Showing 3001 words to 6000 words out of 32414 words

Chapter 2 - MIJIN TA CE BOOK 1

20 Aug 2024

4894

da yayi ya fita sai nima nayi maza na diro daga kan gadonmu na fito na shiga wurin Inna don ganin halin da take ciki.
Cikin rawar jiki da rawar murya saboda kukan da nake yi na ce mata “Sannu Gambo.” Bata amsa min ba, sai ta kalle ni cikin natsuwa ta ce min “Xauki Aliya da Sa’adatu ki xora su suyi fitsari ki wanke musu baki.”
Nayi maza na ce mata “To” naje nayi yanda tace xin, har na idar da Sallah na zo na gaisheta bata motsa ba daga yanayin da na barta, ban daxe da tsayawa a wurin ba sai kawai ga Hajiya Kubra ta shigo cikin zurmemen hijabinta.
Ga dukkan alamu daga idar da Sallahrta ta Asuba ta fito, ga alama kuma ita Innan ce tayi amfani da wayarta ta hannu ta kira ta.
“In ce ko dai lafiya Faxima?” sunan da take kiranta dashi kenan, ta ce “Eh, lafiya Umma.” Na durqusa na gaishe ta na juya na fita, musamman ma da yake ban ganta cikin yanayin fara’a da walwalar da na saba ganinta ba.
Don haka na koma xakinmu na zauna ina tunani, tunanin da zan iya.
Shekaruna na quruciya shekaru ne da ba zan iya furta komai ba game da Babana, don kuwa shekaru ne da nayi su cikin wani yanayi na fuskantar wasu al’amura da ko kaxan bai dace yarinya mai shekaruna ta ma san su ba, balle ta fuskance su.
Kan kace meye wannan? Tuni ‘yan uwan Inna sun cika mana gida, su Inna Aisha, Inna Balki, Inna Hajara, gasu nan dai birjik, wasu na kuka wasu na sakin maganganu a tsakar gida don neman a tanka ayi wacce za’ayi, a wannan lokacin ne na fahimci lalle abinda ya farun ba mai sauqi ba ne.
Tuni Mama ta bar tsakar gida ta koma falonta, ta kuma yi maza ta kame bakinta tayi shiru bata tankawa baqaqen maganganun da wasun su suke saki ba, don tasan karonta dasu.
Ana cikin haka na sake jin sallamar Baba Yahaya a tsakar gidanmu, Hajiya Kubra tana jin sallamar tashi ta fito cikin hijabinta, cikin natsuwa ta nemi wuri ta zauna a qasa cikin ladabi ta gaishe shi, kafin ta soma yi mishi magana cikin yanayin girmamawa, na cewa Alhaji ya gaya maka ina nemanka ne saboda in bi umarnin da ka bani na duk abin da ya faru a cikin gidan nan, kai ne farkon wanda zan gayawa ba shi Alhajin ba.
Ina bin umarnin naka ne kamar yanda nake bin na Baba da ya hana ni fitar da Faxima daga xakinta ba da izinin mijinta ba.
Baba Yahaya ya gyaxa kai nuna alamar gamsuwa da maganar tata, kafin daga baya ya tambaye ta wani abin ya sake faruwa ne? ta ce “Eh to, ni kam ai ban san komai ba, tunda baya kai qara kan laifukan da ake yi mishin, sai dai yayi hukunci na ganin dama saboda ganin komai yayi yana sharewa qalau.
In ban da haka me Faxima zata yi wa mutum yayi mata irin abinda ake yi mata a gidan nan.” nan da nan ta shiga share hawaye tana faxin a roqan mun shi kawai ya bani ita muje gida, inna yi jinyarta ta warke masan abin da muke ciki.”
Ya xan yi shiru kaxan kafin ya ce mata “Hajiya shi babba fa da haquri aka san shi, kin kuma sani sarai ita mace komai gatanta bata da wata darajar da ta wuce ace a xakin aurenta take zaune.”
Ta ce mishi, “Haka ne.” Ya ce, “To ina dalili, shi Alhaji Surajo komai qanqantar abinda ya faru a gidanshi tsakaninshi da yarinyar nan ba za ku bari maganar ta q are a tsakaninsu ba sai kun shiga? Sai kun yiwo gayya kun cika mishi gida?
In ita Gambo bata laifi ne? kuma don ‘yar gata ce a danginta da ke da Alhaji Maikuxi sai ace ba shi da iko a kanta? Tuni Hajiya Kubra ta soma kuka sosai tana fyace majina, ta ce “In tayi laifi Alhaji sai ayi mata duka har da targaxe? Kuma menene laifin nata, ta qi yiwa matarshi aiki? Mai aiki na kawo mata ne?
