Showing 12001 words to 15000 words out of 32414 words
da ta wanke a daidai lokacin da Anwamu ke cewa, ni fa ba kyanta ne yafi komai qona min rai ba, game da ita uh’uh, tsabtarta tafi komai vata min rai.
Mace mai tsabta majadan ke da mummuna ce jan hankalin miji ne da ita, to balle wannan shi yasa na ke gaya miki daina barin yaran nan suna tara miki kayan dattinsu a xakinki kowacce ta tuve to ta wanke kawai.
Ta xan ja tsaki kaxan kafin ta ce uhun, ai mazan nan suna qwararmu. Sai da suka ga mun fara kaiwa inda muka kai sannan suka xebo tsala-tsalan ‘yanmata ‘ya’yan cikinsu suka kawo mana, yanzu wannan in ka ce zaka sa wa miji ido a kanta ai sai ranka ya vaci.
Shi yasa ni a gidana har sayar mishi da girkina nake yi, ko in bashi kyauta ta cikin hikima kuma in san yanda nayi na fanshe ta wata hanyar, tunda in ya kwana wurin nawa ma menene? In ban da kayan vacin rai.
Mama tayi maza ta qyalqyale mata da dariya, ta ce tafxijan ai ba zan iya irin wannan sakarcin naki ba. Ta kwashe bayani tsab na sabon tsarin da ta kawo a gidan na cewar mai goyo bata da miji bata kuma da girki saboda xawainiyar goyonta.
Hajiya Anwamu ta ce, anya Majadan a hakan kuwa ake har yanzu? Qwarai kuwa, in ji Mama, ai tunda ta haifi ‘yar nan har yanzu ban vata girki ba, shi kuma kin san ba ma mai irin wannan fitinar ba ne, da dai an yi.
Amma yanzu ko harkokin cuxewar kasuwar nan da ake ciki ai ta isa ta hana mazannan namu kuzari.
Anwamu ta ce haka ne jimawa kaxan ta sake waiwayawa ta kalli inda Inna take zaune tana taje gashin kanta data gama tsefewa ta ce uhun, ni kam da za’a bar ni da na ce yarinyar nan ciki ne da ita.
Mama ta zabura da sauri alamar kaxuwa ta ce ciki? Kai haba wane irin ciki to a ina ma ta gan shi? Ita ba fita take yi ba balle in ce suna haxuwa a wani wuri shi kuma ba dawowa gida yake yi ba in bana nan tunda ai ko da nake fita unguwa da yaran don bana barin su balle ace sune zasu yi girkin dana bari ai kullum ina tambayar Ado da bana nan kun zo gida ne?
Sai ya ce min ni dai nazo na kawo cefane Inna ce Alhaji fa? Sai ya ce a’a shi bai lura ba.
Cikin zuciyata nayi mamakin jin yanda duk da baiyananniyar qiyayyar da ado ke yiwa Innata ya qi yarda ya gayawa yarshi gaskiyar abinda yake faruwa tsakanin Innan da mijin su in bata nan.
Mama ta sake kallon Aminiyar tata ta ce, mata ai kin san ita xin bata rabo da shafe-shafe kullum a cikin shi take shi yasa nake cewa ita xin ba wata fara ba ce mai ne kawai ya maida ita haka.
Hajiya Anwamu ta ce, to ba zan yi miki musu ba, amma ni dai nasan matar da aka hana miji ya kama hannu tsabtarta da ban take da irin ta wannan yarinyar.
Kalli kyan kitson da ta tsefe ke da kike da mijin kalli kitson da yake kanki. Cikin zuciyata na amince da cewar ita Hajiya Anwamu mata ce mai auna komai a mizanin hankali, don kuwa ni da kunnena nasha jin Babana a irin ranakun da yake dawowa wurin Inna in Mama bata nan yana cewa Inna.
Nafa ga ji da ganin wannan kitson a canza min shi a kuma zizara min lalle in gani in xan ji daxi, wani lokaci ma zan gan shi yana vata kuxi masu xan auki yana cewa ki sayi sabbin under wears ki kuma bada sabbin xinkuna tunda nasan kina da zannuwan da ba a xinka ba.
A duk lokacin da yayi irin waxannan maganganun kuwa to ko da bata tanka mishi ba, to zaka ga tayi abinda yace xin, za kuma ta nuna mishi in an kawo.
Don haka nima na yarda yawan kwalliyar Innata har da yawan kulawar Babana na voye.
