Showing 15001 words to 18000 words out of 32414 words
shiga gaggayawa Baba Yahaya maganganu.
Ya kalle ta ya ce, ba laifinki ba ne shi ya bar ki ki ka zame mishi haka, da har ki ke ganin matarshi da ciki kina tuhumar shi yanda aka yi.” Yayi ficewar shi ya bar su nan a zaune.
Mama ta shiga bori da zage-zage, tana faxin wasu irin maganganu tamfar dai ba daga bakin babba mai shekarunta suke fita ba, Babana yana jin ta bai ce komai har lokacin mai tsawo.
Ban san yanda aka yi ba sai kawai na ji ya daka mata tsawa mai qarfi ya ce, “Ya isa haka. Ya kuma ishe ki haka kin gane?” abin mamaki sai kawai na ji Mama tayi xib, tayi shiru. Cikin zuciyata na ce, “A’a ashe dai itama tana xan tsoronshi ina ma dai ace kullum irin wannan tsawar yake yi mata da wasu abubuwan da yawa, ashe da bata yi su ba.
Babana ya shirya ya fita ya bar gidan, ni ma naci gaba da abin da nake yi ban san abin da nayi ba sai kawai na ji Mama ta zo ta fincike ni tana jana zuwa xakinta.
Tuni na saki kwanon dake hannuna ya faxi na shiga kuka ina magiya ina bata haquri, don kuwa nasan karonmu da ita a kullum nakan gwammace ta haxa ni da Babanmu ya buge ni duk da tsananin dukan nashi don shi duka kawai yake yi min baya shaqe ni.
Mama kuwa bayan shaqa ma sai ta ce sai ta hau kaina ta zauna.
Duk da magiyar da nake yi mata bata fasa ba, can cikin xakinta ta kai ni ta shiga gana min azaba tana yi kuma tana cewa wai ke ga shegiya ko? Na bar muku gida kuna murna ke da uwarki, to na dawo zan kuma yi maganinku.”
Gajiya Mama tayi ta qyale ni don kanta, babu wanda ya zo ya qwace ni, tunda ba ma kowa a cikin gidan in ban da Inna da sauran yaran gida, ita kuwa Inna ko meye za a yi min bata yin magana.
Da kyar na fito na dawo xakin Innata na kwanta ban iya fitowa ba sai wajen yamma. Ina fitowa su Habiba suka kalle ni suka kwashe da dariya suna faxin ta ji jiki ban kula su ba.
Tunda Mama ta dawo Babana ya sake kama fuskarshi ya tsuke tanfar ba shi ne ya wuni yana murmushi ba, jiya da shekaranjiya, yana dawowa ya shiga xakin Mama suka yi maganganunsu, kuma ya fito yazo ya shiga xakin Innata ranshi a xaure.
“To ai sai ki fito kizo ki xora abincin dare ko, ko shima ba za kiyi ba ne za ki bar mutane da yunwa kamar yanda ki ka bar su da rana?”
Inna ta kalle shi ta ce, “A’ah ni ce kuma mai girkin ba gata ta dawo ba? Ya yi maza ya ce, “A’a ba za ta yi ba karvi girkinki kawai tunda dai taimakonki da aka yi aka hana ki yin girkin ya zama laifi a kanshi ake kiran mutane azzalumai.”
Inna ta kalle shi kawai ta juyar da fuskarta gefe, bayan taja mishi wani irin mummunan tsaki, sai dai kafin takai ga gama tsakin nata yayi maza ya wafce bakin nata da duka.
A kixime nayi tsalle nayi waje ina qurma ihu, saboda razana. Inna da ta wuni cikin wani yanayi da na kasa fahimtarta za kuma a buge ta, ban san yanda aka yi ba na gan shi ya fito yana cewa, in ba za ki fito kiyi girkin ba sai a zauna haka, waye mai qananan ‘ya’ya a gidan in ba ke ba?
Rikici yayi yawa a gidanmu, gaba xaya an daina yin girki, Mama ta qi yi itama Innan ta qi. Gaba xaya gidan babu daxi, gaba xaya an shiga wani hali na wani yanayi.
Ni da kaina na qara shiga wani yanayi na tsoro saboda irin kallon da Mama ke yi min, Babana sai jin haushin Inna yake yi, yana faxin wai dama abin da take son ganin ya same shi kenan, shi yasa tayi abin da tayin gashi kuma ya ce ta karvi girki ta qi ta ce ba zatayi ba, tunda dama can ba a bata girkin ba sai yanzu?
