Showing 1 words to 3000 words out of 37977 words

Chapter 1 - HAUWA KULU 4 BY TAKORI

TAKORI   

29 Jun 2024

5884

 YAR CIKIN BADALA
(HAUWA-KULU)


4

PAID BOOK
SUMAYYAH ABDULKADIR
babbangoro2015@yahoo.com
07030137870
(whtsp only)





SADAUKARWA
SADAUKARWA NE GA DUK MAKARANTA LITTATAFAINA YAN CIKIN BADALAR KANON DABO.












HAUWA-KULU 4
A
na i-gobe Sarham zai iso wato ana i-gobe daurin auren Surayyah, har zuwa lokacin Surayyah na gidan Haj. Kulu, sai dai ta zo gidan lokaci-lokaci ta gaida iyayenta ta koma. Ko dakin da Hauwa ta ke ba ta shiga, sai ko in sun hadu a babban falo su gaisa kadaran kadahan, shi ma sai in Hauwan ce ta fara kula ta. Yadda Mama ta yi wa Sumayyah uzuri a kan Madinah, haka ta yiwa Surayyah akan Hauwa-Kulu, wato jininsu ne bai hadu ba.
Amma a hankali in sun zauna daga ita sai Surayyah tana yawan yima Surayya huduba akan Hauwa cewa amana ce ita a hannunsu bata da kowa sais u a Kano yanzu, kuma tunda tana auren dan uwanta dole tayi zumunci da ita, watarana har yayanta sai ta goya.
Mama ba ta san a kasan ran Surayyah ba haka ba ne, kawai ta raina aji da asalin Hauwa ne. Haka kawai ta zo ta zame wa iyayenta 'liability' miji ba ya ta tata, amma an wani girke musu ita a gida sai faman habaka take kamar mai cin yeast.
Mama ta shigo dakin Hauwa rike da wata gora ta ruwan swan ta ce, "Hauwa, kun yi sallahr la'asar ne ki ke faman barcin yamma haka? Barcin laasar baa bin arziki bane.
Muryar Mama ce ta tashe ta daga nannauyan barcin. Ta yunkura ta mike zaune, ta ce, 'Mama lazimi nake, barcin ya dauke ni fa".
Mama ta saka mata gorar da ke hannunta cikin nata hannun, ta ce, "Ga nan zuma ce ingantacciya maganin basir cikin wadanda aka hadawa Surayyah ne, kullum ki sha sosai sau uku a rana", sai kuma gorar tsimi jarka guda. Shi ma ta aje mata a gefen gado har da kofi a kai, ta ce, "Daga yau har kwana uku nan gaba su nake so su zama ruwan shanki, kin ji ko Hauwa'u?"
Kai ta gyada tare da yin godiya wa Mama, duk da ba ta san ko na mene ne ba.
Hauwa ta bi umarnin Mama tana shan komai ta kawo mata da zuciya daya, babu wani tunani na daban a ranta. Tasan dai Mama bazata bata abinda zai cuceta ba duk da tana ta cewa maganin basir ne. Ga tukudin Ghana shima tana ci lokaci lokaci don duk abinda kace ma Hauwa yana gyara fata bata wasa da shi. Fatar da ba ganinta take ba, amma tana kula da abarta sosai, tana kuma tattalin ‘dark complexion’ dinta. Yinin ranar zungur, ko abinci ba ta iya ta ci sosai ba, saboda kayan zakin da Mama ke dirka mata sun cika cikinta.
Saukar yamma Dr. Sarham ya yi a gidan su, banda kalar fatarsa da bata da hasken tasu, tsammani za ka yi mutumin kasar Maghrib ne, 'yar kibar da ya yi ta kara fiddo asalin tsahon sa da kyawun surarsa, ilhamarsa da cikar zatinsa ya kara bayyana sarari a cikin shekarunsa na yanzu wato shekarun fita kuruciya talatin da biyar. 'yar kibar da ya kara ta kara fiddo kamalarsa ta cikakken magidanci mai wadatar jini ajika da rufin asirin rayuwa.
Dr. Sarham Abbas Shanono, ya yi sallama a dakin mahaifiyarsa, don bai samu kowa a babban falon ba. Kuma yayi sallama ba wanda ya amsa shiyasa ya nufo dakin Mama kansa tsaye.
Abin da ya gani ya matukar impressing dinsa, wato Hauwa ce duke a gaban Mama tana yi mata karin karatun Al’qur’ani. Mama Ta dade da fahimtar Hauwa ba ta samu yin zurfi a karatun addini ba, kuma ba ta yi saukar Alkur'ani ba don makarantar allo kawai ta yi a Badalar Kofar Naisa.