To sai dai ita Mama duk da wannan hannunka mai sanda da aminiyar tata tayi mata don ta lura tasa ido ko zata yi sa’a ta gano abinda ke gudana ta qi yarda ta mace to taja ta tsaya kan cewar ai shi Babana ba ma zai kwatanta wani abu makamancin abinda ake za ton ba, don yasan karonsu da ita.
Ban da haka ma ta riga tayi sa’a ba abinda yake gudu irin vacin ranta in ban da haka ai da zama da waxannan bai zamo mai sauqi ba a wurin kullum fa sai tsohon nan ya zo gidannan wai yazo ganinta sai kace shi kaxai ne ya haifi ya a duniya.
Ai kin san dai ba haka kawai yake yi mana wannan zaryar ba.
Hajiya Anwamu ta riqe baki nuna alamar mamaki ta ce ai fa kam da walakin wai goro cikin miya, kin kuma san shi fa duk ‘ya’yanshi da jikokin shi da ake aurarwa inda duk suka je ai karve gida suke yi in ban da nan xin.
Mama ta gyaxa kai alamar jin daxin cewar da aka yi ita kaxai ce ta gagara.
Mama da ‘ya’yanta sun qi sun kuma tsani ace wai ni xin kama da Babana nake yi, balle ma ni yayi suvutan baki yace ai duk gidan nan babu mai kama da Alhaji Surajo irin Humaira sai kaga ta taso da faxanta kuma da iyakacin gaskiyarta faxin zata yi rai a vace tana faxin wannan ai wulaqanci ne.
A ce duk ‘ya’yan da aka haifa a gidan nan ba a samu mai kama da Alhaji ba sai akan wannan mummunan yarinyar, to ta ina kamannin nasu yake? Ku nuna min don in gani.
Duk da wannan baloqoqo da zare ido da Mama ke yi don hana faxin kamannin nawa da mahaifina su can wurin dangin Inna sun dage kan wai ban xauko komai na Mahaifiyata ba, har ma basa gajiya da bayar da labarin wani abinda ya faru sanda Innan take goyona suyi ta dariya.
Wai ana hidimar aure ne a gidan Alhaji Mai kuxi sanda ya auri amaryar gidan ta yanzu Furera Jama’a sun cika sai aka shigo dani ana tambayar ina uwar wannan yarinyar take?
Mai tambayar qanwa take wurin mai babban allo, don haka Inna tayi shiru tana kallonta bata ce mata gata ba. Sai da Hajiya Kubra tazo wucewa taga abinda ke faruwa shi ne ta kalli Inna tayi mata dakuwa, ta ce shaqiyancin banza kina kallo ana tambaya ina uwar yarinya ba za ki sa hannu ki karve ta ba sai kiyi shiru kina kallo?
Sai a lokacin ne mai tambayar ta kalli Inna ta ce yau ga abin mamaki, Binta ce ta haifi wannan baqar yarinyar? Gaba xaya aka kwashe da dariya tayi murmushi ta ce Ubangiji ya rayata ya kuma sa mai albarka ce aka ce amin.
Ko kaxan ni xin bana kama da mahaifiyata, don kuwa yayin da Inna take fara sol, ni xin baqa ce. Inna mai dogon gashi ce ni kuwa gashin kaina matsakaici ne sai dai akwai laushi da santsi da kuma cika kai.
Inna dara-daran idanuwa ke gare ta, ni kuwa nawa madaidaita ne, sannan ita siririya ce ni kuma ba ni da jiki bani kuma na ma xarata tsayi kaxan, to amma duk da haka su Mama sun ce Inna ba da ita nake kama ba, to a danginta na samo kamannin nawa.
Rannan muna kwance kan gado xaya ni da Innata yayin da su Atika da su Aliya suke xaya xakin nata donni kam duk in da Inna take ba na iya barin wurin ko da kuwa Babana yana nan sai in shi da kanshi ne ya kore ni.
Kan hakanne mutanen gidanmu suka qulla mata sharri har ya bazu mutanen waje ma suka ji wai duk cikin ‘ya’yanta tafi sona har ma wai bata haxa son nawa da na kowa.
Ni kam cikin zuciyata cewa nake yi aniyar kowa zata bishi, in ma mai faxan yana faxa ne don ya haddasa mata matsala cikin ‘ya’yan nata mun san duk xaya muke a wurinta.
Inna kamar ki bani gashin ki tayi maza ta juyo ta kalle ni cikin yanayinn murmushi ta ce na ki fa? Na xan yi magana cikin natsuwa na ce ai nawa ba mai yawa ba ne irin naku ke da su Atika, su kam sun ji daxi kama dake suke yi.
