Showing 30001 words to 32414 words out of 32414 words
yanzu Habiba ma shakkar haxuwarmu wuri xaya take yi, don ta gane babu abinda nake so irin danbe ya haxa mu ta kuma riga ta tsorata da waxanda take ganin mayi, don haka ta daina shiga harkata balle aje ga tsokana.
Rannan mun haxu da Ado a wajen wani biki da abokan Baba suka haxa ‘ya’yansu aure, don qara qarfafa zumuncin da ke tsakaninsu, dukanmu mun je har da su Habiba mun kuma sha kwalliya don mu a gidanmu kwalliya muke har da ta gasa.
A yau xin kuma na burge qwarai don har da zinari nayi adon saboda Hajiya Kubra ta dawo daga Ummara, don haka ta sayo min xan kunne da sarqa har da zobe masu kyau da kuma girma qirar Dubai.
Cikin kuxin Innata dake hannunta wanda take sawa ana juya musu, to Ado ma yana cikin abokan ango ya kuma sha kwalliya don ya iya sanya sutura mai tsada gashi kuma kwalliyar tana yi mishi kyau, don ya riga ya qoshi ya zama saurayi mai kwarjini da nagarta.
Wata yarinya da muke tare da ita Sadiya ita ce ta ce lah, su Humaira ga kawunku sai da na waiwaya bayana muka haxa ido dashi sannan na juyo na kalle ta ba kuma tare da na ji kunyar Habiba dake tsaye a gefenta ba, na ce mata uh’uh Sadiya ba kawuna ba dai kawun su Habiba ne, ai ni babu wani abin da ya haxa ni da shi in ban da zaman cin arziki da yake yi a gidanmu.”
Sum-sum Sadiya tayi ta bar wurin don ta san Ado ya ji abin da na faxa su kuma suna girmama shi saboda ya iya kama kanshi, ita kuwa Habiba ta kama fuskarta ta tsuke alamar rashin jin daxi, sai dai bata tanka ba.
Nima na ci gaba da harkokina, ana buxe falo aka soma neman ‘yanmatan da za su taka rawa na fita, ba tare da na damu da tsayuwar Ado a wurin ba, don dai in nuna mishi bai da wata kima a wurina.
A wannan lokacin kusan kowane lokaci Mama bina da kallo take yi cikin takaici da kwafa ban dai san dalili ba ko tasa mata ‘ya’ya da nayi a gaba ne su Habiba da Suwaiba waxanda a baya suka yi matuqar takurawa rayuwata tana kallo, oho.
Sati guda da gama bikin gidan su Sadiya ranar ma ranar wata Juma’a ce, nayi niyyar zuwa gidan Mallam mai babban allo wanda na daxe ina nerman izinin zuwan wurin Babana bai bani ba sai yau. Don haka kwalliya sosai na yi na fito daga gida.
Ado da wani abokinshi Nasiru suna tsaye a inuwar bishiyar qofar gidan mu, ina jin sanda Nasiru ya cewa Ado kai kai kai yarinyar nan haka ta zama? Ado yayi maza ya kawar da kanshi can gefe ga barin kallona.
“Menene na wani kai kai kai? Sai ka ce ka ga wani abin da baka tava sani ba, in ka naso ka wai kayi magana shi ke nan dama ba wani saurayi ne da ita ba, ‘yan uwanta gaba xaya sun samu manema har an kawo sadakinsu amma ita babu kowa babu wani malalacin.”
Nasiru ya ce, ai yarinyar ce kwarjini ne da ita gata bata bada fuska in ka dunfareta da nufin yi mata magana ma dole ka daina don gabanka faxuwa zai rinqa yi. Ya yi tsaki ya ce, ka zama ragon maza kenan, don haka tunda kana cikin waxanda take faxar wa da gaba to bari zan yi maka iso a cikin gidan in yaso ko baka zo taxi ba nasa a xaura auren a kawo maka ita har gida sadaka.”
Nasiru yayi dariya ya ce, wannan shi ne zance ka dai yi ne don ka ji ta bakinta tun yaushe ne ma aka daina yin sadaka da ‘yanmata balle kuma irin wannan mai tsadar.”
Ado ya ce, in na dai an daina yin sadaka da ‘yanmata to wannan kam zan iya sa wa a baka ita, in kuma kana musu to zuba ido kawai kaga abin mamaki.
Wucewa nayi na tafi zuciyata a cike da vacin rai mai tsanani a dalilin jin maganganun cin zarafi da Ado yayi min a gaban abokinshi babu abinda yafi komai qara min vacin ran kuma irin sanin da nayi cewar duk maganganun nashi akan gaskiya suke.
