Showing 36001 words to 37977 words out of 37977 words

Chapter 13 - HAUWA KULU 4 BY TAKORI

TAKORI   

29 Jun 2024

5882

masu gadin kasuwar su ankara wutar ta lashe shagon Alh. Zakari mai atamfa har ta soma laso makwabtansa.
Baba Zakari sai kwasar shi akayi a wheel-barrow zuwa gida saboda sumewa yayi a wurin aka tattakeshi a wurin baa sani ba sabida dafifin alumma da kokarinsu na kashe wutar shikuma sai kara kutsawa yake yi har karfin sa ya kare jininsa ya hau, ya fadi a wurin baa kula ba aka yi ta bi ta kansa ana tuntube ana wucewa saida wasu suka daga shi da kyar suka saka a wheel-barror yaran da suka san shi a kasuwar suka tura shi zuwa gidan sa a dan agundi.
**** **** ****

Tundai da suka fahimci ya tsiyace yau kafin sati ya zagayo nbiyu daga cikinmatan da ya auro zawarawa masu kuruciya suka kama gabansu don tunda ya fadi yake jinya har inda nan ke motsi. Biyu sun zauna sabida yaran su da rashin muhalli wato Zainaba da Alto, don ko da yake cikin daularsa aai su baya tsinana musu komai su suke ci da kansu da yaran nasu ta hanyar yan sanaoin cikin gida.
Jamilu ne kadai yake jigilar kai Baabn nashi asibiti amma duk sauran yaran sun fantsama cikin ganuwa suna sanaar daba, wasu sane wasu kwace, matan kuwa sai addua don sun ki zaman aure sun dabbi maza a unguwar dan agundi.
Abinci wannan babu a gidan Zakari don matan in sun dafa basa bashi, sunce sanda yana da shi su ya basu? yayana kuwa babu mai lokacinsa. Kashi da fitsari duk akan gadon sa yake yin abinsa don faduwar da yayi ta sabbaba masa lalurar ‘stroke’.
Jamilu dake tsaye a kansa maaikacin banki ne da in ya tafi aiki kullum sai kusan dare yake dawowa, nan zai shiga hidimar gyarawa uban jiki da wani yaron makwabtansu da yake biya yana kula dashi in baya nan.
Da Jamilu yaga abin ya kazanta sai ya dauke shi ya mayar asibitin murtala ake kula da shi a bangaren physiotheraphy.
Da jimawa can Salele ya gaya masa Hauwa tayi aure da Likita Sarham suna kasar Saudi Arabia.
Sannan bada jimawa ba sun kara haduwa yake gaya masa Malam Bilyaminu da Inna sundawo gidan su na Badala.
Haka kawai jikin sa ke gaya masa ciwon mahaifinsa bana tashi bane don haka akwai bukatar ya hada shi da dan uwansa ya nema masa gafara a wurin sa don da karkataccen bakin sa ya gaya masa shi ya kori Bilyaminu daga Kano don ya cinye gonar gadonsu shikadai.
Haka ya gaya masa shi ya rushe gidan su bayan ya saya biya shi kudin a gaban shaidu da mai unguwa.
Ba don kuma komai ya rushe gidan ba sai don kada shi Jamilu ya auri Hauwa itama kuma Innar da Hauwan su rasa matsuguni.
Da Jamilu ya tambayeshi cikin takaici ko meye dalinlinsa na yin duk wannan taasar a ma tsayinsa na musulmi gad an uwansa na jini? Cewa yayi saboda tun suna yara ya lura Bilyaminu ya fishi tauraruwa mai haske ya kuma fishi kashin arziki, duk abinda ya sakawa hannu sai yayi albarka, sannan ana yawan cewa ya fishi kyau a duk inda suka shiga tare.
Jamilu kuka riris ya rika yi saida ya kwana uku bai dawi inda babansa yake ba.
A karshe ya tuna shi din dai shi ya haife shi, kuma cikin yaya ashirin da ya Haifa kaf babu mai tsaya masa in bashi din ba.
Haka ya cigabada kula da shi a asibiti har suka yi wata uku yaron da ke taimakawa Jamilukula da shi din ma ya gaji ya kama gabansa don bai ga alamarBaab Zakari zai tashi ko zaune ba.