Ba tun yau ta soma yi mata karin ba. Sun dade tana kara mata daga sama (baqarah) musamman da ta fahimci kwakwalwar Hauwa daban ta ke a wajen rike abu. Hakan ta ke ga duk masu lalurar idanu (they are extra-brainlliants), suna da saurin hadda da saurin fahimta. Tun bayan tafiyar Sumayya ta ke yi mata karin lokaci-lokaci in tana gida ba yau suka fara ba. haka na bokon ma, da yake abu daya suka zaba (LAW) duk abinda ya shige mata duhu in ta dawo gida ko assignment aka bata Mama ce take facilitating dinta.
Sarham ya tsurawa HAUWA ido daga bakin kofa yana dan murmushi, sai duk ya ji shi kamar mara gaskiya, musamman da bai ga wani ‘special’ abu da aka shirya domin taronsa ba kamar yadda Mama ta saba in zai zo, tun daga karkashin zuciyarsa yake jin guilt na yanyameshi. A yadda Hauewa ta duka a gabanta tana daukar hadda kai ka ce diya ce da uwar da ta haife ta.
Hauwa ta yi wani irin kyau da girma a idanunsa, ta murje ta yi sumul da ita kamar dai 'yammatan gidan, wato Sumayyah da Surayyah. Ta kara girma na ban mamaki don a lokacin ta shiga shekaru 19, fatarta har da sirkin wankan tarwada da kai tsaye ba za ka kira ta baka ba, ba tare da kara da (black beauty) ba. Kirjin ta ya cika yayi full da madarar shanu irin dai 'teens' dinnan masu wanke goma su tsoma biyar a gidan 'yan boko.
Mama ta amsa masa fuska a sake, amma Hauwa wani irin shiru ta yi, kamar ruwa ya cinyeta, sai dai ta amsa a zuciyarta don cika umarnin musulunci, wa take ji haka kamar muryar Yaya Doctor???
Mama bata gaya mata zai zo ba koda wasa, duk da ta san gobe ne daurin auren Surayyah, tarewarta ce aka ce sai wani satin, inda zaa kai ta Ikko (Lagos inda Engnr. Aliyu ke aikinsa kenan). To ko daurin auren kanwar tasa ya zo? Don dai ta san ba don ita Yaya Doctor ya zo Kano ba, kuma bazai taba zuwa saboda ita ba.
Sarham ya karasa har gaban Mama ya tankwashe kafafu yayi zaman rakuma a gabanta, kamar bafaden da yayiwa sarki karya, ita kuwa murmushi kawai take tana fadin, "Lale marhabin, maraba da baban Waheedah".
Ya zauna a kujerar da ke fuskantar Hauwa yana ta murmushi yana kallonta, ya ce, "Karatu ku ke haka Maijidda? Masha Allah".
Da farko Hauwa niyyar share shi ta yi, amma sai ta kasa ta gaishe shi a ladabce, sannan ta mike don ta ba su wuri, ta ce, "Mama zan je in yi sallah".
Mama ta ce, "Babu laifi, kice da Mardiyya ta zo ta dauko miki shanyar da ta yi miki, magriba ta kawo kai".
Sarham ya bi ta da kallo, tana ficewa tana dafa bango, yana ta mamakin girman jikin da ta kara da cikar idon da ta kara (idan cikar da ake kira kinfi karfin raini). Akwai wanda ya kai Mamansa iya kula da 'ya'ya mata?
Sai da ta kai bakin kofa ya ce, "Maijidda, kin san hanyar dakin ne? Ko inzo in rakaki?"
Mama ta ce, "Ai ita ba ta fiya son a yi mata jagora ba, ko Mardiyyah ta ce za ta raka ta wani wuri a cikin gidan nan cewa ta ke ta zauna, ta san kowanne ‘direction’ na cikin gidan nan. Mardiyyah ta ce min har a makaranta kanta tsaye ta ke shiga aji, ta manta da ita a baya".
Hauwa ta wuce dakinta ba tare da ta tanka musu ba. Sai da ta bace masa ya iya dauke ido daga hanyar da ta bi, yayi wata sasanyar ajiyar zuciya ce,
"Na ga alama Mama kina jin dadin zama da Maijiddah".
Mama ta ce "ai ba sai kaga alama ba, ba zan boye maka ba ta dauke min kewar Sumayyah gabadaya. Hauwa mutum ce da ta san darajar mutane, ta ke kuma da son karatu, ga kula da addini da girmama babba wannan shaida ne na tarbiyyar uwa mai kyau data samu irin ta mutanen da. Kai dai barta da rashin daukar wargi, kuma ba ta so a ce ba ta gani, yanzu za ta hau fushi ba gaira babu dalili.
