Showing 6001 words to 9000 words out of 37977 words

Chapter 3 - HAUWA KULU 4 BY TAKORI

TAKORI   

29 Jun 2024

5874

tayin auren Hauwa ko ta taba ce masa tana masa shaawar aurar da yarta? Shin an taba yi wa namiji (matured) kamarsa auren da baya so?
Shin me ya sa yake kishin Jamilu, kishin nasa kuma ya tunzura shi ga auren Hauwa hajaran-majaran ganin cewa Jamilu da gaske yake? Shi dai ya san babu kishi ga maza a inda babu SO, kuma babu wanda ya yi masa dole ya auri Hauwa.
Iyayensa suna zaman-zamansu shi ya dauko Hauwa ya kawo musu har ta shiga ransu, bai kuma san dalilin da ya sayo mata soyayyah har haka a zuciyarsu ba, amma ya yarda sun amince da ita wanda babban abun farin ciki da alfahari ne a gareshi.
Ya laluba, ya bincika, ko ta ina bai ga da abin da zai lallashi Mama ta janye takunkumin saki ba, ban da ya dauki Hauwa ya tafi da ita Jeddah.
To amma ya zai yi da ita a Jeddah? A nan kam ba ta da matsalar komai, ya san Madinah ba za ta yi maraba da zuwanta ba kamar yadda kuma ba za ta hana shi yin abin da ya zame masa haqqi ba, sannan ba za ta yi wa Hauwa kowacce irin mugunta ba don keta da mugunta ba halinta bane, kai dai barta da kishinta wanda ya wuce kima, amma tabbas daga shi har Hauwa suka sake suka shiga gonarta sai ta dafa su ta ruwan sanyi babu duka babu zagi. Hakan kuma ba zai hana shi faranta wa Mama rai ba, da ceton igiyoyin aurensa dake reto, da mutuncinsa a idon su Inna ba.
Don haka barcin Dr. Sarham a wannan daren bakidaya bai fi na awanni biyu ba, shi ma sai goshin asubahi ya same shi. Abin da ya kwana mafarki kuma bakidaya a daren bai wuce Hauwan da ya kwana da ita a ransa ba.
Kusan sai da ya makara tashi sallar asubahi, abin da ba halinsa ba, Abba na hanyar dawowa daga masallaci suka hade a kofa, ya ce, Lelen Abba, ya da makara?
Ya sunkuyar da kai.
Abba ya ga har wani ramewa ya yi cikin kwana daya, yayi murmushi a ransa shikadai yace yaro wa ya gaya maka ana raina mace? Ya wuce shi yana cewa, A dinga kula da lokacin sallah, damuwoyin duniya ba masu karewa ba ne, balle su hana dan Adam barci a kan lokaci. Wani lokacin ma mu muke sayo wa kanmu damuwar da kudin mu. Ni ban ga laifin Mai Sharia ba, shes in judiciary, dole ta kasance mai adalci ga dan kowa.
Maganar nan mai sauki ce in baka son ta ka saki ka baiwa maso sonta dama, short and simple, ban ga name zaka sa damuwa a cikinta ba. Ka tabbatar kafin ta tashi daga barci ka aiwatar da umarninta don wallahi ba barazana take maka ba, iyakar gaskiyarta kenan da hukuncin da zata iya dauka a matsayinta na uwa ga kowannenku. Annan mai tabbatar da adalci a cikin alumma.
Ya sa kai ya yi wucewarsa cikin gida.

