Showing 30001 words to 33000 words out of 37977 words

Chapter 11 - HAUWA KULU 4 BY TAKORI

TAKORI   

29 Jun 2024

5880

kuwa kunya tayi balain kama Hauwa da sauri ta saka doguwar rigar barci mai kyau ta bi bayan sa zuwa dakinsa don ta san hanyar dakin. Ta kwankwasa ya amsa da yes daga ciki sai ta shiga.
Ya kalleta ya dauke kai zuwa aikin sa, tace Baban Waheedah please kayi hakuri wallahi ba zan sake ba yayi shiru yana cigaba da operating system dinsa, ta taho kamar zata bi ta kansa yace in kika fasa min laptop sai kin biya ni ta muryarsa ta san inda yake zaune ta laluba ta zauna akan cinyarsa shikuma ya hau kokarin zillewa amma Hauwa bata bashi wannan damar ba.
Sosai ta inganta mishi daren yau kamar babu ciki a jikin ta, kamar babu lalurar ido a tare da ita, yau Sarham shi ya koma dan gata sai yadda Hauwa tayi da shi. Sun farantawa juna rai kamar bazasu ragewa gobe ba kafin su koma maida numfashi manne da juna. Saida ya koma Sarham din sa ya ce mata Maijidda, naji hudubar da kawar ki tayi miki, amma ki sani ni ba daya nake da sauran maza ba.
Ba wani canjin halitta ko tsofewa da zai sa in daina son matata.
Sannan barin ain samu abinda nake so a lokacinda nake so shi yake kara ninka wannan son yake kuma kara kusantoki da zuciyata.
Hauhuwa da wuri kuwa kuwa in duk sati ake yin ta ni kulllum nake so kiyi min.
Makaranta kuma ina sane na barki sai wata shekarar don bana son kiyi jigilar karatu da yaron ciki.
Maganar aikin ido kuma ban gama abinda nake tattarawa ba sannanba zan miki aiki alhalin kinada ciki ba sai Allah ya saukeki lafiya kinji?
The more you give me access to it, the more I addittionally love you.
Don haka ba Sumayyah kadai ba, duk wani wanda zai baki shawara akaina ko akan abinda zai amafni jikinki yabi bayan ni. Ban ce kada kiyi kawance da kowa ba amma ina so ya zama nine amininki sama da kowa, feel free to discuss everything about our marital life with me kin ji? Not the third party wadanda ba lallai bane su san meye sexual likes and likes dina ba.
Kunya sosai ta kama Hauwa, ta roki gafara, ta dauki alkawarin bazata sake yi masa rowar wannan ba, sannan bazata zancen mijin ta da kowa ba sai da shi kansa. Kuma daga wannan ranar ne, HAUWA BILYAMINU, ta fara kiransa da suna MY PACESETTER!!!.

Sati mai zuwa insha Allah za mu shiga umrah cikin makkah ni da ke, daga nan muje Madinah ziyara mu yi addua solely a kan Allah ya saukeki lafiya HAUWA, ya bamu Inna mai albarka, mai irin dukkan halin INNATA, mai tsafta mai kyautar abinci mai kula da yayan ta kamar yadda take kula da ranta.
A karshe ya shafa kanta tana durkushe gabansa yace Allah ya saukeki lafiya Hauwa-Jiddah, Allah yayi miki albarka Hauwau-Maijiddah, yadda kika faranta min yau, Allah ya faranta dukkan rayuwarki.

Hauwa ta ji wani irin dadi ya mamaye ruhinta, ya daura hannunsa a kan nata hannun, ya matse su sosai cikin na juna, alkawari ne ya dauka tsakanin sa da Ubangijinsa; zai yi duk iya kokarinsa ya gyara idanun nan na Hauwa-Kulu, koda remnant cikin yarda da amincewar Ubangijii wato koda ba duka aka samu dawowar su ba.

*** *** ****

Can daga nesa na hango Dr. Sarham Abbas da matarsa Hauwa-Kulu suna dawafi a Kaabah, hannunsa makale cikin nata. A zagayen karshe na kowanne dawafi addua daya suke yi, Allah ya sauki Kulu lafiya, ya bata ikon sharwa da kula da yayanta koda idanun ta basu bude har abada ba, aikinda zaayi mata kuma, wanda zaayi ne immediately bayan ta haihu, Allah yasa ayi shi cikin nasara.
Suka gabatar da cikakkiyar Umrah suka dawo gida Jeddah.
Mama tasa rigimar ya dawo mata da Hauwa ta haihu a gida, tunda haihuwar fari ce. Sarham yace Ina! Ya gama wannan daga haihuwar Waheedah. Saidai a kawo wata ta zauna masa da ita har tayi arbain din.

