Showing 27001 words to 30000 words out of 37977 words

Chapter 10 - HAUWA KULU 4 BY TAKORI

TAKORI   

29 Jun 2024

5877

tun farko naki yarda ta aureka don yayan talakawannan ko a tandun mai aka saka ku sai kun fito kandas wajen nuna halinku na rashin halacci. Banda mutuwa mai tonon asiri ai Madinah matar manya ce ba irinka ba.
Kan Sarham a kasa yana jin cin mutuncin da Daddyn Madinah ke masa bai dago ba saida Daddyn yazo nan. Ya dago a hankali ya dubeshi idanunsa sun kada kamar gauta amma uffan ya kasa cewa. A lokacin aka fito da Madina daga dakin tiyata zuwa dakin jinya aka kuma hana su shiga sai bayan awa daya.
Saida Madinah ta dawo hayyacinta aka bar su suka shiga, family dinta suka rufu a kanta Waheedah na hannunHajjah Ramlah shi suka manta da shi a gefe. Abin yayi masa ciwo kwarai sai Usman ne ya zo ya kama hannunsa zuwa kan Madinah. Ta dube shi, ya dubeta suka kuma hada ido, ta lumshe idanunta bata kara budewa don bata son ma ganinsa a kanta.
Da aka bata sallama ma bayan kwana uku gidansa Daddy ya tafi da ita ba tareda nemsn iznin Sarham ba. ciki kuma an cireshi bayan ya fara girma.
Ko kusa Hauwa bata san me yake faruwa ba amma ta lura Sarhamya rage magana kuma baya cikin walwala kamar da. Shiyasa yau da Sumayyah ta nemi zuwa gidan don tayi weekend tare dasu bai hanata ba yace tana iya zuwa dakinta yana nan. Hauwa kuma yace su koma nasa dakin don nata yayi kusa dana Sumayyah, ta tambayeshi ko hakan bazai zama matsala ga Anti Madinah ba? sai yace bata nan tayi tafiya. Da haka sukayi parking dakinsa soyayya a tsakaninsu sai abinda ya karu.
Jumaah da yamma Sumayyah ta iso gidan daga makaranta.
Har ila yau, shi da team dinsa na Saudi-German suna ci gaba da shirye-shiryen aikin idon da za su yi wa Hauwa.
Tun ba a je ko ina ba Sarham ya gane shigar ciki a tare da Hauwa, tunda yanzu tare suke a daki guda duk wani motsinta ya sani. Wanda ita koda wasa bata san da cikin ba.
Kasa shiru ya yi don farin cikin da ya cika shi, wani na tafiya rariya wani na zuwa, har sai da yayi mata shagube cikin tsokana.
Ya daga PT strip din da ya auna fitsarin ta, yace wai yanzu Hauwa-Jiddah daga zuwa sai ciki? Bazaki barni ma in gama yada samartakata a jikin ki ba mu tsufa tare? Kamar wadda ta yi tuntube da shi a dokin kofa?
Hauwa saita saka kuka don tsakani da Allah ta tsorata da wannan maganar, ciki fa na haihuwa yake nufi? Ta yaya ta sameshi ma bata sani ba.
Yace Cry more Sweetheart, wani kukan ma sai an je labour room!.