Kai! Yau hatta karatun sallah ba daidai Sarham ya karanta shi ba, astagfirullah. Ko da ya idar kuma ya kasa dawowa gida gudun haduwa da Mama. Ya ci gaba da zama a masallaci har sai da gari ya yi haske, sai a lokacin ya tuna yau ne daurin auren Surayyah, kuma karfe tara za a hallara a gadon kaya. Dole ya koma dakinsa wajen karfe bakwai na safe, yana shiga wanka ya fara yi, ya fito yana tsane kansa da tawul da wani daure a kugunsa ya hau kiran lambar Hauwa. Shi kansa bai san me zai ce mata ba. Kawai ya samu kansa da son jin muryarta.
Anyi saa Mama ta bar wayar gun Mardiyyah ita kuma tana sassan Abba, baccin safe dole ne ga Mama in dai ta san bata kwanta da wuri ba, to muddin tayi sallahr asubah zata koma barci, sai inda ‘alarm’ din data saita ya tashe ta, duk da kuwa ta san yau tana da hidimar jamaa amma jiya bata samu barci da wuri ba, bayan ta tabbatar Sarham ya tafi ta maida Hauwa dakinta kwana tayi tana rokon Allah da nafilfili akan Allah ya daidaita tsakanin su.
Mardiyya na zaune tana karanta morning azkar a cikin hisnul muslim kiran Yaya Sarham ya shigo. Tana dagawa ta gaida shi a ladabce, ya amsa, sannan yace, Me ku ke yi yanzu Mardiyya?
Ta ce, Anti tana shafa mai ne ta fito wanka, ni kuma ina azkar.
Ya ce, Mardiyyah maza ba ta wayar kafin Mama ta shigo kinji kanwata?.
Mardiyyah ta tashi ta kai wa Hauwa waya, wadda fitowarta kenan daga wanka tana shafa. Ta yi sallama a nutse, ya yi ajiyar zuciya ya ce, Maijiddah kanwar Sarham, autar Inna da Baba, yar gatan Mamanta, ki shirya maza yanzu ina jiranki kafin daurin aure zamu dan fita, don Allah bana so Mama ta sani, kiyi sauri.
Hauwa ta zaro manyan idon kamar yana kallonta cikin tsoro, Yaya Sarham! Ta yaya za mu fita Mama ba ta sani ba bata yi izni ba?
Ya ce, In ci darajar Inna, in ci albarkacin Malam, yau tana cikin hidima, ba ganewa za ta yi ba.
Musamman in muka bar Mardiyyah a dakin. Zan roke ta in ta shigo ta ce, kina toilet.
Hauwa duk ta tsure, ita ba ta saba abun rashin gaskiya ba, besides mutumin nan ina zai kai ta???
In kuma ya je ya sayar da ita fa duk a cikin rashin SO? Ta tabbata Maman ta fi shi sonta, ita ba ta da wani ‘hope’ a kansa yanzu. Dadin bakinsa na jiya bai wani dadata da kasa ba. Wallahi yanzu za ta iya zabar Mama sau dubu ta bar likitan Inna.
Hauwa ta nisa, jin wata kwalla ta taru a idonta da ta tuna yau shekara guda fa mutumin nan bai kara bi ta kanta ba, bai neme ta ba, bai damu da ita ba sai yanzu da aka ba shi yancin da yake nema ne zai bi ya kalallame ta? Hauwa ta bude manyan idanun nan ta kada su harr! Kaman Sarham yana gabanta, ta ce,
Ni kam babu inda zani Yaya Doctor ba izinin Mama.
Za ta kashe wayar kamar ya sani ya ce, Kada ki sake ki kashe min waya!.
Hauwa ta yi shiru, cikin fushin ban mamaki ya ce, Kuluwa! Na ce ko ba da Kuluwa nake magana ba?
Umarni na za ki bi ko na Mama? Shin ni da Mama wa ya biya sadakin aurenki? Kuma wa ya kawo ki cikin rayuwarsa?”
Hauwa ta sake yin shiru, kamar ta saki kuka.
Ya ce, To idan ni nake auren ki ba Mama ba, na yi miki umarnin Mardiyyah ta kawo ki mota ta yanzu-yanzu kafin Mama ta fito daga turakar Abba, ko two hours ba za mu yi ba, za mu dawo, I promised!.
Za ta yi magana ya ce,
Umarni ne ba jin raayi ba. Ya kashe wayarsa.
Hauwa har da wani gumi dake tsatstsaafo mata a goshinta ta yarfe shi da hannu, ta ce cikin yanayi na shiga rudu.

Mardiyyah na shiga uku!!!”

Ba ki shiga uku ba Anti, ina jin komai kin manta wayar a handsfree ta ke. Anti Hauwa Yaya Doctor ya fi ki gaskiya shine mijinki wanda aljannar ki ke tare dashi ba Mama ba, ki bi umarninshi bazaki tabe ba, na rantse zan rufa miki asiri, ni ma bana son abin da Mama ta ke masa tun jiya wallahi ko abinci bata bashi ba.
Ta zaro abaya mai kyau ruwan toka-toka kirar Dubai ta kawo mata, Hauwa ta karba cikin mutuwar jiki jin an ce tunda yazo Mama bata bashi abinci ba, ta saka da sabuwar ‘brazier’ da sabon pant da vest, duk farare kal sababbi, cikin akwatinta na lefe Mardiyyah ta debo mata su, ta kawo mata khumrah oil perfume da Mama ta bata cikin wadanda aka hadawa Surayyah ta bata ta shafa a koina, sannan ta nannada mayafin abayar a kanta, ta miko mata ‘photocromic glass’ dinta shi ma ta saka, takalmi ma sabo dal ta dauko mata samfurin vincci maras tudun dunduniya da jakarsa yar karama. Hauwa ta yi kyau sosai kamar balarabiyyar kasar Kuwait mai duhun fata amma. Mardiyyah tayi ta cewa Anti kamar ba ke ba yau. Sai da ta leka ta tabbatar Mama ba ta nan a falo kuma bata dakinta sannan ta zo ta kamata zuwa parking lot na gidan.
Tuni Sarham yana cikin motarsa a zaune ya yi kyau shima sosai cikin farar shadda sol sabuwa daga ledarta, kai ka ce shi ne angon da za a daurawa aure yau.

