maidowa gareni tana murmushi. Sai kuma cike da kulawa ta gaidani da jiki. Amsa mata nayi a ?arare, dan haka kawai naji matar batai min ba. Sai dai me bayani naji doctor na mata akan ya gama komai daya dace sai ta wuce dani. Kallonsa nayi a firgice zanyi magana sai kuma zuciyata ta ?wa?eni dan na tuna aljananci da hatsabibancin mai asibitin. A take na canja yanayi kawai na fara masa godiya.
Nurse ?in da suka kula da ni ne sukai min rakkiya har inda motar matar take. Babu abinda zuciyata take face luguden daka da sa?awa da kwancewa. Dole fa a wannan karon na ku?utar da kaina dan wannan ce kawai dama ta ta ?arshe ta ?u?uta a hannun mutumin nan. Saboda zuciyata ta gama tabbatar min shine ya turo matar nan, idan kuma bashi bane to tabbas zai iya min wani tarkon da ita kamar yanda akai min a Kano sanda na baro gidansa.
"Ya rabba aiko nayi mantuwa". Na fa?a dai-dai ina ?o?arin shiga motar da Semi ta bu?e min. Su duka kallona sukai, amma sai na sake zabura cikin hanasu damar min tambaya ina fa?in su jirani zan ?akko na dawo yanzun nan. Yanda naga babu wacce tai yun?urin bina nasan sun fahimceni, daga haka nai gaba cikin ?an sauri-sauri da sassarfa irin ta mai gaggawa. Ina tabbatar da na ?acema ganinsu na canja hanya. Duk da a rikice nake hakan bai hanani nemawa kaina dakiya ba na fara tafiyar nutsuwa. Da ?yar nake iya gane inda nake jefa ?afa har ALLAH ya fito da ni wajen wasu fanfuna da igiyoyin shanya. Akwai mutane tsiraru a wajen suna wanki, da alama wajen an tanadesa ne domin haka. Caraf idona akan hijjab dake shaye a igiya, tuni na tu?e na jikina na ja wancan na saka, ?an kwalin abayar jikina na na?a a fuska tamkar ni?ab. Daga haka na fito a wajen. Tambaya na dingayi har ALLAH yasa na fito a cikin asibitin gaba ?aya dan babu laifi babbane sosai. Ajiyar zuciya mai ha?e da hawaye ne ya kufce min ganina akan titi, sai dai babban tashin hankalin banda ko sisi a jikina banda kuma abin siyarwa sisi. Ba kuma zan yarda kowa yaban lift ba dan an koyan hankali a baya. Haka na shari titi ina addu'a, ganin nayi nisa sosai da Asibitin zuciyata ta tabbatar min da zafa su iya biyo bayana su ganni duk da na canja hijjab. Ai tuni na kauce a titi na shiga wani street da naga an rubuta a ?aramin symbol dake farkon shiga. Ganin an rubuta street nasan komai nisa zan fita, dan haka na zage damtse sosai naita tafiya duk da rashin ?arfin jiki ga kuma rana mai zafi dake dukana ban damuba.....
¡ï¡ï¡ï....
Tun su Semi na irga mintuna har suka kusan ha?a ashirin. Mamaki ne ya kamasu, dan haka ?ayar nurse ?in tace Bara ta duba Samraah ko ta ?ata hanya ne. Mintuna uku da wasu sakanni ta dawo a hargitse tana sanar musu itafa bata ganta ba. Sannan mutanen dake ata wajen sun tabbatar da bata dawo ba. Su dukansu har matar da doctor da aka je aka sanar mawa rikicewa sukayi. A take kuma doctor yay kiran Hayatu a waya...
Tako ina an bincike asibiti babu Samraah. Har cctv footage aka bincika, sai dai ta iya gaba kawai aka ga shigarta wajen inda ake wanki, kasancewar ta wajen babu camaras ?in sai ba'a fahimci komai ba. Saboda ta canja hijjab sannan ta fita, ta inda ta fitan ma camara na wajen yana da matsala. Matu?a Hayatu ya tada musu da hankali, gashi yayi kiran Maash ya sanar masa amma sai ya?i ce masa komai. Ya kuma san minene ma'anar shirun ogan nasa, dan haka ya sake birkicewa ya birkita likita da Nurses har ma da matar nan da tazo ?aukar Samraah ?in. Kai dama kowa na asibitin dan har securitys basu tsira ba da sauran ma'aikatan...
??????????
?uuuuu!! Razanannen taka birkin ya kara?e illahirin titin tare da sautin ihu mai firgitarwa. Ba hamsha?iyar matar dake cikin dan?arereiyar motar kawai ba, hatta da mutane dake kai kawo a street ?in tuni sunyo caa. Sosai Samraah da aka kusa ka?ewar ta matu?ar razana, dan dur?ushe tai ta cusa kanta a cikin ?afafunta nuna