Showing 21001 words to 24000 words out of 37977 words

Chapter 8 - HAUWA KULU 4 BY TAKORI

TAKORI   

29 Jun 2024

5876

tunanin za ta taimaki Hauwa ya daga masa hankali, da ma ya yi niyyar fita tare da ita yau ya kai ta top ten ta yi sayayyar abubuwan da ta ke da bukata, duk da yasan Mama ba abinda ba ta hado ta da shi na amfanin ta ba.
Gyaran muryarsa a kofar dakinta ya sa Hauwa da ke idar da sallar walha juyowa da hanzari don dama a kage ta ke da ganin nasa, tunda ya tafi dakinsa don ya shiryo take jin yunwa.
Ya karaso har inda take ya dagata daga kan dardumar suka karasa gefen gadon, ya zaunar da ita bisa cinyoyinsa yana wani irin sunsuna ta, yace cikin taushin murya,
Maijidda ya ki ka tashi, ya kwanan bakunta? Hope babu pain din sosai yanzu?
Dan murmushi ta yi. Tana sunne kanta a kirjinsa.
Ya ce, naga kamar ba ki yi sallah daidai ba, nan din ba nan ne gabas ba, let me adjust.
Ya gyara mata inda za ta fuskanta a dakin yayin sallah, ya zauna nan makale da ita ya kasa tafiya asibiti, ya ce, Ba ni labarin yadda ki ka kwana a gidanki? How do you feel the night? I know its hurting a little, amma da kinsan rahma da gafarar dana roka miki daren jiya bakidayansa da kin san cewa kin rabauta da albarkar aure.
Aljannarki in dai har tana kasan dugadugaina, ni Sarham na daga miki ki shiga cikin amincewa ta udkhuluha bissalam.
Hauwa dai murmushi take tayi ba ta amsa ba.
To zan tafi asibiti, ko za ki bi ni mu je in fara kai ki ki sayi abin da ki ke so kafin na wuce?
A nan ne ta yi magana, ta ce,
Ba ni da bukatar komai, Mama ta hado ni da komai na bukatata, ka je lafiya ka dawo lafiya Yaya Doctorau! Baban Waheedah.
Yana jiyo bude kofar Madinah ta fito cikin shiri dauke da Waheedah, sai ya ajiye Hauwa a gefensa ya tashi ya fita, yana cewa cikin ransa, zai yi maganin Madinah.
Yana fitowa daga dakin hauwa suka hada ido shida ita, Madinah ta hadiye wani bakin ciki da ya taso mata, ta juyar da kai gefe tace.
Zan fita neman aiki.
Har ya kai bakin kofar nasa dakin sai ya dakata, kafin ya juyo ya yi mata wani irin kallo na gargadi. Madinah ta kauda kai ta ce,
Ah toh, dole in fara aiki yanzu, don ba zan zauna jire maka musakar da ka ajiye a gida ba, ko in zama yar jagora.
Allah ya tsare ni aikin wahalar da babu lada wai aikin kishiya.
Wallahi da ma don kai da yarka ne bana aiki, don in samu lokacin kula da gidana da iyalina, a yanzu na gane ba abin da mace za ta yi ta mallaki namiji da sunan kyautatawa da kiyaye hakkokinsa don hana shi hango wata, sai dai kawai ta bata wa kanta lokaci.
Ya gyada kai yana kallonta da budadden ido, Shi ya sa yanzu ki ka zabi fita gantali, tunda ba ki mallake ni din ba kuma don na yi aure cika sunnar Manzo SAW? Don dai na san ba za ki ce neman na kai ne ya saka ki yin aikin ba.
Ai kamar ba ka ji ba Dr. Sarham, in zauna yi maka gadin mata ne ba zan yi ba, sabida ni dai duk danginmu babu makaho, ban iya yar jagorar zuwa bandaki da kitchen ba.
Sarham ya shige dakinsa da sauri gudun kada ya yi loosing temper ya kai mata mari again irin jiya, yana cewa,
I can relate. Lalura dai ba ta wuce kan kowa ba. Kuma Hauwa ba ta dora wa kanta ba, ni din dai ni na jawo mata.
Haka ko da ya je office din kasa zama yayi ya jima yadda ya saba saboda tunanin halin da Hauwa ke ciki. Don haka karfe biyun rana na bugawa wato lokacin cin lunch dinsa ya baro Saudi-German zuwa Estate dinsu.
Yana hanya Sumayya ta kira shi, yana ganin kiran nata ya ki dagawa, ya shiga gida kenan ya yi parking. Sumayya ta sake kira, tsaki ya yi ya daga kiran nata, bai ce komai ba, Sumayya sai ta sa kuka.

