Showing 3001 words to 6000 words out of 34206 words
Mansoor dake kwance sam?al a ?asa babu alamar rai a tare da shi. A tare suka ?agosa, sai dai me yaraf ya koma alamar babu rai. Wani mahaukacin ?ara Mamy ta fasa mai firgitarwa, tamkar ?iftawar ido sai gata ?asa wanwar itama ta sume musu. Sake harmutsewa ?akin yayi, dole aka kwashesu zuwa asibiti kamar yanda wasu suka bada shawara.....
*_ABUJA_*
Kaifin hasken rana da nake ji mai ?arfi a saman fatar idanuna ya sani motsasu a hankali. Sosai sun min nauyi, dan illahirin jijiyoyinsu a takure suke waje guda. Hannuna da nake ji kamar an ?aure nai ?o?arin motsawa domin kaiwa saman idanun, sai naji an sake dam?esa da ?yau, tare da jin saukar wata murya cikin kunnena. "Bi a hankali akwai abu a hannunki. Sannu kin farka bari nai kiran likita".
Sosai naji gabana ta fa?i. A can ?asan zuciyata na ayyana (likita) a fili kam babu abinda nake iya motsawa a jikina saboda illahirinsa yay min nauyi. Amma sai na shiga ?o?arin bu?e idanuna. Dishi-dishi nake gani, sai dai hakan bai hanasu sauka akan mutumin daya shigo bayansa da wasu mata guda biyu ba saboda yanda hayaniyar maganar da suke taja hankalina. Duk da ba ihu suke ba ko fidda sautin maganar tasu da ?arfi. ?arasa bu?e idanun nayi da ?yar sakamakon jin inuwar mutum a kaina. Wani irin fa?uwar gaba naji ta sake riskata, dan kuwa tabbas a asibiti nake, dan shigar wanda ke kaina tsaye kawai ta tabbatar min da shi ?in likita ne. Sannu suka shiga jeramin, sai dai na gagara amsawa kowa a cikinsu, na dai zuba musu ido ne kawai ina binsu da kallon ?urilla. Ko tambayoyin da likitan ke jeromin game da jikina na gagara amsa masa ko ?aya. Fahimtar kamar a rikice nake da yanda nake bin ?akin da kallo ya sakashi ?yaleni shima. Sai cikin matan da ya shigo da su ne ke ?o?arin cire min allurar drip dake a hannuna. Kusan mintuna biyar muna a haka kafin ya sake juyowa ya fuskanceni. Cikin harshen turanci ya furta. "I understand that you are confused. This is a hospital, you are under the care of a doctor. Alhamdulillah, your body is very easy."
A hankali na kai hannuna saman kaina da har yanzu nake jinsa da nauyi, kafin na sake ?agowa na dubesu murya a karye na ce, "Who brought me? Which hospital is this? Since when have I been?".
Da alama yanda na jera tambayoyin sun bashi mamaki, dan sai da ya ?an waro idanunsa, sai kuma yay murmushi da fa?in, "Oh relax! You will all know. Now they will help you to fix your body, eat something and I will come back and answer your questions". Ya ?are maganar yana nuna min Nurses ?in. Fuska na ?an ?ata, sai dai bance komai ba. Shi kuma ya juya ya fita da Nurse ?aya ya barni da biyu. Da farko naso na?i yarda, dan nafi son na fara sanin a ina nake. Sai dai yanda suka nuna damuwarsu da tabbatar min ?in yardata zai iya ta?a aikinsu yasa na amince. Amma zuciyata ta?i gajiya da daina kai-kawon ganin ?akin da naken matsayin wai asibiti. Saboda sam bai kama da asibiti ba fa, duk da gado da tarkacen ?akin duk irin na asibitin ne, sai dai da gani na musamman ne su. Ga television ga freight, sannan toilet da suka kamani suka kaini a cikin ?akin dai yake shima sam bai kama da asibi ba. Ciwon da jikina kemin ya sakani bin umarninsu nayi wanka da ruwan da suka tara min mai ?umi. Nako ji da?in wankan, na saka doguwar riga irin wadda na cire pitch color da alama ta asibitin ce. Bata sauka min har ?asa can ba sosai, amma dai banyi tsirara ba. Gashi tana da fa?i babu wani takura. Alwala na ?auro na daddafa bango na fito. Da sauri suka iso gareni suka taimaka min muka ?arasa, a saman lallausar sofa ?in ?akin nace su zaunar dani, sannan na bu?aci hijjab na salla da sallaya. Sai dai da alama babu, sai ?aya ce tace bari ta sanarma doctor a kawo min. Komai bance ba, na jingina kaina da kujerar na lumshe idanuna.
