Showing 9001 words to 12000 words out of 32414 words

Chapter 4 - MIJIN TA CE BOOK 1

20 Aug 2024

4897

To balle ita Innata da ko xaya namijin bata dashi, sai mata guda huxu. To amma su mazan waxanda guda biyu sun ci ace sunyi nisa, Baba da kuma Ibrahim don sune a gaban su Anti Suwaiba da Anti Kaltume waxanda a lokacin aurensu Babana yayi komai don ya burge Mama, ya basu mazan da suke so su da uwarsu, alhalin shi ba sune zavin shi ba, ya kuma kashe maqudan kuxi wajen hidimar auren nasu a kayan xaki da walima gami da ciyar da mutane.
Don shi dai ma mijin Anti Suwaiba ko qwaqqwarar sana’a bai da ita, amma Mama taja ta tsaya sai shi tunda shi ne saurayi ai shima Baban namu lokacin da ya aure ta ba komai ke gare shi ba, in ban da ‘yan jamfofinshi guda biyu.
To amma duk da haka da taro ya watse sai Mama ta buxi baki ta ce, wai wannan hidimar da Baba yayi bata yi rabin wacce yayi ba a hidimar auren Innata da yayi, har rayuka suka kai ga vaci kan hakan.
Sannan a hakan a irin soyayyar da Mama ke yi wa ‘ya’yanta na ace su wasu ne a gan su ace sun burge a kalle su ace babu wasu sai su, Baba da Yaya Ibrahim sun qi karatu tana kallon su babu boko babu Arabi, sai gata a gabanta Ado yazo daga qauye yayi karatu har yau xin kuma ba barin karatun ya yi ba.
Yana karatun yana kuma kasuwa ya tsunduma kan shi cikin al’amuran Babana tsundum, mutanen da suka san yanda lamurran gidan namu yake tafiya, faxi suke yi, “Ko da qoqarin Mama wajen samun shigar qanin nata cikin lamurran Babana, to jaruntakarshi kuma ita ce kan gaba wajen saman mishi fada mai yawa.”
Duk wata aika da Babana zai yi to Ado ne, shi ne yake wanke mishi kayanshi, ya goge mishi su, daga zuwan Ado gidanmu ne Babana ya daina kaiwa masu wanki da guga kayanshi.
Shi ke wanke mishi mota, ya share qofar gida ya sare bishiyoyi in ganyensu ya yi yawa, waxannan ayyuka kuma ya kan yi su ya gama kafin fitowar rana, ba kuma sa shi ake yi ba, shi yake sa kanshi, gashi ya iya girmama Babana, dama duk wani mutumin da ya yi nufin girmamawa.
Daga haka ne Ado ya samu shiga wajen Babana, da ma Dattawan unguwarmu duka. Sannu a hankali-sannu a hankali sai ga Ado a shagunan Babana sai kuma Baban ya gwammace zaman adon a kan nasu Yaya Ibrahim da ma sauran yaran shagon.
Saboda jaruntakar shi ta wajen aiki da tsayuwa akan gaskiya, daga baya ne da ya lura ya gane ya riga ya samu shiga mai yawa, ya shiga kwashe mishi dukiya suna kashe-mu-raba shi da Mama.
Amma su su Yaya Ibrahim ta qyale su suna yawo kan Baburan da ta saya musu da kuxinta da Babana ya yi magana kan hakan da tayi sai ta ce “Kai Alhaji kenan, kai baka saiwa yara ba bayan ga sa’o’insu nan da ma waxanda ba su kai su ba na abokanka wa su har motoci iyayensu suke sai musu.”
Ya ce, “Da suka tsaya suna yiwa kansu abin arziki ba? Suna bin umarnin da iyayensu suke ba su in da suma sun tsaya kan karatunsu kamar yanda waxancan xin suka tsaya me zai hana in saya musu?
Ai taimakon kai ne da kullum ka baiwa yaro kuxin motar zuwa Makaranta da na kasuwa, ai gara ka dunqule ka samar mishi abin hawa, to su waxannan basu tasa komai a gabansu ba sai la…”
Tayi maza ta katse shi ta hana shi qarasawa, ta hanyar faxin “A’a, kar kayi musu baki gara kai, yauwa shi karatun boko ai ba shine kaxai hanyar samun arzikin duniya ba, da shi kaxai ne kai ma da baka samu ko kwabo ba.”
Ta juyar da fuskarta can gefe ta daina kallon inda yake.
