Showing 3001 words to 6000 words out of 37977 words
dagamin hankali haka? Daga zuwa na? Me nayi miki haka da zafi Maijiddah?"
Hauwa tace cikin mamakinsa, "kamar yaya da hadin baki na? Wallahi Yaya Doctor kirana aka yi, bansan me ake yi ba, ta tambayeni ne kawai nikuma na bata amsa, nima Yayana na jini nake kallonka, banga amfanin cigaba da aurenmu ba".
Ta kara da cewa "Yaya ka baro su Anti Madinah da Takwara ta Waheedah?"
Takaici ya hanashi amsa mata, ya tsura mata Ido kawai yana cewa a ransa ita ko dan irin kishin nan nasa irin na Madinah bata yi. Bai taba jin Madina ta ce ya take ba balle lafiyar ta. Daga bisani ya mike ya finciki hannunta zuwa dakinsa, suna shiga ya maida kofar ya rufe,
yace "Hauwa open your blank eyes, look into my eyes kice kin yarda mu rabu ki auri wani!".
Hauwa ta fiddo manyan gululun idanunta a kansa tace, "ni Hauwa Bilyaminu, na yarda in rabu da auren Yaya Doctor sabida hakan zai fi mana alkhairi".
Sarham ya sake mata hannu cikin mutuwar jiki yace "wallahi bazaku hadu keda Mamanki ku haukata ni ba". Muryarsa bakidaya ta dushe a sanda yake fadin hakan ya dafe kirjinsa dake zafi. Ya rasa me zai cewa Hauwa ya huce kawai sai ya girgiza kai yayi mata wani sakaran kallo kamar tana ganinsa y ace fitar min daga daki!.
Ta kuwa juya da lalube ta kama handle din kofar ta bude tayi ficewarta.
Bakin gadon sa ya koma ya zauna, kafin ya tashi ya kulle kansa ya rasa abunda yake masa dadi, haka ya rasa inda zai saka ransa. Ya rasa ta inda zai bullo musu. Abu na karshe da yasan bazai iya ba koda za'a dora masa wuka a makoshi shine sakin Hauwa.
Ya samu kansa da daukar wayarsa yana kiran layin Hauwa karo na farko tun bayan tafiyar sa, shi kansa saida yaji kunyar kansa da kansa da yaga number dinta da sunanta na yawo akan screen din wayarsa.
Mardiyya ta amsa wayar sannan ta miko mata kenan Mama ta shigo dakin, HAUWA na yin sallama batareda ta san wanda yayi kiranta ba. Da sauri Mama ta fauce wayar ta kashe sannnan ta rufe Hauwa da fada.
"Yanzu don bakida hankali, kin rako mata, yau sai ya kiraki a waya ki dauka???
Wata goma sha biyu yayi ba kwana sha biyu ba tareda ya kira ki ba. Zuciyar ki kare ya cinye ne halan, ko kuwa mata kika rako duniya don kawai bakida Ido???"
Hauwa batasan sanda hawaye ya tsinke mata ba. Ta sa gefen mayafin ta ta rufe fuska tana kuka. Mama tace "to daga yau na kwace wayar, in da ita zai bi ya samu lagonki ta hanyar bata miki lokaci. Dole in san matsayinki cikin rayuwar sa ko kuma ya bani takardar sakin ki".
Bayan fitar ta daga dakin itama Mama Mai Shari'ah sai taji hawaye ya balle mata, kuma ba na komai bane na tausayin Hauwa ne. Ta san ba don nakasarta ba da yanzu wani zancen ake ba wannan ba. Itama har ga Allah bata so auren ya mutu, tana kwadayin samun tsatso dasu Inna da dawwama da rayuwa tareda Hauwa matsayin surukarta. Amma fifita bukatarta bai yuwuwa, hakan bazai hana ta kwatowa Hauwa 'yancin ta ba wanda addini da al'ada suka bata, don ta lura bata san ciwon kanta ba Sarham ya gama raina mata hankali.
Kasa barci yayi a daren, ya kasa zaune ya kasa tsaye a dakinsa, daga karshe ya canza kayan jikinsa zuwa na barci, ya rufo dakinsa zuwa dakin Mama. Ya sameta tana karkade gadonta zata kwanta tana hawaye bata ko sharewa ba tareda ta san shigowarsa ba.
Ba karamin tashin hankali Sarham ya kara shiga ba ganin Mama na kuka bata ko damuwa wani zai iya shigowa ya ganta. Ya zube gwiwoyinsa a kasa gabanta ya kasa cewa komai.
Mama tayi karfin hali tace "Yaya dai? Takardar ka kawomin ince ko?"
"Kiyi hakuri! Kiyi hakuri! kiyi hakuri Mama. Na tuba na bi Allah na biki".
