Showing 9001 words to 12000 words out of 34206 words
alamar sada?arwa kawai. Haushi da takaici ya saka mutane yimata caa da fa?a, dan duk wanda al'amarin ya faru akan idanunsu sun tabbatar da laifin ta ne ba mai motar ba. Ganin yanda wasu ke ?o?arin kai mata duka ma adalilin yanda har yanzu ta?i motsi daga durkuson razanar da tai yasa matar dakatar da su da sauri ta hanyar ri?ota ta mi?ar. Rawa jikin Samraah ya cigaba da yi har hakan na rinjayarta tamkar zata fa?i. Duk wanda ya kalleta yasan a gigice take har yanzu, dan haka matar ta shiga bama mutanen daketa faman hargowar zagin Samraahn ha?uri tare da jan hannunta ta bu?e motar a gefen mai zaman banza ta sakata. Sai da ta rufe sannan ta sake fuskantar mutanen da har yanzu sun kasa barin wajen..
"Kowa yayi ha?uri dan ALLAH kuma mu mata uziri. A yanayin halin rayuwar da ake ciki yanzu muma zamu iya tsintar kammu a fiye da yanda yarinyar nan take ciki yanzu. Tun dai ma komai bai sameta ba ai Alhamdullahi ko, sai muyi fatan ALLAH ya kiyaye gaba".
Da kalmar (Amin) suka shiga amsa mata cikin nuna gamsuwa da yabama ?ya?y?yawar zuciyarta, dan ba kowa bane zai iya yin abinda tai ?in. Daga haka kowa ya fara watsewa itama ta shiga motar dan ta tsarema mutane hanya har wajen ya fara tara mutane musamman masu gadi na cikin gidaje nata fitowa. Bayan rufe motar ta ?an kalli Samraah ta sauke numfashi mai kauri, batare da tace komai ba taima motar key cike da ?warewa ta harbawa saman titi da ?yau. Tafiyar da bata gaza mintuna uku ba ta samu waje ta gangare gefen titin, dan bata son tai nisa da anguwar ta zamto kuma anan yarinyar take duk da ta ganta da ni?aff a fuska. A yanzu ma dai yarinyar kanta ?udundune yake a cikin ?afafunta, yayinda sautin shashshekar kukanta ke fita ka?an-ka?an.
"?iyata a ganina godema ALLAH ya kamata muyi, dan da abinda yaso faruwa ya faru da ga ni har ke da ba wannan matsayin muke ba ai. Kiyi ha?uri ga ruwan nan kisha ki samu nutsuwa ko". Shiru kamar bazata motsa ba, kusan cikar minti ?aya kuma sai ta ?ago, Samraah ?ya?y?yawace sosai ta yanda hawayen da suka ma fuskarta kaca-kaca bai hana bayyanar hakan ba.
Idanu na tsira mata mai ha?e da sauke ajiyar zuciyar dawowa hayyaci, sai kuma na kauda kai na, a hankali na furta, "Ba kukan tsorata nake ba Hajiya, kukan ba?in cikin rashin tabbatuwar abinda nai fata ne ya sakani kukan nan. Inama ace kin ka?eni na huta da wannan rayuwar da babu komai a cikinta face kayan ?unci da ba?in ciki da ru?ani. Inama ace kin ka?eni na mutu banko shuraba na tafi tafiya ta har abada da babu dawowa na iske su Abbana. Hajiya dan ALLAH ki fitar dani a motar nan na sake tarar gabanki ki bi takain....."
Cikin sauri ta katseni da fa?in, "Haba haba ?iyata wace magana kenan! Miyay zafi haka da irin wa?annan furuci masu tsauri. Ai duk da mun san zamu mutu bama fatan mutuwar a kayinmu sai dai dan babu makawa sai ta zo ne. Amma muna addu'ar a koda yaushe ALLAH ya jinkirta mana kodan tara ayyukan alkairi da neman gafarar UBANGIJI da ga na sharri da muka aikata. Minene matsalarki? Miyasa kike ma kanki fatan mutuwa a wannan ?arancin shekarun naki da zamu iya kallo a matsayin yanzu ma kika fara rayuwar, ko kika fara bu?atar ta? Idan ban shiga abinda ba hurumina ba ki daure ki sanar min ko zan iya fahimtarki da taimakonki da wani abu...."
"Ba taimako nake bu?ata ba Hajiya, sannan babu wani abin sha'awa ko birgewa da ?awatarwa a labarina ko bayana. Ganni ki barni a yanda kika ganni yanzu kawai." na ?are maganar da yun?urin ?alle murfin motar zan fice. Da sauri Hajiyar ta ri?oni tana girgiza kai. "A'a ?iyata yi ha?uri ki saurareni". Juyowa nai na ?an kalleta, sai dai bance komai ba........??