Akwai ranar da Barr. Hannatu ta zo, ta mike za ta ba mu wuri tana lalubar bango, sai Barr. Hannatu ta ce min "makauniya ce ne?" Ai kuwa shikenan, ranar mun ga boni, kada ka so ka ga fushi, duk gidan nan kasa gane kanta mukayi, don kuka ta hau yi, wai Ghana za ta tafi an mata gorin ido.
Saida fa Abba ya sa baki ya ba ta hakuri da kansa muka samu lafiya".
Sarham nata dariya, sune bakin jin kalmar GORIN IDO daga bakin Hauwa, tuni ya manta da guilt din dake damunsa don Mama ko a fuska bata nuna yayi laifin komai ba, ta bar shi ya sake da welcome face, shi ya fi kowa sanin Hauwa ba ta son gorin ido, kuma ba ta so a ce mata mara gani, ko makauniya.
Har gara ma ka ce mata kuluwan da ba ta so, a kan dai ka yi mata kalaman nan guda biyu.
Mama ta tambayi lafiyar Waheedah da Madinah ya ce, “Mama suna lafiya bakidayan su har Sumayyah. Na barota tare dasu a gidan. Mama ta dube shi cikin ido. Tayi nazarin irin hutu da kwanciyar hankalin data gani a tare da shi. Sai ta girgiza kai. Tace.
"Dama ina jiran ka ne kazo muyi magana ta gemu, wadda tafi karfin a yi ta a waya".
Sarham yace "Amma Mama kya bari in huta in dan yi freshen up ko? Ko ruwa yau baki bani ba, ban ga komai na daga delicious dinky a kan dining yana jiran saukata ba".
Wani zazzafan kallo da Mama ta sakar masa sai da ya sha jinin jikinsa a take, kuma nan da nan yanayin fuskarta ya sauya, ba shiri ya tattara hankalin sa wuri guda ya bata. Mama ta dauke ido daga kansa a hankali cikin dabara da hikima da fasahar zance irin nasu na kwararrun lauyoyi ta soma magana.
"Maganar tawa akan HAUWA KULU ne!".
Ya kara shiga nutsuwar sa don kwatakwata babu wasa a tareda Mama yanzu.
"Yarinyar nan masoya sun fara yawa, kuma ko ance musu da aurenta basa yarda, ciki harda Farfesa Alhassan abokin Abbanku na tsangayar su.
To kaga dai itama mace ce, mutum mai cikkar lafiya kamar kowa, kuma yadda nakeson su Sumayyah da zaman gidan aure karkashin kulawar miji irin Abbansu haka itama nake son ta samu.
Yanzu a misali ace mijin Sumayyah ya jingineta a gidan iyayensa tunda ya aureta, alhalin yana ikirarin zamansa take yi, yana aurenta har tsayin shekara guda da sunan ba sonta yake yi ba, in this regard, mu iyayen ta da kai Yayanta wane mataki ya kamata mu dauka???
Kuma kaima ka fada ka sake har a gaban idona da gaban idonta cewa kai kanwar jini ka dauketa ba mata ba.
Don haka nake ganin, abu mafi maslaha shine Sarham ka sahalewa Hauwa aurenka, yadda dana gama bikin Surayya itama in zo in fara shirin nata itada Sumayyah. Wannan karon aure zan yi mata na gata da soyayya da wanda yake sonta itama take son shi da zuciya daya. Don haka Sarham, ina jiran takardar sakin HAUWA-KULU daga nan zuwa gobe kafin ka fita daurin aure".
Dr. Sarham tun daga yatsar kafarsa har zuwa tsakiyar gashin kansa gumi ya shiga karyo, ya rasa a yanayin da kalaman mahaifiyar sa suka jefa shi. SAKI! Saki fa. Kai tsaye Mama ke nema tsakaninsa da Hauwa-Kulu.
Shi ai babu saki tsakanin sa da Hauwa koda babu soyayyar aure. Da wane ido zai dubi Inna Safiya da Malam Bilyaminu yace dasu wai yau ya saki Hauwa???".
Mama bata kara bi ta kansa ba, ta tashi ta bar masa dakin jin shigowar Abba Prof. Ko motsi ya kasa daga inda yake zaune balle ya fita don ya gaida Abba.
Abban ne da kansa ya karaso har kofar dakin Mama sai ya ganshi a zaune kamar sassakakken gunki. Ya ce "a'ah, mutanen Jiddah ne? Maraba lale da Lelen Abba, Jabbama-jabbama, yaya hanya da kuma amaryata-uwata Hajiya KULU?"
Sai lokacin Abba ya lura da irin jibi (zufa) wato gumin da Dr. Sarham keyi daga zaune. Kamar wanda aka fiddo daga tanderu. Abba Prof. yace a hankali.
"Ko lafiya?"