"Ai ba maganar inyi hakuri bane Sarham, amma in tambayeka. Shin Hauwa gunki ce ko dutse ko kuwa sassakata akayi? Bata da feelings kamar na kowacce mace?"
Ya girgiza kai da sauri cikin jin kunya ya kara dukar da kai kasa. "To kaje kayi tunani kamar yadda nace daga yau zuwa gobe da safe, in bata da gurbin soyayya ko yaya a zuciyarka ka sahale mata qaddararren aurennan, ka koma inda ka fito".
Haka ya taso ya fito daga dakin Mama cikin gigita, baya ko ganin gabansa sosai.
Surayyah na gidan Haj. Kulu, an saka ta a lalle, duk da tarewarta sai sati mai zuwa haka bikin ma, amma suna can suna lalle ita da kawayenta yan kwalisa.
Sarham ya zarce dakin Hauwa kai tsaye, ya tsaya a gaban gadon Hauwa bayan fitowarsa dakin Mama, ya sameta tana tufke gashin kanta yadda za ta ji dadin barci, kasancewar ta kure radio cikin wata wakar yaran Larabawan Sudan ba ta ji shigowarsa ba. Sai da ta ji ya kashe radion, Mardiyyah na gaishe shi, yana amsawa a dake da yake yarinya ce mai hankali sai ta fita ta bar musu dakin.
Ba ta san me ya sa ko ta yi fushi da Sarham a can kasan ranta tarin alkhairorinsa ta ke tunowa ba. Su shafe duk wasu kurakuransa da ke idanunta, musamman in ta tuna shi ne fa ya sake maido su cikin Badala, bayan an so har abada kada su dawo, shine Sarham din da ya gine gidansu na tarihi da Baba Zakari yasa zalunci ya rushe shi, shine Sarham din da ya sanya murmushi da farin ciki a fuskar Inna, a lokacin da bata da mataimaki a duniya sai Allah.
Shine mutumin da ya kaita special school ta koyi karatun da yau ya taimaka mata wajen zama MUTUM! Shineshine. Shine komai na cigaban rayuwarta. Don haka ko baya sonta bai zama hujja a gareta ta ram aba, ko ta ki yi masa ladabi ko ta yi fito na fito dashi.
Wannan tunanin kadai ya sa ta tattaro dukkan hankalinta da nutsuwarta ta bashi. Ta gaishe shi da murya mai sanyi, a lokacin da ya zauna a daidai kafafunta. Sambala-sambalan kafafun Hauwa ya tsura ma ido, tana sanye da irin wandon nan na mata na iya kwauri (three quarter) da farar T. Shirt mai hoton zanen katuwar jar zuciya data kama kirjinta sosai.
Hannunsa ya kai bisa kan tafin kafarta ba tare da ya san lokacin da ya yi hakan ba, taushin fatar a ido shiyasa shit aba kafar don jin irin laushinta a zahiri, ya ce, "Maijiddah".
Hauwa ta ce, "Na'am, Yaya Sarham, yaya ka baro takwara ta?"
Ya dan ji sanyi, don ya zaci itama ta dau zafi dashi kamar Mama, da gaske ta dauka da farko, abu daya ta tuna yayi cooling temper dinta. Wato ranar da ya dawo da ita inda ruhinta yake, wato ya gine musu gidan su na BADALA da kudin ginin nashi gidan, hakan ne yasa har gobe bai kammala nashi ginin na unguwar Rijiyar Zaki ba, amma dai yana yi kadan-kadan yanzu. Ya nisa a cikin samun relief. "Waheedah tana lafiya, ta rage kukan dare yanzu, amma da kullum kukanta ke hana mu runtsawa, kodayake nima na jima bana tare da ita, amma ranar da na dawo naga ta daina kukan dare".
Ta ce, "ai daman haka yara suke, sai lokacin dainawarsu ya yi za su daina".
"Ki ce haka Inna ta yi ta fama da ke.
Ta yi wani murmushi ta ce. "Fiye da haka ma. Ni ai Inna ta ce Kukana ina jaririya kamar na jiniyar mota yake, har makwabta ake jiyo shi, a shigo ana tayata rarrashina".
Hauwa sai ji tayi Mama na kwala mata kira. Sarham ya hana mata tashi ta hanyar sarqe yatsun hannunsa cikin nata, sannan ya ja mata yatsun suka bada kara kas-kas! Hauwa ta rasa inda za ta saka kanta don kunya, shi kuwa tafin kafar da yatsun nata ne suka ba shi sha’awa. Sanda hannunsa ya kai ga sauka a kansu bai sani ba, ya dai samu kansa zaune a kan gadon Sumayyah gabadaya, wanda yanzu ya koma na Hauwa yana ja mata yatsun kafa cikin wani iri salo da wani irin feeling dake shigarsa. Gabadaya Hauwa ta susuce ta kidime ta kuma kasa amsa kiran Mama sannan ta kasa janye yatsunta daga alkintasun da Sarham yake yi domin wani abu ne da bata taba ji a kirjinta ba. Sarham ya samu yadda yake so cikin taushin murya da lallashi yace.