Bani da saurayi su Habiba da Suwaiba an kawo sadakin aurensu sannan shi xin da zai nishaxi ya ce wa Mama yana son a baiwa Nasiru abokinshi ni, ina ganin babu abinda zai hana ayi hakan tunda shi ne Mama, Mama kuma ita ce Babana.
Har na isa gidan mai babban allo ban gama wastsakewa daga wannan vacin ran ban gama wastsakewa ba sai dai ina shiga wajen shi na soma murmushi a dalilin son da yake yi min, ina isa gabanshi vacin raina yake gushewa.
Fura na samu yana sha, don haka na zauna muka sha tare ina mitar babu sugar ni ya barni in sa koxan kaxanne shi kuwa yana faxin ai ba zai yiwu ba don ba zan bar ki ki vata min ita ba sai dai in ki kawo wani abin in xiban miki naki sai ki sa duk abinnda kike son sakawa, na ce a’a tare da kai zan sha ya ce to kuwa sai kisha mara sugar.
Ya gama shan furar yana kallona ina qarasa, sahan wacce ya bar min sai naga yayi murmushi na ce mishi menene Mallam? Ya ce kallonki kawai nake yi ina tunaninki sai aukin kwalliya da iya lanqwasa amma har yanzu ban tava ganin wani yazo ya gaishe ni ba a cewar ke kika turo shi na ce azo a gaishe kan?
Yayi maza ya ce zan qosa mana Aisha in ta samu aka kan dake xin ai zata samu xan wani sauqin. Na ce uh ni in ban da saboda Inna da kuma gorin da ake yi min mafa Mallam ni auren nan ba wani son shi nake yi ba.
Ya xan gyara zama kaxan ya ce aure kuwa ai abin so ne Aishatu, Ibada ne kuma rufin asiri ne ina ce kina karanta surorin da na ce miki kullum? Na ce eh Mallam kullum sai na karanta (Yasin) in karanta (Arrahaman) in karanta (Waqi’a) sannan in karanta (mulk).
Yayi murmushi ya ce, madallah ashe qoqari ne da ke to rinqa haxawa da (La haula wala quwata) qafa casa’in da tara take yi qarami daga cikin magungunan nata shi ne baqin ciki na ce to Mallam na gode, muka xan yi hira na miqe na ce mishi bari in shiga ciki in gaishe su don in zo in tafi ya ce min to.
Na gama abinda zan yi a cikin gida na dawo wurin mai babban allo zan yi mishi sallama sai na same shi tare da Alhaji Abba, wasa dani da yake yi tun ina ‘yar qaramata ya sani sakewa nima nake wasan dashi a matsayin ‘yar Inna da xan kawu don shi ya ce Inna uwa ce ba ‘ya ko qanwa ba.
Na kalle shi cikin murmushi na ce, ah, ka ce ka ji nazo ne ka biyo ni? Ya yi wata irin dariya kafin ya kalli mai babban allo ya ce ni Mallam in ce ko dai wannan irin kwalliya da ake tsalawa tana biyan kuxin sabulu?
Mallam yayi dariya ya ce, to ina fa na sani tunda ni har yanzu ban gani a qasa ba, ya qyalqyale da dariya jin daxin abin da Mallam xin ya faxa, ya ce to ko dai ni zan soma zuwa gaishe kan ne kawai Mallam don ka gani a qasan? Mallam ya ce a to ga ka nan ai ga ta ku ku kasan saura.
Alhaji Abba ya kalle ni cikin yanayin murmushi da zolaya ya ce, Yaya ko zan fito ne kawai muyi ‘yar gida ko kuwa Mallam? Mallam ya sake cewa, ato, ai ga ka nan ga ta nayi murmushi na ce sha kurumin ka ni na da ka ke kallona gal a leda zan aura.
Mai babban allo ya ce uhun’uhun ka ji sakarcin nata ba? Da wani gal a leda da ya wuce wanda zai riqe auren yaga darajar iyayenki? Ban kula zancen na mai babban allo ba don naga zancen yana nema yayi nisa. Un, ban kuxin mota Mallam ni zan koma gida don Babana ya ce kar in yi yamma sosai.
Eh, ai yana da gaskiya Mallam yashiga dube-dube yana qoqarin tattaro duk kuxinshi ya bani kamar yanda ya saba yi kullum.
Alhaji Abba ya karkace yana qoqarin cusa hannunshi cikin aljihun wandonshi, qyale ta kawai Mallam bari in karve ka ba da kuxin motar nan a yau tunda ga dukkan alamu ma na fika ganin kyan kwalliyar tata ta yau.
Ya zaro kuxin da bai qirga ba ya miqo min nasa hannu biyu na karva, bai bari ya ji godiyar da nake shirin yi mishi ba sai ya ce min cewar da ki ka yi ni ba gal a leda ba ne ba fa ba zai hana ni biyo ki gida don taxin ba, bari in yi kwaskwarima in zo ki gani ki ga yanda zan zo miki a wani santalelen saurayi za ki gane wannan qatuwar rigar da nake sanye da ita, ita ce ta hana ki gane ni xin na ma fiye miki gal a ledan ba.