Sarham bai san sanda ya zube gaban Abba Prof ba yana rokonsa, kan don Allah ya baiwa Mama hakuri.
"Me ke faruwa? Me kayi mata?"
Idanunsa sun kada sunyi jajir, yace "Abba koma wane irin laifi take tuhumata dashi na amsa laifina.
Amma don Allah ka roketa ta janye kalmar SAKI tsakanina da Maijidda.
Zan iya yi mata komai amma banda saki tsakanin mu. Auren mu na har abada nake burin ya zama. Me zance da su Malam Bilyaminu idan Mama ta takura min na saketa?"
Mama ta dawo dakin tana cewa da babbar murya mai cike da bacin rai daya dade yana cinta a zucci;
"ai kawai cikakken bayani zaka yi musu na irin rikon auren da kake yi mata tunda suka baka ita, cewa kai kanwar jini ka dauketa ba mata ba, suyi hakuri kawai, zaifi musu alkhairi, su karbeta daga hannunmu su aurawa dan Malam Munkaila a kan ka.
Na tabbata zai kula da ita zai bata hakkin ta na aure kamar yadda addini ya ce yayi, ba zai bi son zuciyar sa a kanta ba wai don zumuncinsa da iyayenta.
Ba zai zauna yana rusa mata rayuwa ta hanyar rashin bata gurbin matar aure, at the same time yana rusa lahirar sa ba da sunan wai yana taimaka mata".
Idanun Mama a warwaje take magana kamar zata kife Sarham da Marika, ko ta samu ya shiga hankalin sa ya gane meye a zuciyar sa game da Hauwa-Kulu.
Budar bakin Abba Prof. Sai cewa yayi "Da kyau Mamansu, ina bayanki anan Mai Shari'ah uwar kowa. Ai mu saidai mu ce maka Allah yayi maka albarka ka kawo mana diya abar alfaharin kowadanne iyaye.
Don haka ka sahale mata shi yafi alkhairi in yaso ta cigaba da zama tare damu tana karatunta har Allah ya bata mijin dake sonta da gaskiya. Ko jiya an tambayeni ko tanada aure? Wannan al'amari daman ya isheni, don ko na ce tanada aure ba yarda ake yi ba".
Iyakar tashin hankali Dr. Sarham ya shigeshi irin wanda bai taba shiga ba. Mama ta saka murya ta kwalawa Hauwa kira. Mardiyya ta fito da ita da hanzari ta zaunar a gaban Mama ita kuma ta koma daki jikinta na bari.
Mama ta ce cikin zafin rai "ga ni, ga ka, ga Abba ga kuma Hauwa. Inaso ka sahalewa Hauwa aurenka".
Ta dubi Hauwa wadda ke tsugunne kan kujera a dofane cikin firgita, don ta kasa gane me akeyi, ta san dai abinda zaisa Mama fushi irin haka ba karamin abu bane har dakinta take jiyo tahin fadanta. Mama ta daka mata tata tsawar "ke Hauwa! Nace wannan mutumin ya sake ki haka, ko kinason cigaba da zama da aurensa?"
Hauwa ta hadiyi miyau da kyar, ji kake, mukut, da kyar ta daga manyan idanunta a daidai saitin da take jin sukar idanun Sarham a jikinta. A lokacin shima ya dago, goshi duk zufa, cikin kidima da tsoron abinda zata ce.
Da kyarmar murya Hauwa tace "a'ah, bana son auren, Yaya Doctor ai Yayana ne babu son aure tsakanin mu".
Kai kace Mama ta karanto mata abinda zata fada ne kafin ta kira ta, yadda take maganar tiryan-tiryan cikin kyarmar murya. Mama tace "to kaji, don haka daga yau zuwa gobe kafin fita daurin auren Surayyah ka rubuta takardar sakinta ka bani hannu da hannu, umarni ne ba zabi na baka ba".
Daga haka Mai Shari'a ta bar wurin cikin tafasar zuciya kai kace Hauwa ce diyarta ta cikinta ba Sarham din ba.
Abba Prof. Ma ya gyada kai kawai ya shige dakinsa don Mama ta gama yimasa jarumtar da shi ya kasa akan Sarham saboda yadda yake sonsa.
Ya saura daga Sarham sai Hauwa a dakin Mama, ya ciro hankicinsa daga aljihunsa yana share zufar goshinsa.
Ya dubi Hauwa cikin takaici tana kokarin tashi yace "koma ki zauna, nace ki tashi ne?" Hauwa ta koma ta zauna a kujerar dake fuskantarsa. Babu digon nadamar furucinta a tare da ita.
"Da hadin bakinki Maijiddah aka shirya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login