Tun daga nesa yake hango Hauwa da Mardiyya suna takowa, sai da gabansa ya fadi ganin yadda Hauwa ta koma a zahiri. Tun zuwansa bai mata wannan kallon na tsanaki ba sai yau. Yadda gabbanta suka bubbude ya bashi mamaki musamman kirjinta. Tun kafin su karaso ya bude mata kofar gidan gaba, Mardiyyah ta taimaka mata ta zauna ya dube ta da murmushi, ya ce,
Na gode kanwata ta kaina, nagode Mardhiyyah kinji. Allah ya yi miki albarka, Allah ya kawo miji nagari. Mai albarka kin ji?.
Mardiyyah ta daga masa hannu tana dariya, Amma don Allah Yaya Doctor kada ku dade, in Mama ta fito wajenmu ta ke fara zuwa.
Ya kunna motar yana cewa, Haan, ni yau ina ganin abu, ni da matata ake min duk wadannan iyakokin? To je ki na gode, me Antin za ta sayo miki?
Bakin Mardiyyah har kunne ta ce, Ice cream.
Ya ce, To ke Maijidda kada ki manta da tsarabar Mardiyya.
Fuskarta ba annuri ko kadan, sai cika take tana juya manyan idanun nan ko amsawa ba ta yi ba, ya yi reverse ya fita daga flat dinsu yana ta mamakin duk yaushe Hauwa tayi wannan wayewar da class din bashi da labari?.
Tunda suka hau titi, Hauwa ba ta ce masa uffan ba, bayan gaisuwa a rowace, wata irin gajeruwar gaisuwa wai ina kwana ya gajiyar hanya? kada ki kara kada ki rage bayan wannnan. Shima ganin take-takenta sai ya share ta, yaki amsa gaisuwar, ya saki radion motar ana labaran safe a tashar BBC Hausa. Sun yi nisa sosai da tafiya, cikin muryar jan raayi ya ce, Maijiddah.
Ta juya inda yake, idanunta fal kwallah da kiris take jira ta zubo, don ba ta taba bata wa Mama rai ba, even by mistake a tsayin zaman su na shekara guda. Amma yau shi da ya wulakantata ya zo ya ssaka ta yin laifin da bata san yaya zata yi da shi ba.
Ya ce, Maijiddah ni ne fa, ni kika fara sani kafin Mama. Ki sa a ranki ni na kawo wa Maman ke, kuma ni nake aurenki ba ita ba. In kin yarda da hakan, kin huta, in ba ki yarda ba kece ke da wahala, don ni ba ma yanzu za mu koma gida ba gakiya sai na huta.
Tunda na sauka kasar nan hatsi bai ga baki na ba, ruwa bai shiga hanjina ba duk an daga min hankali ko neman jin uzurina baayi. Saboda Allah in Mama ta daina so na ai ke ba zaki ki ni ba Maijiddah ko don albarkacin Inna, na san da tana garin nan da ban kwana da yunwa ba.
Ta cikin gilashinta take bubbude ido tana kara musu girma. Sai ta ji hannunsa na hagu a kan nata ya damke shi sosai yana cakuda tafin hannunta, yana ci gaba da tuki da hannu guda. Ya ce, Kafin ta kashe min aure, zan dauki nawa matakin, tunda Mama ba ta jin lallashi.
Hauwa dai ba ta san ina suka je ba, amma daga wayar da yake yi da wani abokinsa ta fahimci wajen yin fasfo immigration office’ ne. Kafin su zo kuma har an saka file dinsu a layi na neman fasfo.
Don haka suna shiga ba su bata lokaci ba ta yi ‘thumb-print’ da taimakon Sarham da na abokinsa Rislan maaikacin immigration. Sai da suka kammala Rislan din ya ce nan da kwanaki uku zai kawo masa fasfon Hauwa har gida, hannunsa cikin na Hauwa suka dawo mota, kada ka so ka ga yadda suke jan attention sabida glass din ya boye ainahin rashin ganin kuma ga miji ya kama hannun matarsa a bainar nasi suna shiga duk inda suka zo a immmigration, har suka gama suka fito zuwa motarsu ya bude mata ta shiga ya rufe, sannan ya zagaya ya shiga barinsa, ya tada motar.
Maimakon su nufi gida New Site sai ya wuce zuwa wani wajen daban. A rashin saninta gidansa ne da ya kammala ginawa a rijiyar zaki.