“Na kwana guda bai iya jure zaman gidan da babu HAUWA!.
A lokuta da yawa har wani kirarin baitocin waka Sarhamu ke rero mata, daga baitocin wakar mawaki (Ali Jita), a irin lokutan da soyayya ta cicciko a kirjinsa, wato tayi tantsan a zuciyarsa;
Zana gaida HAUWA-KULU.Sannu HAUWA-..HAUWA..
Baa raina suna da lokacinki HAUWA.
Baa finki haske a zuciyata HAUWA..

Babu wanda zai bata zamaninki a zuciyata HAUWA.
In zaa tara mata wa zata fi ki HAUWA.
Babu wanda zaya ruda zuciyata a kanki HAUWA.
Gimbiyar mata kike a zuciyata HAUWA.
Da zaa bani biro na baki maki HAUWA
To zaki haura lambar da zaa baki HAUWA.
In zaa tara mata wa zata fi ki HAUWA.
To addua nake... Allah ya taimakeki HAUWA.
A irin wadannan lokutan da yake rero mata wadannan baitocin, zaka samu Hauwa-Kulu manne dashi cikin shauki, tana sauraronsa tana murmushi from ear to ear, kanta ya kumbura.. irin na macen da tayi dacen saar mijin da ta san har zuciyarsa yana matukar son ta.
**** **** ****
Ranar da suka dawo Jiddah Madinah ta karbi girki. Ta dade bata ga Hauwa ba, duk da suna rayuwa a gida daya, to wata irin rayuwa suke yi ta kowa tasa ta fishsheshi, wato ba mai shiga shaanin kowa saidai sallama da gaisuwa irin wadda addinin musulunci ya shardanta a tsakanin musulmi. Madinah ta daga ido taga Hauwa da ciki tororo, alhalin bata gani. Wannan kadai ya kara ma Madinah tsoron Allah, ganin cewa mijin da matar ko a jikin su akan lalurarta, suna cikin farin ciki mara misaltuwa na ibadar da suka yo guzurinta suka dawo.
Silar kasancewarsu kullum cikin farin ciki shine wani boyayyen sirri ne na IKHLASI (sincerity); Sun dade da tsarkake zuciyarsu da karbar kaddarar rayuwar Hauwa da hannu bibbiyu, wato sun yarda cewa nakasar ba kasawa bace at all cost, kuma ba itace karshen komai na rayuwar bawa ba.
Sun yarda mara lafiyan da ya samu kulawar iyaye da ilmi mai amfani hakika zai iya hada kafadar rayuwa da kowane mai lafiya, in such a way that, an bashi spacial consideration na abinda yake bukata don gudanar da rayuwarsa ta hanya mai sauki. Ko yau Allah zai bata Da mai lalurar gani, dama kowacce irin lalura ta halittar jiki, Madinah sai taji bata fargaba kamar da, zata maida rayuwar kishiyarta mudubin dubawa ne ta tsaya ta kula da shi tun yana karamin sa, ta bashi kulawa ta musamman a cikin yayanta kamar yadda Innar Hauwa da Mama suka kula da Hauwa cikin yayansu basu bar rayuwarta ta wulakanta saboda nakasa ba, zata tsaya ta gina rayuwarsa yadda in ya girma bazai sha wahala sosai ba, zai rayu ne adequately and independently kamar kowa da taimakon na jikin sa.
Kenan matar Sarham ta zamo role-model, haka ga duk wani mai nakasar ido ya gane cewa makanta ba karshen rayuwa bace.
Ya shiga toilet ya bar Madinah nata sake-sake cikin mutuwar jiki da karin imani, Hauwa ta gaishe da Madina sannan ta wuce dakinta.
Dr. Sarham kenan mai Jidda mai Madinah bada kanka a sare kaje gida kace ya fadi.
Kullum kokarinsa shi ne ya samar da cordial relationship a tsakaninsu, amma hakan ya faskara. Don kowacce gwanace ta gwanaye a kishin SARHAM! Shikadai ransa, sun fi ganewa rayuwa ta gaisuwar musulunci da gasar kyautatawa maigida.
Lokacin da cikin hauwa ya shiga watan haihuwa kuma Sarham ya hana ta dawowa gida bata nuna bacin rai ba, duk dokin ta da ganin iyayenta kuwa, sai yayi kudurin shi kuma zai yi mata abinda zai faranta ranta matuka.
EDD dinta saura kwana uku, tana zaune akan kilishin dakin ta, tana cin mutumin nata gugguru, ta saka tirtstsen cikin ta a gabanta, ta ji kamar sallamar Inna a dakinta.