Yanzu mu da ku ka auro wasu matan a bayan mu haka muke yi musu? Inna Hajara ta leqo daga cikin xakin tana gaishe shi, sannu da zuwa Mallam, nan da nan ya xaga ido ya kalle ta ya ce, ai kuma duk kun zo ne kuna ciki? To duk ku fito, koma ciki ki gaya musu nace duk ku fito ku bar gidan nan.
In na bar nan kuma zan je in gaya wa Mallam har da ku a rura wutar fitinar dake aukuwa a gidan nan.”
Nan da nan suka yi ta fitowa suna tafiya saboda sanin matsayin Baba Yahaya wurin Mallam mai babban allo, matsayin da tuni ya maida shi ya zama xan gida, kuma mu’amalla da shi a matsayin xan uwa.
Yana tsaye a wurin har suka gama wucewa bai kuma fasa faxan da yake yi musu ba, sai da yaga sun qare ne ya kalli Hajiya Kubra dake zaune a qasa cikin ladabi tana sauraronshi ya ce mata.
“Kiyi haquri Hajiya, kiyi haquri na kuma roqe ki kar kije ki ce zaki gazawa Alhaji Maikuxi munin al’amarin tunda shima bai san haqurin ba.”
Gambo dake da ‘ya’ya mata huxu a jere, Kubra in aka barku ke da mijinki kuka yi yanda kuke so xin kun yi mata adalci? Ai ke uwa ce ba sia na tsaya yi miki dogon bayani ba, kin san komai zai yiwu ne ku kaita inda zaku mantar da ita waxannan ‘ya’yan nata?
Kin fi kowa sanin ba zai yiwu ba, to kiyi haquri kawai ki kuma rinqa kwavarta duk da dia kin qi uarda da cewar ‘yarki mai laifi ce, amma hakan ba zai sa kuma kullum ki rinqa goyon bayanta ba, don gyara kayanka Kubra ba fa ya zama sauke mu raba, haka nan kana qin naka ne don duniya taso maka shi.
Ta ce, “To Alhaji na gode, Allah ya saka da alheri.” Ya ce, “Amin.” Ya wuce ya fita ita kuma ta koma xakin Innarta, ta gyara abubuwan da suke buqatar gyara, duk da watsewar da dangin Inna suka yi aka bar Hajiya Kubra ita kaxai, Mama ta kama kanta sosai tana can wurinta ta kame daga yawan zirga-zirga balle aje ga sakin maganganun da ta maida yin hakan xabi’arta ta kullum.
Ana cikin haka ne Baba Yahaya ya sake dawowa tare da wata Dattijuwa Sidiya, kowa ya santa ita da mijinta gyaran targaxe da karaya suke yi ita ya kawo ta shiga ta gyarawa Inna targaxen da Babana yayi mata ta fito ya maida ita.
Rannan a gidanmu Hajiya Kubra ta wuni sai da tayi sallar Magariba aka zo aka xauke ta, Inna ma ta wuni a kwance ga dukkan alamu kuma lafiyarta ta rasa shi yasa ta wuni a kwance nima na wuni rannan ina hidimar xakinmu bata yi ta addabata da yawan aike ba balle aje ga tabkata da dukan da aka saba yi min kullum.
Washegari da sassafe sai ga Baba Yahaya da Alhaji Mai kuxi, ga dukkan alamu kuma daga Masallaci suke tunda su xin makwabtan juna ne, unguwarsu xaya can suke wajen Makama New Axtention. Baba Yahaya ne ya fara shigowa gidan, Babana ya fito daga falon Mama wanda dama nan ne wurin zamanshi ko da kuwa shi xin a xakinta yake.
“Sannu da zuwa Alhaji.” Baba Yahaya ya amsa kafin ya ce mishi “Ni da Alhaji Mai kuxi ne.” Nan da nan yanayin Baba ya sauya, ya ce “To bari in buxe muku falona mana.” Ya ce mishi “A’a, izini ya ce in zo in roqar mishi a wurinka yana so zai shigo ya duba Gambo.”
“To, to ai shi kenan.” Baba ya sake faxi cikin wani yanayi ya kuma wuce ya shiga wurinshi.
Har tsakar gidanmu Alhaji Mai kuxi ya shigo, Innata ta fito ta durqusa tana gaishe shi, bai wani tsaya wajen amsa gaisuwar tata ba, zuba mata ido ya yi yana kallonta.
“Sannu Faxima, sannu kin ji. Sannu da qoqari.”
Shi kuwa Baba Yahaya yana gefe yana kallon shi, shiga cikin Gambo ta miqe ta koma ciki suka kama hanyar fita waje, yana cewa.
