Showing 18001 words to 21000 words out of 32414 words

Chapter 7 - MIJIN TA CE BOOK 1

20 Aug 2024

4899

Mama ta ce haka ne, haka ne abin yake, tayi sallama ta fita.
A waxannan kwanakin yake kawai Mama take yi amma kana kallon idonta kusan sai da ta gama kuka a xaki sannan ta fito.
Kwana uku da haihuwar, Baba Yahaya ya rako Alhaji Mai kuxi suka zo gidanmu ganin jariri, rannan a falon Babana suka sauka ni Hajiya Kubra ta baiwa yaron naje na kai musu sai fara’a yake yi yana qarawa shi kuwa Babana yana gefe shima da alamun farin ciki a tare dashi.
Ya kalle ni yana murmushi, kin yi qani Aisha, sai dai shima baqi ne irinki, Alhaji Yahaya yayi dariya ya ce, to ai gaskiyarsu suma waxanda suka yi farin ai karanbani ne ya kai su.
Shi kam Alhaji Mai kuxi wasa da ‘ya’yan Inna yake yi tanfar jikokinshi don ya ce Inna ‘yarki ce, Inna ta shigo ta durqusa ta gaishe su, ya tambaye ta ina ‘yar uwar taki take?
Babana ya ce mata, biya ki gaya mata ga Alhaji yazo. Mama tazo itama suka gaisa da ta juya zata tafi sai ya ciro kuxi masu yawa ya bani ya ce in kai mata a sai mana alewa, na ce to. Naje na kai mata su. Na dawo na karvi jaririn na kai xakinmu.
Ko da Babana bai yi wa Inna zannuwan goyo ba, Mama ta hana ta ce duk sanda Inna ta haihu yayi mata zanin goyo, to hatta kayan jariran da yayi sai yayi mata itama don har da gangan Inna ke irin haihuwar da take yi saboda tasan in ta haihun zai kwashe kuxin abincin mutane yayi ta kashe mata.
To duk da hakan yayi hidima, goro murza-murza a wadace gami da butter mint da dabino mai yawa, ga ragunan suna tima-tima masu kama da ‘yan Maruqa. Ga abincin suna iri-iri kuma mai daxi, ‘yan uwan Innan ne suka xauke cefanen da aka kawon suka yi don sun saba zuwa sunan Inna su kai yamma Mama bata ba su abincin suna ba a dalilin wai ba a gama ba, don haka wannan karon ba su ma saurare ta ba.
Wunin rannar Inna da ‘yan uwanta da na Babana da abokan arziki suna hidimar suna, ita kuwa Mama bata da aiki sai baiwa mutane labarin yanda aka yi aka haifi yaron tana faxin wai shege ne.
Tunda satan girki aka yi aka same shi, tun tana bada labarin ga masu sauraronta har taje tana baiwa masu yi mata dariya, uwargidan Baba Yahaya Hajiya Haran wacce ta yi wa sunan hidima mai yawa a dalilin wai mijinsu aka yi wa takwara.
Kallon Mama tayi a sakarce ta ce mata, dama dai kin bar bada labarin nan don kuwa kanki ki ke tona wa asiri, ina ruwan wannan jariri da abinda aka yi da zai zama shege?
Ko dama a waje aka yi cikin nashi balle a aure? Sannan gashi nan tubarkalla tanfar amanshi Alhaji Surajo yayi. Nan da nan ta soma sake mata mata maganganu don dama ita da Mama ta ciki na ciki ne kawai.
Kullum Maman takan ba da labarin Hajiya Haran a matsayin maciyar amana, wai duk da irin amincin da ke tsakaninsu ita ce ta jagoranci komai da aka yi na neman auren Innata.
Ita kuwa Haran ta ce aminci ba zai hana ta bin umarnin mijinta ba ta kuma yi duk abinda zata yi don ta nunawa Mama tana tare da ita don su ci gaba ita Maman ce ta qi.
Hajiya Haran ta kalle ta tayi murmushi, ta ce “Mama kenan, to ai ba ni na kar wannan zomon ba ko ratayen shi kuma ba a bani ba balle ya zama sanadin faxa a tsakaninmu, tunda ke kin saba.
Ba’a hidima a gidanki a rabu da ke lafiya saboda zubar da girma, ta ci gaba kuma da sabgoginta tana kuma zaune a falon na Mama bata fita ba sai in wani abu ya kama taje tayi ta dawo.
Can a xakin Inna kuwa wata gwanar ajiyar ce tazo da kaset xin da Muhammadu Shatan dangi yayi wa Babana da Inna waqa, lokacin aurensu. Don haka tuni matasa-matasan cikinsu suka miqe sai faman taka rawa suke yi.