Sai da ya tsaya ya karba musu abincin ‘breakfast a AlAmir Restaurant sannan ya ce ta fito su shiga ba jimawa za su yi ba, wai abinci zai ci. Kamar ba za ta fito daga motar ba, ta ji hannun Sarham cikin nata ya dagota tsaye, ya ce,
Yau ni ne dan jagora tunda na kori Mardiyyah.
Yaya Doctor nan din ina ne? Na dauka mun gama abinda ya fiddomu gida za mu koma?
Ya ce, Ba wani abu, Inna zan daukarwa sako kuma inci abinci, nan din ba wani waje bane gidanki ne dana gina miki keda yayanki.
Ai jin ya ce Inna babu tambaya ta fito don da ma ya san ‘weakness’ dinta a komai Inna ne.
Ya bude gate din da kansa ya shigar da motar ya fito ya rufe, sannan ya kama hannunta suka hau har zuwa dakinsa da ke saman bene kasancewar duk muhimman abubuwansa a dakin suke ajiye. Akwai dindimemiyar katifa a kasa shimfide da bedsheet da filallika. An gama komai na ginin gidan sai fenti ne baa yi ba. Gida ne mai bangare biyu kowanne da dakuna uku da babban falo sai nasa dakin masterbedroom falle daya a saman bene. Suna shiga ya ajiye ledar breakfast din da ya yi order din. Ya maida kofar ya rufe bayan ya zaunar da ita cikin kujerar sofa bed guda daya dake dakin, ya ce,
For Allahs sake, tunda aka daura mana aure, ko ince tun kafin nan, mun taba zama mun yi magana kuwa irin ta saurayi da budurwa?
Hauwa saura kadan dariya ta kwace mata, amma ta fuske, ita yanzu kome zai yi ta baya ta raggo, ta san pressure ne ya saka shi ba wani abu ba, ya zauna kusa da ita, har kafadunsu na gugar na juna. Da sanyin murya ya ce,
Hauwau-Maijiddah. Ya sake cewa, Kuluwa-Hauwa-Kulu, yau zance na zo, da neman iri.
Hauwa ta zumburo baki gaba don ko kadan kashe muryan bai huda ta ba don jin abun take banbarakwai wai namiji da suna Hajara don ba haka ya sabar mata ba, kamar ta ce masa, fisabilillah Yaya Doctor kai ba ka ji kunya ba da ka ke kiran ma kanka samartaka? Ashe bata sani ba tsabar haushin da ya bata a fili ta fadi hakan ba tare da ta sani ba.
Sarham yace ya ce, Naam, wai da ni kike? To bari in gaya miki wallahi na fi saurayi yau jin samartaka, zance kuma na fara zuwa daga yau har mu koma Jeddah”, ya dora hannayen shi kan kafadunta idonsa narai-narai kamar tana kallonsa, ya zare mata glass din ya ajiye a gefe, ya dora wuyansa kan kafadunta cikin dabarar da bata san yaushe hakan ta faru ba ya soma magana cikin wata irin murya mai tsuma zuciya da gangar jikin diya mace.
Na yi kuskure mai yawa Maijiddah da na ke so ki ba ni dama in gyara.
Na san ba a bari a kwashe daidai, amma aka ce matar na-tuba ba ta rasa mijin aure.
Hauwau na san ba ni da wani matsayi a zuciyarki yanzu na rasa, har nawa na da kuwa, duk a dalilin ajizancina.
Ya kai hannunsa na dama bisa habar Hauwa, ya wani irin rungumo ta jikinsa cikin zafin nama yana rirrigawa irin lallashin da ake yi wa baby.
Forgive your husband, forgive him!.
Hawaye masu dumi suka biyo kuncin Hauwa, ta rasa inda zuciyarta ke tsalle-tsalle a cikin kirjinta. Sarham ya sa hannunshi daya ya dago fuskar Hauwa yana kallon yadda hawayen ke gudu a kan kuncinta luwai-luwai da shi jikinta yana rawa. Don wannan kusancin da ya samar a tsakanin su baaia taba faruwa ba. gabadaya ta firgice ta tsorace don tana ganin babu kyau kuma bai kamata ba ace ta yi hakan da Likita Sarham din Inna. Ya ci gaba da fadi cikin muryar da tafi ta dazu ragaita,
Hauwa-Jiddah na tuba na bi Allah na maida kalamaina, na hadiyesu kamar yadda nayi amonsu a cikin wauta da ajizanci irinna dan adam.
Daga yau ke matata ce ta sunnah da na aura don ina so, wallahi tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login