Haan, yau kuma kunnena ya koma yi min gizo da muryar Innata?
To tunda gizo ne bari kawai in koma ya cigaba da gizago. Irin mikewar da Hauwa tayi ta manta da tshohon ciki a jikinta saida Inna tayi maza ta kamata ta zaunar. Tana fadin Yi a hankali, likita ya gayamin yan biyu ne a tare dake.
Zaro idon da Hauwa tayi shi ya tabbatarwa Inna bata taba jin wannan zancen ko makamancinsa ba, haba! Biri yayi kama da mutum. Shagalin da take ji a cikin ta da nauyin sa da girmansa ya wuce na jariri daya. Pacesetter kuma bai taba gigin gayamata ba kada ya tsoratata amma komai biyu yake saye iri daya unisex. Tuni Hauwa ta soma hango kanta rungume yaya guda biyu alhalin babu ido. Wata qudururar sai Ubangiji Subhana. Tun tali-tali Hauwa na kwadayin haifar Da, ko don iyayenta da basu dasu da yawa. Da Ubangiji ya tashi yi mata kyautar Da sai ya bata da gaggawa kuma guda biyu a lokaci guda ciki lalurar makanta.
Akace sau tari wani farincikin yafi gaban ayi masa kuka ko ayi masa dariya. Don haka Hauwa a wannan daren kwana tayi sallah a zaunde, ga farin ciki zuwan Inna ga na albishir dinda tayi mata.
Tun daga ranar Inna ta soma aikin ta na kula da Hauwa dama ta zo da duk wani tanadinta na jego.
Kwanan Inna biyu da sauka nakuda ta fara, Pacesetter ya kwashe su sai asibitin Doctoor Sulayman Faqeeh. Ko awanni biyu baayi da karbar Hauwa a dakin Haihuwa ba a hannun Sarham ta sambalo yammatanta guda biyu, Hassana da Hussaina identical twins masu irin idanun Hauwa da Sarham yayi fata, yatsun da dogon hancin da sumar fulanin Shanonon kuwa duk nashi ne.
Madina har asibitin ta zo ta duba su, dama kuma taje har dakin Hauwa ta gaida Inna shekaranjiya, karonta na farko da shiga dakin Hauwa albarkacin mahaifiyarta. Tayi tayi hajjah Ramlah ta zo barka ta ki, ta dai yiwa Sarham din barka shikadai don su Hauwa basu isa ba, itada Usman sukaje MAX’ sukayowa jariran sayayya ta burgewa suka kawowa Hauwa. Dama wajen kyauta da mikakken hannun alkhairi Madinah ba daga nan ba. Circumstances ne ya canza Madinah, amma a hankali tana farfadowa tana dawowa Dr. Madinah Sorondinkinta da kowa ya sani.
Tun sanda suka fado duniya yayi musu khutbah da sunayen da suka dade da zabar musu wato Hassana (Maimunatu) da Hussaina (Safiyyatu). Mama da Abba dai basu amince ba suka saka shi agaba kan lallai ya maido su gida sai ya ce ai ga Inna ya dauko tazo daga Ghana. Sannan ne hankalin Mama ya kwanta.
Inna ta shiga Makkah tayo Umarah cikakkiya, ta je Madinah tayi ziyarar fiyayyen halitta SAW. Tana rokawa Hauwa da Sarham ‘long life and prosperity’ da zasu raini yayansu, su kuma tarbiyyantar dasu tare a duk inda ta tsaya a indararon Rahma na ubangiji adduarta kenan, ta kuma roki ubangiji idan Hauwa nada rabon gani a rayuwarta, Allah ya hada idonta dana Sarham a gidan duniya ba sai sunje aljannah kadai ba. satin Inna daya a cikin Makkah tadawo Jeddah suka soma shirin tahowa gida Najeriya.
Suna yin arbain suka tattaro har Sarham zuwa gida Kanon Dabo tareda Inna, dona kaima Abba da Mama yan biyu su gansu. Basu san Malam Bilyaminu yana can yana shirya musu surprised ba. Wato abun mamakin shine da Sarham ya kira Malam Isa yace masa ya shigo kasar Kano zai zo ya gaidashi sai Malam Isa yace ai ga BILYAMINU muna tare a soro na, tuni Malam Bilyainu ya dawo gidansa na BADALA tun kafin Innar Hauwa ta dawo. Ya kwaso komai da ya mallaka daga Ghana ya dawo dashi Kano, har ya cigaba da raba sanaarsa a Kofar Wambai ya zama babban dealer dake shigo da gwanjo ya rabasu da kansa ga kananun masu kwance dealer su sayar da dai-daya”.

