Showing 33001 words to 36000 words out of 37977 words
ni.
Anan ne tayi magan cikin hararar sa.
wallahi bai dameka ba, da ya dameka da ka hakura sai sun yi shiru. Yace to sai me? Ba da hakan ba da an same su? Yanzunma kannen su nake hari shiyasa ban sauraresu ba ta zuba jallabiyya a jikin ta zata fita bata saurare shi ba yace dakata, tsofaffi sun ce sai kin yi wanka zaki taba su kada ki shafa masu datti, kodayake ni na san jiki na ba datti sai albarka ta dan dakata jimmm a bakin kofa, ai kuwa Innama ta gaya mata haka wai in taje dakin miji kada gta yarda ta taba su sai tayi tsarki, sai kawai ta juya ta nufi toilet. Ya ce ai kya tsaya in gama hada miki ruwan mai zafi sosai ance baki gama jegon ba har gobe. Tace don Allah don annabi kaje ka basu madara zan kula da kaina ka cika ni da magana ga kukan su yana ruda ni. Tausayi ta bashi sosai yace to ai nima ban yi wankan ba ko inzo muyi tare? Kin ga daga nan in cuda miki baya da dogon wuyanki. Hauwa takaicinsa ya isheta ta shige toilet dinta harda saka key. Sarham yayi jifa da filo ya mike yana saka jallabiyyarsa yana rero baitukan sa na ;
-Addua nake Allah ya taimakeki HAUWA-HAUWA!.
Daga cikin toilet Hauwa tana zuba ruwa mai zafi cikin gashin kanta, take jin sa tana sakin murmushi daga zuciya zuwa ruhi. Ta ce a hankali;
Nima Adduaa nake Allah ya ja da ran maigidana Lelen Abba a dade ana aikin lada.. shi da HAUWA!.
Ya gama dukkan shirye-shiryensa na yiwa Hauwa aiki ranar Litinin amma sai me?
Ya dawo gida yau a bit late kuma ranar girkin Hauwa ne, suna girki a kitchen ita da Mardiyya shinkafar Basmati ta tafaso Mardiyya ta bude tukunyar, Hauwa ta shaka sosai kawai sai taji wani mugun amai ya yunkuro mata.
Ta tsugunne a wurin tana kakari amma aman yaki fita kamar zuciyarta zata fito ta bakinta ga goyon Safiyya a bayanta. Da sauri Sarham ya bar maganar da suke yi da Madinah a falo ya karso kitchen din, kai kakarin me nake ji haka? Dai dai lokacin ta samu aman kore fatau dashi ya biyo makogaronta don azumi take na alhamis bata ci komai ba shirin buda baki suke yi. Da sauri ya sauri ya ida gareta ya daga bayan ta yana shafawa har ta samu ta amayar da komai dake cikin hanjinta. Madina ta gifta zata wuce dakin ta kallo daya ta yi mata tasan ciki ne da ita ana mata amai a kitchen ta wuce daki cikin gigicewa.
Ita kuma Hauwa haka take da Haihuwa cikin lalura Allah mai girma!
Ya kamo Hauwa zuwa dakinta yace Mardhiyya ta gyara wurin. Suna shiga ya soma checking dinta har fitsari tayi ya saka masa PT strip. Wata wawuyar runguma da Sarham yayiwa Hauwa saida ya kayar da ita a saman gadon aurensu. Tana tambayarsa cikin tsoro da fargaba ko meye yakewa murna haka? Kuma me sakamako PT strip ya nuna? Amma bai saurareta ba sai sukuwa yake cikin rawa da waka yana narkewa cikin jikin Hauwa;
“Gimbiyar mata kike a zuciyata HAUWA.
Da zaa bani biro na baki maki HAUWA
To zaki haura lambar da zaa baki HAUWA.
In zaa tara mata wa zata fi ki HAUWA.
To addua nake... Allah ya taimakeki HAUWA.
**** ***** *****
Aikin da baa yiwa Hauwa ba enan a wannan shekarar amma dai tayi borin zuwa makaranta duk da haka. Bayan ta ci kukanta ta gode Allah na gwarne da take ganin wahala ne. Shima kuma da yake lallabata yake ya yarda ta fara zuwa DAAR AL HEKMAH UNIVERSITY a wannan shekarar duk da yaron cikin, ya kuma dauki alhakin kaita lacca da daukota da kansa kullum.
Haka Hauwa-Kulu ta soma karatunta karkashin BLaw (Bachelor of Law) wanda zai dauketa tsayin shekaru hudu a jamiar Daar Al Hekmah, Jeddah, KSA.
Cikin Hauwa wata takwas ta haifi yarta ta uku a duniya wadda ta rokiSarham Allah da Annabi ya saka mata sunan aminiyarta Sumayyah.