Abubuwa suka damu bawan Allah Jamilu gashi ya kai kudin aure an dawo masa da shi sabida gidan su yarinyar sunyi bincike akan gidan mahaifinsa sun samu labarin da baiyi kama da rayuwar Jamil Zakari ba.
Don haka sanda Salele ya gaya masa dawowar su Baabn Hauwa gidansu Jamilu ya je har gida ya gaida Baban Hauwa da Inna. Da farko Inna ta tada hankalinta da zuwan Jamilu Malam yace da ita Jamilu duk sanda ya ga dama yazo gidansa, bashida inda yafi wurinsa. Ya kuma ce da bakinsa inama yanada wata yar da ya baiwa Jamilu!
Wannan kalamai sun saka Jamilu kuka. Gashi dai Allah yayi masa duk wani ludufi da matashi kamarsa yake nema a rayuwa amma baiyi saar mahaifi ba, shiyasa komai na rayuwarsa yaki komawa daidai, musamman ta fuskar aure, ya nema sau biyu ana hana shi. Har hotunan ya;yan Hauwa Jamilu ya gani a wayar Inna nan ma kuka yayi ta yi. Da tuni wadannan zukakan yaya nasa ne ba don halin Babansa ba.
Duk yaji ya tsani uban nasa, ya rika dakacen INAMA BILYAMINU NE YA HAIFESHI BA ZAKARI BA!
Tun daga ranar da ya gayawa Malam Bilyaminu halin da mahaifinsa ke ciki, Malam Bilyaminuya salladawa Inna dafa abinci kullum tareda Zakari. In yaso Jamilu ya zo ya dauka ya kai in ya taso banki.
Inna Safiya uwar Hauwa, bata gardama da umarnin mijinta ko kadan haka take dafa abincin da Baba Zakari yake ci kullum mai dan ruwa-ruwa Jamilu ya kai masa.
Malam Biyaminu yake baiwa Dr. sarham labarin halin da dan uwansa Zakari yake ciki cikin tarin damuwa, ya kuma nemi shawararsa ko akwai maganin shanyewar barin jiki?
Dr. sarham yanata jinjina zuciya irin ta wannan bawan Allah yace zan turo abokina Dr. Sammani (Physiotherapist) ne in sha Allahu duk taimakon da ya dace ya bahi zai dinga bashi a gida su baro gadon asibitin Murtala.
Da farko Jamilu yayi gardama da yaji mijin Hauwa ne zai taimaki Babansa sai ya tuna da Malam Bilyaminu yake Magana bazai yuwu yayi hukunci y ace masa bai masa ba, amma a duniya babu wanda yake kishi irin LIKITA SARHAM!!!
Dr. sammani ya cigaba da kula da lafiyar Zakari a gidan sa, kullum yana zuwa yana masa gashin kashi mai kyau. Duk abinda ake bukata Sarham na tura masa daga account dinsa. Inna kuma bata fasa dafa abincin da ya dace da masu lalurarsa kullum a kai masa ba bisa umarnin irin abincin da Dr. Sammani yayi umarnin ya dinga ci.
Cikin watanni uku hannun Zakari ya fara moruwa, ya soma iya atashi zaune har yana sallah daga zaune. Sai Jamilu ya saya masa wheel-chair yake dora shi ya fiddo shi tsakar gida ya sha iska duk sanda ya zo gidan.
Da haka ya lallashi uwargidansa Alto kan ta tuna aljannahrta ta dinga duba lafiyarsa in baya nan bai ce ta dinga bashi komai ba.
Albarkacin Jamilu malam Bilyaminu yace ya yafewa Zakari amma don Allh Jamilu kada ya kawo masa shi gidansa ko sau daya, kowa yayi rayuwarsa har ta Allah ta cimmasu su duka.
Ranar da anka yiwa Hauwa aikin ido ranar ne Jamilu ya shigo ya tadda gawar mahaifinsa har ta fara kumbura a daki Alto bata sani ba, don yaje seminar ta kwana biyu daga bankinsu.
Dama sai ta ga idon Jamilu ne take dan zagawa dakin da ya tafi kuwa ko kofar dakin bata kallo.
Ya taho gidan Babansa Malam Bilyaminu yana kuka ya gaya masa rasuwar dan uwansa ya kuma roke shi suje ya taya shi suturta shi.