Tun Babana yana yi wa su Yaya Ibrahim da Baba faxa kan abubuwan da suke yi na qin karatu da yawan abokai har ya gaji ya watsar, wataqila ganewa yayi hakanne zai fi komai saman mishi zaman lafiya.
Jarumtaka guda xaya da yayi dai ita ce, ta hana su zuwa kasuwa su zauna mishi a shaguna, ita kuwa ko a jikinta sai su wanke goma su tsoma biyar, qa’ida ne kuma wanda ya kai musu abincin ya koma ya kwaso kwanukan in sun gama ci a kuma yi musu shara.
Abokansu kuwa sun fi kowa mutunci a wurin Mama, don a bayyane yake bata shiri da mafi yawancin abokan Baba na tun ba Baba Yahaya ba ta ce, babban munafuki kenan.
Ana cikin haka suka tasa Mama a gaba wai su a bar su su koma xaya gidan na Babana wanda Ado ke ciki, tunda Baba baya so abokansu suna shigowa gida.
Da farko Babana bai yarda ba, amma Mama ta dage to menene ba gashi manne jikin wannan ba ga kuma Ado a ciki? A dole ya haqura suka koma, nima na xan ji daxi duk da dai ana tura ni kai musu abinci, xebo kwanuka da yi musu shara.
A fili yake gaba xaya ‘ya’yan Mama daga matan har mazan da ma ita Maman kanta basa sona ba kuma sa iya voyewa, babu halin in xan zauna a cikinsu sai ka ji suna cewa.
“Haka kawai muna zaman zamanmu Babanmu yaje ya auro mana wannan matar tazo ta haifan mana wannan shegiyar.”
Da zan xago ido in kalle su don sanin ni da uwata suke zagi, sai ka ji sun daka min tsawa, “Daina kallona in ba haka ba in buga miki ranqwashi.”
Wata ranar ko nayi maza na kawar da kan nawa na daina kallon nasu sai sun bi ni da ranqwashin.
Ko kaxan ba ni da farin jini a gidanmu, nafi kowa baqin jini a ‘ya’yan xakin Innata, na fi su kuma wahala don ni kam kullum a cikin fitina nake, a cikin azaba r duka ba wurin Mama da ‘ya’yanta kawai ba, har wurin Baban nawa.
Gaba xaya cewa suke yi wai ni muguwa ce kuma munafuka halina iri xaya ne da na Innata, in yi ta kallon Inn ata ina tunanin yanda halin nata yake, tunda ni ban tava sanin muguntarta ba balle kuma munafurcin.
Sai dai kuma abin mamaki, duk da wannan matsi da tsana da nake fuskanta a gidan mu wurin dangin Innata, farin jini ne da ni. Tun ma ba wurin Alhaji Mai kuxi da Hajiya Kubra ba.
Tun kuma ba wurin Mallam Mai babban allo da uwar gidanshi Hajiya ‘Yardubu ba, ita kam Hajiya Turai yanda ba kula Innata take yi ba haka nima ba wani shiga harkata take yi ba.
A mafi yawanci ma nakan shiga gidan mai babban allo ban leqa xakinta ba in gama in tafi, sai da shi mai babban allon ya koya min bin ta xakin ta in gaishe ta.
Su dangin Inna kullum sukan danganta tsanar da ake nuna min a gidan namu da yawan son Innata da kuma tausayinta da aka san ina yi.
Donni kam kullum cikin tausayin Innata nake, ban sani ba ko shi ne dalilin da su kuma suka maida ni ‘yar lelensu, ba komai ba ne a wurinsu suyi min sayaiya ni kaxai su bar su Atika da Aliya da Sa’adatu.
Kwata-kwata shekaru goma sha uku ne da auren Innata cikin waxannan shekaru kuwa ‘ya’ya shida cif ta haifa, gaba xayanmu kuma mata ne mu huxu muna nan a raye, biyu kuwa babu su.
Ni da Atika da Aliya dama a jere muke, sai Zainab da Kubra su babu su, sannan Sa’adatu.
Yawan haihuwar Inna ba qaramin damun Mama yake yi ba, duk da cewar da take yi wai mai haihuwar ‘ya’ya mata zalla bai san daxin haihuwa ba tunda shi wai mai son haihuwar xa namiji ne, to amma kuma duk da matan da take haifan ba ta iya zuba ido ba sai da ta xauki matakin shiga tsakanin Inna da mijin nasu.
A wannan lokacin ne Mama ta kawo wata qa’ida ta wai in kana goyo to ba za ka yi girkin gida ba, ba kuma zaka je gun miji ba, ko shi xin yazo wurin ka.
