Showing 27001 words to 30000 words out of 32414 words

Chapter 10 - MIJIN TA CE BOOK 1

20 Aug 2024

4900

mu suka yi ba a yawa sai dai wai su xin manya ne, a kullum aka bamu kuxin namu sai mun zauna ni da Inna mun yi ta lissafin yanda zamu yi mu sarrafa su ta hanyar da za su ishe mu, amma ina!
Ta yanda duk muka juya su basa wuce abin karyawa sai ko kuxin awon hatsi kuxin cefane kullum sai ta nema ga sabulun wanka da wanki ga man shafawa duk waxannan al’amura da Mama ta kawo Babana sai ya mance da cewar ita manyan ‘ya’ya ke gare ta, ga kuma uwa uba qaninta akan dukiyarshi wanda kuma a cikinta suke yin komai.
Don haka maimakon Inna ta samu sauqi sai ya zama kullum matsalolinta qaruwa suke yi, kullum ka ganta a rame ramarta kullum qara yawa take yi.
Inna mai xabi’ar wanki kullum sai ta zama yanzu tarawa take yi sai randa ta samu omo ko sabulu tayi ban kuma san dalili ba, ko Baba ya gane a yanzu babu abinda Inna take so ne irin zaman gidan nashi.
Kusan kullum sai ka ji shi yana kafa mata wata sabuwar doka tare da faxin zaman nan fa ba dole ba ne in da takura a ciki a bar shi, tuni ya daina cin abincin da muke girkawa a dalilin wai bakin shi baya iya cin abinda bai da xanxan.
Don haka kullum Mama ce mai ba shi abinci, zancen kar ya yi hira a xakin ta ma kuma duk bai taso ba.
Tuni ‘yan uwan Inna suka ja suka tsaya kan sai lalle ta fita ta bar gidan wai azabar da ake gana mata tayi yawa, in miji yana son mace ai duk yanda ya kai da tsoron wata matarshi bai yi mata irin wannan azabar.
Tashin hankalin da su Inna Balki yayinta mata suka zo gidan suka yi yasa Babana yin amfani da shawarar da Mama ta bashi na kai maganar gaban mai babban allo ko don ya jarraba dattakunshi ya gani tunda yayi alqawarin randa duk suka sake zuwa gidan aka yi faxa dasu to zai haramta musu zuwa gidan.
Yana zuwa kuwa ya zartar da wannan hukuncin har kuma akan Hajiya Kubra da take matsayin uwa rta, sai ta nemi izininshi gaba xaya ‘yan uwan Inna suka xauke qafarsu suka kuma xauki mataki mai tsanani a kanta wai mijinta ya hana su zuwa wurinta.
Ita kuma tana zaune bata fito ba in ya soma daga baya ta koma amma dai sun san ta nuna rashin jin daxinta kan wulaqancin da yayi musu, don haka duk wani taimako dake zuwa daga wurin ‘yan uwanta ya katse, ba sa ma zuwa balle su ga halin da take ciki.
Ita kuma dama ba zuwa take yi ba, balle kuma yanzu da haka ta faru ko ta tambaye shi zuwa wurinsu sau ashirin baya bari in yaga zata matsa ma sai ya ce da izinina dai na hana in kuma kin ga za ki da naki izinin shi kenan.”
Mallam mai babban allo ne kawai yake xan kewayo mu yazo mana da xan abin hasafi har ma ya bamu kuxi sai ko Baba Yahaya.
Burin Inna a wannan lokacin bai wuce taga an yi aurena ba, tana gidan kullum ta kan gaya min in Allah yasa naga an yi bikinki lafiya to zan koma gidanmu zan koma wurin iyayena da dangina ba zan iya rayuwa babu su ba, in na ce to Inna su kuma su Atika fa? Sai ta ce uh’uh, su ko na bar su babu komai ba za su samu kansu cikin matsala mai yawa ba kamar ke, yanzu ina nan ma yaya? Balle kuma ace babu idona a kusa?”
A yanzu duniya tayi matuqar yiwa Mama daxi sai wani irin qiba take qarawa a daidai lokacin da Inna ke neman lami ta baiwa ‘ya’yanta ta dai samu suci su qoshi kar su kwana da yunwa, wata rana bata samu.
