Showing 21001 words to 24000 words out of 32414 words

Chapter 8 - MIJIN TA CE BOOK 1

20 Aug 2024

4898

dalilin wai bata daxe da yin hidimar suna ba, amma dai duk da hakan ‘yan uwanta sun taru suna kuma bata shawarwari iri-iri.
Ana kammala biki sai manufofin Mama nasa Babana yayi aure suka fara baiyana, cewar ita ta sa shi kuma ba zargi ba ne da kanshi ya faxa cewar Mama ta ce qara auren nashi ne kawai zai kawo zaman lafiya kuma in ya duba da kyau ma ai zai ga gaba xaya abokan shi ma mata uku-uku ke gare su ba biyu ba.
Tun daga ranar da aka yi buxan kai ya haxa su gaba xaya a xaqin Mama don yi musu nasiha kan zaman lafiya da muhimmancin qarami yabi babba Mama ta ce in shi babban ya bi nashi na gaban ko?
Zaman lafiya kuwa ai a wurinka yake tunda kaine mai gida in ka tsaya kan hana zalunci da kuma tsoma yara cikin zaman kishi, amma fa sai kaso hakan tunda ni kam ina ruwana? Ai ni ‘yar kallo ce, menene ban gani ba cikin sha’anin kishiya da sanabenta? Ai babu wani dare da jemage bai gani ba sai na ranar mutuwarsa.
Baba ya ce, haka ne to yanzu tunda ku uku ne yaya ku ke gani zaku ci gaba da kwana bibbiyun ne ko kuwa zaku canza? Ta ce, to sai suyi magana amma ni kam ai ba zamu raba ka da wannan yarinyar ba tayi min quruciya da yawa, kaje can kawai kayi sha’aninka ni na bata nawa girkin in ka yi kwana biyu a wani wuri sai kayi huxu a wurinta.
In gari ya waye dai kazo mu mu mu gaisa mu tattauna al’amura tunda kasan duk cikin su babu wacce takai ni sonka tunda su duk Alhaji suka aura ni kaxai ni ce nan matar Surajo.”
Babana yayi murmushi alamar jin daxi ya ce, to kuma kin san haka kya ce kin yafe musu ni? Ta ce oh’oh ai ba komai, ka saki jiki kayi hidimar ka Alhaji, ai mun riga mun zama xaya.
Ya gyaxa kai alamar yarda, ya ce haka ne, haka ne Majadan, ta ce to menene? Ai na riga na ci dubu sai ceto.
To hakan aka yi, Innata a matsayinta na wacce aka yi wa Amarya ita ce ta xauki nauyin yiwa Amarya girki na kwanaki bakwan da ango ke yiwa Amarya, ta sake yi mata girkin kwana biyun da Mama ta bata kyauta. Sai nan ta yi wa kanta nata girkin bayan Baba ya yi wa Amarya kwana tara ya dawo wurinta.
Ya sake komawa wurin amarya ta sake jerawa amaryar girkin kwana huxu a jere nata dana kyautar da aka yi mata, sannan ta sake yiwa kanta da ya zo wurinta daya fita zai koma wurin amarya ne ta ce to yau kam a baiwa amarya cefanenta, ta fito ta yiwa kanta girki itama zata huta saboda goyo ke gare ta.
Babana ya ce, ai kin yi qoqari kwana goma sha bakwai fa kika jera kina yi ke kaxai sau xaya kuma ban kama ki da laifin yin girkin maguxi ba, Allah ya saka miki da alheri, ta ce amin.
Ya fita ya tafi, ba mu san yanda aka yi ba sai gashi ya dawo wai ba zai yiwu ace tun yau an baiwa amarya girki ba wannan wane irin kishi ne? ‘Yar yarinya ‘yar qanqanuwa ace ba za ayi mata girki ko na wata biyu ba.
Inna ta ce, ai fa kana ta juya ta gyara ta yi kwanciyarta ya yi faxanshi har ya gama ya fita bata tanka mishi ba. Mama ta fito ta karvi girkin tana faxin ai ba zai yiwu ba ace wannan ‘yar yarinyar ta shiga kicin don ana jin haushinta a xora mata xawainiyar da bata isa yi ba, tunda dai ni ce babba a gidan ai dole in shiga hidimar girkin nata.
Inna tana daga kwance ta ce, babbar banza ba, nayi maza na kalle ta don ba xabi’arta ba ce faxin irin waxannan maganganun. Nan take cinta a zuciyarta.
