Showing 18001 words to 21000 words out of 34206 words
saurare. Wani murmushin mai fa?i ta sake saki da cigaba da fa?in, "Godiya nake hajjaju. Dama akwai babbar haja da a yanzu akai cinikinta zuwa gidanku. Na tabbatar irin kalarki ce shiyyasa ma na sayar babu ja'inja bayan na gane daga ina masu sayen suka fito. Na tabbata idan kikaga wannan hajar sai kin sake min sabon biya dan ni kaina bu?atar ku?i kawai ta sakani sallanawa amma raina ya biya sosai."
Amsar da Hajiyar ta bata daga can ya sata sake sakin dariya. "Ayyah! Hajjaju Ayya. Ai ku manyanmu ne. Kodan girmamawa ma kauda kai ga abinda ya dace daku. Sai dai kinga kayan dan na tabbatar yanzu suna gab da zuwa gidan naku. Duk da dai tace zata bada as gift ne. Kuna wani shagali ne a gidan naku babu gayyata Hajjaju?".
Shiru alamar saurare, sai kuma ta tashi zaune da ?yau tana furta, "Woow fantastic Hajjaju. Ai dolene muzo wannan birthday party kuwa kodan ke. Dan haka sai kin gammu".
Daga haka sukayi sallama ta yanke wayar tare da ajiyeta gefe tana wata kalar sha?iyyar dariya. A ranta tana ayyana (lallai yarinyar nan tazo da arzi?i. Ai tun da na ganta nasan mabu?in arzi?ina ce ita, dan zoben da babalawo ya bani yay wani irin haske da bai ta?a yi akan sauran yaran da nasarata ke samowa ba. Sai dai fa nima yawuna ya biya, dan komai yaji a jikin yarinyar nan, ga wani shegen fata kamar na dorinar ruwa. Dan haka sai na ?an?ana koba yanzu ba) ta saki wata dariya a zahiri. Hakan yay dai-dai da shigowar Janny. Ko ka?an batai mamakin gani da jin dariyar da Madam ?in tata keyi ba. Sai ma takowa da tai cike da yau?i jiki na girgiza ta fa?a mata a jiki......
(Hummm??)
????????
*_MAASH MANSION_* Shine rubuce da manyan ba?i da akai da kalar ruwan gold a jikin babban makeken ba?in gate ?in gidan da ya mamaye kaso mai yawa na street ?in. ?irjina yay wata irin masifar harbawa, ba sai an min bayani ba, hakan na nufin wannan katafaren gini shine gidan su Maash ko gidan Maash. (Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un) to yaya hakan ta faru? Maash ?in dana sani ne a Lagos ko kuwa wani ne mai irin sunansa?. Bani da mai bani amsa sai jikina dake rawa sosai amma babu wani yin?uri da zan iya yi. Dan tuni wasu gar?a-gar?an securitys dake tsaren ?ofar sun mi?e, sai da suka gama kallemu ?aya bayan ?aya da gaida Alaja cikin girmamawa sannan ?aya daga cikinsu ya danna remote da ke hannunsa, a hankali gate ?in ya shiga zuge kansa. A jere motocin uku duk suka shiga makeken compaund ?in da sam baida iyaka ga mai kallo, kowacce ta tsaya a muhalin da ake son ganinta. Dolene ka shigo wannan gida ka tsarkake sunan UBANGIJI mai rahama mai jin?ai, dan shike samarwa ga wanda ya so a lokacin da yaso. Gini ne daya ginu karkashin mahaukatan ma?udan ku?a?e da sam zaka iya rantsuwa da ALLAH ba'a Nigeria kake ba idan kana a cikinsa. Dan a iya compaund kawai da abinda ke zagaye da gidan, da kallon ginin a tsaye ya isa tabbatar maka da naira tayi kuka. Wani irin ?un?ulallen gini ne mai matu?ar armashi da ?ayatarwa. Ga wasu irin korayen ciyayi da furanni masu azabar ?amshi da sanyaya gida da ?awatashi da sukaima ko'ina ado. Ga jibga-jibgan motoci jere a cikin rumfuna kusan biyar a tsare acan nesa sosai, wasu ma rufe suke da tempol. Sosai ma'aikata ne ke kai-kawo, dan dole irin wannan gidan yana da masu kulawa ta kowanne fanni. Driver ne ya fara fita a motar ya bu?ema Alaja. Kafin ita kuma tai min nunin na fito. Jikina a matu?ar sanyaye na fito ina mai bin katafaren harabar gidan da kallo. Brain ?ina gaba ?aya ta gama kwancewa, dan tunanina ya rabu biyu ne tsakanin ha?uwar gidan da sunan dana gani rubuce ?aro-?aro matsayin mamallakin gidan.