Kowa yasan don Mama taga haihuwa ta tsaya mata ne yasa ta fito da wannan qa’idar, to amma tunda wanda aka yi domin shi ya yarda itama Innata bata tanka ba, don haka hakan ake yi.
Innata bata da miji sai dai ba girki ne bata yi ba, kamar yanda aka ce na wai mai goyo taji da hidimar goyonta, don kar taje tana girki tana qazanta.
To amma kuma kusan kullum sai Mama tayi cefane ta ajiye ta fita unguwa ta bar ma Innata girkin da ba nata ba ne tayi.
A farkon tasowata xauka nayi kwata-kwata Babana bai son Innata saboda ganin abubuwan da ke gudana a gidan baya iya magana da Inna ko kallon inda take baya yi.
Baya sauraron ta komai nashi ko hidimar shi Mama ce, itama kuma Innan bata xaga ido ta kalli abinda ake yi, sai daga baya da na soma wayo na soma fahimtar al’amura sosai, sai na soma yarda da maganganun da mutane da kuma makwabtanmu masu sa ido kan lamurran gidan namu ke yi.
Cewar ai babu yanda za’ayi Babana ya ajiye kyakkyawar mace mai kyan diri da kyan halitta irin Innata, bugu da qari ga tsabta da yawan ado sannan ya ce bai sonta, sai dai kawai ya kasa mu’amalla da ita a zahiri, saboda an sha gaban shi.
To ilai kuwa, ina soma wayo sai na soma yarda da cewar ba son Inna ne Babana ba ya yi ba, akwai shakku ne mai yawa tsakaninshi da Mama, na kuma qara yarda da hakanne a dalilin ganewar da nayi cewar Mama tana sanya qafarta waje tabar gida da sunan tafiya unguwanninta da kusan kullum sai taje je su.
To shi kuma zai dawo cikin gidan ya baro kasuwarshi kenan sai ya tabbatar ta kusa dawowa sannan zai fice ya bar gidan ya koma shago.
Yana shigowa gidan kuma zai nufi wurin Inna, wurin da bai rabuwa da tsabta da qamshi saboda ita xin mai tsabta ce, iyayenta kuma masu yi mata hidima ne bata neman komai ta rasa har turaren xaki da na jiki da namu na yara kawo mata ake yi.
Baba yana shigowa gida in dai Mama bata nan to zaka ji yana magana cikin natsuwa “Ina Fatima take?” ko kuma ya ce, “Ke Humaira ina Mamanku? In gaya mishi sai ya nufi inda take xin. Sai dai Inna bata sauraron shi.
Innata mai kyau ce, gata da kwalliya ga tsabta duk da nasan ta ne a shekarun da tayi fama da matsalolin aurenta saboda fin qarfin da kishiya ta yi wa mijinta, hakan bai hana ni sanin kwalliyarta ba.
Haka nan mutanen da suka san farkon zuwanta gidan basa gajiya da faxin kai ai farkon zuwan yarinyar nan gidan nan anyi wani abu a wurin, ga kyau ga ado ga yauqi ga murmushi ga ta kuma da girmama mutane.
Rannan ma Mama bata nan tun safe ta bar gidan ita da su Suwaiba. Babanmu ne ma ya xauke su a motarshi ya tafi dasu wai anyi mata haihuwa, ni da Inna ne kawai a gida sai ko Sa’adatu.
Suma su Atika sun tafi Makarantar allo, ni na taimaki Innar ta gama`aikin abincin ranar da Mama ta tafi ta bar mata. Sai da mukk kammala kooai ta shiga xakknta don yin wanka, ni kuma na tsaya ina gyaaa kicin xin da muka yi aikin a ciki.
Yayin da sa’adatu ke bayana tana ta tsala uban kuka, muna cikin haka sai ga Babana ya shigo.
“Ke Humaira ina Innarku take?” nayi maza na ce mishi sannu da zuwa Baba, wanka take yi. Ado ya shigo ya ajiye kayan cefanen da yazo dashi, Babana ya kalle shi ya ce mishi, koma shagon sai an yi sallah sai ka zo ka xauke ni.
Cikin ladabi ya ce mishi, to ya juya ya tafi, shima Babana ya shiga wurin Innata, bai daxe da shiga ba naji Innan tana cewa, ina kike? Kawo min ita, na ce to, naje zan kai mata ita.
Tana zaune kan kujerarta ta kwalliya a gaban mudubi yayin da Babana ke tsaye a bayanta yana magana a hankali tare da kallon abinda take yi na gyaran gashinta.