Mama kullum takan yi wa amarya girki nata da na kyautar da tayi mata sai dai kuma qwandala bata miqa mata cikin canjin cefanen da ke raguwa, mu kuma ta koma min xira mana abinci kamar yanda dama ta faro a baya.
To na da ma da sauqi don zata yi kwana biyu ne Innan ma ta kwana biyu to yanzu ita kaxai kwana huxu take yi, ga amarya fitsararriya babu alamar kunya ko tsoro a tare da ita ga alama kuma ta riga taji labarin Inna kafin zuwanta.
Don haka da shirinta sosai ta shigo cikin gidan, ba kuma yarinya qarama ba ce kamar yanda ake faxa, don kuwa ba za ta rasa shekaru ashirin ba, zuwa da biyu ba kuma wani karatu ta yi ba, mijinne dai bai samu ba sai a lokacin.
Tuni amarya ta gundure ni na rasa yanda zan yi da zuciyata in ji daxi, na tsane ta na tsani duk wani al’amarinta saboda tasa min uwa da tayi a gaba da rashin kunya iri-iri. Babu damar Inna tayi wani motsi sai kawai ka ji ta tana sake mata maganganu.
Mama kuma tana qara zugata tana faxin, a to ai karen bana shi ne maganin zomin bana, in ni anyi min na qyale dole don kar ace girmana ya zube yarinya kam ai ba za ta yarda ayi mata takun da ake yi min ba.
Wani irin kishi mai tsanani ya kama ni game da amarya saboda ganin yanda aka xauke ta aka fifitata akan Innata, take kuma ci wa Innar tawa tuwo a qwarya.
Babana kuma yake zumuxin ta yake faman zirga-zirgan wurinta sai ko wurin Mama, xakin Innata bacci ke kawo shi a dole wataran ma ya qi zuwa wurin nata ya shige nashi wurin yayi kwanciyarshi.
Zuciyata ta kai matuqar zafi game da abubuwan da nake gani, gashi kusan kullum sai naga idanuwan Inna a kunbure alamar vuya tayi ta yi kuka.
Rannan na amsa iran Babana a falon Mama suna zaune dukansu na durqusa ina sauraron maganar da yake yi min. Wannan ba uwarki ba ce da kike kiranta da sunanta?
Na sunkuyar da kaina qasa nayi shiru can cikin zuciyata kuwa cewa nake yi, to ai nima tawa uwar da sunanta kowa yake kiranta, ban kuma tava ji an yi wani tsawa kan hakan ba.
Zuciyata ta tafi wajen tunanin lamurra iri-iri, don haka ba sosai nake fahimtar maganganun da ake ta yi min ba, na dai san kawai na ji kashedin da Baban yayi min na in ya sake jin na ambaci sunan Zubaida da bakina to zan san bolko miya ne, ke Zubaida ko bana nan ta kira ki da sunanki kizo ki gayawa Mama in na dawo zata yi min bayanin komai.
Ta ce, to, cikin wani yanayi na shagwava, ni kam a wannan lokacin in ban da Innata tana cikin gidan, wataqila da gudu nayi na bar gidan saboda yawan vacin ran da nake samun kaina a ciki.
Na daina ambaton sunan Zubaida sai dai kuma bana kiranta wani Anti, in mu’amalla ta haxa ni da ita magana kawai nake yi mata, ta yanayin da zata gane da ita nake yi ba sai na ambace ta ba.
Rashin jituwa mai tsanani ya shiga tsakanina da ita saboda gaba xaya bata shakka ko shayin sakin bakinta ta gayawa Inna maganun ban za na rashin mutunci.
Ko kuma ka ji ta tana yi wa Inna gori kan wasu abubuwan da zaka kasa sanin inda ta samo labarinsu. Haka kawai kuma sai tayi yaji in Babanmu ya dawo sai ace mishi wai Inna ce take yi mata wulaqanci da barazana.
Sai ya tura Mama taje mishi biko in ta dawo ayi ta rattabo mishi bayanai. Wani lokaci ma bayanin yana qarewa Babana zai kama ni ya naxa min dukan tsiya ya kuma gaya min cewar in har ban daina biyewa Innata, ina taya ta baqin kishinta ba to ni da ita ne zamu bar mishi gidan don ba zan yarda da abinda zai kawo rai ba kan iyalinshi ba gara kawai ya kori mutum ya tafi ya bar mishi gida a zauna lafiya.