Bata fi mintuna biyar ba sai gata ta dawo da sallaya da sabon hijjab a ledarsa. Ita ta ciromin shi, sannan ta shinfi?a min sallayar. Har ?asa hijjab ?in ya sauka min sosai dan ko ?afafuna ba'a gani, hakan yasa naji nutsuwa dan dama rigar bai gama sauka ba. Juyawa nai na tambayesa "What day is today?". A tare suka amsa min da, "Today is Monday".
(Litinin) na maimaita a zuciyata. A zahiri kam sai na sake tambayarsu al?ibla. ?ayarce mai kama da musulma duk da shigarta zata iya saka kace ba musulmar bace amma akwai ?aton tabon salla a goshinta ta nuna min tare da bayani, bance komai ba na kabbara sallata. Tun inayi a tsaye har hakan ya nema gagara. Dan dole na koma a zaune kasancewar duk sallolin da nasan suna kaina sai da na ramasu na kwanaki biyun nan da bana a hayyacina.........??
_Masoya ina ?ara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR??????ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE??_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ????_*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing??_*
*_??TSUTSAR NAMA....!!??_*
_(Itama nama ce)_
_?????????? ???????????? ????????_
_???????? ??????_
_???????? ??????????_
.......Tun ina sallan shigowar doctor biyu. Sai dai ganin ban idar ba yana komawa. A na ?arshe suka shigo su biyu dai-dai na idar ina zaune kawai nayi tagumi cikin dogon nazari da son sanin a ina nake wai. Jin muryar da banyi zato ba kasancewar nasan na ku?uta daga garesu yasa na ?ago da sauri. Shi ?inne kuwa. Wato yaron mugun nan Maash. Ganin yanda ina ?agowa ya du?ar da nasa kan ?asa kamar wani munafuki ya sani cigaba da kallon nasa kawai. Doctor ne ya katseni da tambayar yaya nake jin jikina yanzu. Cikin janye idanuna na amsa masa da Alhamdullah. Ya nuna jin da?insa kafin yay min nuna da mutumin nan. "Now you will get all the answers to your questions from him. I will send a nurse with your medicine. If you eat, she will give you." daga haka ya juya ya fita. Shiru ?akin ya ?auka kusan na minti ?aya, kafin a ?ufule cikin dasashjiyar muryata mai nuni da banda lafiya na furta, "Ya akayi na dawo gareku? Ina ne nan kuka kawoni?".
Sake du?ar da kai yayi kamar mai tsoron bani amsa, sai kuma a hankali ya furta, "Kiyi ha?uri nan asibiti ne. Yaya jiki?".
Wani irin takaici ne ya ?uleni, dan haka cikin sake zafafa harshe na amsa shi da, "Ba ruwanka da jikina. Kaje ka sanar ma wanda ya aikoka yasa likitan nan ya sallaman. Sannan ku fita a sabgata. Idan ba haka ba zan sakaku nadama da dana sanin sani na. In ba hakaba zan tabbatar muku TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE". Daga haka na yun?ura a hankali na mi?e, ko inda yake ban sake kallo ba na koma saman gadon. Dai-dai nan Nurse ?in nan ta dawo...
*_KANO_*.
A matu?ar tashin hankali zuciyar Mamyn su Mansoor ta gama shiga. Dan suna isowa asibitin ta farfa?o ita. Amma Mansoor kusan awani uku kenan likitoci na tare da shi ba kuma su musu bayanin komai ba. Sai dai faman kaiwa da komawa suke a tsakanin ?akinsa zuwa ofisoshinsu. Tun tana hawaye har ma sun ?afe ta koma na zuci. Nadama take ji na sake shigarta akan abinda ta aikata. Lallai tayi dana sanin biyema shawarar ?ar uwarta. Inama zata iya maida hannun agogo baya. Data goge komai da yake a yanzu da maida baya data shu?e. Dan har ga ALLAH Mansoor shine ?a mafi soyuwa a zuciyarta. Kodan tasha matu?ar wahala ne a yayin haihuwarsa, ko kuwa dan kamanin da yake da mahaifinsa. Sam bazata iya jure rasashi ba. Dan bazata ta?a yafema kanta ba.
"Mamy dan ALLAH ki zauna ki huta, in sha ALLAHU ?an uwana zai tashi. Kinga kema fa ba lafiyar ne da ke ba". Attahir ne mai maganar cikin tsantsar damuwa ganin yanda Mamyn tasu ke faman kai kawo ga hannunta dafe da kanta. Yasan komai zai iya faruwa da ita, dan bata gama dawowa dai-dai ba ta fito a ?akin da aka kwantar da ita. Anyi-anyi kuma ta?i ta koma dole aka ha?ura aka barta. Dan Dad ?in su ma haushin dagiyar tata ya sashi komawa can gefe ya zauna kawai bai sake kulata ba.