Ita Mama ta daina cin naman saniya sai kaji saboda Ado ya karve ta cefane, ita da bakinta naji ta tana gayawa qawayenta ai ita yanzu ta huta, Ado ke yi mata komai tun daga ce fane zuwa sauran hidimominta ‘yan kuxin da Alhaji ke bayarwa ajiye su kawai take yi saboda ba ni banin yara, qa’ida ne in sun miya da kaji da daddare to da safe kuma za su karya ne da farfesun kifi ko na bindi.
Gashi kuma ba za su zauna a falonta su karya ba sai ta ce wai ina dalili? Gara dai a baza qatuwar tabarma a tsakar gida kowa ya baje, nan za su baje har da Babanmu da zai ga wucewar Sa’adatu ya xan gutsuro wani abu cikin abinda suke ci ya miqa mata sai ta ce Alhaji kenan, to kasan abinda suka ci a xakinsu?
Ta manta cewar ko da ma me muke ci xin muna da haqqi cikin nasun tunda da kuxin ubanmu ake yi, Ado bai da wata harka ko sana’ar da zai saman mishi kwabo in ban da zaman shagunan Babanmu da yake ji ko kuma zuwa mishi aika zuwa aikan da zai yi wuya ace sau goma ba a dawo an ce ga wani abin da ya samu kuxin da aka yi akan da su ba.
Haka kuma dole Babana zai haqura don kar Mama ta tambaye shi Alhaji ba ka san asara ba ne? to wane bincike zaka tsaya yi a kanta in dai ba so ka ke kayi abinda zaka zobe ladanka ba?
Na tsani Ado, na tsani in xaga ido in ganshi a cikin gidanmu gani nake tanfar har da shi cikin abubuwan da suka yi dalilin shigar mu da Innata cikin halin da muke ciki, gashi don raini da wulaqanci sai ya shigo gida ya gaida Mama da Zubaida ya juya ya fita bai gaida Innata ba.
In har da wani abinda na qi na kuma tsana cikin zuciyata to bayan Mama qanin nata ne.
Rannan ina xakinmu a kwance cikin dare ban san Babana ya shigo xakin Inna ba, don a yanzu ranar da yaga dama ne kawai yake zuwa wurinta, ko da kuwa kwanan nata ne sai ya shige wurinshi yayi kwanciyarshi.
Salatin shi na jiwo da qarfi tare da jan tsaki mai tsananin qarfi, kafin ya soma faxin “Kai wannan fitina da yawa take, ni Surajo naga abin da ya ishe ni, kin gani Fatima, tun dai ni a wurinki na gajiya ba kya ganin qoqarina bare alherina komai nawa a raine yake a wurinki, bani da fita a wurinki ba ni da shi a gun danginki kiin zo kin same ni cikin iyalina kin takura mana kin tasa mu a gaba da dokoki komai aka yi ki ce baki yarda ba kin watsa min haxin kan gida kin raba min kan ‘ya’yana sannan a hakan baki gamsu ba.
To in kin ga har yanzu kina da matsala to za ki koma gidanku ne kawai, donni na gaji na gaji abin ya ishe ni haka. Ya balle qofar ya fita cikin daren har ya isa xakin shi bai daina mita da faxin maganganu ba.
Inna ta miqe tana haxa kaya a cikin daren nan fito na same ta tana yi tana kuka wataqila yau ma so take ta tafi ban sani ba, tana ganina ta soma share hawayenta na ce mata kar ki tafi Inna, za ki je gida ne ki haihu a can?
Kin san dai in kin tafi yanzu ba bin ki zai yi ba, ‘yan uwanki kuma ba za su dawo da ke ba, kiyi haquri ki daina gaya mishi damuwarki kiyi mishi shiru kawai, ba ke ma kina da abinda kike shiryawa ba? Ta gyaxa kai nuna alamar eh, na sake ce mata to kiyi haquri ta ce min to.
Na koma xakinmu na kwanta cikin zuciyata tunani nake yi burin Inna bai wuce ta yi ta haqurin zaman gidanmu har zuwa lokacin da zata ga an yi aurena, in yaso sai ta tafi, ita a ganinta don ta bar su Atika ba komai ba ne don su basu da irin matsalar take ganin ni ina da ita.