Sumayyah wadda har lokacin ake ake kai ruwa rana akan maganar aurenta, don Hajja Ramlah ma tabi bayan su Madinah tace ya nemo wata, bata ga dalilin sai wadda ke kin yar uwarsa zaice zai aura ba. Baban su kuwa wato Ahaji Attahiru tun karin auren Sarham dama basa ga maciji shi da Sarham don yaji ciwon abinda yace masa a asibiti lokacin da zaa yiwa Madina tiyata. Don haka ma da yaji wai kanwar Sarham ce Usman yake so bai saka baki ba kuma bai yi adawa ba ya dai ce sai abinda suka shawarta shi da yar uwarsa.
Shikuma Usman ya dage baiga dalilin da zaa ce Madinah ce zata yi masa deciding matar da zai aura ba tunda gaba yake da ita. Don haka ya kai karar Madinah gun Kakar su Haj Laila kan tana bata masa zancen aure ta karkashin kasa a gurin iyayensu. Haj Laila sai kawai ta tada waliyyai suka tafi gun Abba suka kai kudin aure, Abba bai karba ba yace sai yayi magana da Sarham tukunnah tunda shi yasan Usman fiyeda kowa.
A karshe dai Kakar saida ta tafi har Jeddah ta samu Alh. Attahiru ta gyara komai tsakaninsa da Sarham, tace ita bata ga dalili ba da don suna son autar su Madinah zasu ce bazaa yiwa Madina kishiya ba tunda ba alkawari sukayi a rubuce ba na cewa daga kanta Sarham ba zai kara aure ba, kuma wulakantata yake yi ba sannan polygamy aladar mutanen Kano ce. Itama da suk ganin baayi mata ba harsuke reference da ita to bari ta gaya musu gaskiya Alkalin Alkalai ya so yi ita ke lalata zancen duk inda yaje neman aure har ya gaji bari, tace tayi nadama lokacin da yayanta mata biyu suka ki auruwa har bayan digiri na uku suna gabanta. Don haka su bar Usman ya auri wadda yake so yar gidan mutunci wato gidansu Sarham su bi su da addua. su daina biyewa kishin Madinah sauda dama tana gyara gidanta ne shi Usman ta saka shi a matsala don ta san suna matukar sonta.
Da waannan Haj Laila ta gyara zancen auren Sumayya da Usman. A wata asabar, a masallacin jumaa na tsohuwar jamiar Bayero aka daura auren SUMAYYAH SHANONO da USMAN SORONDINKI. Kasancewar duk suna birnin Jeddah daga angon har amaryar kuma Sumayyah na tsakiyar karatu dole iyayen da kakannin ne sukayi yinin bikinsu sukadai. Sumayyah ta koma gidan Bhaiya dakin Hauwa acan aka shafa mata lalle dole Madinah ma ta saki ranta albarkarkacin Sarham da Usman da yae ta mata hidima don ta sa hannu a aurensa. Ita taje ta shirya musu kasaitaccen gidansu a Jeddah ta tsara komai dama dai Madinah ba daga nan ba. yayinda Hauwa ke kula da yaranta da danyen jegonta da kawayen Sumayyah da ke cike a gidan kowa nata shaawar yaran Hauwa da yadda take sabgar kula dasu musamman wajen breast- feeding. Sarham dole ya daga kafa a gidansa sabida hidimar da akeyi kuma shi Abba Prof. ya turowa kudi ya hada da abinda ya tara musamman don auren Sumayyah ya baiwa Madinah ta zabar mata kayan daki daidai karfinsu. Duk da cewa Usman yace baya bukatar komai amma saida suka yi wanda zasu iya kasancewar Usman yana ISDB ne tareda Babansu.
Watan Hauwa uku kenan da haihuwar Sumayyah yarinyar tayi bul-bul gwanin shaawa haka kamanninta da Sumayyah yayi yawa, a lokacin Hauwa na shekararta ta biyu a (BLaw) Sarham ya gama duk wasu shirye-shiryensa na yiwa Hauwa aikin ido. Ya saka ranar Litinin 5/5 a matayin ranar da zai shiga da Hauwa tiyata, ya kuma kira waya ya gayawa gida, nasa iyayen dana Hauwa, sannan ya gaya musu itada Madinah.
Ya roki Madinah wata alfarma data sanyaya mata jiki.
Na san a policy dinki Munawwarah, babu taimakawa kishiya, amma ina rokon ki ki taya Mardhiyyah kularmin da yaya na, har Allah yasa ayi aikinnan na mahaifiyarsu lafiya a gama, kuma idan Waheedah ta shiga wajen su ki daina cewa Mardiyyah ta daina goya mata su bazata iya daukar su ba sabida girman jikinsu, in ma ta tika su da kasa babu ruwanki yan uwanta ne, kinji ni ko?.