Sabuwar kulawa, sabon amarci ya balle wa Sarham da Hauwa a dalilin wannan niimar da ke tattare da mace mai yaron ciki. Sarham da Hauwa sai sam-barka, a yayin da Dr. Madina ta yi nisa kan ayyukanta na Dr. Siddiqah, da ayyukan tiyatar ido na sa-kai (philanthropic eye surgery) da takeyi don taimakon marasa karfi bayan ta warke daga tiyatar da aka yi mata.
Daddy ya tabbatar mata tunda Sarham yaki sakinta ta ruwan sanyi kamar yadda ya bukata, wallahi kotu zaiyi kararsa sai ya saketa. Bazai zuba ido ya kashe masa ya ba.
Hankalin Madinah yayi matukar tashi gashi an hanata sauraron Sarham. Aka ce tsakanin mace da miji sai Allah, lokacin da ta sauko tana son ta karbi mijinta ya dade da sabawa da Hauwa, irin sabon da ko ita Madinah da ya kwashi ‘decade’ yana soyayya da ita bai yi shi da ita ba.
Kasancewar shi ne komai din Hauwa a gidan, dakinsu daya makwancinsu daya kullum, kullum kafin ya fita sai sun karya kumallo tare wanda shi yake sarrafawa da kansa, da rana kuma zai sa ‘mudam’ din cikin estate dinsu su yi mata home delivery’ na abincin rana, idan kuma ya dawo da daddare ya girka musu. Yayi musu wanki a injin wanki ya zauna zaman goge mata abayoyinta da hoover.
Ita da kanta Madina ta koma tunanin anya wannan sabuwar rayuwar ta zaman gida da iyayenta suka zabar mata mai billewa ce? Gashi mijin ba sakinta yayi ba yanata bin Daddy har office da ban hakuri itama Madina yana bata. Ta soma tuno yadda yake saka apron ya shiga kitchen yana girki tukuru domin hidimtawa miskiniyar matarsa. Duk a kokarinsa na sauke nauyinsu su duka da Allah ya dora masa da kuma cewa da tayi baza basu abinci duk ranar girkinHauwa ba.
Ta yarda Sarham ba mijin yadawa bane domin nagartarsa ta wuce ta sauran mazan da ubanta ke mata hange. Don haka ta soma tunanin mafita, wato yadda zata koma dakinta ba tareda daddy yayi fushi da ita ba don ita kanta ta san Sarham bai yi mata laifin komai ba laifinsa daya ne kara aure na tawaliu. Don haka ta koma lallashin Daddynta, ta tuna sanda Sarham ya ce in har ba za ta dinga dafawa tare da Hauwa ba kuma ba za ta yi muamalar makwabtakar musulunci da ita ba, to ya yafe cin abincin nata shima da take ajiyewa a dining ta fita.
Ta tuno irin kalaman batancin data ke masa amma duk Sarham ya shanye bai taba korarta daga gidansa ba. Irinsu;
A wane dalili za ka ce wai lallai sai na zama kukun matarka? Ka gaya min inda shariah ta dora min wannan nauyin.
A wane dalili za ka dage lallai sai na yi muamala da matarka? Na gaya maka in na raina kasuwa ko sauti bana bayarwa a cikinta.
Shin ajin rayuwata da na matarka daya ne da za ka ce sai na muamalanci wadda ko matsayin zama yar aikin gidanmu ba ta kai ba?
Ire-iren kalamanta kenan gareshi tun zuwan Hauwa, da saidai Sarham ya daga ido a hankali ya dubeta da wani irin kallo na mamaki da disappointment.
Ya ce,, In wani ne ya gaya min cewa Madinah za ta rasa hankalinta, kyakkyawan tunaninta da iliminta na jin kan alumma kai har ma da imaninta, a dalilin KISHI wallahi zan musa. Sai dai kash! Im witnessing it myself to the mere of my disappoitnment.
Ina fatan wannan halin da ki ka ara ki ka yafa babu gaira babu dalili ba zai shafi rayuwar yayana ba, wato ba zai sa ki raba min kansu ba. Da sunan Mamar wadancan ba ajinki ba ce. Ya Allah ka cire rabon shaidan daga zuciyar matata Madinah.
Ya Allah Ka raba ta da GIRMAN KAI da superiority complex wanda shi ya hallaka Kakanmu Annabi Adamu A.S.
Daga fadin hakan sai ya sa kai ya bar mata dakin. Jikin Madinah ya yi matukar sanyi yau, da tunaninta yazo nan, irin sanyin jikin da rabonta da shi har ta manta, tunda Hauwa tazo zuciyarta ta zama gardamammiya ta tsaya cur a kirjinta sai yau ta russuna.
Dr. Madinah Attahiru. Ta soma kokarin tattaro ragowar mutuncinta wanda ta san, har abada ba mai gushewa ba ne daga idanun Dr. Sarhamu.
Itada Usman sukayi shawarar Sarham ya gayawa Haj. Lailah hukuncin da Daddy yayankewa auren ta. tace ita kuma tanason komawa dakinta bazata kara tada hankalinta ba.
Haj. Lailah suka shiryawa zuwa Saudiyyah itada Usman musannan don ta lallashi Daddy tayi sasanci, har bukatar Usman na auren Sumayyah sun gayawa Haj. Lailah ita kuma ta kama Attahiru da fada tace wannna ba gata yakewa yaransa ba yaranma sun fi shi hankali, ita Madina wacwcw data fi karfin ayi mata kishiya? Taga Nana Aisha da Nana Khadija ma duk da kishiyoyi suka zauna. Tayiwa Daddy kaca-kaca ta kuma saka shi ya kira Sarham a waya yace ya zo ya dau matarsa.
Sarham a take ya baro office yaje ya taho da Madina daga gidan mahaigfinta. A hanya kuma kafin su iso gida suka kara dinkewa, suka fabhimci juna, ya kara yi mata kyakkyawan bayanin da yafi na baya akan Hauwa da muhimmancinta ga rayuwarsa kuma ba wadda za iya bari saboda yar uuwarta.
Abu na farko da Madinah ta fara yi bayan dawowarta gidan shi ne, in za ta fita office ta kan leka ta ce wa Hauwa za ta fita, Hauwa da yake bata kullace ta kamar yadda ita ta kullace ta ba sai ta amsa har da adduar.
Allah yasa a dawo lafiya”.