“Baba Yahaya ba ka yi min adalci ba Alhaji, ka zalunce ni ka sani na kawo yarinyar nan in da ba za a yi mata adalci ba, bayan kasan komai amma duk da haka kaje ka haxa ni da Mahaifina.
To nima na ce ban yafe ba, ku haxu ku rufe ni da duka tunda itama abinda ta faxa kenan aka yi mata wannan zaluncin.”
Baba Yahaya ya ce, “To naji muje.” Ya tasa shi a gaba suka fita.
Rashin jituwa mai tsanani ne ya nemi shiga tsakanin Alhaji Mai kuxi da Alhaji Yahaya waxanda ban da ‘yan uwantakan da Mallam Mai babban allo ya haxa a tsakaninsu su xin makwabtan juna ne a unguwa xaya sannan a kasuwama shagunansu kusan wuri xaya suke.
Alhaji Mai kuxi yaja ya tsaya kan bai duba kusanci da zumuncin da ke tsakaninsu ba, yasa Mahaifinshi ya tilasta shi bada qanwarshi ‘yar qaramar yarinya a inda yasan ba za ayi mata adalci ba, saboda ya fifita son amininshi a kanshi, sai da mai babban allo ya tsawatar.
Tun daga wannan lokaci Mama ta shiga sakin maganganu masu zafi a tsakar gida saboda ta gane Babana ya xauki matakin daina yin duka ko da ta kai mishi qarar Innata sai dai kawai ya yi magana da fatar baki, abinda ita kuma ba haka taso ba, tunda ita qa’idar ta ne kullum sai taje ta ce mishi ga abin da aka yi.
Ko kaxan Mama ba ta so Babana ya xauki irin matakin da Babana ya xauka ba na kamewa daga yin duka don kuwa kusan kullum sai na jita tana yada magana a tsakar gida.
“Ni fa kar mutum yaga wasu guntayen iyayenshi marasa girma da sanin darajar Surukuta sun zo sun yi wa Alhaji burga ya tsorata yayi zaton ko ni ma a tsoracen nake.”
Ta tave baki ta ce, “Ko kaxan ni xin nan a gidana rashin jini ne rashin tsagawa, baka shiga sabgata ba ba ruwana da kai, amma kana doso ni da rashin mutuncinka, to kama ka zan yi in naxa maka dukan tsiya ba mai Kuxi ba ko mai dala ne ina daidai dashi duk da a gaban Innata take furta irin waxannan kalaman, ta kuma san da ita take yi bata xaga ido ta kalle ta ba, balle ta tanka mata.
Amma duk da haka wai bata tsira rannan akan ruwan bunu ruwan tin da babu komai cikin shi sai ganyen tea. Mama ta ce, “Wai Innata ta kwashe wa ‘ya’yanta ita ta basu xan qanqani.
Nan da nan kuwa ta shiga zage-zage, Babana ya leqo yana tambayarta “Menene ya faru ne?” Ta galla mishi uwar harara ta ce, “Ai don ka ji ina cewa zan bata kashi ne yasa ka zaburowa ka fito kana tambayata?
To ai ko kana tsaye zan yi hakan, don na gaji da irin cin kashin da ake yi min a cikin gidannan, zan yi in gani ko nima za’ayi min irin wuju-wujun da aka yi ta yi da kai.” Ta zubawa Inna ido tana mata kallo irin na wulaqanci.
“Ke nan ga ‘yar gwal ko? Ki zo gidan mutane kina musu rashin kunya da rashin mutunci saboda iyayenki, ba su yi miki tarbiya ba in an tava shi su ce za suyi wa mutane iskanci, to ni ba Alhaji ba ce babu ruwana da iya shegensu maganinki zan yi ba Mai Kuxi ba, aje a turo min mai babban allo in ya tashi zuwa kuma kar ya zo da allon katako ya zo dana qarfe.
Inna ta kasa haquri ta ce, “A’a me iyayena suka yi miki? In dai akan wannan ruwan tin ne gashi nan na juye miki.”
Garin juye ruwan ti wani ya xallu a qafar Mama, nan da nan ta qara fusata wai Inna ta qona ta, ta shiga xura wa iyayenta ashar. Inna ta juya ta nufi xakinta tana faxin “kiyi ta zage-zagenki ni kam ai kowa ya ji abinda kike faxa yasan bada iyayena mike yi ba, tunda kowa yasan su yasan su xin ba mutanen banza ba ne.”
Abinda kawai ta faxi kenan Mama ta bita ta jawo ta tana tambayarta su waye ne na banzan? Bata kai ga bata amsa ba ta rufe ta da duk ta turmushe ta a qasa ta hau kanta ta danne tana ta faman naushinta da kyar Babana ya samu ya xagata a kanta, ya kaita xakinta tana ta faman huci tana zage-zage.