To amma yaushe? Yaushe za’ayi auren nawa tunda ni ko saurayi guda xaya ban tava yi ba, ban tava samun saurayin da ya kalle ni ya ce min ke ‘yanmata ji mana, me sunanki? Ni fa sonki nake yi ba balle a ce an zo qofar gidanmu ana kirana balle har a biyo ni da wani xan hasafi kamar yanda kullum nake ganin ana yi wa su Habiba a kowane lokaci naga Mama tana nuna wa Inna irin hasafi da ake yi wa su Habiba wanda a ciki zanga har da sabulayen wanka da na wanki har ma da su omo sai in ji zuciyata tana cewa ina ma nima in samu saurayin da zai rinqa yi min irin wannan kyautar da Innata ta huta da tara wankin da take yi tunda nasan tara wankin yana cikin lissafin damuwoyinta.
Amma Mama sai ta nuna mata ta kwashe su duka ta yi tafiyarta da su ba za ta bata ko qwalli xaya ta ce ta wanke kayan qannen su Habiba ba, duk da addu’o’in alherin da take yi musu in ta ganni tanfar dai wacce ake yi wa qwalele.
Rannan cikin dare Inna ta haihu yau ma xa namiji muka sake samu ni da ita mun yi murna Baba qarami shima ya samu xan uwa sai da na tayata ta yanke wa yaron cibiya ta yi mishi addu’o’i ta naxe shi a zani ta bani shi na kwantar dashi na juye mata ruwa taje wanka na dawo na naxe ledar da ta shimfixa ta haihu akai na goge komai na gyara shi tsaf.
Na kawo mata ruwa don ta wanke shi ta kalle ni ta ce min wanke shi ki koya nace ah Inna ai ba zan iya ba ta ce koyi na zauna na wanke shi tsaf ina yi ina canza mishi ruwa har sau uku da na gama na shafa mishi man da muke shafawa na kuma sanya mishi riga cikin rigunan Baba qaramin da Inna ta adana don shi kam bai samu an sai mishi komai ba.
Na kalle ta na ce, mata to me za ki ci? Ta ce babu komai ai bana jin yunwa tausayinta ya yi matuqar kama ni don na riga na saba ganinta tana cin abinci da na sha mai yawa idan ta haihu sanin da tayi ba mu da komai a xakin shi ne ya sanyata ce min ba ta jin yunwa.
Naje na tsiyayo ruwan xumi a flask na sa mata suger kaxan da lipton na kawo na bata ta karva ta kwankwaxa, ta ce min to sannu je ki ki gaya musu na ce to naje na qwanqwasawa Mama qofa.
Babana ya fito daga xakin Zubaida saboda jin qwanqwasa qofar da nake yi, yaya lafiya? Na ce mishi Inna ta haihu, Mama ma ta buxe ta haihu ne ko zata haihu? Na ce mata a’a ta haihu ne.”
Ita da Babana suka yi hanzarin shiga xakin na tsaya a tsakar gida sai da naga sun fito daga xakin sannan na shiga.
Washegari da sassafe Hajiya Kubra ta iso gidan saboda aiken da aka yi musu cewar Inna ta haihu, a wannan haihuwar gaba xaya dangin Inna babu wanda ya leqo ta daga Hajiya Kubra sai ko Hajiya ‘Yar dubu, sau biyu ina jin Inna tana gayawa Babana cewar tana so a sanya mata sunan Babanta wato a yi wa Alhaji Mai kuxi takwara, amma ranar sai kawai na ji Mama a tsakar gida tana faxin wai Ado aka yi wa takwara, don haka sunanshi Adam.
Ai kuwa dai Mama a irin hidima da xawainiyar da yake yi da gidan ai gara da ki ka sa aka yi mishi takwara, in ji Zubaida. Cikin zuciyata na rasa abinda zan ce iyaka dai sai naga kai ni kam babu ma dai abinda ya dace da ni illa in fidda raina kan tunanin aure da ma sha’awarshi.
Tunda ma na riga nayi sa’a bani da samarin tunda in dai ma aure irin na gidanmu ne nima haka za aje ayi min irin yanda nake ganin ana yi wa mahaifiyata, to ai ina ganin barinshi kawai shi ne zai fiye min sauqi tunda bana ganin kamar zan iya irin haqurin da take yi.
Duk da vacin ran da na samu akan sunan da aka sanyawa yaron nayi wanka nayi kwalliya saboda Innan bata xauki sanya mishi sunan Ado da wani zafi ba, ta ce kowane mutum da sunanshi yake zuwa.
Da hantsi na fito bayan nayi kwalliya sosai don in ma muna rashin komai to ni kam bana rashin kayan kwalliya gidan Anti Ramla nayi nufin zuwa don babu wani abin armashi da na gani a sunan namu, sai nazo wucewa ta falon Mama karaf sai na ji tana ce wa manyan qawayenta da suka riga suka zo mata sunan, ai bata ga komai ba tukuna ai sai na nuna mata ni xin ni ce ai sai na sata tayi nadamar auran mun miji da tayi.