Da yamma rannan kowa ya zo yayi wa Inna salamma zai tafi ‘yan uwanta za su kawo kyauta su bashi na qunshin goro da minti da dabino gami da cincin, babu ruwansu da cewar kai wanene?
Da daddare rannan a xakinmu bayan watsewar Jama’a babu masaka tsinke saboda tarin kaya na sutura da na amfani, atamfa-atamfa turmi ashirin Inna ta samu mafi yawancinsu masu kyau.
Don ko daga gidan Baba Yahaya wanda sunanshi aka sanyawa yaron manyan super biyu aka kawo mata da rigunan yaro guda bakwai gami da sauran tarkace, ga kuma wasu lesuna da shadda da material guda goma can gefe waxanda Alhaji Mai kuxi ya yi mata.
Rannan yanda Hajiya Kubra ta wuni cikin hidimar kai-kawon ganin abin da ake yi haka har cikin daren bata huta ba, qoqari take yi wai taga ta samar wa komai muhallin da ya dace dashi.
Ni kam sai murna nake yi bini-bini sai in matsa jikin Innata in xauki yaro ko in zuba mishi ido ina kallon shi, ji nake tanfar kar Hajiya Kubra ta tafi, musamman da yake tunda ta zo babu wanda ya zungure ni balle ya doke ni. Ko wannan fitinanniyar aikar ma an rage yi min ita.
Washegarin suna da sassafe su Anti Ramla da Anti Sajida matan Baba da Abba surukayen Hajiya Kubra suka sake dawowa, kamar yanda tayi musu umarni suka zo suka qarasa gyara komai suka kuma soye ragunan suna ta kasabta komai ta baiwa kowa nashi gaba xaya makwabta da dangi har qauyen su Babanmu Giyaxe sai da ta bayar ta ce a kaiwa Mahaifiyarshi tare da goro da minti da kuma turamen atamfofi biyu.
Mama ma aka bata nata tare da turmin super guda xaya amma wai sai ta dawo da zanin ta ce a bar wa maijego kawai ta xaura.
Da yamma rannan Hajiya Kubra ta koma gida bayan tafiyar surukayen ta kafin ta tafi kuwa sai da na ji ta tana jaddawa Inna cewar lalle ne ta kula da kanta da kuma ‘ya’yanta ta ce, to.
Washegari da sassafe tun Innan bata sauko daga kan gadonta ba Mama ta aiko wai ta fito ta baiwa jama’a abin karyawa. Inna ta leqo tsakar gida ta ce mata ina kwana?
Da kyar ta buxe baki ta amsa sai da tayi ta sake, ta kalle ta cikin natsuwa ta ce “Mama ko za a ba su na yanzu ni in yi na anjima tunda ai na gama daga abincin dare ne muke canjin girkin.
Ta ce, yau an baki daga na safe in kuma ba za ki yi ba ne sai ki faxa.” Ta ce, to, ta koma xakinta ta bani umarnin kintsa mata shi da baiwa qannena ruwan wanka ita kuma ta sanya suwaita da hijabi ta fita.
Inna tana kicin tana aikin abin karyawa ni ina xaki ina jin Mama tana cewa tunda ki ka san zuwan gun miji a kowane lokaci ai ya kamata ki san hidimar gidan shi ma a haka nan kuma gidana ne yanda naga dama haka zan dama a kuma sha dole gidana ne ni da mijina da ‘ya’ya ki ka zo ki ka same mu ni da mijnin da ‘ya’yana.
Kin ga zai yiwu ki ce za ki kawo min wani fi’ili? Ai sai dai kawai in kin ga ba za ki iya ba kiyi gaba kamar yanda saura suka yi.
Inna ta dawo xakinta tana murmushi ta bani kuxi ta ce in sayo biredi da madara. Nayi maza naje na kawo mata, nan da nan ta gama abinda zata yi ta rabawa jama’a, ta bani na Mama na kai mata.
Na dawo kenan Habiba ta biyo bayan ta zo ta tsaya qerere akan Inna da ke yiwa xanta wanka, ta ce mata in ji Mama wai wannan abin karyawar da ki ka basu kunu da qosai za ki rinqa yi, ta ce mata “to”.
Rainin da Habiba ta yi wa Inna yana ci min tuwo a qwarya, sai dai babu yanda zan yi, tsoronta nake ji saboda kusan kullum sai tayi mini duka.
Rannan ban san laifin da nayi ba sai kawai na ji Mama ta qwala min kira, da sauri na amsa naje in ji kiran sai kawai ta ce min in shiga can cikin xakinta.