Da kyar ta soma magana jin Yayan bai katse ta ba, bai kuma tambayi dalilin kukan nata ba, saida ta gaji don kanta tace.
Ni dama na san Aunty Madinah ce ajalin zumuncinmu, Bhaiya, na san dama sai ta raba mu, tunda har yau ka ki daga kirana da gangan, kuma ka ce kada in kara zuwa gidanka har abada.
Sarham takaici goma da ashirin ya ishe shi.
Sumayya, wace irin yarinya ce ne ke fitinanniya mai kishi da matar Yayanta?
Sumayya ta zaro ido, kamar Sarham yana kallonta, ya ce, Yes, na gaji da korafinki a kan Madinah, na gaji da gaya miki ba ta isa ta sa ni ba, ba ta isa ta hana zumuncina da kowa nawa ba.
Kada ki koma daukan alhakinta, na yi karin auren ma don dai ku yarda Madinah ba ta fi karfina ba bata mallakeni irin yadda kuke zato ba shima ban tsira ba.
To yau na dauko Hauwa na hada da Madinah, za ku daina yi min kallon sakarai a son matarsa ko?
Ba tun yau ba na gane ke irin kannen mijin nan ne fitinannu marasa adalci, yadda ki ka dauki Madinah ita ko kusa ba haka ta dauke ki ba.
Ki bi rayuwa a sannu Sumayyah, ki daina saka wa kowanne dan Adam kahon zuka, babu mai bai wa wani numfashi ke da ita, kuma ba ki san ranar da Madinah za ta iya yi miki a rayuwa ba.
Ina yi miki nasihar nan ne a matsayina na dan uwanki ba a matsayin mijin Madina ba.
Change your behaviour Sumayyah da duk kannen miji masu irin halinki, don kuma mata ne, gidan aure za ku je, kada kaddara ta kai ku gidan masu irin halinku abubuwa su cabalbale muku. Ki sa a ranki the more ki ka bar matar Yayanki ta zauna lafiya da shi, the more kema za ki samu zaman lafiya da naki yan uwan mijin, tarihi maimaita kansa yake Sumayyah.
Sumayyah na kuka ta ce, Na daina, wallahi Bhaiya na daina kinta babu dalili, ni na ga ishara Bhaiya don yanzu ga shi tana ramawa, farin cikina duka yana hannunta tunda ta yi rantsuwa ko ni na saura ya mace a duniya Usman ba zai aure ni ba.
Bhaiya mu kuma, nida Usman, muna matukar son juna.