Gaba xaya suka kwashe da dariya cikin zuciyata na ce, oh’oh ko me zata yi wa Inna wanda ya zarce wanda take yi mata a yanzu oho? Tausayin Inna ya sake kama ni da na tuna duk da halin da take ciki bata nadamar auren Babana da tayi na kuma tabbatar a zuciyata ko ma me Mama zata yi ko tasa ayi mata ba za ta iya sata tayi nadamar da take cewa zata sa ta tayin ba.
Tunda ita da bakinta ta ce min bata nadamar aurenshi domin ta haife mu a tare dashi, don haka ta gamsu da koma menene.
To ban san me Mama ta faxa musu ba, wataqila don na shagala da tunani to amma na ji Hajiya Anwamu tana ce mata uh’uh Mama, uh’uh kar ki fara, kar kiyi wannan abinda kike shiryawa, ba don komai ba sai don kowa yasan wannan yarinyar ita ce uwarta.
Kinga kuwa tura in ta kai bango to bata cika daxi ba, ita kuwa wannan yarinya da kike kallonta yanda fa bata yi kama da uwarta a halitta ba haka nan ko kaxan halinsu ba xaya ba ne don haka qyale mata ‘yarta kawai ai kin samu ina laifi wata da nakuda wata faxin sunan xa?
Ban da haka ban da haka ko hana ‘yan uwan yarinyar nan zuwa in da take da ki ka yi ai ya ishe ta.
Ina fita waje Habiba da Suwaiba na gani suma sun sha kwalliya kamar in wuce su in yi tafiyata sai na tuna maganganun da na bar uwarsu tana faxi, don haka sai na matsa kusa da su na same su.
Suwaiba dai tuni ta riga ta tsorata dani, don sau biyu ina yi mata dukan tsiya. Na isa wurin kenan sai na hango Ado yana fitowa daga cikin gidansu yasha kwalliya yayi matuqar yin kyau, kallo xaya nayi mishi na kawar da idona daga gare shi.
Na kalle su na ce musu, me na ji ku kuna fa xa xazu? Habibna ta ce, abinda ki ka ji muna faxin shi… kan ta gama nayi maza na café bakin nata nufina wai in yi mata yanda itama da take yi min, sai Ado yayi maza ya qaraso yana faxin.
“Kai, kai ku bari ku bari, ke fa fitinanniyar yarinya ce.” Yana maganar yana nuna ni da xan yatsa, na galla mishi harara na yi mishi wani lalataccen kallo na sama da qasa sia da na murguxa mishi baki kafin na ce mishi daxin abin dai a gidan ubana nake fitinar duk iyayin mutum bai da yanda zai yi dani tunda shima zaman cin arziki yake yi.
Bina da kallo Ado ya yi, kallo kuwa mai tsananin cikin kaxuwa da mamaki bai tava sanin zan iya yin abin da nayin ba. Nasa kai na wuce nayi tafiyata, daga shi har su Habiba babu wanda ya ce min qala.
Ban dawo gidan ba sia da yamma, nazo na samu Hajiya Kubra tazo ta tafi ga kuma kayan da ta kawowa Inna zannuwan da ba su wuce goma ba, sai kayan jarirai babu wani yawa suma sai dai ta kawo mata kuxi masu xan auki wai ta riqe a hannunta saboda hidimar yara.
Tun ban gama zama ba Inna ta soma tanbayata me yaron nan yayi miki ki ka zage shi? Na ce shi yazo ya gaya miki na zage shi? Ta ce a’a su Habiba ne suka gaya wa Mama shi ne ta ce min in gaya miki kar hakan ya sake faruwa.
Don haka kar ki sake, na ce an zagi Ado Inna suyi abinda za su yi an zage shi, Inna ta zuba min ido tana kallona zata yi min magana na ce mata kar kiyi min faxa akan shi Inna ki bar ni kawai ‘yan abu kazan uba na sake mulmulo wani ashar xin na antaka musu.
Shiru tayi tana bina da kallo saboda ita ba mai son tashin hankali ba ne, na nemi wuri nayi kwanciyata ba tare da da na gaya mata hirar da na ji Mama da qawayenta suna yi ba.
A

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login