"Oya muje".
Furicin Alaja ya katse min tunani. Tamkar wadda ?wai ya fashewa a ciki na fara takawa a hankali ina bin bayansu. Drivern ta ne yay saurin bu?e dankareriyar ?ofar mai wani irin zubin ?yau da ?aukar hankali da duk mai kallo zai iya tabbatar da an sayeta da ku?a?e masu nauyi. Alaja ce ta fara shiga da sallama, yayinda ni kuma ke biye da ita kamar bindi. Sai sauran abokan tafiyarmu biye damu. Sai dai babu sauran yaran da aka ?akkomu tare da alama an barsu a mota. A ha?a??en falo dake matsayin main perlor muka fara ratsawa. Komai na cikinsa a tsaftace yake ga ?amshi da sanyin ac kamar ka ?ingire barci. Sai dai babu kowa a cikinsa ko television ma a kashe yake. Bamu tsaya anan ba, mun shiga falo na biyu daya kasance katafaren gaske. Ha?uwar falon ba'a magana. Dan ya ?awatu da ?awatuwa ta musamman. Komai sai ?yalli da ?aukar ido yake tamkar ba'a talauci a duniya. Shima dai ?amshin ke tashi mai nutsuwa, sai ?afar bene da suka zama maha?ar sassan gidan guda uku. Gashi ?aton gaske bana wasa ba, dan duk da set na kujeru kusan biyar da ke cikinsa group-group zama a iya kawo wasu set goma sha biyar duk ya ?auka batare da wasu sun matsi wasu ba.
Anan kam akwai mutane. A hankali dattijuwar matar dake zaune cikin kujera 1sitter da laptop a gabanta tana sarrafawa a group na set ?in kujerun dake farkon shigowa ta ?ago fuskarta ?awace da murmushi, laptop ?in da tun shigowarmu ta dakata da sarrafawa ta ture gefe, cikin ?asaitacciyar muryarta ta furta, "Idanu na ne kemin gizo ko kuwa mafarki nakeyi? Da ganin Auta".
Dariya Alajah tayi tare da nufarta ta rungumeta. Dai-dai nan wasu ?yawawan ?ammata uku dake can ?ayan rukunin kujerun suka taso suma a guje suna fa?in, "Oyoyo Aunty Mamah. Juyowa tai ta rungumesu suma cike da kulawa da farin ciki. Sai da suka gama murnarsu suka nutsu kafin su maida hankalinsu garemu. Ni suka fara zubama idanu, kafin su maida ga sauran hajiyoyin fuskokinsu a washe da murmushi suna musu barka da zuwa cikin nuna girmamawa. Ni dai ina daga tsaye gefe dan haka kawai naji shakkar ?arasawa garesu har sai da Alajah tai kirana tare da nuna min na zauna. Inda ta nuna min ?in nakai zaune ?asan carpet. Kaina a ?asa batare dana kallesu ba na shiga gaishesu. Hajiyarce kawai ta amsa, amma ?ammatan nan ko kallo ban ishesu ba. Musamman ma babbar ciki wani kallon tsana data wurgamin tun farko sai da najisa har a ?asan raina. Dan haka nima sai banbi takansu ba...
Munyi zama na kusan mintuna talatin a wajen kafin hajiyoyin nan biyu da muke tare da su su mi?e alamar zasu wuce. Hajiya da Alajah ne sukai musu rakkiya. Yayinda ni kuma aka barni nan ma?ure waje guda ?ammatan nan na bina da kallon banza. Kusan mintuna biyar sai gasu sun dawo. Basu zauna anan ba, sai umarni da suka bama ?ammatan cewar ai kiran Mama Bilki shugabar masu aikin gidan taje dani sashensu zasu nemeta. Hakan kuwa akayi, dan atake babbar cikin ?ammatan ta ?aga telephone tai kira, cikin gadara da izza ta isar da sa?on Alajah da tuni sun haye upstairs ta ?aya daga cikin ?afar bene ukun data ?awata makeken falon na alfarma. Ba'a ?auki wani lokaci mai tsaho ba sai ga wadda nake ?yautata zaton Mama Bilki tazo. Babbar mace ce sai dai baza'a kirata tsohuwa ba. Abin mamaki kuma jikinta fes kamar bamai aiki ba, amma tabbas zata iya haihuwar kamata. Cikin fara'a da kulawa ta bani umarnin tasowa na bita. Nima sai na mi?e jiki a sanyaye nabi bayanta ina mai sakin ajiyar zuciya. Dan dama zama a tsakiyar shegun yammatan duk ya gundireni. Ina jin wata a cikinsu na sakin tsaki amma sai nan juyoba balle naga wacece.