Malam Bilyaminu har cikin kwakwawarsa sai da yaaji mutuwar Zakari, ya soma ambaton innalillahi wa inna ilaihi rajioun. Suna kokarin fita wayarsa tayi kara.
Sarham ne.
An kwance idon KULULU Malam!
Mama ta amshe wayar tace Malam Bilyaminu sada Hauwa da Innnarta..
Duk sun kidima shi, ya rasa ta ina zai fara, janaizar dan uwansa zai tafi ? ko sauraron inda aka kwana a Jeddah da masu tiyatar ido?
Inna ta amshe wayar da sauri jin kukan Hauwa cikin wayar, tace HAUWA-KULU, KULUN MAJADUN, KULUWAR INNNARTA yaya akayi ne?
Cikin kuka Hauwa tace tana rufe ido daga kallon dariyar da Mama take mata, tace cikin rada kada Mama taji, wadda ke manna mata Sumayya cinyarta tana ta canyara kuka tana neman nonon uwarta.
Inna dama ashe! Ashe-Ashe haka LIKITAN KI YAKE DA KYAU?? Ashe haka yake murmushinsa? Ashe haka yake komawa in yana dariya?
Wayar ta subuce daga hannun Inna domin faduwa tayi a wurin cikin sujjadah. Tun bat agama jin arshen bayanin Hauwa ba, na cewa in ta cire gilashin da aka kara yi mata yanzu bata gane fuskar kowa, tana gani ne da taimakon gilashin.
**** **** ****
SHEKARU MASU YAWA A GABA
(HAUWA BILYAMINU DISABILITY SUPPORT CENTER).
Shine sunan NGO din da Hauwa ta bude a shekarun girmanta. Bayan kammala LLB, BL, da LLM. Da yaransu maza da mata har guda bakwai tareda PACESETTER dinta. Barrister Hauwa Bilyaminu, ta bude (DISABILITY SUPPORT CENTER) da sunanta, domin tallafawa mata da yara masu nakasar idanu, inda ta zama jagora ga mutane masu nakasa kowacce iri ce musamman ta ido, tana coaching, tana mentoring dinsu akan harkar ilmi da cigabansu. Sannan tana ‘advocating ga gwamnati da alumma kan dabbaqa ‘disability right, inclusion and justice for people with disabilities’.
Sannan kuma cibiyar nayi wa masu bukata ta musamman training na skills acquisition daban-daban musamman akan sanaa, ilmin naura mai kwakwalwa ga masu matsalar gani, da koyar dasu rubutu da karatun Braille da amfani da assistive technology da sauran ‘soft skills’ da zasu taimaka musu. Har a hankali cibiyar ta soma samun tallafi daga International Organizations irin su Sight-savers, AGILE, PERL da Commonwealth.
Shekarun HAUWA-KULU (50) a duniya suka bar Jeddah, wato da tafiya tayi tafiya Dr. Sarham da iyalinsa bakidaya suka dungumo suka dawo gida Najeriya bayan yayi retire da asibitin Saudi-German, inda suka sauka a gidan su na tarihi dake unguwar Rijiyar Zaki suka cigaba da rayuwar kauna da soyayya da kula da yayan su, a lokacin Dr. Sarham ya mallaki asibitin ido nasa na kashin kansa, hakan kuma bai sa ya bar aiki da gwamnati ba. Da yaransu goma cur; na Hauwa 7 na Dr. Madinah 3.
A lokacin Hauwa Bilyaminu ta zama UN Volunteer akan Disability Support and Inclusion, sannan ta zama wakiliyar dabbaqa ‘Sustainable Development Goals’ a kasar Najeriya.
-TAKORI
Na bibiyi labarin Barr. Hauwa-Kulu ne har zuwa ranar yau ta taron Meet&Greet, wadda hadakar kungiyoyi masu zama kansu suka shirya domin karramata da fito da ita duniya ta ganta, bayan buya da take a bayan fage tana ayyukan tallafawa nakasassu, da taya ta murnar cika shekarun haihuwarta 50 da shekarun aurenta 31, sannan da karbar ragamar jagorancin kungiyar lauyoyi ta kasa da aka fi sani da Nigerian Bar Association
-SUMAYYAH ABDULKADIR
22/10/2023
07030137870
(WHTSP ONLY)


















Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login