Mama dama tayi shirin zuwa Umrah a wannan shekarar kasancewar watan Ramadhan ya kama. Don haka ta hau shiri don tuni ta samu visar Umrah. So take ta isa Jeddah kafin ranar da zaa yiwa Hauwa aikin.
Dr. Madinah ta kai gwauro ta kai mari ana I gobe zaa yiwa Hauwa aikin idanunta, tana fafatawa da zuciyarta da kuma shaidan, a karshe ta rinjayi shaidan din, da taimakon Ubangiji.
Ta fuskanci maigidanta Dr. Sarham da ke fitowa daga toilet cikin fararen kayan barci, ya yi wanka ruwa na yarari daga kansa yana yarfewa da santala-satalan hannayensa.
“Babansu Waheedah, please ina so ka bani dama in shiga cikin ‘team’ din ku, wato likitocin da za su yi wa Hauwa aiki gobe. Albarkacin musulunci. Ina so a yi wannan aikin ladan da ni. I mean it.
Hawaye ya digo daga kwayar idonta. Ta tuno tarin rashin kyautawarta garesu shida Hauwa, da tarin gorinta ga nakasar Hauwa, yau ga HAUWA-KULU-MISKINIYA-MUSAKA ta cikawa SARHAMU da gayu gida da yaya, don ita ta fahimci abinda su duka hankalinsu ma bai kai ba, a matsayin ta na mace kuma cikakkar likita cewa Hauwa-Kulu wani cikin ne da ita, tana boyewa Sarham wannan karon kada ya kara fasa yi mata aiki. Duk abin da zai dawo mata da Sarham dinta na baya (very jovial) domin ya dan canza mata tun dawowarta gidan, saboda yadda take ja baya da duk wata harka ta iyalinsa, tana so ta dawo dashi yadda yake a baya kuma mai yarda da ita, don haka duk abinda tasan zai faranta masa shi ta ke son yi yanzu. Duk da ta san baa bari a kwashe daidai.
Ya kama hannunta suka zauna tare a bakin gadonta, ya ce,
Ni na dade da sanin Madinah-Munawwarahta mai kirki ce, mai imani ce kuma mai tsoron Allah ce. KISHI ne mara amfani yake sarrafa min ita a baya.
Ina rokon Allah ya albarkace mu bakidaya ni da ku iyalina, ya hadamin kan yayana ko bayan raina.
Ni na san ba za ki iya alaka ta jiki da Hauwau ba, sabida kina mata kallon tasgaro ga soyayyarmu, kuma ‘barrier’ ga cikar farin cikinki, wanda ko daya in kin duba ba haka ba ne.
Ki sa a ranki aurena da Maijiddah rubutaccen alamari ne daga Allah (S.W.T) wanda ni ma ban taba hasashensa ba, sannan ba gazawarki ce ta wani bangare tasa na yi shi ba.
Haka nake so duk mata irinki su saka a ransu, sai a samu zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsu da mazajensu.
Komai Ubangiji ya nufeka da yi, ko Ya rubuta yana cikin kaddararka, hakika sai ya same ka. Addua ba ta canza kaddara amma tana rage tasirinta.
Don haka ban auri Hauwa ba sai da na yi addua da istikhara cewa, idan ba alkhairi bace a gare mu, ni da ke kada Allah ya ba ni ikon aurenta.
Madinah ki yarda ba ki gaza da ni ta kowanne bangare ba, sannan rashin gazawar taki baya nufin shikenan bani da hurumin auren kowa kuma. Hudu Allah ya halattamin. Bayan Hauwa ma Allah Ubangiji ya halatta min wasu biyun sai in ban yi raayi ba, ko ba sa cikin kaddara ta.
Allah Ubangiji ya yi umarnin a kyautata wa MISKINI da MARAYA a cikinAlqurani, wannan rubutacciyar ayar Ubangiji ce.
Don haka kyautatawarki ga Hauwa ko akasinta yana cikin mizanin ayyukanki na alkhairi da na sharri. Na gode da kika fara karkata mizanin don ya koma na alkhairi”.
Madina ta yi maza ta rungume shi tana kuka, ta ce, Wallahi daga yau na tuba da duk abin da nake yi a kanta. Ka bani dama in shiga cikin likitocinta in yi ‘repenting’ kuskurena ko Allah Ya dube ni ya yafe mini.
Amma ka sani KISHI da kishinka Sarham wani abu ne da har abada ba zan daina ba, saboda ba ni nake sawa raina ba, halitta ne. Alkawari daya iya yi maka shine; zan koyi rike linzaminsa… in dinga controlling dinsa ta hanya mai kyau.