Su masu kyau farare sol-sol ni kuma baqa mumm….kan in qarasa tayi maza ta xaure fuskarta nima nayi maza nayi shiru waya ce miki baqi muni ne?
Ta zuba min ido tana kallona, sannan ta xan saki fuska kaxan ko kaxan baki da muni ba kuma zaki yi ba, ko kin ji ana ce miki mummuna kar ki sake damuwa ki dai kuxura ranki cewar za ki natsu ki zama mutuniyar kirki mai kamun kai da natsuwa.
Mai girmama na gaba da ita, mai jin maganar iyaye, mai maida hankali akan karatunta mai jin tausayin qannenta, kin ji ko?
Nayi maza na ce mata to Inna, ta juya ta ci gaba da kwanciyarta zuwa can sai naji ta ce min, kin fara girma yanzu kuma ke xin mai manyan varage ne, amma duk da haka ina so kiyi karatu tunda ni ban samu damar yi ba, don haka kar ki yarda ki kula kowa kiyi karatunki kawai nace mata to.
Yawan maganar karatu da Inna kiyi min yasa na zamo ko a bani kuxin Makaran ta ko kar a bani to zan taka da qafata in tafi Makarantar secondary ta qofar fada inda muke karatu.
In na tashi kuma sai in qarasa gidan Malam mai babban allo in ci abinci in huta in na yi Sallah in zo gabanshi in biya karatuna na Alqur’ani da kuma littattafan sannan sai ya bani kuxin mota in shiga in dawo gida.
Kan hakan ne Mama take cewa Babana wai ba ina zuwa makarantar don nafi kowa son karatun bane a’a ina zuwa ne saboda gidan mai babban allo, su kuwa su Habiba ba su da kowa a wurin shi yasa suke fashin zuwa.
Rannan na dawo gida daga Makaranta da yamma babu kowa cikin gidan sai Innata sai kuma Babana shi kuwa na san ya dawo ne a dalilin yasan Mama da ‘ya’yanta basa zuwa, nayi zan shiga falon Inna sai na ji Babana yana cewa kai kukan mata sai a barku.
Wato ashe duk ta sani a gaban nan da aka yi a kanki bin ta bai ishe ki ba? Ke kin fi so dai kiyi ta ganina cikin fitina? Ki voye ciki a jikinki wata bakwai ba za ki gaya min ba sai yau?
Alhalin kuma na tambaye ki yafi sau nawa in akwai shi ki faxa don a san yanda aka yi dashi tunda ina amfanin fitina?
Inna ta ce babu, to yanzu yaya za’ayi kenan? Ta sake ce mishi ai ban sani ba kai nake sauraro. Ya ce to kin ga ni bana son abin da zai tayar min da hankali.
Ina ganin asibiti kawai zamu tunda kema gashi ko yaye yarki baki yi ba, bata ma tafiya, uhun, sannan ana ganewa sai ace ba ki da miji amma ga ki da ciki yaya kenan?
Inna ta ce, kana nufin kenan a cire? Ya ce eh to kin san wani abin dole kan saka kayi shi ba don kana so ba, ni fitina ce bana so.
Ta ce, to ai sai ka gaya mata kawai cewar ba naka ba ne, yayi maza ya daka mata tsawa ta hanyar tambayarta wane irin zancen banza ne wannan?
Nan take ta soma kuka tana faxin ita ya maida ita gidan su ya taimake ta ya mayar musu da ita tunda ita bata da halin zuwa da kanta su barta ta zauna.
Inna ta urunce da kuka gaba xaya tana faxin ya mayarwa iyayenta da ita tunda akan tsoron kar matarshi tasan tana da ciki zai iya kaita wurin haluka hankalin Babana yayi matuqar tashi.
Ya shiga faxin ni Binta? Ni da bakina na ce ki zubar da ciki? Na ce muje a san menene abin yi? Nayi sallama a bakin qofar sau biyu kafin ya amsa na shiga ina wucewa zuwa xakinmu shi ma yayi maza ya fita wataqila dama zaman ya ishe shi.
Washegari kuwa da safe sai kawai ga qaton cikin Inna ya baiyana tanfar dai dama wani abu take sa wa tana xaure shi manyan riguna da hijaban da take sanyawa ma yau taki zani da riga ta saka da tayi wanka bayan ta gama kwalliyarta ta fesa turare ta kuma shiga zirga-zirga da kaiwa da kawowan da ta saba ba a xauki wani lokaci mai tsawo ba kuma na ji Mama tana wani irin firgitaccen salati a tsakar gida.
