Showing 6001 words to 9000 words out of 32414 words

Chapter 3 - MIJIN TA CE BOOK 1

20 Aug 2024

4892

xaya ni da kaina jikina rawa yake yi.
Habiba da ta kasa haqurin kayen da aka yi wa uwarsu, ta sunkuto tavarya da gudu tazo zata rafkawa Hajiya Kubra, cikin kuskure da rashin dace sai kawai ta sake timawa Mama tavaryar a gefen fuskarta da iyakacin qarfinta, daga ita har Mama lokaci xaya suka qurma wani irin ihu mai tsananin firgitarwa.
Habiba tayi waje a kixime tana neman taimako. Hajiya Kubra tana jin za su shigo tayi maza ta xaga Mama dake kwance jina-jina ta sulale tayi ficearta, ta bar Mama tana yiwa makwabta rantsuwar Alqali ne kawai zai shiga tsakaninsu, su kuwa suna faxin “Abin dai kam bai yi daxi ba, a gefe kuma sai dariyar Mama suke yi don babu wanda bai san abin da gidanmu yake ciki ba.
Jinya sosai Mama tayi har da su zuwa asibiti, da su xaukan hoto duk rantse-rantsen da ta yi tayi na xaukan mataki da kai magana kotu duk ya tashi a banza, iyaka dai ta sake tasa Babana a gaba da fitina wai shi xin ya gajiya an shigo har cikin gidanshi anci mutuncin iyalinshi bai yi komai ba.
Kan haka har ta kira iyayenta suka zo suka sanya Babana a gaba ina jin shi yana mayar musu da bayanin yanda aka yi duka, su xin ma dai basu gamsu da shirun da Baban yayi ba, sun ce in yana haka a gidanshi ai sai ayi abinda babu kyau, duk da dai sun gaya wa Mama rashin kyautawarta kan cin mutuncin abokin mijinta da tayi a gaban mijin nata.
Tun daga rannan kuwa ban sake ganin Mama tana yunqurin dukan Inna ba, don Hajiya Kubra ta gaya mata in ta yi miki laifi ki faxa, amma duka tsakaninki da ita babu in kuwa ki ka yi ganganci ki ka yi, to nima zan yi miki irin wanda na iya, don ba baiwarki ba ce matar mijinki ce irin amfanin da kike yi mishi irinshi itama take yi mishi.
Ba kuma sai na ce miki yana sonta ba, tunda kina ganinta da ciki kina ganinta da goyo, don haka kin yi kaxan fitinarki ta rabata da mijinta.” Waxannan baqaqen maganganu na Hajiya Kubra sun sosawa Mama rai, don na ji ta tana nanata su a gaban Babana yafi sau nawa.
“Ni ina Humaira taje ne?” maganar da na sake jiwowa kenan daga cikin gidanmu, wacce tayi dalilin katse min tunanina, na dawo kan abinda nake ciki a lokacin baqin ciki da takaicin Mama suka sake lulluve ni, don kuwa kowa ya sani zan yi mu’amalla da Mama ne kawai bisa tsoro, amma ba don so da qauna ba.
Wannan dalilin ne ma ya sanya ni na zamo mai iya kwaikwayon Mama da al’amuranta duka babu wani abin da yake yin shi xabi’ar ta ne wanda bana kwaikwayon shi.
Ko a yanzu ma kuwa tsayawa nayi na shiga kwaikwayon maganar tata.
“Humaira.” Na’am, zo ga wanki, to na yi, Humaira, na’am zo ga shara, to nayi, Humaira, na’am zo ga aika, to na yi. Humaira, na’am zo…….”
“Mama ki ke kwaikwayo?” da iyakacin qarfinta tayi min tambayar, nayi maza na bar abinda nake yin cikin kaxuwa na zuba mata ido ina kallonta, tsoro ya bayyana a fuskata. Habiba ce yata da nake bi ta xakin Mama, wata ashirin ne tsakanina da ita, abinda kullum Mama take nanata gaya min kenan.
A duk lokacin da wani abu ya shiga tsakanin mu zata jaddada min ko sanda uwarki tazo gidan nan ta samu Habiba ne watanta goma sha xaya, ke kuwa wata tara daidai tayi ta haife ki, don kamar a hannunta ta shigo dake. Bisa wannan bayani da Mama take yi minne ya zama dole in yi wa Habiba ladabi da biyayya, irin wanda bata yi wa uwata xaya bisa gomanshi, tunda zata aike ni ta sani aiki ta yi min hukunci, ita kuwa tawa uwar bata isa tayi mata ba.