Tafiya mukai mai tsaho sosai data bani mamaki dan kamar bama a cikin gidan muke ba. Kasancewar bata hanyar da muka shigo dasu Alaja bane yasa ban iya na fahimci komai ba. Sai ma sake zama wata ba?auya nayi dan kalle-kalle nakeyi iya iyawata. Sosai nake sake girmama girma da ?udira ta UBANGIJI. Dan wannan gida sai ka rantse ba hannu ne ya gina shi ba saboda ?awatuwa da ?annar dukiya da akai wajen saka masa kayan alatu. Ban sake tabbatar da gidan ?aton gaske bane sai da muka ?ullo wata hanya data fiddomu wajen ginin tanan ma. Ashe ta gaban girmansa ba komai bane. Ta can baya da ginin apartment na masu aiki yake ?angaren maza daban na mata daban shine ainahin ?aton gaske. Dan shi ta can gefe akwai ?aton garden da ko ba'a fa?a maka ba kasan shi ?in ne. Sannan daga hannun dama akwai wani ?aton wajen wasanni na yara da manya. Akwai wajen ?wallo, wajen..... Kai dama wasu daban da ban gama tantancewa ba dan iya abinda idona ya hango kawai nake sanar miki Bily. Shi kansa sashen masu aikin da muka shiga sai da notikan kaina suka nema kwancewa. Dan tamkar ba na masu aiki ba. Komai fes akwai kuma kayan ?awar suma duk da basu kai na sashen masu gidan ba ko kusa ko ka?an. Amma dai duk mai hankali ya kalla yasan an girmamasu an mutuntasu. A tare ?ammata kusan takwas da muka samu a falon zaune suna kallo suka zuba min ido fuskokin wasunsu da fara'a, wasu ko kallo ?aya sukai min suka ?auke kawunansu. Sannu wanda suka nuna kulawar su suka shiga yi min, hakan yasa nima na amsa musu da kulawa tare da gaishesu duk da sukansu bazasu wuce sa'anni na ba har ma da wa?an da zan iya girma..........??
_Masoya ina ?ara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR??????ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE??_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ????_*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing??_*
*_??TSUTSAR NAMA....!!??_*
_(Itama nama ce)_
_?????????? ???????????? ????????_
_???????? ??????_
_???????? ????????????_
__________
_Koda ku?inka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ?an kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sau?i da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin bu?atunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ?an yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ?ai-?ai zamu tsaya ba harda sari ga mai bu?ata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sau?i da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. ?an kasuwa masu sari da masu sayen ?ai-?ai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*??_
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG
https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5
___________
......Wajen zama Mama Bilki da naji sun ambata da Mama ta nuna min, babu musu na zauna. Ta nuna wata dake gab da inda nake tana fa?in, "Sayyada kawo ma ba?uwarmu ruwa da abinci ko". Cike da fara'a wadda aka kira Sayyada ta amsa tana mi?ewa. Wata ?ofa dake a falon can inda ?aton dining table yake na katako ta nufa, mintina ?alilan kuwa sai gata da tire madaidaici a hannunta. A gabana ta dire tana murmushi da fa?in, "Sister ga abinci ko."
"Nagode".
Na fa?a a hankali nima ina murmushin ya?e. Wajen zamanta ta koma ta zauna. Yayinda ni kuma na zuba ma abincin ido nai shiru har sai da Mama Balki ta zungureni sannan na kawo numfashi. Abincin ta nuna min alamar naci, na ?an sauke ajiyar zuciya. Sai kuma cikin tausasa murya nace, "Mama dan ALLAH zan fara salla tukunna".
Cike da fara'a tace min, "Lah ai babu komai ?iyata. Kinga A'i tashi ki rakata ?akinku sai tayi a can kunga kun samu abokiya kuma kun zama ku uku kamar kowa. ?an tsuke fuska wadda aka kira da A'i tayi, sai dai kuma batace komai ba ta mi?e. Nima mi?ewar nayi nabi bayanta ?an lungun da naga ta nufa. Dogon corridor ne mai ?auke da ?ofifin ?akuna kusan goma. Hannun dama biyar haggu ma biyar. Babu yabo babu fallasa bayan mun shiga ?aki na biyu a hannun dama ta nuna min ?ofar bayi. "Ki shiga nan". Daga haka ta juya ta fita. Komai bance da ita ba nima, face cikowa da idona yayi da ?walla. Ji nake komai ya ?wace min, gaba ?aya nama gagara hasashe balle tunanin komai akan wannan rayuwa dana jefa kaina. Dan a yanzu kaina nake zargi ba kowa ba. Ina ma kaina kaico akan bin hajiyar nan da nayi, sai naji inama tashar na nufa koda ro?o na samu ku?in motar zuwa Kano. To amma bakin al?alami ya riga ya bushe. Ni bama wannan ne tashin hankalina ba. Son sanin wanene mai wannan gidan shine tashin hankalina. Karfa ya zamto ANYI GUDUN GARA ne AN FA?A GIDAN ZAGO. Kai amma da nayima kaina kaico. In sha ALLAHU ma bazai kasance hakan ba.