Wannan menene ki ke son nuna min shi Fatima? Ciki ku ka yi ban sani ba? Lalle yau za’ayi abinda za’ayi a gidan nan, dama cin amanata kuke yi kuna satar kwanana?”
Inna kam bata tanka mata ba, aikinta kawai take yi. Mama kuwa sai faman zuba ashar take yi tana faxin “Su Habiba su fita su kira mata Babanmu, duk inda yake.”
Inna ta bar tsakar gidan ta dawo xakinta tayi zamanta, na kuwa san in ban da tasan ba zata tava Inna ta kwana lafiya ba, da ta gwada yin hakan.
Rannan cikin dare ba mu san abin da ya faru ba, iyaka dai da sassafe naga Babana ya shigo xakin Innata, na ji shi yana ce mata “To buqatarki ta biya Binta kin nunawa Mama cikinki kin tayar mata da hankali, kin yi sanadin da tayi yaji ta bar miki gidan, shi kenan ko?
Inna ta ce, “Tana da gata ne tana da wurin zuwa ni da ba ni da wurin zuwan ba gashi…” yayi maza ya katse ta “Muje can xakina sai muyi magana.” Inna tayi maza ta ce wa? Tafxijan.
Rannan Baba ko tsakar gidanmu bai leqo ba, yana xakin Inna suna ciki su biyu gaba xaya hidimar gidan ni aka bar wa har abincin rana sai bayan Azahar na ganshi ya fito ya shigo wurin shi yayi wanka ya tafi Masallaci.
Da ya dawo ya ci abinci ne na ji shi yana cewa, “Bari in je kasuwar in ga abinda suke ciki.” Ta ce mishi “To, a dawo lafiya.”
Har washegari Mama bata dawo ba, a dalilin Babana bai je biko ba duk da aiken da aka yi na ana neman shi, gidanmu ya zama gwanin daxi sai murmushi yake yi yana hirarshi maimakon da da kowane lokaci fuskarshi a xaure.
Kwanan Mama biyu sai ga Baba Yahaya ya dawo da ita. Da alama shine yaje bikon ta kuma biyo shi duk da cewar da take yi shi xin munafuki ne.
Mama ta dawo gida cikin wani qarin zafin ita kanta dai kana kallonta kasan tana cikin vacin rai mai tsanani, ban da haka kuma kallo xaya zaka yi wa fuskarta ka gane ashe ba qaramin gumurzu suka yi da Baban namu ba kafin ta tafi.
A tsakar gida Babana ya zauna shi da Baba Yahaya da Maman suna maida magana, don Maman ce ta nemi ayi hakan duk da shi da ya kawo ta cewa ya yi to ni na tafi Allah ya kiyaye na gaba.”
Ta ce, “A’a ai gara ka tsaya ka ji abin da abokin naka yake yi.”
Mama ta maida bayanin komai dalla-dalla na yanda aka yi taga Inna da ciki alhalin ita xin bata da kwanan miji. Baba Yahaya ya kalle ta ya ce, bata da kwanan miji kamar yaya? Ta sake rattabo mishi wani bayanin har dai ya fahimci komai.
Sai dai maimakon yayi magana kan cin amana da zaluncin da ta ce anyi mata, na satan mata kwana a kai wa wata sai reshe ya juye da Mujiya.
Baba Yahaya ya soma yiwa Babana magana cikin vacin rai mai tsanani, ba laifin Hajiya Majadan ba ne duk abinda yake faruwa a gidan nan Alhaji laifinka ne.
Da ka kasa tsayuwa da qafafunka ka zama kaine mai zartar da hukunci a cikin gidanka. Yanzu ace an zartar da hukuncin hana ka baiwa binta haqqinta na kwana har sai ka saci jiki ka shiga wurinta don kawai bata girki?
Girkin me nene? Ita mace dole ne sai tayi girki kafin ayi aure da ita? Yarinyar nan guda nawa take da kake yi mata irin wannan zaluncin? Har yau xin nan fa bata cika shekaru talatin ba tana da shekara goma sha shida ne aka baka ita.
Yaya za’a rinqa gana mata azaba ana wulaqantata kana kallo?
Maimakon ayi maganar da zata zamo mai daxi ga Mama sai kawai aka shiga yin wadda haqurinta ya kasa jura, ta