"Maijidda kin amince za ki bi ni Jeddah? Ranar dana tashi komawa?"
Hauwa ta zaro manyan idanunta waje, ta ce "Karatuna fa Yaya Dacta? Kuma ka manta na amsawa Mama cewa na yarda a raba aurenmu?"
Sarham ya samu kansa da kara matsawa jikin Hauwa, ya sunkuya daidai kunnenta yana mata magana kamar cikin rada, kamar ba ya son wani ya ji, kamar akwai wani a dakin bayan shi da ita.
"Mamanki kawai tana so ta ce ne in disguise kin girma haka, kina bukatar mijinki a kusa da ke. Kin daina yi min zaman jiran daki. But she doesnt really mean it. I mean the divorce.
Don haka ki shirya gobe da sassafe za mu je immigration’ a yi miki fasfo, mu tafi mu bar mata gidanta. Sai ki shirya kawo wa Mama jikoki sharp-sharp daga Jeddah ta kara yarda na cika duty na, ke kuma kin amsa kira na da so da kauna".
Wata irin kunyar Sarham da bata taba ji ba ta zo ta lullube ta, irin wadda ba ta taba ji a rayuwarta dashi ba. Kamar yau ne farko da wani namiji ya ce za ta haifi 'ya'ya tare da shi. In bata manta ba, Yaya Jamilu ma ya taba cewa har rainon 'ya'ya shi zai taya ta.
Ta yi maza ta janye kunnenta daga radar da yake yi mata, domin wata irin kasala take saukar mata, garin kokarin janyewar kuma goshinta ya bugi nashi, ya ce,
"Ouch! Maijiddah kina buge ni da katon goshinki".
Ta yi maza ta rufe fuska da tafukanta tana cewa, "Ka yi hakuri, ai ka san bana gani".
"Da wani ne ya fada kuma da yanzu cibi ya zama kari, da yanzu kin ce ya miki gorin ido, ni matata Hauwa na gani, tunda hankali ke gani, ido gululu ne". Aka ce tsakanin mace da mijinta sai Allah sai ga Hauwa na dariya.
Ta ce, "Kayya, wannan idon gululun gaske ne, ko dan yatsa na bana iya gani".
Sarham ya yi maza ya ce, "Na yi alkawarin sai inda karfina ya kare da inda ilmi da bincike suka kare wannan karon wajen ganin idonki ya dawo daidai. Na gama gano matsalar idonki yanzu. Kada ki fidda rai da rahmar Ubangiji Maijiddah, shi da kansa ya ce,
"Lah taqnadou min rahmatullah”.
Sabida ke har kwas na tafi Egypt na tsayin watanni uku ba haka kawai naki zuwa ba Meji. Scientifically and medically kuma, based on contemporary research, type of cataract dinki is 100% curable idan aka dace. Glaucoma shi ne idan ya tsananta yake zama ‘irreversable’. Amma kowacce lalura watarana mai wucewa ce idan Ubangiji yasaka hannu, kin ji ko Maijiddah?"
Sai ga Mama ta shigo a fusace Sarham yayi maza ya saki hannun Hauwa. Cikin takaicin su su duka tace.
"Hauwa'u baki ji Ina kiranki bane?" Hauwa jiki na rawa ta mike daga jikin Sarham tana cewa "dama.... dama... Gani nan Mama, wallahi yanzu za". Mama bata tsaya jin kame-kamenta ba ta kama hannunta suka fice daga dakin suka barshi a wurin.
Dr. Sarham yayi ajiyar zuciya ya fidda wayarsa ya hau kiran Inna, bugu daya Inna ta daga da sallama, cikin tsokanar da suka saba kamar ba surukai ba Inna tace "Likitan larabawa, likitan idanun duk duniya!".
Ya yi 'yar dariya mai ban tausayi cikin karfin hali ya gaida Inna, nadama tana kara mutstsike shi, inda kunya ai baya kai karar Mama gun Inna ba wanda dalilin kiran da yayi mata kenan, don haka sai buge da gaya mata ya zo Kano daukan Hauwa su wuce Saudiyyah tare, bisa umarnin Mama da Abba, tunda sun yi hutun jamia.
In ya so in hutun makaranta ya kare sai ta dawo Kano, ta tare a gidan sa na Rijiyar Zaki saboda zuwa makaranta”.