Naja na tsaya ina faxin “Mama me nayi? Mama kiyi haquri.” Ta ce, “Ba zan yi ba ta waiwaya ta kalli Ado dake gefenta ta ce mishi shi kenan je ka sai ka dawo. Ya tashi ya tafi ba tare da ya ce mata uffan ba.
Ta tasa ta biyo ni cikin xakin tana faxin, ai dama tara ki nake yi ina kallon iya shegen da kike yi sarai kin xauka zasu xauwama min a cikin gidanne?
Mama ta soma kama hannayena tana naxewa ta kwantar dani a qasa ta haxa da qafafuwana ta danne ta hau kaina ta zauna da iyakacin qarfinta, ta shiga mintsinin cinyoyina ina ihu ina faxin waiyo Mama, waiyo numfashina don tasan ta toshe min kafar hanci guda xaya.
Numfashin da nake samu baya isa ta nishi yafi damuna ba tsananin nauyinta da azabar mintsinin da take yi min ba, ya tsaya nunfashin ki mutu don uwarki sai me ba na rage mugin irin da ake tara min a gida ba?
Azaba ta ishe ni na kuma gane da gaske Mama bata damu ba don numfashin nawa ya tsaya ba ban san yanda aka yi ba sai kawai jina nayi na kama mazaunanta dake daidai bakina da haqorana da iyakacin qarfina.
Ihun da Mama ta qurma mai tsananin qarfi shi ne wataqila yayi matuqar firgita ni, har ban san yanda aka yi ba sai kawai na ganni tsaye a tsakar gida ina huci cikin tsananin firgita don tsoro, ganewan da nayi na kuvuta ba kuma a girma da arziki na kuvutan ba, wani mummunan abin nima nayi mata ya sani kartawa da gudu na nufi gidan Mallam mai babban allo.
Ina tsugune gaban Mallam sai zare ido nake yi bayan na gama mayar musu da bayani, Hajiya ‘yardubu ta ce kai wannan zalunci da rashin tausayi da yawa yake, amma babu komai wata rana ba za ta yi ba.”
Mallam ya xan yi murmushi ya ce, “Itama yarinyar ai da nata laifin, haka kawai za a kama ta da duka ne bata yi komai ba? Ai ba ita kaxai ba ce.”
Hajiya ‘yar dubu tayi maza ta ce, uh’uh Mallam, babu wanda bai san lamarin gidan nan ba, kai dai ayi sha’ani kawai.” Mallam ya ce, “To Allah ya kyauta, ta ce amin.
Abinci kawai Mallam ya bari naci yasa Hajiya ‘Yar dubu ta taso ni a gaba ta dawo dani gidanmu, gabana sai faxuwa yake yi, yayin da ta tasa ni muka shiga wurin Mama.
Maman tana kwance tana ganin Hajiya ta miqe ta zauna tana yi mata sannu da zuwa, suka gaisa ni kuma ina durqushe. ‘Yarki ce tazo mana gida da wani bayani na rashin hankali, shi ne na ce to bari dai in dawo miki da ita in ji gaskiyar lamarin, tunda dai ai banza bata kai zomo kasuwa, sannan sha’anin nan na ‘ya’yan yau maganarsu ba abin kamawa ba ne, in dai ba zahiri aka gani ba.”
Mama tayi ta bayani na kame-kame har tana gayawa Hajiya wai na cije ta a mazaunai, ta ce a’a shi ne abin mamaki cizo a mazauni kuma? Tayi maza ta bar maganar ta shiga tambayarta Mallam da sauran mutanen gida, wataqila ta gane abinda bayanin nata yake nufi.
Na shiga wani hali na tsoron kar Mama ta ce zata kama ni akan cizon da nayi mata, bata yi hakan ba wataqila don maganar ta yayatu da yawa har gidan Baba Yahaya an ji, ya kuma yi wa Babana magana kan irin dukan da ake yawan yi min alhalin na riga na fara girma.
To sai dai Habiba duk inda muka gamu sai ta buge min baki wai ladan cizon Mama da nayi.
Rannan na dawo daga gidan ‘yar Inna Balki da aka gama bikinta wacce kuma take matuqar sona Ruwaila.
Ina rungume da jakar ledar da ta bani kayanta kala biyu masu kyau da kayan kwalliya dangin su janbaki da hoda da gazal da man shafawa, gami da turare na zuba a ciki ina ta murna nazo zan wuce Habiba dake tsaye da qawarta a waje sai kawai tayi maza ta tare ni ta kaiwa bakina duka.