_Kuyi ha?uri da wannan Please. Zuwa anjima idan na samu damar yin wani zan ?aro muku. Wlhy abubuwane suka min yawa amma ina fatan kammalawa na dawo muku da ?arfina????_
_Masoya ina ?ara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR??????ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE??_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ????_*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing??_*
*_??TSUTSAR NAMA....!!??_*
_(Itama nama ce)_
_?????????? ???????????? ????????_
_???????? ??????_
_???????? ??????_
........A hankali ta ?an sakar min murmushi da fa?in, "Ko zaki iya mun alfarma".
Cikin ?osawa nace, "Tami?".
"Ta sanin inda zakije yanzu?".
"Ban san inda na nufa ba, sai dai ina fata da addu'ar koma ina ne ya kasance hanyar cimma ajalina".
?an jimm Hajiyar tai kamar mai nazari, sai kuma ta saki murmushi mai ban mamaki tana wani juya idanu cike da salo, "Bazan hanaki tafiya ba, amma zan so ki bani dama ta ?arshe muje gidana, maybe zan iya nuna miki hanyar cimma nasararki ta barin duniyar kamar yanda kike fata".
Idanu sosai na tsira mata tamkar mai son tanka?e gaskiya da rairayeta akan fuskarta, kusan minti ?aya na ?an kauce zuciyata na ayyana min na bita na samu mafaka koda na wasu kwanaki ne, dan na tabbatar a yanzu na koma Kano makirin nan zai iya bina. Kuma Abba da su Kawu bashi ni zasuyi, amma yanzu idan na la?e a bayanta zan iya kiran Yaya Musaddiq muyi shawara dan shiga Kano kai tsaye yanzu ha?ari ne. Sai dai kuma ita kanta bawai ina jin na yarda da ita bane ba ma ai. Amma bari na gwada sa'ata mugani. fuskata na ?ago na ?an kalleta da fa?in, "Kina so kiyi wasa da hankalina ne kawai Hajiya".
Da sauri ta dakatar da in da fa?in, "Ko ?aya ba haka bane ba. Mizaisa nai wasa da hankalinki ni kuwa, dama kawai nake bu?ata daga gareki zaki tabbatar da abinda na fa?a ?in in sha ALLAHU".
Nan ma dai shiru nayi ina kallonta kawai, tai saurin fa?in, "Ki yarda dani koda na sati guda ne, idan kinga ba hakaba zaki iya ?aukar mataki kowane iri".
Shiru na sake yi na wasu ?an sakanni kamar mai nazari, sai kuma batare da nace komai ba na dawo da jikinna cikin motar sosai tare da jawo ?ofar na rufe kamar yanda take. Sosai Hajiya ta sauke ajiyar numfashi da har ya bani mamaki, sannan ta ?an kalleni, sai dai batace komai ba. Nima ban sake cewa komai ba ina dai addu'a a zuciyata ALLAH ya hanata nasarar cutamin, ALLAH kuma yasa ba daga ?ar?ashin makircin makirin nan Maash tazo gareni ba.
(???????)
Tunda Hayatu yake bai ta?a shiga tashin hankali irin na yau ba musanman a yanzu da yake waya da Maash yana mai sanar masa guduwar Samraah daga asibiti. Dan Maash ?in yayi wata ?ar tafiya ne ta gaggawa, tunda ya fara harkar business duk inda zai je yana tare da Hayatu, amma a wannan ga?ar ya barsa saboda al'amarin Samraah da ya kasance da ga shi sai shi suka sani.
Har tsawon mintuna biyu babu alamar Maash zai amsa. Kuma yana online. Hankalin Hayatu ne ya sake tashi, muryarsa har har?ewa takeyi wajen sake fa?in. "Wlhy nayi duk yanda kace Sir, zaman jiran isowarsu gidan kawai nake ma amma tai kirana wai basuganta ba. Ba laifina bane, ba daga ?angarena bane aka samu kurkure ka yarda dani. Ka kuma bani izinin sanarma ?an sanda na tabbatar tana cikin garin Abuja bata isa fita ba". Shiru nan ma Maash ya?i ya tanka. Wayar Hayatu ya cire daga kunnensa ya duba, har yanzu yana online ?in dai tankawar ce bazai yi ba. Yafi kowa sanin halin Maash yanzu, dan ko iyayensa bazasu fa?a masa hakan ba. Ko motsi da idanu ogan nasa yayi yakan fahimci yaren balle. Ya tabbatar shirunsa a yanzu na ?acin rai ne, kuma bazai tanka masa ?in ba har sai idan shine yaso hakan. Hakan kuwa akayi, bai tanka masan ba shi kuma ya kasa yanke kiran saboda shakka, haka ya ha?ura akaita ?ibar masa ku?i har tsahon fin awa sai da shi uban gayyar ya gaji dan kansa ya yanke kiran sannan hayatu ya kai zaune cikin kujera jagwab dan tun ?azun ko zaman ya kasa yi. Kansa kawai ya dafe yay shiru zuciyarsa na gudu. Dole ma duk yanda zai yi yayi dan gano yarinyar nan kafin cikar awanni ashirin da hu?u. Idan ba hakaba yasan akwai matsala.....