Sannan biyayyar da nake yi matan ban sa an sata tayi min adalci ba, wuni take yi tana jibgata da duka, ko da kuwa daga zaman cin abinci ne ko a wurin wasa, saboda Habiba na haqura da duk wani abin da ya shafi wasa, saboda yanzun nan zata rufe ni da duka, ko da kuwa ba da ita nake wasan ba, saboda rashin ‘yanci irin wanda nake ciki.
Ni har Suwaiba qanwar Habiba dake xakin Mama wacce ita xin na girme ta da watanni tara dukana take yi, ban kuma isa in ce zan rama ba, sai Mama da Habiba su rufan min suce wai cin zalinta zan yi.
“Mama ki ke kwaikwayo, za ki gama da gamonki kema kin san saura.” Tayi maganar cikin yanayin jinjina kai alamar wai zan ji jiki kenan.

Na zovara baki na vata rai sosai, abinda nayi ya bata haushi har ta kawo hannu da nufin buge min bakin nawa, nayi maza na kave hannun nata tare da faxin.
“A’a me nayi miki? Ban yafe ba.” Tayi maza ta sake kawo min wani bugun, nima na sake cewa “Ban yafe ba, muguwa kawai azzaluma.”
Ado ya leqo cikin zauren, “Kai kuzo nan Mama tana kiran ku.” Ado shi ne yaron da Mama ta xauko daga qauyensu ta kawo shi gidanmu ta ajiye, ita da Babana suka haxu suka maida shi xan gatan gidan, saboda irin son da Maman take yi mishi.
Qanin ta ne uwarsu xaya uba kuwa kowa da nashi, a wancan lokacin da ta kawo shi, shi xin ba kowa ba ne face wani xan dogon yaro xan siriri xan baki, xan bagidaje-bagidaje, kana ganin shi kasan daga qauye yake, ko gajiya da aiki bai yi, don ya saba yin wanda ya fishi.
In kuma aka cika mishi kwano da abinci ya cinye shi tas, amma sannu a hankali sai aka wayi gari Ado ya murje ya zama qosasshe ya zama wankan tarwaxa, ya zama xan gaye, ba zaka tava ganinshi ka gane bai daxe da fitowa daga qauyensu ba.
Kan kace meye wannan? Sai gashi ya zama santalelen saurayi saboda ya samu ya xare kan dukiyar Babana, ba wannan ne abin da yafi komai qona min rai ba, irin zuwa gidan mu da ya yi da takardarshi ta kammala karatun Secondary wacce ko credit xin da ake nema bai gama samu ba, amma ya gyara jarrabawar a gidanmu ya tafi (Federal Poly) yayi diploma ya sake dawowa ya shiga (A.T.B.U) yayi karatun digiri xin shi.
Amma gaba xaya nawa ‘yan uwan maza waxanda dukansu Maman ce ta haife su suna zaune a gida suna sakarci, sun qi karatu sun kuma qi tsayawa kan al’amuran Babana, su taimake shi kan harkokin kasuwancinshi sai Ado ne dai akan komai, amma wai Mama tana kallo hankalinta kuma a kwance bata da wata matsala.
Komai na gidanmu Ado ne yayi matuqar shiga ran Babana, bai gajiya da yabonshi, yanzu zaka ji shi yana cewa “Jarumin yaro ne mai tsayuwa kan al’amuranshi gashi kuma komai kasa shi zai yi maka.”
Mutanen da suka san gidanmu suka kuma san Mama da xan uwan nata sun san Mama da Ado sune babbar matsalar da Babana yake fuskan ta amma ba rashin kasuwa ba.
Sai dai ita Mama kullum takan danganta matsalar kasuwar Baban nawa da yawan aure-auren da take cewa yayi, musamman wai auren shi na baya-baya wanda aka rufe mishi ido yayi ta kwasar dukiyarshi yana bayarwa.
Tun farko zuwan Ado gidanmu ba wani jituwa nake yi da shi ba, saboda bai tava shiga harkar Innata ba, bai tava samun lokacin xaga ido ya kalle ta ba balle ya samu na lokacin gaisheta, haka nan ‘ya’yanta bai mu’malla da su iyakar shi Mama da ‘ya’yanta.
Don haka nima sai na zamo bana kallon shi, bana shiga harkokin shi, bana gaishe shi, bana sauraron shi don nima bana son shi.
Itama Mama mai ‘yan uwa ce da yawa, sai dai duk jama’ar da suka santa sun san bata wata mu’amalla ta ku zo ku gani da kowa sai da ‘yan uwan da ta haxa uwa da su, bata damu ba ko uwa xaya uba xaya ko uwa kawai in dai uwa tana ciki to shi kenan.