Ke fa halina dake kenan, ke fa halina da kenan babu halin in dawo gidan nan saboda ke sai kin vata min rai, to ka daina dawowa mana, tayi maganar a wani yanayi da ya sanya ni hanzarin cewa, gata don su san na shigo xakin.
Har ta miqa hannu zata karve ta sai kuma ta ce min shiga ban xakin can kiyi mata wanka sai ki kawo min ita don kar ta vata min jiki.
Na ce to, na je yin abinda tace xin duk da kukan Sa’adatun.
Ina cikin yi mata wankan naji Babana yana cewa, wai me kike nufi ne da waxannan abubuwan? Ta ce abinda nake nufi kenan mu zauna kamar yanda aka ce mu zauna.
Ya fara magana kamar zai yi faxa ban san dalili ba sai kuma naji ya canza yana cewa ke baki da wayo, tayi maza tace eh, ai nima na sani.
Zo ki ji abinda zan gaya miki, bata kai ga bashi amsa ba na fito da Sa’adatu zan bata ita har lokacin bata gama shafe jikinta da mayukan dake kan madubin nata ba, waxanda ni na kawo mata su daga gidan Alhaji Mai kuxi.
Ke tafi da yarinyar nan Babana yayi maza ya daka min tsawar da ta sani nayi maza na juya na bar xakin na fito tsakar gida ina rarrashinta daga baya mana goyata na nufi zaure naja na tsaya ni kaxai jikina sai faman vari yake yi saboda tsoron abinda zai faru tsakaninsu, tunda na fara jin Baba yana cewa ai tunda kin ce ba kya jin rarrashi to kuma wannan abin da ya shafe ki ne kin san dai baki isa…
Ban yarda na ji qarshen maganar ba saboda tsananin tsorarta da nayi na kar in ji ya nufe ta da duka.
Lokaci mai tsawo Baba ya xauka bai fito daga xakin ba tun ina tsorace har dai na haqura na shiga sabgogina tunda itama Sa’adatun ta haqura tayi barci.
Sai zuwa can naga ya fito ya shiga wurin ya xan daxe kafin ya sake fitowa yazo zai wuce mu a zaure ya kalle ni ya ce min, kai mata ita ta shimfixe ta nayi maza na ce mishi to.
Ina shiga xakin Inna gabana ya sake faxuwa, saboda kukan da na same ta tana yi, gashi kuma gaba xaya kwalliyarta dama gyaran gashinta sun lalace.
Tasa hannu ta karvi Sa’adatu suka kwanta tare tana bata nono, ni kuma na fito na shiga kicin don bin umarnin da ta ba ni na xora mata sanwan abincin dare.
Kullum qa’idar Babana kenan Mama tana barin gida zai dawo ya samu Inna ko da kuwa dawowar nashi zai zama dalilin faxansu, ya tafi ya barta tana ta kuka ya gwammace yin hakan.
Har a wurin dangin Baba Innata ba wani farin jini ne da ita ba saboda Mama ta riga ta saye su da ‘yan kyaututtuka gashi kuma ita Innan a cikin kulle mai tsanani take, don ko nan da can Babana bai barinta taje.
Koda kuwa abinda ya shafi danginta ne sai dai in dolen ta kai dole, ‘yan uwan Babana da suke son Inna sune waxanda suka haxa uwa da uba da shi waxanda Mama take mu’amalla da su ta koma vangaren ‘ya’yan da yake uba xaya dasu.
Don a cewarta na uwa xaya uba xayan su da uwarsu ma’ana kakarmu kenan basa nufinta da komai sai sharri don su suka fi kowa son ganin Baba yana aure. Tsiyar mutum ba zai sihirce mata yaya ya mallake mata su ba.
Duk da halin da zaman Inna ke ciki a gidanmu na rashin ‘yanci da rashin walwala ga rashin damar yin mu’amalla da miji a bayyane sai dai komai a xarare koma a tsorace, hakan bai hana kishin Mama tsananta a kanta ba.
Kullum qawayenta suka zo ko wasu ‘yan uwanta da take yarda ta tattauna sirrinta dasu to hirarsu bata wuce hirar Inna. Idon su a kanta yake, hankalinta da tunaninsu gaba xaya wurinta yake tafiya.
Rannan ina jin ta ita da aminiyarta Hajiya Anwamu, kai wannan ja’irar yarinya da an barta ta samu sakewa a gidan ita da mijinta da ban san yanda ta zama ba.
Mama ta kalli inda Inna take shanyar kayan ‘ya’yanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login