"Attahiru bazaka gane ba. Nasan bazaka fahimta ba. Barni kawai kaji. Barni da abinda ya dameni. Ni da kaina na jefa rayuwar yarona a bala'i. Da nasan haka zata kasance da ban aikata ba. Da ban hanashi aurenta ba. Attahiru idan na rasa Mansoor nima zaku rasani ne wlhy".
"Dan ALLAH Mamy ki daina fa?a. In sha ALLAHU bazamu rasaki ba. Ki kuma daina zargin kanki kowa baya wuce kuskure ai. Mansoor zai samu sau?i. Ki masa addu'a".
Kuka mai nauyi ta sakar masa tana ?o?arin dafe bango saboda jirin dake neman yaddata taji ya kwasheta. Da sauri yayi kanta ya ri?ota. Da taimakonsa suka zauna yana jera mata sannu. Dai-dai nan shima Dad ?in su ya taso, hakama ?annensu da suka ha?e kai gefe suna kuka. A ru?e duk suke tambayar miya faru, sai da ta ?ago ta ce musu ba komai sannan suka shiga sauke ajiyar zuciya. Hakan sai yay dai-dai da fitowar amintaccen likitansu Dr Gana. Kamar wa?anda aka zabura duk suka mi?e garesa har Mamy. Har rige-rigen tambayarsa yaya Mansoor suke yi. Shiko ya ?an bisu da kallo cikin damuwa. Sai kuma a hankali ya furta, "Alhaji idan babu damuwa na ganka a office mana. Amma Hajiya tai zamanta Please".
Tsantsar tashin hankali ne ya bayyana a fuskokinsu. Yayinda Mamy ta fashe da kuka sauran ?anensu na tayata. Shi kansa Dad ji yay ?afafunsa sun masa matu?ar nauyi. Haka shima Attahir ya gagara tashi har sai da doctor ya sake musu magana sannan. Attahir ne ya fara jarumtar mi?ewa, sannan shima Abban ya tashi suka nufi office ?in su biyu kowanne na jin zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri tamkar zata faso ?irazansu ta fito waje.....
_Ni kaina Bilyn ku zuciyar tawa bugawa take. ALLAH yasa dai ba rasa Mansoor mukai ba??????._
*_ABUJA_*
¡ïSosai na birkicema likitan nan akan nifa sai nasan a inda nake. Hankalinsa ya tashi, dan ya tabbatar min in har ban kwantar da nawa hankalin ba aikinsu zai iya komawa baya. Ganin fa ba saurarensa zanyi ba ya sanar min in a Abuja ne cikin MAASH HOSPITAL.
"Abuja?!".
Kansa ya jinjina min da sauri. "Yes, yes. You were brought from our branch in Kano. Once you have finished receiving the medicine, you will return. Please calm down"
Rasama mi zance masa nayi, sai kawai nayi shiru ina kallon PA da suka shigo kusan tare. Shi doctor ya zata na fahimcesa ne, dan haka ya sauke ajiyar zuciya da cigaba da kwantar min da hankali. Ko kulashi ban sake yi ba. Har ya gama ?a?atunsa ya fita. ?auke idanu nai da ga kan PA ina mai cije lips ?ina da ?arfi. Na fahimci wa?an nan mutanen so suke sai mun kai matakin ?arshe da su. So suke sai na bijire ma maganar Yaya Musaddiq da Mansoor. So suke sai na musu fallasar da zata ruguza dukkan tanadinsu. Kamar PA ya fahimci mi nake ayyanawa a raina. Takowa yay ya ?araso gaban gadon ya ajiye ledar hannunsa. Kafin ya ciro wayarsa a aljihu yay ?an danne-danne batare da yace komai ba ya ajiye min saman table da akai crossing a tsakiyar gadon da magunguna a kai da dama sune Nurse zata bani na birkice musu. Harara na ?ago zan watsa masa sai idanuna suka sauka akan fuskar wayar. Tamkar waccan ranar yanzun ma tar-tar nake ganinsa. Yanda ya kafeni da shegun idanunsa kaifafa kalar na maguna ya sakani sake ?aure fuska tare da ?arasa antayawa PA ?in nasa hararar da nayi niyya. Sai dai ashe shi harma ya fice ya barni da wayar. Wani irin takaici ne ya sake ru?un?umeni. Dan haka na rumtse idanuna da ?arfi ina jin matu?ar zafi a raina. Kafin na bu?esu gaba ?aya a fusace kan wayar. Shiko shiru yay kawai yana kallona da kaifafan idanunsa da nake jin tasiri su har a cikin jinina. Duk da yanda nake jin tasirinsu ban janye nawa dake masa kallon tsana da takaici ba. Cikin kaushin harshe da disashiyar muryata ta marasa lafiya na furta, "Kai ko akwai zuciya a ?irjinka?".