Bisa wannan ne ma ta zamo ‘yan uwanta na wurin uba ba kasafai suke zuwa mata ba, saboda komai nisan garuruwansu da suka baro bata yarda baquntar su ta wuce ta kwana uku sai ka ji tana yada magana tana faxin da aka ga ka zama mutun ne fa ake nemanka, amma kana qarami menene ba ka gani ba?”
“Kwaikwayonki take yi Mama.”
Muna shiga ciki abinda Habiba ta fara faxi kenan.
“Kwaikwayo kamar yaya?” tayi tambaya don buqatar qarin bayani, Habiba ta samu damar da ta tsaya rattaba bayani sosai da sosai na abinda ta tarar ina yi.
“Maman take yi wa wannan iya shegen?” Babana ne ya qara yin wannan tambayar, na xan kalle shi kaxan can cikin zuciyata na ce tanfar dai yau ba a wurin Innata yake ba, kullum nan ne wurin zamanshi ko da kuwa girkin na wanene amma ita Innata ko girkinta ne, to sai ya faki ido yake shiga wurinta in dai ba qararta aka kai mishi ba zai je yayi mata hukunci nan ne zaka ga ya shiga kai tsaye.
Babu ruwan shi da wa ke da haqqi saboda Mama bata yardar mishi baiwa mai haqqi haqqin shi ba.
Abubuwan da Habiba ta kwatanta da suka bayyanawa Babana cewar maganar Mama da tafiyarta na tsaya ina kwaikwaya, ya baiwa Babana takaici mai yawa, zuba min ido yayi yana kallona, cikin takaici da baqin rai mai yawa, irin kallon da naga ya yi min xin ya sanya ni nima na waiwaya baya don ganin waxanda suke tsaye.
Ado ne da Habiba waxanda su dukan su biyun ana cewa za’a kama ni za su yi sanadin da za a yi hakan.
“To ba dole tayi ta kwaikwayona ba, Habiba ai samu tayi duk abinda take yi ai ta sani gata gareta mai yawa a gidan, ga ta kuma ‘yar lelen Baba.” Ta qarasa maganar cikin wani yanayi da ita kaxai tasan abin da take nufi da hakan.
Babana ya ce, “Ba fa na son kina yi min irin wannan maganar a gaban yara, ni na ce miki ina da wata ‘yar lele?” Mama ta ce, “Uhun, Alhaji kenan, bari dai in ja bakina kawai in yi shiru tunda ba ni da ikon yin magana, sai ka hayayyaqo min a gaban yara tunda ni ce marainiyar yaronka.
Amma in ban da haka iya shegen da wannan yarinyar nan take yi a gidan nan in da wani ne wanda ba a tsoron uwarshi da danginsu ai da bai kwashe qalau ba. Sai dai nima ba ina ganin laifinka ba ne kan hakan da kake yi, da azo ana tuhumarmu kan abin da bai taka kara ya karya ba, ai gara muyi ta haquri da ita.”
Da irin waxannan kalaman kullum Mama ke tunzura Babana tasa shi yayi abinda take so, yayi min hukunci irin na azabtarwa, saboda babu abinda ta tsana a rayuwarta irin ta ganni ina zaune lafiya ko da kuwa ba wani walawa nake yi ba.
Shi kuma Babana ya kasa tunawa kanshi cewar su dangin Inna basu tava zuwa sun same shi kan wani abin da shi ko Mama ko wani can daban ya yi min ba, duk kuwa da sun saba ganina da tabon duka iri-iri a jikina, su kullum maganarsu kan tsaya ne kan abin da ya shafi ‘yarsu.
Sai ya yi ta biyewa Mama yana gana min azaba, ko da yake dai nakan gwammace nashi hukuncin komai tsananin shi akan na Mama, tunda ita bayan duka shaqe ni take yi ta tattara ni wuri xaya ta hau kaina ta zauna, wai sai na ji nauyinta, ita xin kuma ba qaramin nauyi ke gare ta ba, don kuwa jibgegiyar gaske ce.
Miqewan da naga Babana yayi, ya sanya ni juyawa da gudu da iyakacin qarfina, don nayi zaton kama ni zai yi, wajen juyawan nawa na banke Habiba dake bayana, shi kuwa Ado na kwantara mishi kwanon dake riqe a hannuna, man gyaxan dake ciki kuma ya kware mishi a fuska da jiki gaba xaya.
Mama ta kama salati tana faxin, “Wai ga wani abin al’ajabi, wai ga abin mamaki ni majadan naga abinda ya ishe ni yake kuma nema yafi qarfina.”
“Kamo min ita Ado, kamo ta maza in baka bulala ka hukuntata, ja’ira kawai mara kunya.” Babana ne mai wannan maganar, yayin da ita kuma Mama take faxin.
“Wannan shi ne wani zance kai baka hukunta al’amarin gidanka ba sai Ado? Kaja mishi kawai qarin baqin jini itama ba so suke su buxe ido su gan shi ba a cikin gidan nan.”