Ya kara kawata gidansa tun kafin Inna ta dawo ya zuba musu komai na bukatar rayuwa yadda suke rayuwarsu a gidan su na Ghana.
Ina rijiyar farin ciki take Hauwa ta fada da jin wannan labari da Sarham ya bata. Hauwa tafi kowa murnar dawowar iyayenta cikin Badala ba don komai ba sai don cewa har gobe ruhin HAUWA-KULU yana nan cikin gidajen Badala. Don haka walima sosai Sarham ya shiryawa su Inna don kowa dake Kofar Naisa ya san sun dawo, inda aka gayyato dukkan makwabtansu na kusa dana nesa. Baka jin komai a Badalar Kofar Naisa ranar walimar nan sai labarin Malam Bilyaminu, batansa da abinda Zakari yayi masa, da labarin Innar Hauwa da Hauwa data makance Allah yayi mata ludufin rayuwa tayi a aure a Saudiyyah da makanta da komai ta haifi yan biyu son kowa. Ai an ance ma gawurtaccen likitan ido take aure acan din.
Wai wacce Hauwar kuke nufi? Ba dai yarinyar nan mai ciwon ido na apolo Hauwar Inna ta lokonsu Malam Isa ba? Ita fa, wadda Salele yake yiwa jagora”.
Ai kuwa wqadanda aka gayyata dama wadanda baa gayyata ba a kofar Naisa duk sun taho walima da gulmar gani da ido gidan Malam Bilyaminu dan kofar Naisa. Mama da wasu daga cikin yan uwanta dana Abba da ke Shanono da Mardiyya sun samu halarta. Mardiyya da Salele sune masu rabon abinci da abin sha natake away ga mahalarta taron. An ci an sha anyi hanian an yi hotuna da vedio na tarihi yan biyu kowa ya gansu ya daukesu ya musu addua.
Sunje wa Mama zasuyi sati a wurinta nan Mama ta koma gyaran haihuwa, wanan karon wane gyaran amarci don Maman Farida guda ta yiwa waya tace tayiwa Hauwa gyaran haihuwa ko nawa ne zata biya.
yan biyu kuwa kusan tsakiyarMama da Abba Prof.suke kwana suna lelensu da shafesu da addua. Ana I gobe zasu koma Jiddah Abbah ya sa Sarham a gaba yace sai ya gaya masa ina zancen karatun Hauwa ya kwana, da yanzu ta gama year two dinta a wanda ta jingine. Sarham yace ya samar mata makarantar da suke Inclusive Education wato jamiar DAAR EL-HIKMAH UNIVERSITY da sun koma zata fara don haka wanna karon Sarham da kansa ya bukaci tafiya tareda Mardhiyyah don ta taimakawa Hauwa da rainon yan biyu da sauransu.
Dakin Sumayyah aka baiwa Mardiyyah take hidimar ta da yan biyun ta, tana taimakawa Hauwa su in zata shayar dasu ta rike mata daya. In kaga yadda Hauwa ke hidimar yayanta wajen saka musu diaper da yi musu tsarkin kashi da goge tumbidi da bada madarar jarirai abun zai matukar baka mamaki, haka duk kuka idan dayansu tayi ta san me take bukata. Sarham in yana gida tareda shi ake komai duka da yanata shirye-shiryen makarantar Hauwa a lokacin amma kuma tunda ya kyalla yaga ta fara sallah a wani dare abubuwa suka canza. Baiwar Allah tayi kokarin nuna masa cewa yan biyunta basu yi kwari ba Sarham yace Allah yasa jiya aka haife su, nima tun haihuwarsu banida kwari, Allah shine mai rayawa kuma shine mai kashewa kin ji ko? In kuma wannan yarinyar ce ta kara yi miki huduba sai in bar ki da ita in karo ta uku. Ya fada yana saita alamuran yadda yake son su Hauwa na kwallah har da tsane hawaye tana fushin da Sarham bai san tana yi ba a lokacin sabida ya tafi da yawa, bai nutsu ba sai da ya kwashe gyaran Mama tsaf a daren yau. Da aikin tukudin Inna. Ya bar Mardhiyya da yan biyu tana ta fama, duk sun rikice mata da kuka sun ki kama madarar da take basu a feeder.
Shiyasa ake cewa Uwa tafi tausayi yayan ta, sai da ya koma Sarhamun sa sannan ya koma lallashi. Yace Maijidda abun alfaharinki ne ace mijin ki cannot do without you. Ni kadai nasan manejin danayi har kwanakinnan arbain, kiyi hakuri ni bana gudun kaddarar yaya karewa ma son su nake yi, so nake ki cika min gida dasu son samu duk shekara ki juye min yan biyu. Bari in gaya miki abinda bai kamata in gaya miki ba nafi samun duk wani contentment da duk nutsuwar aure idan ina tare da ke. Soyayya daban, sexual satisfaction shima daban. Madinah ina mata soyayya ke ina miki so da kauna wanda yafi gaban ina ganin ki in iya kauda kwadayina sai dai in bakida lafiya to wannan kuwa zanjure har ki samu lafiya. Ni likita ne na san yadda zan kula da lafiyar yaya na kin ji ko?
Ta gyada kai cikin sanyin jiki, yana daura mata tawul a jikin ta yace karbo su ki basu nono kukan su ya dame

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login