“Haka kawai kaje ka xauko masifa ka kawo min cikin gida, ba dole in tsaya in yi maganinta ba, tunda kai ka kasa?” yana fi towa daga xakin Mama ya kai min maka, kafin ya daka min tsawar da ta katse min komai.
“Me aka yi da ki ke qur ma wannan ihun kina nema sai kin tara min Jama’ar unguwa a gidana?”
Shiru nayi na bi Babana da kallo har ya shiga wurin shi, an daki Innata an farfasa mata baki da hanci alhalin ba wani laifin ku zo ku gani tayi ba, amma ina kuka ya make ni ya ce, wai ba ayi komai ba.
A hankali na faki idon mutane na fita na bar gidan namu na taka da qafata na tafi har Makama extention naje na gaya wa Hajiya Kubra abinda ya faru duka, ta ce “To babu laifi zauna ki karya kiyi wanka ki sauya kayan jikinki, sai ki koma gidanku.” Na ce mata “To.”
Ina dawowa gida na samu Inna cikin wani yanayi, ko dukan da Babana ya yi mata wanda gaba xaya dangin Inna suka yi ta kai-kawo akai suna faxin maganganu bata ji jiki irin wannan ba, iyaka dai a wancan ta samu targaxe a hannu shima kuwa ta kare dukan da ya kawo mata ne da hannunta.
Cikin zuciyata na ce, “Wato dai da banbanci tsakanin dukan miji da kuma na kishiya?”
Ban san yanda aka yi ba, Baba Yahaya ya ji abin da ya farun da yamma sai gashi yazo gidan, don jin abinda ya faru. A gaban Babana Mama tayi wa Baba Yahaya wanki irin na babban bargo, ko dama can kuma nasan ta daxe tana da cikinshi don ko maganarshi zata yi bata ambaton sunanshi sai dai ta ce mishi munafuki.
Haka bata zuwa hidimar gidanshi wai shi da matanshi sun ci amanarta, Baba Yahaya yana ganin haka ya juya ya fita ya bar gidan ya barta tana ta zage-zagenta, tana haxawa har da abokin nashi wato Baban namu, har tana ce mishi wai tunda shi ya kasa to ita zata yi mishi maganinsu.
Tana nan tana jiran zuwan Alhaji Mai kuxi, zata nuna mishi bai da wayo, zata gaya mishi magana irin wacce bai tava ji ba, zai gane shi xin qyalle shi kawai ake yi da wata tevar shi kamar qullin kayan wanki.”
Har Babana ya gaji yasa kai ya fita ya bar gidan Mama bata gaji tayi shiru ba, sai tambaya take yi a kanki na fara ganin kishiya? Guda nawa aka yi min? ke ce ta shida, ke ki ka fi kowa? Shafaffiya da mai, ki zo min gidana ki ce za ki gallabe ni, ke xin banza!
Ai tunda abin ya zama haka, to za mu sa qafar wando xaya tunda kuma na gano abin naku tsiya ne da kuma rainin hankali, to zan tasa ki a gaba zan ga yanda za’ayi kiyi zaman gidan nan, sai dai ko in shi mai kuxin ne zai zo ya taya ki zaman ko?”
Ana cikin haka sai ga Hajiya Kubra ta shiga cikin gidan tana faxin, “Mama ja’ira Mama mara mutunci, Mama mai rashin kunyar qarya, to don kin daki Faxima sia me? Sau nawa ki ka haife ta? Don kuma yi kanki don xan girman da take baki kina rainawa ya qara zubewa, hakan kuma ba zai hanata sake haxa shimfixa da mijinki ba, sai dai ma ta qara. Tsohuwar banza kawai mara mutunci.”
A fusace Mama ta fito tana tambayarta “Ke ce ki ka zo baki turo Mai kuxi ba?” Hajiya Kubra ta ce, “Ai sai kan abinda yafi qarfina ne ki ke ganinshi yaje ke kuwa ni ce zan yi maganinki sakaryar banza wacce uwargidancinta bai amfani mijinta da komai ba sai qarin fitina. Sakaryar tsohuwar da ta rasa masu zaunar da ita su gaya mata gaskiya.”
Ban san yanda aka yi ba sai kawai naga Hajiya Kubra tayi jifa da gyalen da take yafe dashi kan kace meye wannan tuni danbe mai tsanani ya kaure a tsakaninta da Mama, sai ji kake yi xixim-xixim-xixixim!!
Don kuwa su dukkan su ma’abota qiba ne da kuma jin qarfi, sai dai kan ka ce meye wannan Hajiya Kubra ta kai Mama qasa tim! Abinda ya firgita gidan gaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login