Rannan Inna tana wanki tana matsewa tana ajiyewa a qasa, kusa da bahon xin wankin nata saboda sai da ta wanke wurin da zabor yayi tas kafin ta fara wankin ni kuma ina gefenta ina wanke-wanken da Mama ta sani a ina kuma yi mata magana a hankali sai kawai ga Zubaida ta fito daga xakin Mama tazo ta keta tsakaninmu ta taka wankin da Inna ke tarawa da qafarta mai sanye da takalmi.
Inna ta miqe ta tsaya tana kallonta ta ce aiya Zubaida wannan kaya da kika taka na riga na wanke su, sai kawai naji ta ce an taka xin menene? Ko shure su nayi na watsa su me zaki yi? Tana faxin hakan kuma sai kawai naga ta shure tarin kayan sun watse sunyi xai-xai a qasa mai datti.
Ban san yanda aka yi ba, sai kawai na samu kaina da tambayar ta ha’a wannan wane irin abu ne haka? Ta wanke kayanta kin taka tayi magana kin watsar mata da qarfinki? Ta ce an watsar ko kina da abin yi ne mai uwa?
Ta miqo hannu ta murxe min baki ta saki don kawar da kan da na yi bakin nawa ya suvuce daga yatsunta ta sake miqo hannu zata sake. Na kaiwa hannun nata duka da iyakacin qarfina.
Lah, ni kika buga? Da qarfi tayi tambayar Inna tana faxin ki bari ki qyale ta kawai kije xaki, amma ina? Idona ya riga ya ru fe don haka Zubaida na sake kawo min duka ban tsaya ba rarumarta kawai nayi da wani irin qarfi da ban tava sanin ina da shi ba na jefar da ita cikin kwanukan wanke-wankennan.
Ga zaton Mama duka zata yi min in aka yi danben, don haka tana ganin mun fara ta bar falonta, ta shige can cikin xaki. Inna tana kiranta tazo ta raba don ita kaxai ba za ta iya ba, ta qi kulawa.
Sai data ji Zubaidan da kanta tana ihu saboda mummunan shaqan da nayi mata sannan ta fito a guje, ta xaga ni akanta. Ta kuma yiwa Babana waya ta ce mishi maza-maza ya bar abinda yake yi yazo gida gani nan ni da uwata mun taru zamu kashe mishi amarya.
Inna tayi murmushi kawai ba ta ce komai ba ni kuwa can cikin zuciyata na riga na gamsu don haka ban damu da hukuncin da za a zo ayi min ba.
Babana ya zuba min ido cikin matsanancin vacin rai bayan ya gama sauraron jawabin Mama na cewar ni da Inna ne muka taran mata. Ya ce “Ke Binta.” Gabana yayi mummunan faxuwa ga zatona cewa zai yi ta bar mishi gida ko ga takardar saki ya bata.
Sai na ji ya ce zan sa qafar wando xaya dake a gidannan ba dai kina baqin ciki da abinda nake so ba, to ai kuwa kin rinqa vacin rai kenan za kuma mu haxu a daidai. Tashi min daga nan ki koma xakinki don bana son ganinki a yanzu.”
Inna ta miqe ta fita ta bar ni a tsugune a zuciyata ina farin cikin ganin abinda nake tsoron akan Inna bai faru ba, don haka duk wani abin da zai faru to ni kam in dai a kaina ne zan yi haquri da shi.
Ke kuma Humaira bar min gidannan tunda ba kya jin maganata tafi duk inda ki ka ga dama na bar musu ke.”
Na fito gida sanye da jiqaqqen hijabina ina kuka saboda ban tava tsammanin irin hukuncin da Babana zai yi min kenan ba, na kora daga gida, na xauka dukana kawai zai yi ya bar ni in yi zamana tare da Innata.
Gidan Baba Yahaya na tafi baya nan a gida don haka nayi zamana kamar yanda Baba Hairan ta umarce ni. Bayan na gama rattaba mata bayanin komai. Ai kaxan ya fara gani in dai bai yi himma ya gyara lamarin cikin gidan shi ba. Ci abinci kije kiyi wanka in kin gama kije ki duba cikin kayan ‘yan uwanki ki zavi wanda zai yi miki daidai.”
Na ce “To” ban san yanda aka yi ba ina zaune ina shafa mai ta juyo ta kalle ni, Salati mai tsanani naji ta saka wannan wane irin tabo ne haka a jikinki? Na xan yi murmushi na sake zubawa tabon ido ina qarasa vare waxanda basu varu da kyau ba wake yi miki irin wannan duka Humaira?”