Bayan na idar da salla na jima zaune a wajen shiru, dan har sai da A'i ya biyo bayana sannan na mi?e na bita. Kamar yanda na barsu haka na samesu. Sai dai an sake samun ?arin mutum uku suma duk manyan mata dan da ka?an Mama Balki zata iya girmarsu. Gaishesu nayi a ladabce, duk suka amsa min babu yabo babu fallasa. Na ?an ji jikina yay sanyi, sai dai ban bari al'amarin nasu yayi tasiri a raina ba na fara cin abincina. Ka ?an na tsakura nace na ?oshi, Mama Balki tai murmushi da fa?in, "?ar nan ba?unta zakiyi mana?".
Murmushi kawai nayi kaina a ?asa batare da nace komai ba. Itama sai tayi ?ar dariya da cigaba da fa?in, "To ai shikenan. Bara nayi wani karanbani duk da Aunty Mama bata sanar min ke wacece ba ko matsayinki. Amma dai duk wanda aka kawo nan mun san namu ne ai. Minene sunanki?".
Shiru nayi jimmm kamar bazance komai ba. Sai kuma na sauke ajiyar zuciya a hankali na furta Kandala".
Su dukansu sai da naga alamar shock a fuskokinsu game da jin sunan nawa. Amma ganin yanda na fiske abuna ya sasu basarwa. Wasu a cikinsu suka furta Masha ALLAH. Yayinda wasu suke ta?e bakuna a yamutse. Mama Balki ce ta katse yanayin da nuna kanta. "Ni sunana Balkisu, amma suna kirana da Mama Balki kamar yanda kika ji. Ni ce shugabar duk wani ma'aikacin wannan gida musamman mata. Mijina kuma shugaban ma'aikata maza. Wannan kuma ta kusa dake Sayyada, sai Afrah, sai Sumayya, sai A'i, sai Asiya, sai Bintu, sai Mansura, sai Kairat, sai Bahijja, sai Sadiya suna kiranta Aunty Sadiy, itama tana da miji. Ta nuna ?aya daga cikin manyan matan nan uku da suka shigo daga baya. Sai Aunty Kubrah itama tana da miji, sai aunty Falilah. Dukanmu muna aiki ne a wannan gida. Kowa kuma da fannin sa. Wasu gyara, wasu wanke-wanke. Kowa kuma da sashen da yakema aiki dan komai a ?a'idarsa yake. Idan har kema tamuce zamuji fannin da aka kawoki ki kasance".
Sosai ?irjina ke wani kalar luguden daka tunda ta fara. Sai dai inata dauriyar danne yanayin nawa. A rain kuwa komai ya dagule min, babu abinda nake ambato sai kalmar (Na shiga uku. Yanzu kuma boyi-boyi na koma kenan? Mike shirin faruwa dani ne haka?). Bani da mai bani amsa, dan haka na maida hankalina ga Mama Balki dake cigaba da min bayani. Sai dai sam bana fahimta har tayi ta gama. Mun cigaba da zama har akai kiran sallar la'asar. Sai a sannan dukanmu muka mi?e. ?akin dai ?azun naje tare da wadda ta rakani A'i sai abokiyar kwananta Bahijja. Bahijjar akwai fara'a, dan sai jana take jikinta cike da kulawa. Muna idar da salla ta kwashe tarkacen kaya da suka jibge a ?ayan gadon ?akin dan uku ne ta ce, "Nan shine gadonki Kandala". Yanda tayi maganar da murmushi ya sani nima mayar mata da murtani ina jinjina kai, kafin na ?ora da mata godiya. A'i dai na jinmu amma tai kamar bata ?akin. Bahijja dake ?o?arin saka uniform ta sake kallona da fa?in, "Kiyi kwanciyarki ki huta mu zamu je can sashen yin aikin yamma. Idan kuma zakiyi kallone to muje falo".
Da sauri na girgiza mata kaina. Sai kuma na murmusa da fa?in, "A'a bari na kwanta ?in, ai bazaku jimaba ko?".
Tsaki akaja kafin ta bamu amsa, atare muka kalla A'i dake ?o?arin ficewa alamar itace tayi tsakin. Murmushi Bahijja tayi da maido idonta gareni. "Karki damu da ita haka take kamar mai aljanu. Nima farkon zuwana haka ta dinga min kamar mai jin haushin mutane. Amma bari kiga nan da kwana biyu