Rannan da sassafe ya shigo xakinmu bai ma tsaya amsa gaisuwar da take yi mishi ba, ya ce mata, shirya kije gidan ku.” Ta ce, kai madallah, ya juya ya fita ni kuma na soma kuka yayin da ita kuma ta shiga shirya xakinta tana kwashe kayayyakinta masu daraja tana kai su xakin kwananta tana kuma gaya min abinda take so in rinqa yi wa qannena, ni kam ko amsawa ba na yi saboda kukan da nake yi.
Ta gama kintsa komai ta kulle wurin ta jefa xan makullin a jakarta sannan tayi shirinta tamfar wacce zata unguwa, ta xauki jakarta ban sani ba ko kukan da taga ina tayi ne ya sa ta ce min xauko min jakar muje ki raka ni sai kiyi sauri ki dawo ke Atika kar ku fita ko ina, suka ce to.”
Muka fito sai da muka yi wa Mama sallama bata wani amsa ba muka wuce muka fito qofar gida muka shiga Taxi zuwa gidan Alhaji Mai kuxi, sai dai savanin yanda ni da Inna muka zata cewar Babana ya ce taje gida ne da wata manufa ta barin gidan.
Ashe qararta ya kai wajen Alhaji Mai kuxin. Faxa mai tsananin Alhaji Mai kuxi yayi mata, tayi ta kuka bai kuma fasa yin faxan ba, haka nan bai bata wata dama ta cewa ga abinda aka yi mata ba.
Sai bayan fitarshi ne ta samu ta yi wa Hajiya Kubra bayanin komai, ta yi dariya ta ce ai in baka iya tsiya ba to ba ka yi wa kanka ba, ashe kema kin iya iya shege? To amma ai da ya baki umarnin karvar girki sai ki bi ba kema ki bijire ba.
Wato shi babu wacce zai tanqwasa ta tanqwasu kenan? Ba ki kyauta ba ai kin rama abinda tayi miki yaushe rabon Mama da yin yaji in ban da wannan karon?
Ki koma xakinki in kun je kuma ki ka samu bata xora girkin ba ke kuyi rashin girki a gida ai wulaqanci ne ta ce to, muka kamo hanya muka dawo gida.
Muna shiga xakinmu Inna ta ce min in je in gyara mata kicin, ban kuma san abinda ta tuna ba ta ce min ke dawo, taje ta kama aikinta da kanta, ta gama girkin aka kaiwa Mama abinci ta ce ta qoshi, suma su Habiba haka.
Ta gama komai ta kintsa ta dawo xakinta tayi sallar Magriba ta zauna taja carbi sai da tayi Isha’i sannan ta shiga tayi wanka ta fito ta shafa mai tasa su Atika suka je suka kwanta, mu ma muka hau gado zamu kwanta sai ga Babana ya shigo.
Fuskarshi a xan sake, yana xan dube-dube kina fa jin daxinki Binta, sai kawai ki kalelece jikinki da xakinki ki tasa ‘ya’yanki a gaba kuyi kwanciyarku cikin qamshi babu abinda ya dame ki da miji ba kya nemanshi saboda ba ki damu da shi ba.
In dai ‘ya’yanki suna kusa da ke to shi kenan zance ya qare, musamman ace ga Humaira, ta ce eh to su na mallaka sune nasan da wuya ace an yi nasarar raba ni da su a zihiri da baxini, amma miji fa?
In na qwallafa rai a kanshi ai sai in yi ta wahala tunda ba zan same shi a lokacin da nake so ba. Yayi murmushi ya ce, qarya kike yi ki ce in kin neme ni ba za ki same ni ba, ba ki neme nin ba ma ina kawo miki kaina duk da vata min ran da kike yi, ban tava bari kin rasa ni ba, wurina girki kawai aka hana ki amma ba a hana ki mijinki ba, kuma da aka hana ki girki da kwanan ai ba kiyi magana kin ce ba ki yarda ba, shiru ki ka yi nima na taya ki yin shirun.
Inna ta ce, kai dai ai sha’ani, ya ce to shi kenan ai sha’anin zance dai kuma ai ya qare, tunda gashi yau kin karvi girki ga ni kuma a xakin naki.
Ban san yanda aka yi ba wataqila sai lokacin Babana ya ganni a bayan Inna don tsawa na ji ya daka min ya kuma shiga yiwa Inna faxa, ina dalilin da take barina ina shigowa nan xakin ina kwanciya bayan ga sauran ‘yan uwana a can. Sum-sum na tashi na fita.