Na ce ban yafe ba, ta sake kai mishi wani dukan na sake cewa ban yafe ba, zata sake sai qawar tata ta ce mata “Haba Habiba, wane irin cin zali ne wannan? Don kawai kin ga tana yi miki shiru-shiru?”
Da sauri Habiba ta ce, kar tayi shiru ta rama mana taga irin yanda zan yi fici-fici da ita, kwanannan ma zamu yi maganinku don Mama tasa Babanmu yayi aure har ma ta samo mishi budurwar har an kai sadaki zaku sani.
Sum-sum na wuce na shiga gida, gabana sai faxuwa yake yi jikina kuma yayi matuqar yin sanyi don kuwa ko ban san komai ba ban kuma isa komai ba rayuwar gidanmu ta riga ta karantar dani cewar kishiyar uwa ba qaramar aba ba ce, sannan ganin Habiba tana murna ya isa ya fahimtar dani cewar don mahaifiya ta za’ayi auren.
Duk da kashedin da Inna tayi min na jin magana in zo in gaya mata da na shiga xakinta kasa yin shiru nayi, durqusawa nayi gabanta da gwiwoyina duka biyu na ce mata Inna Habiba ta gaya min wata magana ki bar ni in gaya miki.
Ta ce, to gaya min, na kwashe bayanin duka nayi mata ta xan yi shiru zuwa na wani lokaci kafin ta ce min babu komai kar ki damu kanki kin ji ko? Na ce mata to, ina ce kina yin addu’o’in da na koya miki?
Na ce mata eh, ta ce to ai shi kenan. Da daddare Babana ya shigo wurinta saboda ranar ma girkinta ne, bata wani canza mishi ba, wai don ta ji labarin yana neman aure ina jin shi yana tambayarta wai ni menene amfanin gadon jariran can da aka sai miki ne?
Yasa hannu ya xauki yaron da muke kira Baba qarami ya maida shi ciki ya kwantar, ban san yanda suka yi da Inna ba iyaka dai da safe bayan mun kammala komai muna zaune a xaki ni da ita sai ta ce min.
“Da gaske ne Babanku zai yi aure har ma wai bikin ya matso, Mama ce ta hana shi gaya min wai don kar in hana auren ni da Babana.” Na zubawa Inna ido ina kallonta, ban ma san abinda zan ce mata ba, sai ta sake ce min babu komai kar ki wani damu ranki na ce mata to.
Kwana biyu da yin haka na ji Babana yana cewa Innata ga wannan kiyi haquri, ki sayi wani abu ko bna ita Mama ta ce bata buqatar komai nawa, ita auren kawai da zan yi ya ishe ta farin ciki.”
Inna ta ce, haka ne tayi shiru, to amma dai ai kin san babu wata mata da…” Inna tayi maza ta ce, mishi uh’uh mu bar wannan zancen kawai, na gode, Allah ya qara buxi, ya ce to amin ya fita. Bayan fitar tashi ne ta aike ni in kaiwa Hajiya Kubra kuxin daga nan kuma in ce mata in ta samu lokaci ta tamb ayi izini tazo tana son ganinta.
Zaman lafiya sosai aka shiga yi tsakanin Inna da Babana, maimakon tayi mishi borin jin zafin auren da zai yi sai kawai tayi kamar bata ji ba, tunda Mama bata maganar ba ta kuma taso ta ji, shima Baba a wannan lokacin hidima sosai ya yi wa Innar saboda jin daxin haqurin da tayi.
Tunda bai saba ganin hakan ba wurin uwargidan da za’ayi wa amarya, don haka sai yayi ta qoqarin ya nuna mata cewar bata da matsala a auren nashi, ko da yake dai ni nasan can cikin zuciyar Inna akwai damuwa ta dai haqura ne kawai ta danne don kar ta tonawa kanta asiri, tunda tasan bata da ikon hana auren.
Sati biyu ne kawai bayan wannan lokacin sai muka wayi gari ana yin buki a gidanmu, Mama sai kawai da kawowa take yi cikin murna da farin cikin Babana ya sake auren budurwa.
Sai murmushi take yi tana faxin wannan ai ni ba kishiya ba ce a wurina ya ce, nima zan yi mata irin adalcin da uwar Fatima take cewa tana yiwa kishiyoyinta tunda ita ba za ta yi min irin cin zarafin da Fatima tayi min ba tunda iyayenta ba su yi mata irin tarbiyar da na Fatima suka yi mata ba.
An sha biki a gidanmu ba kaxan ba, Inna dai bata wani yi gayyata ba a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login