Inna hawayen farin ciki ya zubo a saman kuncinta. Yau Hauwanta ce da aure a kasa mai tsarki, kasa mafi girman daraja a dukkan kasashen duniya.
Ta yi ta zubo wa Sarham addu'a da albarka irin yadda ta saba, wadda ta kara sa Sarham cikin jin guilt mai yawa na abinda ya aikata wa Hauwa, kafin suyi sallama.
A take ya fito daga dakin Hauwa ya nufi nasa dakin cikin damuwa, yana kissima Allah ya kaimu wayewar gari ya samu damar fita da Hauwa yin fasfo dinta, daga nan suje gidan sa na rijiyar zaki, duk yadda zaiyi zaiyi ya wanke dattinsa daga zuciyar matarsa, kuma zai hadiye duk wani ‘silent punishment’ din Mama, in dai a karshe zata yarda ya tafi tare da Hauwa Jeddah, sai yayi duk yadda zai yi ya gyara kurakuransa duk da ya san baa bari a kwashe daidai.
A ganin sa bai makara ba, zai iya gyara komai, wuyarta dai su kebe shi da Hauwa a wurin da babu interference na iyaye babu gilmawar kowa, wato a inda babu Mama mai yiwa Hauwa kwatar yanci, zai samu wannan damar kadai idan ya fita da Hauwa gobe da safe. Amma bai san meyasa duk wani azanci da confidence da yake dashi na zai iya gyarawa din ba tareda kowa yaji ba, yake jin yana gudu yana barinsa. Don bai san matsayin Hauwa a gun Mama ya kai har tayi kuka kan rashin kyautawarsa gareta ba.
A daren yau dai da Mama ta yanke masa wannan hukuncin, jinsa yake kamar mai nakuda, musamman data zo har gabansa ta dauke Hauwa zuwa dakinta mai nufin bata amince da kebewarsu ba, ya yarda da gaske Mama take ba barazana take masa kamar yadda ya dauka ba, don haka duk ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya kasa kwanciya, ya rasa ta ina zai bi ya lallashi Mama. Shi kansa ya san abin da zai yi ya bata wa Mama rai har ta zubar da hawaye a kai, ba karamin abu bane. Ya fahimci Mama ta saka Hauwa a ranta fiye da yadda ta saka Madina a ranta ta kowane bangare, ta amshi Hauwa ne wholeheartedly sabanin Madina da dama tana kullace da abinda Babanta yayi musu, na rainin arziki, da auren da Madinah ta fara yi kafin shi ashe bata yafe ba, wannan abu kwarai ya ba shi mamaki don ya dauka tuni ta manta, ya kuma jinjina wa Mama don wani abu ne da a farko bai yi tsammani ba wato cewa zata so Hauwa ta karbeta.
**** ***** ****
SELF-EVALUATION
A
bu daya Sarham yake so ya tantance a ransa da kwakwalwarsa daga yau zuwa gobe kadai, wato he has to evaluate himself in 24 hours kafin cikar awannin da Maisharia ta bashi, he has to find-out; shin YANA SON HAUWA-KULU???
Wannan wata tambaya ce da Sarham bai san amsarta tuntuni ba, sai yau da yake cikin tsaka mai wuya, wato a sanda aka bashi zabi tsakanin cigaba da zama da Hauwa da kwace ta don ta koma ga wani wanda yafi shi sonta, wato ranar da ya samu kansa tsakanin samu da rashinta cikin rayuwarsa ne kadai ya gane Hauwa nada matukar muhimmanci a zuciyarsa da rayuwarsa kuma ya damu da ita fiyeda yadda zai iya bayyanawa. Sannan zamanta matsayin matarsa ta sunnan shi ya bashi kwanciyar hankalin da yake ciki a yanzu, wanda a baya ya rasa da ya nemeta a rayuwarsa da fadin garin Kano ya rasa.
So yake ya tursasa wa ransa ya yarda cewa, har gobe Madinah kadai yake yi wa so na soyayyah, to amma me? Sai ya gane cewa yau Mama ta bankado sirrin dake kwance dankam shekara da shekaru a kasan zuciyarsa game da Hauwa. Bayan duk wasu self-examination ya yarda YES! Hauwa-Kulu tana da wani gurbi bayan na kanwar jini a tare dashi ko ya ki Allah, ko ya ki Annabi (she has a special place in his heart), wanda acan baya yake (underestimating) dinsa da gangan, in ba haka ba me ya kai shi saka wa first daughter dinshi WAHEEDAH sunanta? Shin soyayyarsa ga Inna ce kadai ta yi attaching dinsa gare su irin haka b tareda soyayyar mace ba? Shin Inna ce ta saka shi aiko da kudi duk wata daga Jeddah (for their survival) ko kuwa tunanin karatun Hauwa-Kulu? Shin Inna ta taba yi masa