Mai babban allo sai faman dariya yake yi yana faxin har da su kwaskwarima a ciki kenan, ka yarda kai xin ba gal xin ba ne tunda sai ka haxa da kwaskwarima. Suna dariyarsu ni kuwa na sunkuya na tsince ‘yan kuxin da Mallam ya riga ya fito dasu, shi kuma sai faxi yake ka ganta ko? Ba kaga irin halin nata ba sai ta haxa har da nawan ta kwashe.
Na isa gida gaban Innata cikin farin cikin gamuwa da Alhaji Abba da nayi, tuni na man ce da takaicin maganganun banza da Ado yayi min sanda zan tafi, na samo mana kuxi Inna na gamu da Alhaji Abba ina murmushi nayi mata bayanin komai na xebo kuxin daga cikin jakata, kin gansu?
Na nuna mata itama tayi murmushi ta shiga yi mishi addu’a na gama lissafa su dubu goma sha uku ne na sake wani murmushin na ce mai kuxi ne Abba ko qirga su bai yi ba ya bani. Ta sake wani murmushin cikin jin daxi ta ce, eh ai shi arziki haka yake ba daga yawan shekaru ba ne kyauta ce kawai daga mai bayarwan na ce haka ne.
Na dunbazu wasu kuxin na miqe zan fita don na saba in mun samu kuxi bani kawai Inna take yi ta ce in sayo mana abinda nasan shi ne muhimmi, ina za ki da waxannan kuxin?
Cikin natsuwa tayi min tambayar na ce mata sabulun wanka da na wanki zan sayo mana masu yawa don su daxe basu qare mana ba, sai ko biskit da indomie saboda su Baba qarami ba ta yi magana ba shiru tayi alamar ta amince kenan, na wuce na fito da nufin sayo abinda zan je sayowa.
Sai kawai na hangi Ado a falon Mama sun haxa kai suna qus, qus, qus, ga alama kuma basa son wani ya ai abinda suke tattaunawan, gabana ya yanke ya faxi kar dai maganar da Ado yayi xazu a waje mai kama da shaqiyanci ne yake shirin mai da shi gaskiya?
Har naje na dawo ba su gama maganar ba, hankalina ya yi matuqar tashi don kuwa nasan Mama da Ado za su iya yin komai a kaina, don Innata tayi baqin ciki, tunda sun riga sun tsarawa kansu cewar ni xin bata haxa ni da kowa ba cikin ‘ya’yanta.
Nan da nan hirarrakin Mama da qawayenta da nayi ta ji suka rinqa dawo min, roqon da suke yi ta bar wa Innata ‘yarta kar ta sake jefa ta cikin wani baqin cikin, ko ba a gaya min ba kuma nasan ba kowa ba ce wannan ‘yar ni ce.
To ga Ado ga kuma abinda na ji ya fito daga bakinshi gashi kuma na gansu suna tattaunawa, irin tattaunawar da suka saba yi in suna shirin qulla wa Inna wata qullalliyar.
A xakinmu na rasa yanda zan yi in gaya wa Inna da nake ciki tunda ita kuma a yanzu damuwarta ta ragu in ma bata gushe duka ba ta samu abinda za ta baiwa ‘ya’yanta su ci gobe da jibi da gata da citta, don haka sai kawai na wuce naje na hau gado can cikin zuciyata ina tunanin me zan yi wa Ado?
Me zan yi mishi in nuna mishi cewar ni ma xin ta Maman ta ce kowa ya ci tawo da ita miya yasha. A yanzu kam madan ni kam ina ganin kamar zuciyata ta kai wani matsayi da bata da wani wanda ta qi ta kuma tsana take jin zafin shi take neman samun damar xaukan fansa a akan shi irin Ado.
Washegari da sassafe Innata ta amsa kiran da Babana yayi mata a xakin Mama a gaban kuma Maman har ma da Zubaida.
A gaban Maman kuma da Zubaidan ya baiwa Innata wa’adi na kwana uku wai in fiddo da miji ya haxa mu da su Habiba yayi mana don ba zai yi auren Habiba da Suwaiba ya bar ni a cikin gidan ina zaune ina zubawa matanshi rashin mutunci ba.
In ma dai mu bi wannan umarnin da ya bayar ne na kawo mijin cikin kwanaki ukun da ya ambata ko kuma mu tattara mu bar mishi gidan.
Mu ci gaba cikin yardar Allah a littafi na biyu tare suka fito.
HAFSAT C. SODANGI
07035586299
18/7/2012
28/8/1433 Hijira