In ki ka yi hakan, ni kuma na daga miki kafa, ki shige aljanna ba jainja Madinah.
Ya subhanallahi. In ji Madina tana kara kanainayewa a jikinsa.
Amma wani hanzari ba gudu ba, bana bukatar taimakon kowanne likita a aikin da zan yi wa Hauwa, ni kadai nayi nazarina kuma nikadai na gano kan matsalar, don haka nikadai zan yi in kika cire (perioperatives) dina da masu allurar tafi da ranka (anaesthethians). Its a ONE MAN JOB!!!
**** **** ****
ASIBITIN SAUDI-GERMAN
RANAR AIKIN IDON HAUWA-KULU
(KARO NA BIYU)
Dr. Sarham, da sauran masu taimaka maa a yayin tiyata sun zama ready a dakin tiyatar da zaa yiwa Hauwa aikin ido, haka masu allurar anaesthesia. Dr. Madinah Attahiru, ta turo yar uwarta Hauwa Bilyaminu a kan gadon marassa lafiya tana sanye da korayen kayan aiki na wanda zaa yiwa tiyata, haka shima likitan korayen kayanne a jikinsa da hularsu. Bisa umarnin likita Sarham, masu allurar tafi da ranka suka fara, daga nan suka shiga aikinsu ba ka jin tashin komai sai tashin yaren likitanci a yayin surgery na idanu. Kalmomin da su kadai suka san me suke nufi da fadarsu. Da yake sun dade da gano matsalar Hauwa-Kulu tuntuni sun kuma dade da tsara komai daga binciken da suka dade suna gudanarwa akan idon Hauwa nada nan aka gama phacoemulsification surgery din, cikin abinda baifi mintuna 45 ba.
Ana fatan kwancewa nan da awanni biyu masu zuwa. Zukatan su Mama, Madinah, Sumayyah, Usman, da Mardhiyyah dake gefe goye da baby Sumayyah, ga ‘yan biyu suma a hannunta na hagu da dama tana lallashinsu kamar su fita daga cikin kirazansu with so much high anticipation.
**** **** ****
KOFAR DANAGUNDI (KANO)
C
ikin rikicewa da tsananin tashin hankali yake ta trying kiran wayar Dalha ana cewa bata shiga, sai ya koma kiran dansa Jamilu cikin hada uban gumi. Baba zakari kenan cikin gigicewar rasa Dalha babban yaronsa daya tattarawa dukkan jarinsa ya tafi Cotonou domin shigo da atamfofi. Ba wannan ne karo na farko da suka fara wannan sanaar shida Dalha ba sun fara da yi kadan kadan ne har Dalha ya tabbatar Zakari ya gama amincewa da shi kafin yace suyi babban sari na atamfofi da shaddoji kasancewar karamar sallah ta matso.
Amma yau kwana goma sha biyar ya kasa samun layin Dalha wato tun tafiyarsa. Da ya kasa samun Dalha sai ya koma kiran Jamilu, Jamilu ya daga ya tabbatar masa motarsu Dalha ta kife a bisa binciken da yasa aka yi masa kuma ba abinda ya tsira a motar, kamar yadda babu wata rai data tsira.
Tsananin gigicewa (bata mutuwar dalha daya shekara kusan 10 yana wahalta masa ba, aah ta kafatanin dukiyarsa da ya tattatara ya damka masa ya tafi da ita ne) tasa ya kama hanyar Singa a kafa, yana tafe yana sambatu, duk nisan kofar Danagundi zuwa kasuwar Singa bai ganshi ba, saboda tashin hankali.
Bai yarda da abin da Jamilu ya fada ba shi ya sa ya taka sayyadarsa har Singa, don ya san yana zuwa zai ga Dalha a shago yana fama da kwastomomi yadda suka saba kullum.
Tun daga nesa yake hango hayakin dake tashi kamar bakin hadari a kasuwar SINGA. Ya kara daga kafa yana fadi a ransa lallai damuna ta zo ba shiri a watan da ba nata ba. irin wannan hadari haka?
Yana kara matsowa yaga dafifin mutane suna darawa yan kwana-kwana suna wucewa da motar su bayan already wutar tagama cinye rabon sa, ciki har da sashen yan atamfa. A kusa da shi yaji daya daga cikin yaransa yaa gaya masa.
“Baba Zakari sai hakuri. Haruna ne jiya da yamma ya jona heater a shagonmu, sai ya manta ya tafi gida, kuma a kofin roba ya jona, shi ne heater ta cinye kofin ta kama shagon da wuta”.
Abinka da wutar dare, ko kafin