Na sake wani murmushin kafin na ce mata, Mama da Babanmu, ta ce tirqashi, taja bakinta tayi shiru. Baba Yahaya kuwa yana dawowa ta kai ni gabanshi ta mayar mishi da bayanin komai yayi min faxa sosai akan danben da aka ce mishi nayi da Zubaida kafin yayi tsaki ya ce, kai Alhaji Surajo lamarinshi sai shi.
Gida ba doka ba oda? To ya ya za’ayi a zauna lafiya? Baba Hairan ta ce, ai duk Mama ce ta dama gidan nan, kalli jikin yarinyar nan ka gani ta matso tana qoqarin kwaye rigar dake jikina, wai yaga tabban, ni kuwa ina qi saboda qirjina cike yake da nonuwa na riga na shekara goma sha shida.
“Barta kawai Hairan, ai na riga na san komai babu wani laifin Majadan da nake gani, nashi yafi yawa don shi ya bnar damar shi ta cewar shi ne Maigida mai wuqa da nama a hannunshi ya bar ta take yi mishi kwavar da taga dama.
Yanzu wannan abu da me yayi kama, ace ‘yarka tayi danbe da matarka ina alherin haka? Wa kuma gari ya waya? Sannan wai ya zartar da hukuncin korarta, to taje ina? In ban da tayi hikimar zuwa nan xin da wani wuri ta nufa da wa gari ya waya?
Kwanana huxu a gidan Baba Yahaya kafin ya dawo dani gida a dalilin wai Baban nawa yana nemana.
“Ka gyara zaman gidanka Alhaji, ka fita cikin wannan ruxani da ka sanya kanka kai da iyalinka, musamman ma ‘ya’yanka abin zai dame ka fa don in ba sa’a kayi ba zumunci zai yi wuya a tsakaninsu. Baba ya ce “To su wa zasu sha wahala? Ai sune qanana, ba shi ke nan ba tunda dama uwarsu da danginta ne basa so ayi zumuncin don su sake koya musu mugun abu suna qoqarin ganin sai sun watsa min haxin kan gidana.
Baba Yahaya ya ce, ai gidanka bai tava zama cikin haxin kai ba Alhaji, yau in da da fitina aka fara wannan zaman da wannan rikicin da sai ka ce to gara itama duk juyi iyayenta a tsaye suke akan zaman nata in ban da haka ai da tuni zaman naku ya zama labari kamar yanda na sauran matan ya zama.”
Ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min shiga gida Humaira kar in sake jin wani abu ya sake faruwa tsakaninki da wata mata musamman ma ita Zubaida, dukkansu iyayenki ne dukkansu ki rinqa girmama su saboda matan ubanki ne kin ji ko ba ki ji ba?”
Na ce mishi na ji, to in ki ka sake ni da kaina ne zan yi miki hukunci don ba zamu yarda ace ‘ya’yanmu ‘yanmata suna mana danbe da matanmu ba, wannan lalacewar ai ta kai in da dai.
Babana yayi kwafa alamar dai har lokacin yana cikin tsananin vacin rai game da lamarin.
A wannan lokaci mun shiga hali mai tsanani a gidanmu ban da maganar faxan da nayi da Zubaida wacce yaja ya tsaya kan shedar da Mama ta bayar ce gaskiya cewar Innan ce ta kwashewa Zubaida qafa yasa na kada ita.
Ita Innan da shi kuma suna cikin wani rikicin na zaman hirar da Babana yake yi a xakin Mama sai sha xaya ko sha biyun dare kafin ya shiga xakin mai girki.
Gari na wayewa kuma can wurinta zai sake komawa a dalilin wai ita tayi kyautar kwananta. Inna taja ta tsaya kan tunda ba ita aka yi wa kyautar kwanan ba, to kuma babu abin da zai tauye mata kwanakin girkinta.
Sai abin ya tsaya can a tsakaninsu ita da wacce ta yi wa kyauta kan haka dai nasan ta kulle mishi qofa yafi sau goma shi kuma yayi mata duka har sau biyu.
Rannan dai aka wayi gari Inna bata nan a gida babu kuma wanda yasan lokacin da ta fita. Mama da Zubaida sai maganganunsu suke yi a tsakar gida na nuna murnarsu kan abinda ya faru.
Ni kuwa ina xakinmu ina yiwa qannena hidimar da ta dace in yi musu don hatta Baba qarami bata tafi da shi ba, na gama basu kunun da na dama musu kenan Mama ta kira ni ta bani abin karyawar gida tana kuma zagina kan munafurci na da kuma ware qannena da wai nake yi ina nuna su kaxai ne nawa.
Har dai na koma xaki ban ji Zubaida ta tanka mata ba savanin da da itama kanta zagin nawa take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login