Ya dawo gida yau da wuri than usual ya samu Sumayyah ta zo gidan, suna falo itada Hauwa. Lokacin an kai kudin auren su itada Usman Kano. Duk basu ji shigowarsa ba daga ita har Sumayyah sun baiwa kofa kofa baya. Sumayya na mata famfo irin na yaran likitoci.
Wallahi Aunty Hauwa kin bari kinyi saurin samun ciki, maimakon ki bari sai nan da yan shekaru biyu haka kina sa shi kuna yan dabaru da bazasu cutar da lafiyarki ba, not necessarily family planning na asibiti ai kin gane, amma kawai kika bari kika dau ciki as early as six month da zuwanki ko amarcin baku ci yadda ya kamata ba. Ga zancen aikin idon ki ya shantakar dashi tunda ya lura kinada ciki, kuma ke kullum yazo shikenan sai ki amsa kira ba dan jan ajin nan namu na mata koyaushe yake so zai samu, ai ni wallahi sai mun shekara uku nida Usman kafin mu fara tunanin tara yara, kuma sau biyu ko sau uku a sati zan ke yarda, ba kya ko tunanin yaya ake haihuwa, bafa sauki ne da ita ba, ke kinga yadda mata ke gumurzu a dakin haihuwar? Alhalin in kin haife shi ke ba ganin dan zaki yi ba, maimakon ki bari sai bayan aikin idonki muga abinda Allah zai yi.
I am imagining yadda zaki raini yaro a hannunki without seeing him, it will not be easy for you a halin yanzu, ga Bhaiya ba hakuri kullum yana like dake ko zama a office baya yi sosai yanzu, baya barinki ki huta ko kadan ki maida jikinki, bayan ana son gap don a maida ruwan jiki, shiyasa sanda Madinah ta tafi bai damu da tafiyar ta ba, ya san yana hutawa sosai, har fiyeda in tana gidan. Na tabbata ita ba haka take barinsa yana caskalar ta kullum ba, duk kin wani rame kamar ba luscious Hauwar Mama ba.
Yanzu da kin haihu baby yana tsotseki, shima ba hakura zai yi ba, duk su taru su tsofar dake (at twetieth) dinki. Maganar karatunki ma naga alama ta bi ruwa, Mama tayi tayi ya dawo dake in bazai saki a makaranta ba har ta gaji ta zuba masa ido.
Sarham ya yi maza ya koma da baya ya bar gidan, yana lissafa irin yadda zai ci uban Sumayyah laada waje.
Asibiti ya koma ransa a mugun bace da Sumayyah. Ya kirata a waya lokacin tana dakinta ita kadai ta bar Hauwa cikin zurfin tunanin, kome Summy ta fada haka ne Sarham baya tausayinta ta wannan fannin kuma ta tabbata ba haka yakewa Madina wannan rashin tausayin ba, kullum ba hutu kamar ya samu engine har gashi mutane sun soma noticing tana ramewa. Dole ta sake lale itama ta koyi jan aji kamar yadda Sumayya tace.
Sumayyah na dagawa da sallama yace Summy! Tace naam Bhaiyana
Ba wani nan. I am no more your Bhaiya daga yau. Fito ki bar min gidana kada ki lalata min tarbiyyar matata.
Na rantse da Allah in sha Allah wata mai kamawa zaa tattaraki ki tafi naki gidan mijin, shi ki je ki ja masa ajin ki gane in zai yi tolerating iskancin ki, kada in kara ganin kafarki a gidana sai kin haihu kinsan ciwon haihuwa da darajar mijin aure.
Sumayyah ta bude ido da baki a tare, nan ta gane ya ji gulmarta. Ta soma afi tana hurwar kayimin rai na tuba Bhaiya, kayimin aikin gafara Bhaiya, subutar baki ne, I dont really mean it. Yace subutar baki ko raayin banza na mata yan duniya kike son cusa mata, naki nayi mata aikin idon, da can ke kika sani? Ko kuwa mace na fama da kanta sai in kwantar da ita in fede mata ido wani abu ya samu Baby na? Wallahi Sumayyah kilbibinki ya isheni dama nasan kina kaita Saloon a cikin estate kuma na gaya miki tun na farko bana so, tunda ina sayo mata shampoo na wanke kai dana zaba mata, wanda bazai canza mata launin gashin kanta daga asalin na hausawa ba.
Sannan ina sane da cewa kin kawo mata wasu mayuka da sabulai na banza da hofinki, wai irin wadanda kike shafawa, kina so ki koya mata bleaching ne? Na taba ce miki kina da kyau ko shafe-shafen yammata yana burgeni? Itada ko ido babu!