Tuni aka koma wani irin zama tsakanin Mama da Babana sai su suka san irin shi duk kuwa da cewar shi xin baya iya shiga xakin Innata akan idonta, ko da kuwa girkin nata ne, ko da daddaren ne ma yakan shigo ne bayan ya xan faki idonta.
Amma duk da haka bata gamsu ba tunda dai tasan yana shigan, a wannan lokacin bata da wani zance da ya wuce na kowa ya ji tuwo-tuwo da ita miya ya sha.
Ai wannan cin mutunci da aka yi mata in bata rama shi ba to ba iyayen da suka haife ta ne iyayenta ba.
Inna kuwa bata kulawa ko dama can kuwa ba xabi’arta ba ne tunka maganganun Mama sai in ya zame mata dole, haka nan kowane lokaci Babana ya shigo xakinta. Ba ta ce mishi don me?
Ko kuma sai yanzu? Sai dai kawai tayi amfani da wannan damar wajen ganin ta kyautata mishi kamar yanda Hajiya Kubra tayi mata umarni.
Inna tayi girkinta na kwana biyu ta fita girkin Ado ya kawo cefane babu alamar Mama zata karvi girkin tayi na fito daga xaki zan je aikan da Innan tayi min sai na ji Adon yana ce mata.
“Haba Mama, gidan nan fa ko an qi ko an so gidanki ne, yaya za ki rinqa yin abubuwan da kowa zai gane akwai matsala tsakaninki da Baba, kin ce za ki yi maganinta na ce eh, yana da kyau kiyi hakan to kuma sai kiyi ta qin yin girki?
Bayan kin san babu abinda Baba ya qi irin hakan? Yanzu wannan abin da ya farun ba murna suke yi ba? Kuma don kin ganta da ciki bata da kwana sai me? Sai ki xaga hankali?
Shi Baba fa ina ganin kamar in aka cika mishi ciki zai iya xaukar matakin da babu daxi, ki wastsake kawai ki koma hidimarki, ki sake kama mijinki, ki tattare abinki ki riqe kar kiyi sakacin da zata samu wata dama a kan shi, don haka kar ki bari yau mu dawo daga kasuwa ba kiyi girki ba, abin ba zai yi kyau ba in da hali ma sakwara za ki kirva don na ji ya ce min yana marmarinta.
Ki san yanda ki ka yi ku ka daidaita in yaso sannu a hankali sai kiyi maganin nata cikin ruwan sanyi daga ita har wannan mara kunyar ‘yar tata.
Nayi maza na kauce na bar wurin don kar su hango ni, Mama ta ce a kamo mata ni, cikin zuciyata na qara qin Ado na ce, ina ma dai Tanko aka sanya mishi ba Adam ba, tunda halin shi yafi kama da halin mata baya gyara sai zuga gashi da taya kishi maimakon ya zamo mai ba da haquri.
Kan in dawo daga aika sai kawai na samu Mama kace-kace a kicin tana aikin girki, naje na faxi aikan da aka yi min xin na zo na shiga kicin na soma taya Mama aikin girkin abincin daren da zata yi tunda in ba hakan nayi ba sai in shiga wani hali alhalin su Habiba ko suna kallonta ta nayi ba taya ta suke yi ba.
Ni kam bana iya qin taya ta don ina tsoron Mama ina kuma tsoron azabar da take gana min.
Tunda Mama ta shawo kan Baba suka daidaita sai kuma al’amura da yawa suka yi ta vullowa, a yanzu in tayi girki to xan qanqani take sawa Innata, mu ma ta xan minxira mana su kuwa su Suwaiba ta tura su xakinta ta zuba musu yanda suka ga dama in mun zo mun ce ba mu qoshi ba sai ta ce kuje ku sha ruwa.
Da yake an ce muku akwai wata baiwar uwarku a gidan nan da zata rinqa yi muku girki kuna wage bakunanku kuna xurawa, duk zaku ci uwa ku daga ku har uwar taku ba dai ta ce itama ita ce ba?
Ni da ku ne a gidannan ni kam tunda naje neman qari ta rattaba min wannan bayanin ban sake komawa ba, da na gane kuma Inna kan ba mu nata ne ita ta haqura sai na daina ce mata ban qoshi ba, suma su Aliya na hana su tunda dukanmu muna da wayon mu.
Rannann na farka cikin dare a firgice saboda xaxa min dukan da naji anyi, “Ke tashi ki koma can xakin.” Nayi maza na buxe ido jin maganar Hajiya Kubra, me kuma ya sake faruwa? Tambayar da ta zo cikin zuciyata kenan.