????????
Wata shegiyar dariya Alhaji Sadisu mai agogo babban aminin Abba ya saki harda ?ya?y?yewa. Cikin ?uluwa da nuna jin haushi kuwa Abban ya zuba masa idanu. Sai kuma ya yun?ura zai tashi amma Alhaji Sadisun ya ri?osa yana fa?in. "Afuwan afuwan Imamu. Wlhy abin naka ne zabban dariya. In kana abu sai naga kamar wani ?an yaro bai mai garjejen saurayin ?a kamar Abbas ba. Yo banda abinka Gwaggo ai gata tamaka wlhy. Ka bu?e bakin aljihu kawai malam musha biki ai ba wuce auren kai ba. Dama dai kaine kaso maida kanka pastor zama da mace ?aya shekara fin ashirin bayan ALLAH ya baka dukan rufin asiri. Yo ALLAH na tuba da ana yin fin hu?u da ba tuni nayi ba".
"Amma dai ai na sanar maka matsalata ko Alhaji Sadisu. Kuma kaina shaida ne akan halin Jalilah tunda na gwada son ?ara auren a shekarun baya har sau biyu amma aka nema nakasa yaran mutane."
"Yo dan ta samu nasara a baya sai akace yanzu ma ka karaya zata samu. Alhaji Imam zama namiji kaji, tun farko kai ne kake ?ata shirin dama da kake sanar mata da wuri. Kayi shirunka yanzu har sai ?inyar makaho ta nuna a hannunsa sannan ka bada filin fara wasan jifa tunda tsoronta kake ji".
"Humm bazaka gane ba kawai, amma zan iya yarda da shawararka akan ?oye matan. In kuma hakan zata faru fa sai dai na nema auren a wajen kano."
"Wannan duk mai sau?ine, kabar komai a hannuna kawai. Kai dai jeka ka fara shirin gyara inda amarya zata zauna nan da sati ?aya zan maka jagora kai da kaina sai ka gode min saboda inda zan kaika wlhy".
Murmushi Abba yay a karo na farko, dan haka kawai yake jin kuma batun ?ara auren na sake masa tasiri a zuciya....
??Hummm Abba cin amana ko.
_________
Gida ne mai ?yawun gaske madaidaici muka isa a anguwar mai tama kamar yanda na gani a symbol, dan komai najin da?in rayuwar gani da ido a kwaishi. ?amshi da tsarin gidan yafi komai ?aukar hankalina, dan haka nake ta ?an kalle-kalle a kaikaice. A karo na babu adadi Hajiya da tuni takai zaune cikin ?aya daga kujerun falon ta dubeni ganin yanda nai tsaye a farkon shigowa. Cike da kulawa ta ce, "?araso ciki mana ?iyata. Kar kiji wani shakku ko tsoro, wannan shine gidana anan Abuja, sai dai bana zaman daya wuce sati biyu a cikinsa a duk ?arshen shekara. Sai kuwa idan wani uziri ne ya kawoni nakanzo nai kwana ?aya biyu har ma zuwa uku wasu lokutan na koma. A yanzu haka ma kwana biyu ya rage na wuce". A hankali na ha?iye yawu alamar son cewa wani abu, sai dai kafin nace ?in Hajiya ta katseni ta hanyar ?wala kiran sunan "Janny!".
"Yes Ma'am".
Wata murya ta amsa daga can gefen wata ?ofa da hanyarta aka shirya kujeru da tebiri. Kafin na gama nazarin tsarin da kujerun dining ?in sukayi da zamansu a wajen wadda Hajiya ta kira da Janny ta fito. Budurwa ce itama sai dai zata girmeni sosai, da gani shigarta da uban gashin attachment dake saman kanta ya isa baka amsar ba musulma bace. Cike da girmamawa Janny ta sake gaida Hajiya tana ?an satar kallonna. Nuna ni Hajiya tai da fa?in, "Kije da ita ciki, tai wanka a bata abinci".