I am observing you Summy, ke shaidaniya ce wasa-wasa, duk abinda kike yi wai ke a dole sai kin mayar min da mata yar duniya ko, na ce bansan kalarta bane sanda na aureta?
Ko bansan yadda gashinta yake ba? Ko nace miki in farin fata nake so na Madinah bai ishe ni ba? Ke dai wallahi Usman ya shiga uku, Maijiddah ki bar min kayata yadda nake sonta, muna zaman mu lafiya cikin fahimtar juna da kula da bukatun juna zaki hargitsa mu ko, kema kuma zuwanki kasar nan ne duk kika fara wadannan duniyancin. A da ba haka kike ba wallahi Sumayyah.
I love my wife and her natural beauty, dont dare try to change her for me.
Haka ya cashewa Sumayyah son ransa, har saida ta fidda kwallah. Cewa take In sha Allahu Bhaiya bazan sake ba. na tuba nabi Allah na bi ka.
Kafin in dawo ki tabbbatar kin bar min gida na, tunda ba nida ke muka hada kudi muka auri Hauwa ba.
Jikin Sumayyah na rawa ta shiga dakin Hauwa ta dau jakarta tace Anti Hauwa wannan mijin naki hummm! Sai Allah ya baki hakuri, kinsan Allah mijin ki aljani ne wajen jin magana, Mama tace haka yake da zuqo zance a kunnuwansa tun yana yaro, na tafi, sai an kwana biyu.
Bata kuma gaya mata yaji komai data fada ba. Ta bar Hauwa cikin sake-sake tayi tafiyarta tana cewa Summy kiyi min bayani mana? Daga can bakin kofa ta ce in yazo yayi miki fashin bakin da kansa kuma bazan kara baki shawarar komai ba, daga yau ba ruwana da sabgarku, mijin ki ya maida ke duk yadda yake son ganinki, ni dama nawa shawara.
Murmushi Hauwa tayi tana fadi cikin ranta Sumayyah da Bhaiyanta ba dama ne, ayi fada ayi dadi. Inama itama Zulkifl yana raye da haka zasu zama kamar Sumayyah da Bhaiya, yau fada gobe shiri. In suna shiri kuma sun fi kowa ji da juna.
Sarham bai dawo gidan ba sai dare, yana hanya ma Madina ta kira shi tace motarta ta baci yazo ya dauketa a asibiti sai ya biya ya dauketa sannan suka wuce gida, suka tsaya suka yi take away na pizza da KFC don yau girkin Hauwa ne bana Madina ba ko ya saya ne ko ya girka musu, don har bayan Madina ta dawo bata karbi yiwa Hauwa girkin abinci ba saidai in ta dafa yanzu tana zuba musu ranar nata girkin.
Suna shiga gida ya nufi dakin Hauwa, ta sha wankanta tana shafa mai ga hoda a gefe. Yayi salama ta amsa, ya bata peck a kumatu, ya shafa cikin ta wanda zuwa yanzu ya soma turowa cikin zani, yace hope hes kikcking well? cikin rashin fahimta tace waye? yace baby! Mai sunan Innata. Ta kare fuska da tafin hannunta ta ce aa gaskiya mai sunan Mama ce Yaya doctor. Nan suka hau gardama yace sai an fara saka Inna ita kuma tace sai an fara da Mama.
Daman jiranka nake ka dawo, in shafa hoda ka gayamin ko tayi daidai? Shiyasa tun dazu ban shafa ba yana fesa turare ya juyo ya ce ba na ce ki dinga shafa abarki ko yaya ba? in tayi yawa inna dawo na gani zan gyara miki? ta soma shafawa ya koma daga bayan ta ya dora kai a masangalin wuyanta fuskar shi da tata cikin mudubin hannun ta sun yi kyau har sun gaji, sun yi matching dukkan su choculate incomplexion da wani irin annuri da hasken imani a fuskokinsu. Daga nan Sarha ya kama hannun ta ya cirata tsaye ya soma kokarin kai mata sumba, nan da na ta noke ta ja baya, ya sake rikota yace lafiya? idonta narai narai tace wai mu bazamu dinga hutawa bane? Ina laifin sau biyu a sati ni gaskiya.. Nan da nan ya gane hudubar Sumayyah tayi aiki ta wanke mata kwakwalwa, yace ok. Ok to bari kiji in gaya miki daga yau Sumayyah na koreta kada ta kara zuwar min gida. Ya suri mukullin dakin shi ya bar dakin, yayi fushi sosai, kuma gashi girkinta ne bana Madinah ba don haka ya koma dakinsa ya kunna laptop ya hau aikin da bai yi a asibiti ba.
Hauwa duk taji guilt ya dameta data tuna tafiyar Summy ba shiri da abinda ta fada mata sai ta gane yaji hirar su ne. ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login