Showing 24001 words to 27000 words out of 32414 words

Chapter 9 - MIJIN TA CE BOOK 1

20 Aug 2024

4901

yi a yanzu kuwa ni da ita mun shiga taitai juna bana shiga harkarta ko xaga ido in kalle ta bana yi, itama bata shiga tawa ta kuma rage yiwa Inna irin hawan qawarar da da take yi mata.
Ina zaune a xakinmu ni da qannena su suna kallon katun xin (AVATAR) da na sanya musu yayin da ni kuma nake ta faman share-share da goge-goge kamar yanda kullum muka saba yi da Inna.
Can cikin zuciyata kuwa tunaninta nake yi itama ta tafi gidansu kawai taje tahuta da wannan wahalar da take ciki tabar mu kawai tunda mu gidanmu ne a cikin ta aka haife mu mu zauna muyi ta shanta amma kuma da na tuna yin hakan yana nufin ba zamu sake zama wuri xaya da ita ba sai kawai na ji hawaye suna gudu a idona.
Babana ya shigo xakin ya same ni ina kuka ya yi kamar bai ga kukan da nake yi ba ya ce min, “Yauwa ki kula da su kin ji ko?” na ce mishi “To.” Yasa hannu a aljihu ya ciro kuxi ya bani ya ce, ki voye wannan in kuma buqatar wani abu ki sai muku na ce mishi to.
Har yayi kamar zai fita sai ya sake juyowa cikin murya qasa-qasa ya ce min, ina Innarku ta ce miki zata tafi? Na ce bata gaya min ba, na ji kukan Baba qarami ne kawai na fito na gan shi shi kaxai a kwance.
Kwana biyu a jere babu Inna babu dalilinta, an neme ta gaba xaya bata nan. Bata gidan mai babban allo bata gidan Alhaji Mai kuxi yayinta maza da mata duka an je bata nan gaba xaya hankula suka tashi ko ba a gaya min ba kuwa nasan Babana yana cikin waxanda suka fi kowa damuwa.
Don na ji yana cewa Mama abin nan kamar wasa fa an nemi Binta ba a ganta ba, ta yamutsa fuska ta vata rai ta ce ai sai kuyi ta nema abinda dama take so kenan da yake ku kuma kun iya xaurewa qarya gindi in ba haka ba yarinya ce qarama balle ace ta vata?
Tayi maza ta riqe baki ta ce, au, haka fa in ba a yi neman da kai ba, Alhaji Mai kuxi ga kuma munafukin abokinka, taja bakinta tayi shiru, zuwa can ta sake cewa ai ace ma kana da tsayaiye da daxi sai kayi ta dama tsiyarka yanda kaso dole a qyale ka ayi ta bi in ba haka ba ai ina? Ta sake yin shiru, shima ya tashi ya fita ya bar mata gidan.
Kwana biyar da barin Inna gida na fito da safe ina goye da Baba qarami don ko Ali ya da Atika baya yarda su tava shi sai ni, a qofar gida naga Babana yana tsaye naje zan wuce shi tunda dama naje na gaishe shi.
“Zo nan Humaira.” Da sauri naje na same shi na ce mishi, gani Baba. Ya yi kamar zai fasa gaya min maganar da zai gaya min xin sai kuma ya ce min yanzu in na shirya zanje wajen maganar Innarku.”
Da sauri na ce mishi Baba an ganta ne? ya ce eh, dama ashe tana can ne sabon gidan Alhaji Abba dake can bayan (C.B.N Quarters) can ya kaita ya voye ta kin san dama ba wani mutunci ne dashi ba tunda ya wayi gari ya gan shi da kuxi a hannu na lura yana yiwa mutane kallon banza na fitar harkarshi.
Kin san kuxi a hannun yaro in ba mai natsuwa ba ne sai ya shiga aikin rashin hankali da wulaqanta na gaba dashi, don ko gidan nan da yake zuwa wurin Innarku ba gaishe ni yake yi ba sai in ta qure mun yi kacivis dashi.
Shi yasa ma nake ganin tunda shi ne mai xaure mata gindi take yi min iya shegen da take yi min to ina ganin zan haqura da ita ne kawai don in samu ma gidana ya zauna lafiya musamman ma da yake Mama tayi min alqawarin zata kula min da ku.
Na kalli Babana na ce mishi, to Baba Allah ya zava mana mafi alheri, na wuce shi na tafi.