Babana ya biyo ni tsakar gida inda nake tsaye ina ta faman vari, ina kuma kuka saboda na riga na tsorata da abinda zai same ni. Innata kuwa tana sunkuye tana wankin kayan ‘ya’yanta bata xaga ido ta kalle ni ba, balle ta ce “Me ke faruwa? Amma sai Babana ya shiga cewa shaqiyancin banza shaqiyancin wofi, mu nan gidan ba a kawo mana shaqiyanci dama kin yi maza kin bari don masu koya miki ba riba zasu ci ba, wahala kawai zasu yi ta ja miki.”
Yana gama faxin hakan ya shiga shirva min bulalar dake riqe a hannunshi, wacce yasa Suwaiba ta miqo mishi, na shiga ihu ina buga tsalle ina faxuwa a qasa don tsananin gigicewa.
Sai da Mama ta tabbatar na jigata ne ta fito daga falonta tana faxin “Ni fa bana son irin wannan ja min maganar da ka ke yi, kai kasan halin ja’irar yarinyar nan sarai ba a tava ta ba ma ihu take yi don dai ta qulla wa mutane sharri a unguwa ace to ga ta can ana azabtar da ita, tunda tasan muna tsakanin ‘yan sa ido to balle kuma an tava ta.”
Yana huci yake faxin “To ina ruwana da maganarsu, za su hana ni yin hukunci a gidana ne?” Mama tasa hannu ta karve bulalar daga gare shi tana faxin, “Ai kuwa dai magana abin a guje ta ne tunda ko kai xin ma kana dai faxa ne kawai, in ban da kana gudun maganar ai wani iya shegen da ba ayi shi a gabanka kana kallo ba.
Bata kuxin mangyaxan ni ta sayo min tunda wancan xin a gabanka ta kifar dashi, kana kallo.”
“Nawa ne kuxin?” Ya tambaya tare da qoqarin fiddo da wasu kuxin daga aljihun shi, ta ce “Kwalba biyu ne.” daga ni har shi barin abinda muke yi muka yi muka kalli Mama, ni na bar kuka na zuba mata ido shi kuma ya tsaida hannu a aljihunshi ya bar zaro kuxin.
“Kwalba biyu ne?” ya buqaci sani, tayi maza ta xaure fuska ta ce, “To zanyi mata qarya ne ba gata ba? Tambaye ta mana. Ni kam ko da Babana bai yi kuzarin tambayata ba qiris ya rage in buxe bakina in qaryata Mama, in ce gongoni ne biyu ba kwalba ba.
Sai kuma naga yin hakan ba zai amfane ni da komai ba, tunda ba zai hana Babana biyan kuxin kwalba biyun ba, ni kuma sai in sake shiga cikin wani matsanancin hali, don cewa Mama zata yi na qaryatata a gabanshi yana kallo, ko ma ace Inna ta ce ta sani yin hakan tunda ni kullum laifina na Inna ne, ita ke sa ni komai in dai na sharri ne ko kuma danginta.
“Ke da masu koya miki iya shege ba zan yi maganin ku, zan sa qafar wando xaya daku.” Abinda ya ci gaba da gaya min kenan.
Bayan ya miqa wa Mama kuxin ita kuwa ta karve su ta juya tayi tafiyarta, bata sake aiken nawa ba wai kar in je in sake kifar mata, can cikin zuciyata kuwa nasan ba sake saye zata yi ba.
A kullum irin kalaman da Babana kan furta kenan an koya min halin tsiya an yi min huxubar banza, an cusa min xabi’ar da ba za ta amfane ni ba, zai yi maganin mu alhalin shi xin bai tava kama wani ko jin wani yana yi min xaya daga cikin waxannan abubuwan da yake faxa ba.
Illa iyaka dai abinda ita Mama take gaya mishi kenan. Kan hakan ne ma ni ko magana baya yi in dai wadda ta shafi muhimmin abu ne a gabana, sai ta nuna mishi ni ta hanyar yin zunxe ta ce mishi dama dai kayi shiru tunda ga ‘yan baka nan a kusa.
Amma ta yarda yayi a gaban su Habiba, waxanda a wajenta wasa zaka ji suna faxin Babanmu ya ce, kaza ya ce kaza da maganar zata fito kuma ya zamo ba wacce ake son ji ba ne sai Maman ta ce mishi ai ta hana shi sakin bakin shi a gabana ya qi ne yasa ta zuba mishi ido.
Gidanmu gida ne da ake da qarancin ‘ya’ya maza, ko a xakin Mama mai gadaran uwargidanci da ‘ya’ya maza guda uku ne mazan, mata kuma biyar.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login