Shiru babu alamar zai tanka min, sai ma janye idanunsa da yay a wani kalar slowly ya maida kan laptop dake gabansa. Dan alamu ya nuna kamar a study table yake zaune. Cikin sake jin wani sabon ba?in cikin na kai hannu saman kaina dake sara min. Fahimtar bazai amsa min ba ya sani cigaba da fa?in, "Anya kai Musulmi ne?".
Cak ya tsaya daga barin abinda yake yi, dan haka ya ?ago muna kallon juna cikin ido, idanunsa sun wani ka?a blue ?in gwaiduwar tsakkiya ta ?ace ta zama siririya like mage sak. Zamansa ya gyara na ?asaita da isa da ke tabbatar da shi matsayin ingarman namiji, ga wani irin shegen kwarjini da nake ji ya mamaye ?akin har kamar na matsu kai kace a gabana yake mayen. Ganin haka ya sakani cigaba da maganata batare da na damu da duk abubuwan dake tattare da shi ?in ba.
"Idan har kai musulmi ne bana jin kasan HARAMCI da HALLACIN dake cikin dokokin addinin musulunci. Idan kuma har da zuciya a ?irjinka tabbas bata masu IMANI bace. Ina mai baka shawara kada kai wasa da wuta a tafin hannunka, dan wutar da UBANGIJI zai ladabtar da ma'abota bijirewa ta ninka wadda ake girka maka shinkafa a duniya kaci sau dubu bisa dubu. Idan baka sani bane zan fa?a maka a yanzu ni ?in MATAR WANI CE. igiyoyin AURE ne a kaina ba igiyoyin ?aure dabba a turken turka ba. Kaji tausayin kanka, da gujema sa?ama UBANGIJI ka maidani inda ka ?akkoni gidan aurena hannun MIJINA da IYAYENA."
"Idan nan ne GARIN AUREN ni ne MIJIN kuma fa?". Ya fa?a cikin wata iriyar muryar dakiya da gizago mai tsarga zuciya. Dan yanda sautin amon muryar tasa da kaifinta ya tasirantar da furucin nasa a tsakkiyar kaina ka?an ya rage zuciyata bata ?ullo ta bakina ta fito ba. Amma duk da hakan sai ga tari mai ?arfi ya sar?e min numfashi. Gaf-gaf jikina dake a cikin yanayin rashin ?arfi ya fara rawa. Bamma san lokacin da bakina ba ya furta "MIJI?!". Sai kuma kaina yay wani irin masifar sarawa da ban ta?a ji ko tsinkayen irinsa ba. Ga nauyi da idanuna sukamin har inajin jijiyarsu na ja kamar za'a fincike min su. In dai har wannan ake kira hawan jini to tabbas ya sameni kuwa a yanzun nan. Dan ?irjina kansa yay wani irin nauyi. A karo na biyu hankalina ya sake neman barina. Nai ya?in maidosa jikina tare da ?agowa ina kallonsa domin son tabbatarwa. Amma a maimakon amsa ma da nake bu?ata garesa hankalinsa kwance yake cigaba da aikin gabansa. Wani irin kallo nake masa mai kama da firgici, yayinda shima ya zuba min nasa cat eyes ?in cikin yanayin i don't care tamkar zai cinyeni da su.
Cike da salon izza da ?asaita ya wani sake tsuke fuska da yamutseta sannan ya furta, "Har yanzu kina da sauran dama. Domin guri bai ?ure miki ba na komawa inda kika fito. Ki bama yarona video ko fadar inda yake a ?akko gobe ki koma garinku. Sa?anin hakan cigaba da dawwama ?ar?ashin mulkin mallakar Maashhhh. Ke baki mori rayuwar taki ba. Ba kuma ki iya yin komai akan abinda kike tunanin iyawa ba".........??
Yayanmu Barka da salla, ban sani ba ko a duniyarku kunyi azumin kuma?????????.
_Masoya ina ?ara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR??????ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE??_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ????_*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing??_*
*_??TSUTSAR NAMA....!!??_*
_(Itama nama ce)_
_?????????? ???????????? ????????_
_???????? ??????_
_???????? ????????_
.......Wani irin sake sarawa kaina yayi, dole na kai hannu na sake dafesa tare da saurin dafe ?arfen gadon dan ji nake zan zube ?asa, hasalima sam bana fahimtar maganganunsa a yanzu. Sai kalamansa ne na farko