Murmushi Janny tayi a karo na farko, cike da girmamawa ta amsawa Hajiya tana nufoni. "Sannunka". Abinda Janny ta fa?a kenan tana mai ri?o hannuna. Ban amsa mata ba, sai ma ?o?arin turjewa da nayi alamar bazanje ba. Hajiya dake kallonmu ta sake sakin murmushi. "Kinga ?iyata nasan mike a ranki, karki damu shi komai na rayuwa mataki-mataki ne tamkar ajin makaranta. Ki kwantar da hankalinki zamuje ga?ar da kike bu?ata. Bani nai miki al?awari ba".
"Amma Hajiya....."
"Shiiii!! Kar kice komai bita kawai". Hajiya ta fa?a cikin katseni tana tsuke fuska a karo na farko. Canjawar fuskar Hajiyar ya ?an firgitani, dan haka nabi Janny kamar yanda aka bata umarni tun farko....
Cikin dauriya da danne duk abinda ke mun kai-kawo a cikin rai nayi wanka na fito fes dani cikin doguwar riga mara nauyi ?ar kanti da Hajiya ta bani na saka. Ga wani ?amshi mai da?i na tashi a jikina. Hatta da dun?ulallen gashina da zaman asibiti yasa baya samun gyara sai da na wanke na busar da hair dryer dana gani a toilet ?in. Yanda na fito da shi ne a bu?e yasa Janny sakin baki tana kallona. Fuska na ?an tsuke amma sai hakan bai sata yin shiru ba sai da tayi magana. Da ga ?arshe ta la?emin wai zata tayani gyarawa. Mai sosai Janny ta saka min masu da?in ?amshi da ma wasu abubuwan da suka sake mi?ar da tsahon gashin nawa daya fara dankwafewa tsaff, sannan ta fake min shi a ribbons. Ni a karan kaina sai da naji da?in kan nawa dama a kwanakin nan ya isheni da ?ai?ayi. Shiru nayi kawai zaune ina ?arema kaina kallo, a take naji tausayin kaina ya kamani. Wasu hawaye masu zafi da ?aci suka shiga sakko min. Hannu nakai na sharesu da sauri, saboda tuna nayi al?awarin bazan sake kuka ba akan halin da nake ciki. Plate ?in da aka kawo min na abinci na ?an tsurama ido, sai kuma na tureshi gefe dan bana bu?atarsa a yanzu duk da uban ?amshin dake tashi mai tabbatar da abincin zaiyi da?i koda banga minene ba. Zamewa nai kwance a saman lallausan carpet ?in da shima ke ta tashin wani irin ?amshi mai da?i, gashi tsaf babu datti. Gajiya da wahalar dana sha ya sa barci yin awon gaba da ni cikin ?an?anin lokaci..........??
_Masoya ina ?ara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR??????ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE??_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ????_*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing??_*
*_??TSUTSAR NAMA....!!??_*
_(Itama nama ce)_
_?????????? ???????????? ????????_
_???????? ??????_
_???????? ??????????_
......"Madam bafa taci abincin nan ba, ko bu?e plate ?in ma batai ba kuma tayi barci." Janny ta fa?a cikin nuna damuwa.
?aramar dariya Hajiya ta sauke tana wani lumshe idanu, sai kuma ta bu?esu akan Janny cike da salon irin na wayayyun mata da suka gogu da sanin duniya. "Barta yunwar ai ba ?ar gidansu bace, dan kanta ma zata ?auka taci".
Dariya tayi itama Jannyn da jinjina kanta. "Hakane Madam. Amma yarinyar yana da ?yau fa sosai, ina ka samo shi haka? Ko dashi zamuje Lagos ne?".
"Tsintacciyar mage ce, dan haka ma na dawo da tafiyarmu gobe kafin ta canja shawara. Saboda na kula babbar kaddarace wannan, kwalliya da sutura kawai take bu?ata".
Sosai Janny ta washe ha?wara, dan duk hausar da Hajiya tai tsaff ta gane kasancewar taji hausa sosai. Hajiya ma murmushin taketa faman yi, dan ita kanta tasan zata ?aru da yarinyar sosai...
Washe gari kamar yanda Hajiya ta fa?a suka tashi da shirin wucewa Lagos, harda Samraah nan dako sunanta basu sani ba har yanzu. Tunda suka tambayeta sau ?aya tayi shiru basu sake tambayar ba. Tun jiyan kuma tana ?aki kwance sai dai akai mata abinci a ?akko kwano.. Janny ce mai ?o?arin kai-kawon, Hajiya dai nata bada umarni kawai, bakuma ta sake neman ganin Samraah ba tun shigowarsu gidan sai a yanzu da suka kwana suka yini dan tafiyar yamma zasuyi.
Ita dai Samraah bata san ina zasu je ba. Koda ta tambayi Hajiya kuma sai cewa tai ta jira zata gani. Badai tace ita ?ar Kano bace, zata bata mamaki ne. Al'amarin kamar asiri Samraah ta gagara cewa da Hajiya