Da daddare har na turo qofa na rufe na kuma kullewa Inna qofarta da take kwana bayan na kintsa shi na kuma tattara duk wani abu mai daraja na shigar mata ciki, gaba xaya sun yi barci nima abin da ya hana ni kwanciya ina damawa Baba qarami kunun da zan ba shi ne in ya tashi cikin dare.
Sai kawai naji ana tava qofa nayi maza naje na buxe, Innata na gani. Tsalle nayi ina ihu na qanqame ta. Mama ta leqo da sauri ta ga abinda ke faruwa, ta ce au kece ki ka dawo?
Ta ce, eh mana ina wuni? Bata tanka mata ba ta juya gun Babana wanda nima sai lokacin na gan shi a tsaye a tsakar gidan ga alama dai tare suke, ta ce mishi uhun ai dama tunda naga ba ka dawo ba na ce kana can wurinsu.
Gaba xaya suka rurrufe mishi qofa ya dawo xakin Innata wanda ban so hakan ba, naso ace ya yi zamanshi a can don nima in samu in shaqi qanshin jikinta da na daxe ban ji ba.
‘Yan kwanaki kaxan xin da Inna tayi bata gida har ta xan canza, ta yi girkinta na kwana biyu ta fita cikin kwanakin kuwa Babana baya hirar dare a xakin Mama iyaka dai ya shiga da safe su gaisa kamar yanda yake yiwa kowacce sai kuma da rana in ya dawo, nan ma nanne wurin zamanshi.
Amma da daddare yana shigowa daga Masallaci in anyi sallar Isha’i wurin Inna yake shigowa, Mama kuwa sai yada maganganu take yi shi kuma in ban da harara da tsaki babu abin da take yi mishi.
Kwana biyu da dawowar Inna Hajiya ‘Yar dubu tazo gidanmu ina xakin Mama ta shiga suka gaisa ta fita ta nufi wurin Innata tana barin xakin Mama ta kalli Zubaida ta ce mata wani maganin uban ya sake bayar wa a kawo mata duk zanci abu kazansu ba dai da ni suke yi ba.
Na tashi nima na fito xakinmu nazo don in qara gaida ‘yar dubu sai na same ta tana cewa, Inna wannan hanqoro da ake yi na kashe miki aure fa ba gata ba ne.
Da ma kin yi haquri kin zauna a xakinki kin daina kai qara da faxin maganganu da ya fiye miki daraja yanzu irin maganganun da wannan yaron yayi ta gayawa mijinki da ya zuciya ya ce ya haqura da wa gari ya waya?
Duk wani gatan da za’ayi miki yanzu ya wuce ayi miki tattalin yanda za’ayi ki zauna a xakinki tare da ‘ya’yanki? Ke mai ‘ya’ya mata? Huxu ne fa dake a jere ga su nan reras, don ma sauran babu kuma don zafin rai irin naku na ‘ya’yan yau da ba a gaya muku gaskiya xanki mai wata bakwai da za ki tafi ai sai ki goyo abinki ki tafi dashi.
A’a ke ga mai zafin rai kin ajiye shi kin tafi to dube su shi da wacce ki ka bar wa xin yanda suka zama, su ‘ya’ya in gaya miki in suka kintsu suka zama mutanen kirki ne suke zama na kowa da kowa, amma in suka lalace to na mai su ne shi kaxai.
Dama kin yi hankali kin yi karatun ta natsu ki gane vata kanki da baqin kishin gidanku ya kamata kiyi ba ta waxannan yaran ya kamata kiyi ki tsaya kiyi musu tarbiya ki tsaya musu da addu’a, Ubangiji ya raya miki su ya kuma basu mazan da za su riqe su.
Shima wannan yaron Mallam yana nan yana jiran shi don Alhaji Yahaya yaje yaga yawa Mallam irin baqaqen maganganun da ya rinqa gasawa mijinki sakaryar yarinya kawai shashasha mara wayo.
In sake jin kin kai wata magana can gidanku za ki gamu da ni, in kina da matsala ki kai wurin Mallam Yahaya tunda ba shi da wani daban a cikinku, ta tashi ta fita ta bar Inna tana ta faman kuka, nima jikina yayi sanyi.
Can cikin zuciyata na xan ji tausayin Baba karo na farko da na ji hakan a game da shi, ko waxanne irin baqaqen maganganu Alhaji Mai kuxin ya yi ta gasa mishi oho.
A wannan lokacin sai na samu kaina da jin tausayin Babana, maimakon tsananin jin z afin shi da da nake yi, a yanzu sai na gane ma fi yawancin abubuwan da suke faruwa a gidanmu ba sonsu yake yi ba, illa iyaka dai ba shi da yanda zai yi an riga an sha gabanta.