Sai kawai na ganta riqe da jariri sabon haihuwa, nan da nan na wastsake saboda sanin Innata ta haihu. Nan da nan na shiga murna ina farin ciki, Hajiya Kubra sai murmushi take yi alamar itama tana farin ciki.
Babana ya leqo “Sannunku da qoqari Hajiya.” Tayi maza ta ce, ‘yauwa sannu Alhaji.” Ya ce, “Babu matsala dai ko?” ta ce, a’a babu lafiyarta qalau haka nan xanta, ya yi maza ya ce na’am ta ce eh ai xa namiji muka samu gashi nan kamanshi xaya da Humaira, ya yi murmushi ya yi addu’a ya juya ya fita.
Mama ta turo kai cikin falon daidai Inna tana fitowa daga wanka ta ce, “ai ke kaxai ki ka haihu a xaki baki kira kowa ba? Lalle yarinyar nan kina jin wani abu.
Hajiya Kubra tayi murmushi ta ce, “Ba ita kaxai ba ce ina ciki.” Mama ta xan kaxu alamar bata san Hajiya Kubra tana ciki ba, ai kina ciki ne Hajiya? Ta ce eh, ai nazo suka shiga gaisawa.
Inna tana zaune tana shan kamun gyaxan da Hajiya Kubra ta dama mata, Babana ya sake leqowa babu wani abinda ake buqata ko Hajiya?
Tayi murmushi ta ce, a’a babu, tanfar dai ace gaskiyar Mama da ta ce Babana mai xabi’ar son haihuwar xa namiji ne, kusan ace mancewa yayi da Mama tana gidan ya shiga zirga-zirga da kai-kawo na sintirin ganin jariri da tanbayar lafiyar maijego.
Gari na wayewa dangin Inna suka kama zirga-zirgar kaiwa da komowa, da suka saba kan kace meye wannan sun cika gidan sai hidimarsu suke yi cikin farin ciki da annashuwa don ma dai suna tsoron Mallam mai babban allo don ya ce in suka sake zuwa gidan aka yi faxa da su to zai hana su zuwa in ban da haka da ba qaramin iya shege suka yi wa Mama ba.
Da Azahar rannan Babana yana xakin Mama nima ina ciki ina gyara mata farcenta sai kawai na ji ta ce mishi a qa’ida fa wannan xan ba naka ba ne, don kuwa shege ne tunda s atan kwana aka yi aka je gun uwarsa.
Nan da nan Babana yayi fici-fici ya vata rai ya shiga yin tsaki yana faxin wannan wane irin zancen banza ne? bai ma xauki wani lokaci ba ya tashi ya fita ya bar mata xakin.
Jego mai d axi Inna ke yi saboda Hajiya Kubra tana tare da ita, nan take wuni nan take kwana tana kula da ita da komai nata, Sa’adatu tana wurin Inna Balki tun ranar da aka yi haihuwar ta tafi da ita gidanta, gashi komai a wadace Babana yake bayarwa babu kuma halin Mama ta tauye shi.
Rannan ma ta shigo xakin saboda ganin jariri da uwarshi, ko sun tashi lafiya saboda sanin Hajiya Kubra na nan suna hira da ita, tana riqe da shi a hannunta sai kawai ta ce wa Hajiya Kubra mazan nan da ki ke ganinsu fa munafukai ne, ba su da gaskiya ko ta anini.
Tayi murmushi ta ce mata, ba duka ba ne, Mama ta ci gaba da yi mata bayani don ta gamsu da maganarta, har tana kawo mata misali da abinda ya auku na gidanmu, ta qare maganar tata da cewar to ko ke Hajiya ai ina ganin sai kin yi haquri da waxannan amaren naki yara.”
Hajiya Kubra ta sake wani murmushin kafin ta ce mata, to kin san shi haqurin iri-iri ne, kamarni kin ga amaryata ta farko sa’ar Binta ce, tunda an yi auren Binta da wata uku ne kawai ya yi nashi auren.
Shekara xaya da rabi bayan nan kuma ya qarato bana shiga harkarsu da mijinsu in dai bana sa zasu yi wani rashin hankali in tsawatar musu ba. To shima ya sani ya san na kame girmana, don haka yana bani girmana suma suna bani girmana saboda sun san mijinsu ba zai yarda su kawo min raini ba, tunda ban raina kaina a gabansu ba.