Sarham ya daskare da mamaki, kafin ya ce, Are you sure kin daina negative behaviour toward her?
Sumayyah ta yi rantsuwa kan cewa ta daina, ya roki Madina ta yi hakuri ta barta da dan uwanta, she promised to become a changed person. Daga yau ba ruwanta da sabgar matansa. And she will treat both his wives equally (tana nufin Madinah da Hauwa) duk zata daukesu abu guda.
Murmushin samun kwanciyar hankali ta fannin Sumayyah Sarham ya yi, ya ce,
Thats my sister, kada ki damu da Madinah idan Usman mijinki ne Allah zai baki, idan kuma ba mijinki bane Allah bai rubuta ba, amma ki bar mata dan uwanta in ta dage bata so Sumayyah babu abinda yake dole a rayuwa, kuma bazaki rasa miji ba in sha Allahu har wanda yafi Usman komai. Ni banason aikin zubar da kima kinji?
Ki hado kayanki ki dawo ki zauna tare da mu cikin aminci in fara ganin canji daga yanzu, ga Maijidda na kawo.
Wani dan ihu Summy ta saki na murna da farin cikin isowar Hauwa birnin Jeddah.
Da ya dawo gidan yayi saar ganin Madinah na gida ba ta je ko ina ba, don ga shi nan yana jiyo sautin talabijin daga dakinta, kuma ba ta rufe dakin ba, don haka tunda ya shiga dakin Hauwa ba ta kara jin duriyarshi ba, watakila ya manta cewa ko abinci ba su bata ba a gidan.
Ya shiga dakin Madinah da sallama, Waheedah ta taho da saurinta zuwa gare shi ya sure ta ya dauka.. ya samu Madinah na cin abinci ta yi girkinta na gani na fada iya cikinta.
Ransa ya kara baci sosai, amma ya hadiye fushinsa ya bi ta da lalama.
Ina fatan kin bai wa Maijidda nata?
Ta ciko cokali mai yatsu (fork)da soyayyen dankali ta kai bakinta ta cika bakin taf, ta tauna a yangace ta hadiye sannan ta ce da shi,
Da ma hakkina ne ciyar da matarka? Gaya min inda addini ya ce ciyar da Hauwa hakkin Madinah ne, daga kai har matarka ba kwa gabana wallahi, don ni in na raina kasuwa ko sautu bana bayarwa.
Ba abinda ya hada ni da matarka Hauwa ta ke ko Kuluwa? Face addinin musulunci, kowa ya iya allonsa a gidan nan ya wanke, tunda dukkanninmu muna kwana da miji daya ban ga dalilin da zan zama kukunta ko yar jagorarta ba.
Kai wallahi Baban Waheedah idan ka nemi takura min a kan matarka, ko ka ce lallai sai ka hada sabgata da tata, to kuwa zan nemi wani apartment din in yi parking acan ni da Waheedah, in ya so in barka da yar makauniyarka ku shana.
Ta soma kuka tana ci gaba da fadin, Sarham! Ka gama wulakanta ni a duniya. Ka ci amanar yarda da soyayyar gaskiya da na baka.
Jiki babu kwari Sarham ya zauna a gefen Madinah, da muryar da ya san yana sace zuciyarta a lokacin samartaka yau ma yake yi wa Madina magana cikin salo na mijin da yasan kan matarsa.
Ki yi hakuri kin ji ko Munauwarahta. Abin bai kai da ki yi parking ki bar mana gida ba. Tunda har ki ka yarda za ki ci gaba da zama da iyalinki baki barni ba, duk da irin sabawar da na yi miki, wannan kadai ya sa na jinjina miki.
Sannan na kara martaba ki da na dawo na tarar ba ki yi yaji ba a wancan karon.
Sai yanzu don Hauwa ta zo? Kada ki manta ita ma aurenta nake kamar yadda nake aurenki, in kika bar mana gidan ai ba za mu ji dadin gidan ba balle mu shana.
Za mu kasance cikin damuwa ne da kewarki, kuma duniya da makwabta su zage ni cewa, don na auri Hauwa na raba gida da Madinah ta.
Amma ina so ki sani, ni ne uwar Hauwa, ni ne kuma ubanta a kasar nan da ba ta da kowa. Haka ni ne guardian dinta, ko da ace tare take gari daya kuma kasa daya da iyayenta ni ne majibincin lamarinta. Don haka duk wani abu da zai cuta mata ko ya taba mutuncinta agidan nan wai don wannan lalura da Allah Subhana ya dora mata dalilina, kamar yadda kike yawan gorantawa kamar ba mai ilmin addini ba Madinah ba zan lamunce shi ba.
Son ki da kowa yake fadin ya yi min yawa, bai yi yawan da zai sa in kasa yin abinda ya kamata ba. Amma Madinah ko ba soyayyah yar usuli tsakanina da ke a matsayinki na matata uwargidana, sannan my first love, wallahi a kan wata mace daban da na kara aure ba zan taba wulakanta ki ba.
Balle kuma ga aure, ga Waheedah a tsakani, uwa-uba soyayyar nan da nake miki tun tali-tali ba ta canza komai ba, kullum karuwa ta ke, sabuwa take kara komawa Madinah.