Ta haka sai na koyi daina ganin anyi abu in gayawa Inna in ta ganan wa kanta kuma in bata haquri in naga da Babana a cikin abin kuma in ce mata kar kiyi faxa dashi Inna daina gasa mishi maganar da zata vata mishi rai.
Kinga dai kin hana shi hirar xakin Mama ya daina duk da tsananin hakan a wurin shi tunda kina jin irin habaice-habaicen da take yi. To qyale shi haka komai yayi, kiyi haquri ta ce min to.
Ta haka sai Inna ta riqe kwanakin girkin ta guda biyu sune nata in ta shige su zata yi komai don farantawa mijinta in ta fita kuma bata sake xaga ido ta kalli Baba balle har ta gane wane abin haushin yayi?
Gashi tunda muka yi wannan tsiyar da Zubaida tana shakkar gaya wa Inna magana, sai dai kuma wani abin can daban, don haka har yanzu Mama bata gamsu ba daina zuwa hira xakinta ran girkin Innata ba qaramin tayar mata da hankali ya yi ba.
Ban san yanda aka yi ba sai kawai gani nayi Babana ya sake taso ni a gaba kan maganar gaida Zubaida, Inna ta ce min rinqa gaishe ta na ce mata to. Kullum zan tsaya a qofar xakinta in gaishe ta ko kuma a tsakar gida, wata ran ta amsa wataran tayi kamar bata ji ba.
Rannan na fito daga xakinmu da safe naga Mama da Babanmu akan qatuwar tabarma sun haxu har da Zuwaira suna karyawa. Na tsuguna na gaishe su dukansu har na miqe zan tafi sai Mama ta ce. “Humaira mai gaisuwa yau da yake da Babanku a wuri ita ma Zubaida ta ci arzikinshi an gaishe ta.”
Nan da nan Babana ya tunzuro ai bata gaishe ta ko? Mama ta ce uhun to ai gata nan kusa da kai menene na tambayata ni? Ya juya wajen Zubaida da tanbayar ta gyaxa kai ta ce mishi eh.
Nan da nan ya shiga banbami yana faxin za ki gani zan nuna miki duk abinda ki ke yi ina qyale ki ina yin hakanne kawai don kaina ba don tsoron wani ba, ba kuma wani ne yake sa ni nake yin abinda nake yin ba, don na ji ana cewa wai ni bana amfani da ra’ayina sai na wanda aka tsara min.
Akan gaida Zubaida ne aka kafa min dokar da ta hana ni zuwa Makaranta gaba xaya tun daga ta boko har zuwa ta allo saboda wai ina qarasawa can gidan su Innata wai kuma a can xinne ake koya min mugayen halayen da kullum nake fitowa da sababbi.
Ko ba a gaya min ba ni na san Mama ce tasa aka hana ni zuwa Makaranta daga baya ma aka ce an cire ni don dama tunda muka zo aji biyar muka yi jarrabawar kwalifayin aka ce ni kaxai ce naci, ni kaxai ce Gwamnatin jiha zata biyawa jarrabawar (WAEC) da (NECO), su su Habiba da Suwaiba sai dai in iyayensu sun matsu da su rubuta su su biya musu ko kuma su sake maimaitawa zuwa baxi.
Ta sanyawa karatun nawa qahon zuqa ta tsani ganin na shirya zan tafi Makaranta tunda su su Habiba sun daina zuwa sun ce son kai aka yi musu saboda Malaman namu sun san Mallam mai babban allo.
In tsaya cewa nayi baqin cikin hana ni karatuna ma vata lokaci ne kawai tunda ina son yin shi Inna ma tana so in yi gashi yazo qarshe aji shida nake.
Inna ta kalle ni ta ce, to ke ki rinqa sammakon zuwa gaishe ta a gabanshi mana don ya yarda kina gaishetan, ya barki ki rinqa zuwa karatunki. Na ce ba zan sake gaishe ta ba Inna ya hana ni yin karatu don na daina gaida ita in rayu cikin jahilci shi kenan ina ce sai buqatarshi ta biya.
Tayi maza ta ce hauka kike yi ne da kike gaya mishi irin waxannan maganganun, naja bakina nayi shiru illa iyaka ban iya hana hawayen da ke zuba gudu a idanuna ba, Inna tayi tayi in canza daga matakan da na xauka na daina gaida Zubaida har Maman ma sai in jera kwana biyu ni ba ta ga idona ba.