Ni kam kin fi gaban wulakanci da tozarci da ki ke kira min a idona, haka Hauwa, she have a special place in my heart, ina son gaya miki yau ina son Hauwa ne yadda nake son ki, ba kuma saboda mahaifiyarta da wasu dalilan da nake ta fada a baya ba aboda wauta da ajizanci, na dade da janye dalilaina.
A yau ina fada ne da babbar murya ina son tane kasancewarta matata kamar ke. Sauran alamarin na kuma bar wa raina.
Don haka it is up to you now, duk hukuncin da ki ka yankewa aurenmu zan karbe shi Madinah, wanda ki ka ga shine daidai, ni dai na gaya miki iyakar gaskiyata ina sonki, ina kuma son zama da Hauwa har karshen rayuwata, ba zan taba ce miki bana son Hauwa ba, wai don ki daina sababbin halayen da kika tsuro dasu, ko ki daina cewa kin daina hada jiki dani wai saboda na auri Hauwa bata gani waye-waye, umh, Madinah akwai bukatar komawa islamiyya anan, bokon naki ya rinjayi addini.
Kisa a ranki daga yau kowacce cikinku da matsayinta a gurina wanda babu na wacce zai rinjaye ni in yiwa daya abin da bai kamata ba, ko in rabu da daya saboda daya. Muddin ina cikin hankali na.
Don haka in kin ga barin gidan shi ne mafitarki babu damuwa, ni bana son ganinki cikin wannan halin da wadannan sababbin halayen da ki ka aro ki ka yafa saboda Hauwau.
Don haka duk abin da kika ga shine daidai har hana ta abinci din da rashin samar da muamalar musulunci a tsakaninku ki ci gaba Madinah ba kabarinmu daya ba.
Yarinyar nan ko da ta ke makauniyar da ki ke ta goranta mata, tofa ba ta taba ganina ba, sannan ba ita ta ganni ta ce tana sona ba, haka ba iyayenta ne suka ba ni sadakarta wai don ta makance ba.
Ni na ce na gani ina so a bani, na aureta cikin mutunci kamar yadda na aure ki. Dalilin da nake ta fada cewa, shi ya sa na aure ta ni ban sani ba, ashe zai iya zama SO. Tunda baka taba auren macen da ba ka so”.
Yayi shiru yana observing tasirin maganganunsa a tare da ita, da gaske maganganunsa na dukanta yadda baya zato. Bai damu da yadda fuskarta ta canza tayi jazir ba ya cigaba da maganarsa.
Na gaji da cewa da ki ke kina kyamar hada jiki da ni wai saboda na auri Hauwau, shin makaho ba mutum bane, ko shi ba shi da tsarkin addinin musulunci a tare dashi? Madinah ina addininki ne? Ina imaninki? Ina compassion dinki na likitancin ido? Anya Madinah ke ce? Anya GIWAta ce wannan ta koma MONSTER haka?
Yanzu dai zabin yana hannunki, na ci gaba da zama da mu ko aah, tunda dai na gaya miki iyakar gaskiyar da ke zuciyata Madinah, da kuma abin da zan iya dauka da wanda ba zan iya dauka daga gare ki ba. Hauwa zama daram, daga nan har ranar da muka daina numfashi.
Sarham ya mike ya bar dakin ya bar Madinah ta hada tagumi. Sai tsiyayar gumi take yi. Dakinsa ya koma ya yi wanka ya sanya riga da wando marassa nauyi ya shiga dakin Hauwa sai ya samu barci yayi awon gaba da ita ya kuma san yunwa ce. Wuyanta ya lankwashe a kan filo, gyara mata kwanciyar yayi ya fito zuwa kitchen.
Tunanin me zai dafa ma Hauwa mai sauki yake yi, don dole ya sanya shiga kitchen da kansa cikin schedules dinsa na yanzu. Ba zai dogara da taimakon kowa akan kula da Hauwa ba, tunda shi ya ce da iyayenta da nasa zai iya.
Ko da kuwa Sumayya ce ba zai kawo ta gidan ta zauna wai don ta kula masa da mata ba, sai dai ta zauna don radin kanta. Yayiwa Mama alkawarin shi da kansa zai kula da ita, kuma zai fara daga yanzu.

Madinah dai na jin motsi a kitchen ba ta san waye ba, don haka ta fito don ganin waye a kitchen dinta kada ayi mata barna tunda ta san dai amaryar ba gani take ba.
Sarham ta gani ya yi kace-kace yana aikin girki. Yana hada zufa na rashin sabo. Ko iblis ce ita, dole ta ji ba dadi a ranta, zuciyarta kuma ta kara gasgata abubuwan da ya fada mata na matsayin da shi Sarham ya baiwa Hauwa-Kulu a rayuwarsa.
Yana kallonta ta zo kofar kitchen din ta koma cikin sauri, ga jin kishin mijinta na dafawa kishiyarta abinci ga guilty conscience daya hanata sakat, na cewa bata kyautawa, ta kasa zaune ta kasa tsaye, a tsakar dakinta, ta yaya ita za ta dinga dafawa miji abinci? Shi kuma ya zage kwanji yasa ‘apron’ ya dafawa kishiyarta?
Kuka wiwi Madina ta soma, abu goma da ashirin ya damu Dr. Madinah Sorondinki, a karshe ta yanke wa ranta fita sabgar Sarham da matarshi Hauwa-Kulu take ko Kululu! Gara ta saka su a gefe kafin su manna mata ciwon hauka.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login