Rannan ina jin ta tana cewa wata qawarta muu ai ta riga ta riqa, kin san ita ‘ya mace in ta riga ta xanxani garxin namiji to shi kenan rashin kunyarta sai ta buwaya.
Qawar tata tayi dariya ta ce, Mama kenan wannan wani namiji ta sani? Rashin kunyar ‘ya’yan yau dai kawai, da in suka riga suka fara girma sia kaga kamar menene? Balle wannan ja’irar yarinyar da kullum ka ganta ka ra kyau take yi tanfar wata mai rikixa.
Ai da gani ake tanfar qannenta za su fita, amma kin gani da yake dai kawai shi mai kyau to Allah ke ganin dama ya yi shi, ga kuma uwa uba tsabta da iya kwalliya.
Mama ta ce uh, ai ku ku ke qara zugata amma in ba zuga ba to wa tafi kyau cikin yaran gidan? Nan in da kike ganinta ma lakaci guda xaya bata dashi in dai na kirki ne to ina kyau yake?
Abinda kullum ake yi min gori dashi kenan rashin saurayi shekaruna goma sha bakwai a dunmiya amma ban tava saurayi ba ko a gida ko a hanya wani bai tava tsare ni ya ce min ke ‘yanmata ji mana, wa sunanki, sonki nake yi ba a tava yi min hakan ba sai dai in ga sa’annina da ma waxanda ba su kai ni ba da yawa ma nafi su kwalliya dama kayan kwalliyar don ni xin ma’abociyar ado ce da kuma kayan adon saboda Hajiya Kubra da dangin Inna da suka maida sai min kayan kwalliya tanfar ni kaxai ke gare su.
Ko da Babana ya daina hirar dare a xakin Mama ran girkin Innata hakan ba yana nufin babu matsala ba ne, a’a suna nan birjik basa ma lissafuwa, babba daga ciki dai akwai minxira mana abincin da Mama ke yi kusan kullum a cikin neman abin da zamu ci Inna take.
Babu kuma halin Mama ta xora tukunya itama ta xora ba ma zai yiwu ba, don haka sai dai ayi ta kame-kame, gashi kuma wai Mama ta ce sun yafewa Babana hidimar qanana-qananan abin buqata na gida dangin su omo, sabulun wanka da na wanki.
Man shafawa har su kayan Sallar yara saboda wai hidima da nauyi sun yi mishi yawa, kowa ya yi wa ‘ya’yanshi kan hakanne yasa Inna ta ce to ko za a rinqa yin wadataccen abincin da yara zasu rinqa qo shi.
Tun kafin Babana ya yi magana Mama tayi, Mama ta ce ai yanzu nan duk irin abincin da ake yi a gidan nan yara sun ce miki basa qoshi? Tirqashi, ina yaran suke? Su zo nan su gaya min su wanene ba sa qoshin?
Yanzu ashe a irin qoqarin da Alhaji ke yi na ganin asiri ya ruhu har da wani mai qorafi akan abinci? Baba ya ce, ai Binta kam akwai qorafi akwai mita, akwai fitina. Ta dai ce ga abinda aka yi mata yauwa! Ko ga abinda ba ta yarda dashi ba uhun!
Mama ta ce, to kaga, maimakon suzo suna yawo dakai a gari suna vata maka suna tunda su zuriyarsu bata rufin asiri ba ne raba girkin nan kawai kowa ka ba shi nashi. Baba ya ce, a’a ai sai dai suyi abinda zasu yi amma ba zan raba girkin gidana ba.
Ta ce, ai kuwa da ka raban da yafi maka ni da Zubaida muna haxe tunda ita ai ba mai matsala ba ce, tunda tazo gidannan ka ji tayi da wani in ban da su da suka matsa mata? Ya ce haka ne, ta ce to ware ka bamu namu itama ka bata nata taje tayi tayi tana baiwa ‘ya’yanta suna ci suna qoshi.
A haka aka raba girkin gidanmu, Inna ita da ‘ya’yanta su kuma girkin su yana haxe ita ce kuma mai yi tun daga ranar da aka raba girkin kuma ya zama komai Babana ya kawo tanfar wawashe shi ake yi.
Tun daga hatsi zuwa kayan haxin, Babana da komai suyo shi yake yi ya ajiye sai aka ba shi shawarar daina sayen komai wai ya rinqa bada kuxin kawai ya kuma yarda kuxinsa biyun namu duk da ba ninka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login